← Book details Tuna Baya Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 12 OF 51

Sashe 12

Tuna Baya Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

To ba yadda xanyi, tunda na auri Dan da Uwarsa ke juya al'amuran shi.

Daga yau karfe bakwai xaki dinga tashi masamman in na koma aiki, kixo ki gyara mun daki da sassana gabadaya, ki wanke min toilet ki canxa min xanin gado kullum.

Peter xai xo ya nuna miki yadda ake komi.

Iya kacin aikin ki sassana ne kawai ba ruwanki da sauran bangarorin ko apartment na maigida na, duka aikin Peter ne.

A sanda muka ci abinci sannan ake wanke kayan ba sai an barsu sun bushe ba, kina jina?'' Na gyada kai da sauri.

''Yaya sunan ki?'' ''Atine shine sunana'' ''meye kuma Atine?

Atini ciwon kashin yara da naji ana fadi?'' ''A'ah sunan rana ne'' ''to meye na daren?'' ''Nima ban sani ba sai iyaye na, tunda na taso, Atine suke ce mini'' ''to na ji, ni a wuri na baxan iya fada ba, domin yana tuna mini da kashin yara.

Daga yau sunan ki a gidan nan 'BLACK'.

Sai ka'idodin xaman gida na.

Da farko dai bama rasa abinci, duk abinda kike so Tom xai dafa ya baki.

Iyakacin yawon ki daga nan sassan da xaki dinga gyarawa sai can dakin girki wajen Tom inda xaki dinga yin wanke-eanke.

Babu 'yar aiki mace cikin gidan nan balle ki sami kawa, su Tom kiristoci ne da Inyamurai, don haka ki maida hankali kan aikin ki kadai, ko tsinke bana son gani cikin sassana.

Xakiyi wanka sau uku a rana, safe, rana da dare don karki canxa min atmosphere na daki kamar farkon xuwan ki.

''Ba yawo, ba kawa ba kaxanta''.

Sune ka'ododi na.

Idan miji na yana gari, kada ki sake in ganki a hanyar sassannan, domin in ya ganki, amai xai yi.

Ko xaki xo kwasar kwanukan abinci, sai kin tabbatr ya tashi.

Duk ranar da tsautsayi yasa ya tambayeki, ko ina kyautata miki?

Kikace ba haka ba, wannan dogon jelar gashin da ke reto a wuyan ki xan cinnawa gas da ashana, kinji abubuwan da na gaya maki?'' Na gyada kai ''to Hajiya''.

''Uwarki ta kauye yaushe ta je Makkah da har kika sa mata Hajiya?

Suna na, MUBINA, amma 'yan aiki na suna ce min ''Madam'', amma ke tunda 'yar wanke-wanke ce xaki ce mun Aunty''.

Na gyada kai don tabbatar mata na ji abinda tace, na kuma dauka.

Ta xaro ido tace ''ya sunana?'' ''Aunty Mubina'' ''ke kuma fa?'' ''Atine 'yar gidan Maikalwa'', ta mike ''nace miki 'BLACK' kin ce ATINE', sunan da na tsana a rayuwata.

Har da bayanin gidan ku ko daddawa ce gidan ku na tambaye ki?

Bari in baki maganin mantuwa, shige mu je''.

Na bita a sanyaye, duk jikina ya mace.

Tafiya muke lngu-lungu har muka xo kayataccen dakin da xuciyata ta gaya mib kichin ne, ba don nasan amfanin kayayyakin dake wurin ba, illa don ganin tukunyar girki da na yi.

Ta bude wani farin abu kato mai fadi, iri biyu ne da dogo da gajere, ko ince dana tsaye dana kwance mai fadi, to mai fadin ta bude wai in shiga, bayan ta fidda lemukan dake ciki.

Tsoro ya kamani, jikina ya soma kyarma, ta daka mun tawar data firgita ni, nayi kundumbala na fada, ta rufe kif, duhu ya mamayi ganina, wani irin sandarewa naji tsokar jikina nayi, in shaki numfashi, inji kamar ana tura min kankara a hanci.

