← Book details Tuna Baya Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 50 OF 51

Sashe 50

Tuna Baya Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

Yace'yauwa 'yar matata shiyasa nakeso kauna da begenki sbd bakya yimin MUSU,bakya yi mun KARYA kuma bakya HA'INTA ta
120...

Nace 'banason in takura anti mubina ne,tay missing mijinta 4 so long zama na zai zama tamkar takura ne agareta....

Ya katseni yace'zan kula da adalci in Allah Ya yarda karewama ke ki zauna a sassan kasa nida ita mu manne a sama mu sha amarcin mu ke kuma ki karata da karnin ki ke daya ko ba haka kike so ba?

Nay murmushin izgilanci nima,amma fa shaguben sa ya taba zucia ta na rama abunda yake mun in nayi mai gatse nace'ka jishi kaman gaske....

Muka tuntsire da daria.

Da wadannan hirarrakin muka fito (Boiend 745) muka fada jirgin dan kabo mai zuwa abuja.

Muna sauka daga matattakalar jirgi na sha mamakin dimbin al'ummar da suka zo taryenmu,'yan jaridu, manema labarai da kuma wakilan national television authority tare da tawagar Minister of Foreign Affairs sunzo taryen ogansu.

A gaba gaba na gane anti mubina, muhd bello, fati, abdulraheem, assha, taufiq, ibrahim, peter.

A gefe 'ya'yan bello ne mukhlas da taheer sun kara girma sosai.

Naji haushin rashin ganin jawad a cikinsu, sai nake kimanta girman da 'ya'yan bello a yanzun na tabbata zai fisu.

Ga yayyuna awal da sani jingine jikin motarsu da yayar assha mansina.

Ragowar duk ban gane su ba.

Anti mubina na sanye cikin rantsattsen leshi ruwan kasa wato kalar da oga ke so sai washe min hakora take wanda yafi kama da kuka.

Ta juya tasa hankici ta share wasu ambaliyar hawaye da majina da suka kawo mata ziyara cikin wayau da dabara ba tare da kowa ya gane ba.

Ita ko zubaidar jifanta take da tsadadden murmushinta sai hantar cikinta ta shiga rawa.

Ko farcen BLACK dinta a yau abun kallo ne,ga mata 'yan uwanta ma balle maza.

Bar ta kayan kawar da take daure da su hannu,kafa,wuya,gashi da kunne tamkar haifaffar Morocco.

Kalarta ko abu ne da zai saka a shakku,don bazaka ce baka ce ko fara ce ko wankan tarwada ba,kawai ita daban ce wato unique ko a cikin dimbin matan dake wurin.

Da ta doso su wani lallausan kamshi kurum ke dukan hancinan al'umma tamkar don ita kadai aka halitto wannan mayataccen turare.

Ita kam duk a yawon ta kasashen dunia,da sayen turarukanta har a birnin Paris,bata taba jin kwatankwacin irin wannan kamshin ba.

Ga wata irin cika ta halitta komi nata ya kai ya kawo, tamkar reshen bishiyar da iska ke kadawa sannu a hankali.

Da tayi murmushi hasken wasu fararen hakora kaman kankara ne suka dallare ta.

Ashe dai wannan itace real zubaidahhh da takejin labari?
[11/3, 8:38 AM] A A Dboy: *_POST BY GROUP OF HYPE HAUSA NOVELS BOOK WHATSAPP 08064400100_
[11/3, 8:41 AM] A A Dboy:
*TUNA BAYA*
~BOOK 2~
~THE END~
Tuna Baya2 120-127 End
121...

Lokaci daya wani tunani yazo mata duk wani shiri da tay na kuntatawa rayuwar zubaidah ta karfi da yaji,sai ya warware taji zubaidah ta burgeta ta kuma bata sha'awa.

Idan tace zata kawo fi'ili ko kishi akan wannan gagara gasar mace, lallai ita zata kwashi kashinta a hannu.

Ashe dai da talaka da mai kudi duka daya ne a wurin Allah sai ma ya daukaka talakan ya dankafar da mai kudin a sanda Yaso,Shi Allah bbu ruwan Shi kuma arziki nashi ne bbu inda baya yinsa.

