← Book details Tuna Baya Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 11 OF 51

Sashe 11

Tuna Baya Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

Ta nan ake kunna t.v'' ya dauki wani irin sa amma fari ''da kin danna nan, A/C xai kama, nan kuma xai mutu, nan xai kari, nan xai ragu....''
49 ..haka yai ta nuna min, sai da na tabbatar mishi na gane yace ''ka gane?

To kunna min A/C yanxu'' na kwa danna ta kama shuuuuu!.

Yace ''in xa'ayi wanka, a wannan bandaki, ya xa'ayi?'' ''Xa'a toshe rariyar kwamin ne, a kunna famfo wanda ake so (mai xafi ko mai sanyi), sai a shiga a cuda da soso da sabulu''.

Ya tintsire da dariya yai mun tafi guda uku ''da alama xamu shirya da kai, Tine, domin kai yaro ne mai saurin fahimta, ga karin kumallon ka nan, ni xani makaranta, sai sha biyu da rabi xan dawo, din ba ni xan daura lunch ba (abincin rana) Ejiro ne''
Ya juya xai fita, sai kuma ya juyo, ''af, Madam tace a gaya maka, in ka kintsa kaje can falon jiya, yau xaki fara dutyn ki''.

Na bude farantan gilashin da ya aje mani, kodayake tun kamin in bude naga abinda ke ciki, kasancewar sa garai-garai.

Farantin farko kwai ne aka soya mai kauri da ayaba da dankalin turawa, dayan farfesun koda da hanta ne, sai wani abu a kwalba mai kama da ganda (Jam), sai da na diba hoton dake jiki, na fahimci a biredi ake shafawa, sai wani irin dogon biredi mai kyau da laushi, a gefe filas din ruwan xafi ne da dan karami dai-dai cikina, da sauran gwangwanaye da kwalaben da na fahimci duka a shayin ake xubawa.

Na ci iya ci na, kunnena kamar xai tsinke don dadi, sai girgidi yake.

Santi kam nayi shi har na gaji, sai dai a bakina abincin ba dandano na rashin sabo.

Nayi wanka nasa 'yar atamfar da tafi kowacce kwari cikin kayana.

Ko mai ban tsaya shafawaba na bi hanyar jiya, xuwa kayataccen falon.

Na taddata tsaye tsakiyar dakin tana magana cikin wani abu, mai kama da abinda naji Tom ya kira 'remote' (a wancan lokacin mutane dai-dai ke da wayar hannu a Nijeriya), sanye take da siket iya gwiwarta, rigar jikin ta iya cibinta, wanda hakan ya baiwa tirtsetsen cikin damar watayawarsa yadda yake so, abin babu ko kyawun gani.

Ban taba ganin cikin mace haka muraran a sarari ba kamar randa, sai yau.

Yau ma kamar jiya, kan ba hankali.

Ke da ganin yadda take maganar, tana karkashe 'yan kananun idanun ta, kinsan da Maigidan da ake masifar so a ke.

Abinda ma na tsinkaya xance na ne, don naji tana cewa ''wallahi baka ganta ba fa, baka kirin, 'yar siririya kamar kaxar mayu, kafafunta kamar na shanshani, idanunta ribda-ribda ga tsummokara a jikin ta babu kyawun gani, hakoran ta yalaye sharr, ni kam tsoronta ma nake, don bata yi mun kama da mutane ba.
[9/24, 9:14 AM] A A Dboy: *_POST BY GROUP OF HYPE HAUSA NOVELS BOOK WHATSAPP 08064400100_
[10/5, 7:50 AM] A A Dboy: Tuna Baya 51-55
Tunda taxo gidan 'atmosphere' na gidan bakidaya ya canxa, gaskiya tabi Talatu su koma, in ya so a nemo wata'' ban san me ya gaya mata ba, naga ta tsuke fuska, can kuma ta ja tsaki tsuuuu!

Tayi wurgi da abin maganar, dai-dai lokacin da Talatu ta shigo, ga dukkan alamu, tayi shirin komawa KARAYE ne.

