← Book details Tuna Baya Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 28 OF 51

Sashe 28

Tuna Baya Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

Daya kammala digirinshi na farkone mubina tazo hutu daga portugal. ganinta na farko da taheer ta rikicewa babanta itafa taga miji mr dango ya tausheta da cewa ta dakata harsai sunmaida taheer wani tukunna, yadda bazai iya qin amsa bukatar suba donshi yasan taheer Kamar yunwar cikinsa.

Mace bata gabanshi a yanzu macen ma irin mubina kwata_kwat
(life_style) nasu badaya bane.

Ba mamaki inyayi mishi maganar ta alokacin ya tattara yakoma hostel. hakan akayi mr dango yadauki nauyin karatun yahai da taheer a sussec, university of washington seatle.bayan kammala digirinshi na biyu mr dango ya tura mubina washinton jami'ar da suke karatun M.sc dinta akan qididdiga(Accounting) yakuma danqawa taheer amanarta.
5.....
yaya kuwa xai yi wasa da amanar ubangidanshi?

Ya shiga kula da mubina bil haqqi tsakanin shi da Allah,tare dakokarin ganin ya rabata harka da kowanne namiji.

Yana nuna mata illar hakan ga mutuncin ta na ya mace musulma mai daraja.tace ai kome nakeyi inayi ne sabidashi,don ni?akan me to?

Tace akan ina son ka da auren da ka ke cewa nayi, alokacin dana lura kai baka masan ina yi ba".tun daga lokacin tashiga nuna mai soyayyah afili daya ga abin na gaskene sai yayi ta lallabata data bari sukare karatun xai aureta. dawowarsu nigeria yayi daidai da mutuwar autinsu data rike su mubina, dama mahaifiyarsu tuni ta gudu tabar babansu tun suna kanana sabida dukan da yake mata inyashawo giyarshi ko allurar sojin ta motsa.

Wannane yasa mr. dango tausayawa su mubina da basu tarbiyya ta kowanne yayi abin da zabawa rayuwarshi.

Mimi mai bin mubina a tanzania take karatun tarihi shi kuma yahai yakoma beijing din china inda yasamu aiki da kamfanin(bill gate)na sana'anta na'ura mai kwakwalwa.ashekarar mr.dango ya samar mai aiki a'foreign affairs' wanda sadaukar da kai da mai hankalinshi ya bashi matsayi daban-daban acikin ta har kawo yau,wato bashi baban (minister) na foreign affairs gabadaya da shugaban kasa yayi,badon shekarunsa sun kaiba illa don juriya da jajircewa bisa aiki da gaskiya irin nasa.
6.....

Ya gina kankareren gida abuja amma dango yace bai dace yashigaba har sai yayi aure.

Acan karaye maimartaba ya bude mai wuta, fulani amsa gaisuwar shi ta daina, sunce yaxo gayarinya ansamar mai yar hakimin kiru ya shashantar da maganar har yasa sun ji kunya,toh wannane ya tayar mai da hankali har ya doshi mr.dango da maganar a matsayin neman shawara,don shi a duniya bai gayarinyar da ya tabaji wai yana soba,
Dagana turai harnamu yakanga dukkan matan yanzu matsayin marasa kamun kai yan (selling-face) tunda duk yaga yadda suke tafiyar da rayuwarsu,suke kuma yimashi baro-baro daga na turai harna africa a ganinshi babu korai balle ya kwankwasa ya zabi na kwarai.yanason gina rayuwar iyalinshi ne da mace tagari.kamilalliyar mace da bata dauki dunia matsayin gidan hutu da jindadi kawaiba,a'a wadda zata tsaya tsayin daka waje daya tayi amfani da lafiarta, karfinta, kuzarinta, iliminta, da addininta wurin tarbiyyanta da kula da y'ay'anta,ba gafalalla wadda duniar kadai tasa agaba(tamkar su mubina kenan) budan bakin mr dango sai cewa yayi ai shi tuni ya samar mai mata,qanwarshi mubina, don baiso yayi nisa dashi sabida qaunar da yake masa.