Kamin kowa ya tadda zubaidah ta runtumo da gudu ta rungumeta tace my little sister kunzo lafiya?

Yallabai aka saki baki cikin mamakin abunda tayi wanda ko a kokon ran shi bai kawo hakan ba, to bashi kadai ba ni kaina nay mamaki.

Mu duka biyun muka doshi al'ummar mu masu aikin camera nayi masu video nayi, shashashun'yan jarida kuwa tambayoyi suke tayi mana 'yaya zaka kwatanta farincikin ka mai girma Minister a wannan rana?

Ganin cewa mubina dango tay nadamar abunda ta aikata tay murna da dawowar zubaidah?

Hajiya mubina yanzu kin yarda da kaddara kenan zaki zauna da 'YAR RAINON Ki,koko na yau ne kawai?

Shin zaki kwato dan ki ne koko kin hakura kin bar mata kin amince RAINO MA WANI ABUNE MAI MUHIMMANCI GA UWA TA TSAYA TA RAINI ABINTA?

Ko kallon su batayi ba,ya dawo gareni''Hajia zubaidah me zakice kan tonon sililin da dango tay miki a dunia cikin jaridun mu da kafafen yada labarai?

Anya zaku iya yafewa juna?

Muka dubi juna nida anti mubina muka yi murmushi.

Wannan kadai ya ishe su amsar su na cewa nida ita duka bbu mai kuma TUNA BAYA.

Illa rayuwar da zamu gina a gaba.

Dani da ita muka fada motar gidan kwamishina ibraheem hardo, shi kuwa yallabai yabi tawagar ofishin sa ne shi da Bello haka yayyuna da sauran mazan har su mukhlas duk sunbi babanninsu.

A motar daga ni har anti ba wanda yace da kowa komi, hakannan ba wanda ya kalli kwayar idon dan uwansa.

Haka kawai naji na samu kaina da kunyar anti mubina amma ita sai na lura jikinta a sanyaye yake tayi ladaf tay lakwas ta sakko ta saduda,ta kuma yi dammarar zana na fisabilillahi.

Gidanmu ya sha gyara sai ma'aikata ke kai kawo suna entertaining bakinmu,tun safe har dare muna ta harkar jama'a bamu zauna ba.

Sai karfe goma sha dayan dare kowa ya watse.

Sai masu gadin.

Anti mubina ke ta kai kawo tana shirya local dishes bisa dinning abunda ya bamu mamaki daga ni har yallabai,a raina nace lallai dunia mai juyi.

Ban taba ganin anty ta shiga kicin da zummar dafa koda ruwan zafi ba tsayin shekaru 8 da nay tare da ita,dunia mkrnt ta ishi dan adam riga da wando,babbar riga har da hula (mata mu mike don Allah mu gyara rayuwar aurenmu lokaci bai kure ba.

Son jiki da girman kai bbu inda zai kai mu a zuciyar mazajen mu saidai ya dankafar da mu inji takori).

Ta kammala jera komi ta jefe mu da cokalin dake hannunta tace kowa yaci girki na yau zai bani lambar dana cancanta.

Yallabai ya dago daga wayarshi da yake latsawa ya galla mata harara yace 'makarantar girkin kika shiga ko yaya da za'a baki makin?

Na lura bata ji dadin gwasalen da yay mata ba ni kaina banji dadin ba nace'rabu dashi antynmu dole ne ma ya bada makin irin wannan gara haka?

Ta sadda kai tana murza 'yan yatsunta kawai shi da kansa ya lura bai kyauta ba.

Ya kira sunanta ta dago ya sakar mata murmushi yace'to me aka shirya mana?

Maman jawad ta hakika?

Anan ne tay murmushi tabbacin ya faranta mata tace 'ni da ke fried rice nay mana sai stuff marrow da stuff cabbage,shi kuwa dama local dishes dinsa ne gaya nan' nace'kin kyauta antin mu ya harareni a lokacin da ya kai lomar farko yace antinki dai nikam bandani don haka ki daina jimilla.

