Sashe 3
Tuna Baya Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read
Don haka baxan ce son Bello nake ba, amma ya dame ni, kyawun surar shi da cikan kamalar shi abin so ne ga kowa.
Ba ga surar shi kadai ba ma, yanayin shi ma abin so ne, tsari da xubin halittar shi abin burgewa ne,balle ga mu kauyawa.
Ban taba ganin shi ba sai ranar, sai de nasha jin labarin shi da irin karamcin shi.
Dana ganshi se naga ashe yafi yadda ake tsammanin shi.
Wato dai ganinsa yafi jin sa.
Na kuma fahimci ashe macijin sari ka noke ne; bashi da mutunci ga wanda bai sanshi ba,ga wanda yasan shi, shi mai masifar mutunci ne.
Kenan idan har ina son sanin hakikanin wanene shi, kamar yadda xuciyata ta nace da son sani, dole ne in binciko tambayar shi ta shin waye BELLO WAZIRI KARAYE?
To a ina xan bincikan?
Oho!
Motsin dawowar Auwal naji a xaure,na bashi lokaci na tabbata ya gama duk abina ya saba,naje rumbu na fiddo masa abincin ranar sa, gudun kurna ne muka yi da miyar taushe.
[9/24, 9:09 AM] A A Dboy: *_POST BY GROUP OF HYPE HAUSA NOVELS BOOK WHATSAPP 08064400100_
[9/24, 9:10 AM] A A Dboy: Tuna Baya
Nayi sallama ya amsa, yana xaune bisa kwayar tabarmar karaunin da ke dakin, a hannun shi littafin boko ne yana ta rubuce- rubuce, na aje akushin na xauna gefen sa nace ''sannu da aiki yaya, rubutu kake tayi, kullum baka gajiya da rubutun nan dai'' ya aje biron yayi murmushi yace assignment aka ba mu nake ta kokari, wallahi naso ace Baba ya yarda an sa ku makarantar boko, babu abinda yafi ilimin xamani dadi Atine, xaki rubuta, xa'a rubuta miki bayani ki fahimta kamar da baki ne ake gaya miki...'' Auwal xuba yake, a yayin da ya fahimci ido nake binsa dashi kurum, amma xuciya ta bata tare da shi, tana ga wani dan matsakaicin hoto cikin firem da ke aje can gefe, Bello ne, rungume da yayan mu Sani, suna sanye da kayan kwallo na Manchester United kungiyar kwallon kafa da Sani ke masifar so, kullum ya dawo kasuwa, kallon kwallo yake tafiya can bayan gari, sai da yasan yadda yayi ya takurawa Goggo ta bashi kudi, ya kukkulla da taimakon abokai ya sayi irin kayan su.
Hankali na ya dawo ga kalmar dana ji Auwal ya ambata yanxun nan wato assignment, tabbas naso naji ta a bakin Bello, ranar da ya xage ni, ban san ma'anar ta ba, illa xuciyata ta fassara ta yadda taga dama.
Nace ''Yaya menene assignment?'' Assignment aikin gida kenan, kamar wani aiki da xa'a baki ace kije gida kiyi a nutse, a karbi sakamakon washegari, kin gane koh?'' Na maida ido daga kan hoton nace na gane, yace wannan na hoton naga baki san shi ba?
Bello kenan dan gidan Wazirin Karaye Ai yaron, yana da mutunci sosai, ga son mutane, ga faran-faran, ga ilimi, Bello zakka ne a Karaye baki daya''.
Nayi xugum, a raina nace ''ikon Allah!
Mutumin dake xage talaka, ya ci mutuncin iyayen su, shine kowa ke so?
Inda ranka kaga da yawa, wannan kadai ya isar mani tambayar wanene Bello Waziri?
Amsar da kowa xai bani kenan.
Sati biyu suka shude ban ji labarin dan gidan Waxiri ba.
Xuciyata, cike take da begen sake ganin wannan kasaitacciyar fuskar rashin mutunci.