Baya iya wulaqanka wannan mutun bare har yabada mishi qasa a ido yace baya son jininsa idan yayi la'akari da yadda yazamo silar dukkannin'achievements' dinshi a rayuwa.
7....,
Hakanan kuma su mubina an hada da kai sunan taheer zangon kataf, donhaka yazamo bayada katabus sai abinda dango yace har akayi auren. hakika bai son mubina ya aureta,sai dai yana son babanta,yana ganin mutuncin balarabe dango,har yau har gobe yana ganinshi a matsayin ubangidansa, duk da cewa a yanzun zai iya sayen aikinshi kansa dangon dake aiki da 'presidency'. sai dai qin mubina yafara gushewa daga ranar da ta dauki cikin gudan jininsa abin sonsa (MUHAMMAD JAWAD).

Duk da cewa bayan auren ta komawa munanan dabi'unta,kamarbin kyawawan maza da qarya da homa tun bayan farawar aikinta a bankin omega.haka mubina sai bayan aurenta da taheer ta shiga nadamar auren, da wanda take ganin qidahumi, bai san takan rayuwa ba, bai kuma san koshi wanene ba, yana daidai da kansa da barorin gidansa yana kuma al'adunsu na qauyawa,shekarada shekaru yana cikin birnin tarayya amma wani baqauyen mabazai ci abinda yake ciba. wai kamarta ace mijinta dayake matsayin (minister) guda tuwo yakeci kuka yake sha,kuma abokan hirar shi sune masu shara da goge gogen gidansa.wannan ba qaramin abin kunya bane agareta.bakuma tareda shawara da itaba yafada kasuwanci mai gigitarwa, takai bayaga hannun jari,a yanzu haka kokarin bude kamfaninshi na qashin kansa yake a Rome (italy)domin sarrafa takalman fata na zamani da jakunkuna na mata da maza,
8....
haka a yanzu kamfanin'caystal' daya zuba hannun jari a portugal cikin birnin lisbon,jarinsa ya rinjaye na mutane hudu mamallaka kamfanin suna neman yabasu wasu adadin kudin ya mallaki kamfanin gaba daya.yayinda kamfaninsu na saqar kilishi(carpet)dake canada a yanzu nashi ne shi kadai. abinda ya biyo bayan haihuwar jawad kun jishi.
*** ** ***
farkon fara neman atine da bello, bai dade da fara karatu a jos ba. shikansa bellon baitaba tsammanin zai iya aure a wanccan lokacin ba. to amma me?tun ranar daya bararma atine kalwa, baiqara samun tunanin kanshiba saina y'ar tsakuwar qauyensu atine.shikansa harmamakin kansa yake,ba abinda yake burgeshi da atinen gidan mai kalwa irin tsiwarta da qaunar babanta. dama yasha jin abokansa yakubayi ko masu take masa baya na cewa wai yarinyar don tanada kyau, take tsiwa da jinkai,bakuma wanda ya isa ya taba babanta duk fadin qaraye ta kyale ko waye kuwa,komi tsawonsa,komi gemunsa haka komai kaurin rawaninsa,yace da mai bada labarin shikuwa sai ya sata kuka,ko waye?to wallahi banda shi. tuni daman suka shirya tsokanar da zasu yi mata ,tunda tace babanta ne bataso ataba mutuncinsa.
9.....
tsokanar data jawo mai dimbin nadama daga baya daya fada mayuwaciyar qaunar atine. qaunar dabai taba jiba a rayuwarshi baikuma taba tsammanin wai namiji nayiwa mace ba.

Ranar data kawo rigar ruwanshi ta dangwarar tace ba wanda ya isa yataka mata uba a gidanshi ta kyale, har kukan tausayi da so yayi daga ranar bai qara mu'amala dasu jibir ba,don aganinsa duk su suka jawo mishi.ya zauna ya zanawa atine doguwar wasiqar ban hakuri da nuna mata cewa tsokana ce kawai suke mata don raha da sanin halinta. abin haushi atine bata iya karatuba wasiqar na cikin kayanshi data bayar a dawo mishi dasu ko budeta ba'ayi ba,data tabbatar, atika zai aura ba itaba.