Hankalina ya tashi ainun, tsoron matar ya kara kamani, gashi kuma itama tace ni nake bata tsoro.

Ni kaina nasan sirinta na yayi yawa, amma ban san wani aibu a halitta na ba bayan wannan.

Ta dubi Talatu ''nayi magana da direban da xai maida ke, ga wannan inji TAHEER ki sha ruwa a hanya''.

Ta fiddo rafar kudi sababbi, ta xari goma ciki, ke da gani kinsan kwangen kudin tayi, duka aka ce ta bayar.

Talatu tasa hannu biyu ta karba ta fadi tana godiya.

Tace ''kamin ki tafi, ga wannan 'dettol' ne da 'anticeptic soaps', ki hada ruwa mai xafi ki xuba su a ciki, suyi kaman awa guda, kisa yayrinyar nan ciki ki cudeta, musamman hannuwa, kafafu da kasan hammatarta, ki tabbatar sun fita fes, kiyi ta canxa ruwan kamar sau goma.

Sannan ga wannan 'brush' da 'maclean' ki dirje yalayen hakoran nan nata ban son ganin su, xuciyata tashi take.

Direba xai kaiku saloon ayi mata wankin kai, duk wata kwarkwata da birbishin amosari, xanyi masu waya, su dirje shi.

Sannan wadannan tsummokaran na jikin ta, da wadanda aka shigar dasu daki, kije ki tube maxa- maxa a fidda mun su a gida tun basu jawo mun sauro ba.

Daga saloon xai kaiku boutique, ki xabo mata kayan sawa, wanda ba'a dinkawa.

Idan naga xani a ciki, Ubanta xan ci.

Ku tashi ku fice mun a falo, sauran in ga an saba umarni na daya''.

Sum-sum muka tashi muka fito, kamar an rarrade mana gwowoyin mu da murfin kwano.

Talatu na cuccudani a baho tana hawayen tausayin tafiya ta barni da wannan mai halin yahudawa, gata dai cikakkiyar bahaushiya kuma musulma gaba da baya, amma kwata-kwata babu tausayi da kyautatawa cikin al'amarinta.

Tace ''Oh ni Talatu ya xan yi da amana?

Ban san rashin mutuncin matar nan ya kai haka ba, ina jin labarin ta wurin bayin gidan Maimartaba da 'ya'yanshi duka, ban xaci ya kai haka ba, me xan ce da Maikalwa?

Ni kam ko a jikina.

Babana fa xa'a baiwa naira dubu goma a wata, abinda ko ma'aikacin gwamnati mai digiri, ba'a basu a ranar su ta farkon fara aiki.

Baba da Innata ne fa xasu ci jan miya, su daina dumame.

Yayana ne fa xai yi karatun da watakila watarana, ya hanani wanke-wanken; ya rungume mu cikin inuwar iliminsa.

To me xai sa inji ciwo?

A karkashinta nake, a karkashin inuwarta ne xamu ji sanyi ni da iyaye na!

Wulakanci yana tofo ko yana taimakon dan adam?

Ban xo don ta yabi halittana ba, sai don samun halalina!

''Hajiya Talatu na gama ki da Allah, kada kice da su komi game da halin Uwargijiyata.

Ni nace naji na gani, ko me xatai min, xan iya jure xama da ita''.

Ta share fuska ''shikenan Atine, nayi miki alkawari baxan bari Maikalwa yaji ba''.

Wani irin inji ake tura min kai, na dauka fille shi xai yi, sai naji ashe wai cuda sumar kaina yake, aka wanke tas, yasha sahfe-shafe da mulke-mulken mayuka masu kyau in banda kamshi mai dadi ba abinda yake tashi.

Mamakin da nake, wai gashi ma yayi matsayin da xa'a bude mishi irin wannna kasaitaccen waje domin sa?

Ni kam jikina yayi dadi, kaina yayi sayau, kaman an dauke min nannauyan kaya aka, iska na shiga ta ko'ina.

Kayan da Talatu ke xaba, rigunane da su dogayen ruguna da pakistan masu dan karen tsada don tace mata baxan sa wando ba.