Yau Goggo ta tashi da rashin lfy jikin babu dadi tun da safe, Inna kuwa sabgar ta take ba abinda ya dame ta da ciwon Guggo, tana girki tana 'yan wanke-wankenta irin na wanda gida yayiwa dadi.
Da daddare wurin karfe takwas, garin Karaye, hadari yai holoko, sama tayi fari fat da kwantaccen hadari, sai iska da tsawa gami da cida ke kadawa kunnuwan 'yan adam ganga.
Wannan bai hanani sulalewa in fice gidan kakana Liman ba, wai in amso addu'o'in da ya ce inxo in amsa bayan sallar isha'i in yiwa Guggo na, daren Juma'a ne ana yin dace da samun karbuwar addu'a.
Tafe nake faram-faram, iska na kada ni inda duk ta ga dama, dama gani jiki kamar sillen kara, siririya ce ni sirit kamar haihuwar bakwaini, koda yake Guggo ta ce a BAKWAINI aka haife ni.
Fuskata ma siririya ce, doguwa, mai dauke da siririn dogon karan hanci kamar shape din karas, wadatattun manyan idanu, kullum yanayin su kamar na mai jin barci, xubin su kamar kwan kaxar hausa, a takaice, komai nawa siriri ne maras kauri irin na Inna na, Amarya.
Jin taku nayi a baya na, ga layin ba kowa, hasken farin wata da hadarin yasa ina gano inuwar, dogon mutumin da ke bina, kamar mai gadi na.
Na kara sauri akan nawa na da.
Iska ta yaye dan yalolon gyalen da nike yafe dashi, ban tsaya ba, sai na kara da sauri- sauri gudu-gudu, shima dankwalin yayewa yayi, ina ganin in na tsaya bin shi nima iskar dauke ni xatayi.
Bakin tufkakken gashi na ya shiga fidda sheki da kyalli cikin hasken farin watan.
Sai na daura dukkan hannuwa na na a ka, wai in suturta kan.
Kakkaurar murya, wadda na tabbata duk Karaye, mutum daya ne mamallakinta, dai- dai sanda na kai kofar gidan Liman ita ke kiran ''A-ti-ne''.
Nayi hanxarin juyowa, Bello ne, ban ce komai ba, illa na ja na tsaya, sai na tuna bani da ko mayafi balle kallabi.
Na shige gidan da sauri na daga Asabarin Luba, duk a tsorace nake, Luba tayi salati tace ''Ke lafiya, ba dai Indo ta rasu ba?''
Nayi ajiyar xuciya mai karfi ''a'ah Inna Luba!
Iska ce ta dauke mayafin, ta dauke dankwalin, nima saura kadan ta dauke ni.
Ga kuma wannan dogon mutumin, wa ma yake da suna?
Dan gidan Waziri yana bina, muryar shi abun tsoro ce, tace ''Atine xauna nan,'' na xauna, tace'' ki nutsu nasan halin ki kinji?
Ki saurari Bello dan gidan Waziri yaron kirki ne, ba xai cutar da ke ba, Baban ki da Malam xasu ji dadi idan baki wulakanta shi ba.
Ba yarinyar da Bello ya taba cewa yana so, duk fadin Karaye, haka duk dangin su, Maimartaba ma ya bashi diyar shi yace baya so, idan kika samu ya so ki, Allah ya taimake ki, mutum ne mai ilmi sosai, Atine na, kinji?'' Inna baki san wannan ba, shine ya xagi Baban mu, ya....'' ''ni ba wani abu nace ba, kurum cewa nayi ki saurare shi, ki ji me xai ce da ke?'' shikenan Inna, Malam ya kwanta ne?'' ''ya jira ki tun daxu baki xo ba, ya bawa Sani ya baki, nake jin mantawa yayi (Sanin).
Ta bani mayafi na yafa na fita.
Har yanxu yana tsaye jikin dakalin gida, sai naji tausayin shi, ni mutum ce mai tsananin tausayi don ko kiyashi bani iya kashewa da gangan balle in wulakanta mutum.