A rayuwarshi bazai mance da ranar dayaje yiwa baban atine ta'aziyar goggon atine ba,ya shaqi wani irin turare mai kama dana 'yan bori. tun daga ranar rayuwarshi bata qara komawa yadda take ba jin kansa yake kamar bashiba ga wani suna daketa kuwwa a kwanyarsa wai ATIKA maimakon ATINE.
10....
bayan an sallamoshi daga asibiti yaji duk atine ta fice mai arai,atika kawai yake son aure.ya shiga tambayar kansa shin maima yagano a jikin wannan kwailar yarinyar?

Ba kuma zai manta ranar da muhd.jos yashigo da ita gidan shina bayan gari ba suna zaune dasu fatimah,jiyayi kamar baima santaba sai ranar.su fatima sukace da ita kamar KYANDIR ya kasa tsawatar masu, saima yaga dacewar sunan da halittar atinen.kai shi baima taba ganin siririyar yarinya irintaba ba don tana da kyan fuskaba da ance da ita ba mace ba.

Anan ma ji yayi ya qara tsanarta, tare da ganin shirmensa da wautarsa wai na neman aurenta ada.

A rayuwarshi bazai taba mancewa da MUHAMMAD JOS ba, yakan tuno ranar da muhd yasashi gaba a ranar daya tura kayan neman auran atika gidansu atine,yayi tayi mishi kuka da hawayenshi jabe-jabe kaman ba sojaba yace bello meke damunka?

Shin kayi gamone?

Wannan wane irin wulaqanci ne?

Amma shidin ko gezau ,yace bai chanzawa,atika yakeso ba atineba idan shine ubansa to kada ya daura mishi aure da atika.
[10/19, 9:38 AM] A A Dboy: *_POST BY GROUP OF HYPE HAUSA NOVELS BOOK WHATSAPP 08064400100_
[10/20, 10:27 AM] A A Dboy:
*TUNA BAYA*
~BOOK 2~
Tuna Baya2 11-20
11....

Akwai sanda zuciya ta ciyo muhd yace wallahi inya gama karatu atine batayi aure ba zai aureta. bello yace dashi ai sai yayi dama tuni yagane take-takensa kan atine. wai! wannan ya fusata muhammad bukur jos,ya rabu da bello
Shekara uku bai neme shi ba. daga baya ne karatu ya sake hadasu suka koma kamar da,don yalura bello bai auri atikar ba.

Abinda ya faru shine ranar da bello yakai zancen ga waziry,sai ya zazzageshi yace ya zai maida shi karamin mutum a idon dunia?yaya sun gama komi na aure, daurin aure kawai yarage yadawo yace yar yake so ba kanwar ba?

Wannan karantane manya basa magana biyu.kuma ko bayan ransa bai yarda wani cikin 'ya'yanshi ya nemowa bello auren atika ba
12.....
ina!

Bello idanun shi sun rufe ruf, baya ji baya tunanin komai sai atika.ya kai karar waziry wurin maimartaba kan yaki nemomi shi auren da ya keso,amma dan kawauci irin na mutanen da, maimartaba bai yi shawara da waziry ba,ya ture mutane kai kayan bello wa atika gidan maikalwa. waziry na zaune mallam mamman yazo ya same shi wurjanjan yana tambayar shi wa bello ya aikawa lefe cikin yayansa? yace wallahi bada yawunaba, bai masan bello ya aikaba,yaran yanzu ne ka haifesu baka haifi halinsu ba.ya sawa mallam mamman kuka yana rokanshi kada ya aurawa bello y'a'yanshi kodaya.mallam mamman yace a'a, baza ayi hakaba shifa zai zauna da yarinya don haka ba ruwansa wadda yakeso cikin 'ya'yanshi shizai aura masa don bello yafi qarfin komai a wurinshi.kuma da atika da atine duk dayane ba banbamci .
13....

Maimartaba ya kira waziry ya taushashi da cewa ya kyale bello tunda shi yace yanaso.wata baiwar gidan waziry ce tatseguntawa hajia rabi mahaifiyar bello cewa matar baban atine da bello zai aura anata labari agarin cewa ta asirce bello ya komawa auran 'yarta ba atine ba,hatta ciwon daya kwanta a jos itace sila domin asirine ke bin jikinsa, kuma su don kudi da sarauta suke son bello, amma qauna ta haqiqa bello atine yakeyi mawa. tace au hakane?
Chapter 28 · 0% Book details