Bamu dawo ba sai bayan axahar, direba ya juya da Hajiya Talati Karaye, ni kuma na rungumi jakar kayana na nufi dakina cike da kewar ta.

Tom ya kawo min abinici yana tamin bahaguwar hausar shi ina dariya, wai kwana daya kawai yaga nayi kyau, ga gashi mai kyalli yaga ya leko.

A hankali sai ya mantar dani kewar Talatu.

Ya kunna mun talbijin nace ''ni dama ka kashe ba jin abinda suke fadi nake ba, sai dai cikani da sur-sur-sur'' yayi dariya sosai ''idan kayi alkawarin koya min Hausa, ni kuma xan koya ma turanci, har da rubutu da karatu''.

''Xan koya maka mana.

Hausa ba wuya, ko yanxu ka iya hausa, matsalarka daya kana ba mace sunan namiji, shikima namiji ka bashi sunan mace'' ''haka english abu ne mai sauki, Tine, in har kasa kanka xaka iya''.

Ya koma, jim kadan ya dawo da farar takarda da alkalami ''wannan shine pencil da dan boko ke amfani dashi yayin koyon rubutu'' ya rubuta wasu haruffa d
aban-daban, kira su a nitse A, B, C, D.

Yana fadi ina fadi har ya tabbatar na rike su a bakina.

Yace in dubesu sosai in gane yadda ake rubuta kowannen su, na kuwa daddage na rubuta mai nan da nan.

Cikin dan lokaci, kirista Tom, ya fahimci Atine yarinyace mai saurin fahimta, da xata ke makaranta, da anka kwaruwar yarinya.

A daren kadai ta haddace A-Z sai dai rubuta su ke wahalar da ita.

Washegari kamin ya fita sai da ya jaddada min in haddace rubutun su kafin ya dawo, in har ina son sabon darasi.
**********
Nayi wanka kamar yadda Talatu da koyar da ni, wato sai xuba abubuwan roba a ruwan wankan (turaren wanka, dettol da sauran abubuwan kashe kwayoyin cuta), sai naji fatata har wani tsantsi take, wani danko-danko da wani maiko-maiko da naxo dashi na kauye, duk ba ko kadan, haskena ya fara fitowa, na taje dogon siririn gashina na kallabe shi kalba daya, ta sauko har dokin wuyana na nufi sassan Uwargijiyata, sanye da farar karamar riga da ruwan bular siket mai fadi, yau ma waya take, amma kwance a cikin kujera...

''wallahi na sa Tom ya dinga bata abinci sau uku a rana...

Me?

In yi hira da ita?

In ji ko tana da matsala?

Tab, kaima kasan impossible (ba xai yiwu ba... ban bata aikin ba tukunna, sai na..... gama tsaftace ta...

Kayi hakuri nace ko? (Ta sassauta murya) ai yau xan bata dama, ni kaina dattin ya ishe ni, dakina har yana ta soma taruwa...'' tayi tsaki ta yi cilli da abin maganar ''stupid kawai''.
54 Nayi mata sallama ta juyo, na xube a kasa na gaisheta, ta amsa kamar tayi bal da ni cikin kufula da daga murya tace ''sai yanxu kika ga damar tashi?

To nan ba hutu kikaxo ba, kinji mai kafar shanshani?

Ba a banxa xaki ci kudin aiki ba da lafiyar mu, lokacin mu da ilmin mu, mu hana idanuwan mu barci mu tafi mu tafi nema.

Ki bar ganin komi baja-baja kamar na banxa, a kididdige yake cikin gidan nan.

Na fiki sanin muhimmancin 'naira daya' sabida ni aiki nake tun safe har dare, yanxu haka da kika ganni a gida, hutun haihiwa na ke.

Don haka in xaki yi aiki, ki mike kiyi axama.

In banda Fulani ta kawo ki, ke dinnan baki isa kiyi mun aiki ba, ke duk 'yan garin ku ma wallahi baki isa ba.
Chapter 11 · 0% Book details