Tay serving kowannenmu da abunda yake so ba tare data kula da zancen sa ba don ta lura neman baki yake da ita,ta tura min plate dina itako taja gongonin heinz beans ta tsoma cokali tana sha banyi mamaki ba don Tom ya taba gaya mun wai ita bata cin abunda ya hau wuta ba.

Bayan mun kammala cin abincin yallabai ya kira mu main falonshi,dukkaninmu yay mana nasihohi masu ratsa zuciya,ya nemi hadin kanmu kan zaman lapia na har abada a gidan sa don dukkannin mu kowacce da muhimmanci ta gareshi.

Ya kare da cewa'banajin zubaidah sai ke mubina don Allah ki canza halin ki, ni kuma In Sha Allah zan yi kokari in kasance mai adalci a tsakanin ku.
122...

To bayan watanni biyu ne na haife ki MAHASI, bayan matsananciyar nakuda, sunanki na usli MAIMUNATU kasancewar sunan fulani ne muke kiran ki mahasi.

Rayuwa ta cigaba da gara mana yadda bamu zata ba da budi da cgb ta kowanne fanni.

Anti mubina ta shayar da mu mamaki don daga ranar har inda yau ke motsi, bata taba kawo wani mugun hali ba.

Mun dinke mun zama daya kamar Ya da kanwa don baka sani ba ko shigo gidanmu sai ka za ci ba kishiyoyi bane,Ya da kanwar ta ne.

Duk wani akidun ta na banza da shirmenta na da ta rabu da shi tana koyi da komi daga gareni,hakana aikin ma ta aje shi ta daina sai kasuwanci.

Saidai har gobe ita kanta tana da masaniyar cewa ita da ZUBAIDAH ba daya bane a zuciyar TAHEER.

Ranar sunanki ne fatima ta gane cewa nice ATINEN BELLO.

Data bude baki a ranar tafi minti ashirin bata rufe ba sabd mamaki da ta'ajjibi.

Yadda akayi ta sani ma kuwa shine tana rike da ke a hannun ta tana fadin kamanninki da yallabai masu ban mamaki sai yay murmushi yace' Yar atinen-bello kenan ta koma 'yar fatin- bello...

Bello yay murmushi a kunyace yana kawas da kai daga gareshi yace 'yallabai ai ba abun mamaki bane,tunda kuwa wani baya haihuwar dan wani kamar yadda wani baya taba auren matar wani.

Wannan rubutaccen ne don haka ka daina TUNA BAYA..(past),just d present!

Nidai fatana ko bayan raina inaiwa mukhlas rikon MAHASI.

Hawaye suka zubo min na tausayin bello nay saurin daukewa kamin yallabai ya gani.

Na tabbata Bello Waziri ba karamin kauna yake mun ba irin kaunar nan wadda har a nade dunia baza'a aina ba saidai alhmdlh yay dace da macen kwarai mai kaunar shi fiye da komi a rayuwarta.

Kuma ko da ta ji nice atinen,ba abunda ya canza na amincin dake tsakanin mu.
123....

Hakika kauna ta gaskia wata aba ce da Allah Subhana ke dasa mana a zuci wadda kuma take a tsakanin abubuwa guda 2,samu ko rashi.

Na sani na so Bello nd i still luv him(astagfirullah inji atine) shima yaso ni ba kadan ba to amma soyayyah ba itace aure ba.

Allah bai kaddari akwai aure a tsakaninmu ba.

Ya rigaya ya kaddaro cewa kowanne abokin rayuwarsa dabam ne dana dan uwansa wannan ne kawai abunda na yarda da shi.

A tun ranar da aka haifeki a asibiti da mukhlas ya daukeki budar bakinsa sai cewa yay 'momyn jawad inasonta kyakkyawa ce zaki aura min ita?

Nay murmushi nace'insha Allah ko bata son ka ka aureta ka gama muddin ina raye.

Yallabai yace'balle ma me zai sa tace bata son shi?

Alhalin ya fita kyau?
Chapter 50 · 0% Book details