Sanye yake da wata irin jibgegiyar rigar ruwa ta kare jiki daga dukan ruwan sama, sai kyalli take kamar leda a cikin hasken hadarin.
Ya harde hannuwan shi bisa kirjin shi, ya kurawa hadarin ido kamar mai son karanto wani boyayyen al'amari a cikin sa.
Jin motsin fitowa na yayi saurin sauke kai.
Biyo ni kurum yayi bai ce komai ba, kaxalika nima.
Hadari ya gama gangamowa, sai yayyafi ya soma sauka yaf-yaf a jikin mu, da kan rumfunan kwanon dake layin karar babu dadin ji.
Na dukunkune hannuwa na cikin tsananin raxana, alamun tsoro, xane baro- baro cikin idanu na masu haske.
Da ni kadai ce xurawa xanyi da gudu, shiko ko a jikin sa yace ''Atine, bakya magana, baki gaida na gaba da ke, why?
Na lura in xa'a kwana ana tafe dake baxaki magana ba'' nayi shiru, ya sake cewa ''Atine bakya gudun ruwan nan ya taba min lafiyar ki?
Nayi hanxarin dago ido na dube shi ta wutsiyar ido, kallo na yake da idanuwan shi masu kwarjini, wani abu na ji ya tsirga har kwalkwalwata.
Ban ankara ba naji yana rufa min wani abu mai dumi.
Suman tafe nayi, shidewar wucin gadin raxana.
Sai da na dawo dai-dai na fahimci, jibgegiyar rigar turawan ce cikin jikina, ni Atine Mamman Maikalwa.
In banda wani irin lallausan kamshi, ba abinda ke tashi cikin rigar.
Dai- dai sanda muka kawo kofar gidan mu ruwan ya jike shi sharkaf, amma bai ko damu ba.
Na mika hannu na xare mishi rigar shi, hannun shi na dama yasa ya danne nawan yace ''No, ajiya ne na baki Atine, xan karbi kayana idan na dawo.
In an tambayeki thickcoat na wanene, me xaki ce, Atine?'' Iyakar rudewa na gama rudewa, fitsari ya cika min mara fam, na sunkuyar da kai jikina na kyarma yayi hamxarin dauke hannun shi a nawa da sauri yace ''Atine, xan tafi, tunda baxan samu alfarmar kalma ko daya a bakin ki ba.
Shin kin nemo amsar tambaya na na kwanaki?
Da nace ki binciki wanene Bello Waxiri?
Na san kin binciko amma amsar tayi miki sabani da tunanin ki?'' Yayi murmushi, duk da bashi nake kallo ba, tafin kafata na kura ma ido, na ji sautin murmushinsa a hankali, a xuciyata ina gasgata xancensa, kwarai naji sabanin abinda nayi tsammani, amma hakan baya nufin na yarda, tunda ni ban ga haka akan kaina ba.
Ba kuma tare da ya kuma neman jin komi daga gareni ba ya cigaba da cewa '' yau ma ga new assignment, kije ki binciko, menene yasa Bello Waxiri ya sa maki rigar shi?
Abinda bai taba yiwa wata yarinya a garin Karaye ba?
Menene yasa kika kasa duban idon Bello Waxiri ko kadan, sabanin kwanakin baya da kika gaya mai magana son ranki?
Atine, na barki da wannan, sai da safe''.
Nafi mintuna biyar tsaye a wurin kamar an kafe ni, kamin in dawo hayyaci na na shiga gida, su Atika tuni sunyi barci Baba ne dai nike jiyo sukurniyar shi a turakar shi.
Na xare riga a hankali, na janyo aci bal-bal na kyasta ashana, haske ya gauraye dakin.
Na dubi riga da kyau,ta hadu ta burgeni iyaka, Ban taba gani riga mai kyawun ta ba.
Wannan kamshi, ni'ima ne ga ma'abocin shi.
Na samu kaina da rufa riga a kaina ina shakar kamshinta ina murmushi a hankali.
Wai shi wannan bai san ni yarinya bace, ya cika minni kwakwalwa da naganganun da suka fi karfin hankalina?