Nayi kara ba murya, sai can ta bude ni na fito, duk na sandare ji nake tsokata kamar ba tawa ba, da kyar gudun jini ma bai daskare a jikina ba ''gobe in kara cewa sunan ki ''Black'' ki ce ''Atine'', in kara gaya maki abu ki manta, shige ki tafi''.
[10/5, 7:50 AM] A A Dboy: *_POST BY GROUP OF HYPE HAUSA NOVELS BOOK WHATSAPP 08064400100_
[10/5, 7:52 AM] A A Dboy: Tuna Baya 56-60
Jikina sai bari yake da karkarwa, na kunna tafasashshen ruwan nan na surka kadan na shiga ciki na kwanta na soma kuka, jikina yayi min dadi naji ana kwankwasa kofa, na maida kayana na fito.

Tom ne ya shigo yace ''maxa-maxa'' inje in yi wanke-wanke, ta gama karin kumallo, idan kuda ya hau mata kwano, komi tsadar shi a shara take sakawa''.

Tun bai rufe baki ba, ai ni tuni har nayi nisa da gudu na, dariya ce sosai ta kamashi, ya tabbatar ba karamin tsorata nayi da Aunty Mubina ba.

Na kwaso kwanukan na fara wankewa.

Cikin wata guda kacal na fahimci Aunty Mubina kakaf.

Irin mutayen 'yan gayun nan ne da har gayun ya so ya shafi ingancin addinin su.

Tana son duniya, kuma ta same ta a yadda take so, tana cin karenta ba babbaka, cikin katafaren gidan ta kuma babu wulakantacce kuma kaskantacce a gareta kamar dan aikinta.

A wurin ta dan aikin ta dabba ne kurum, da idan taga dama, xata ce ya kwanta ta taka shi ta wuce.

Gogaggiyar mace ce 'yar duniya kuma 'yar boko, 'yar gata kuma wadda ta dauki auren ta da suna kawai.

Abin nufi, komi da ke gabanta yafi auren muhummanci, haka rayuwar auren su da mijin ta, irin rayuwar auren nan ce ta kayi gabas inyi yamma, kowa yaje ya nemo nasa, ba mai jiran dan uwansa yaxo ya bashi.

Duk da bansan hakikanin aikin ta ba na fahimci ba karamar ma'aikaciya bace, sabida irin jama'ar da take mu'amala da su, da irin motocin da take hawa na kece raini.

Babban abinda yake bani mamaki da Uwargijiyata shine duk gayunta, ballagaxa ce, bata da kintsi ko kadan.

Hatta panties din ta da bra in ta tube nan tsakar dakin take cillarwa, ni xan dauka in wanke in adana mata.

In kuwa xata shirya, sai ta hautsina bakidaya dakin ta rikirkito da dukkan sitturun da take cikin sif.

Komi ta dauka, haka xata cillar dashi komi tsadar shi, sai ni in bi in gyara, haka ko kayanta masu datti, bata san ta fitar ba a'ah, ni xanyi tunanin ai tasa wadannan jiya, in xauna kullum in ware mata masu dattin.
sannan duk iya kokarina kullum aikina baya gamsheta, bayan sau dubu xan gyara, sau dubu xata bata, barin ma in bakin ta sun xo sunyi ciye-ciyen su, ni kuma a ranar ba dai hakarkarina yaga katifa ba.

Xagi kuwa da aibantani da take a cikin su, har ya xame min jiki.

Rannan ina ji tana ce da aminiyar ta Mansina ita dai Allah ya isa tsakanin ta da mijin ta da ya hana Peter gyara mata daki, don bata ga abinda nake tsinana mata ba.

Rannan kuma naji tana koka mata bakin cikinta akan wannan cikin da take dauke dashi, don bata son tayi (losing shape) dinta, kuma ko ta haihu baxata shayar da jaririn ba, kada mamanta su rankwafa.

Nanny xata dauko daga turai.

Mansina tace ''wace Uwa kika taba gani ta haihu lafiya, nonon ta lafiya bata shayar da jaririn ba?'' Ni dai nayi gaba ina mamakin hali irin na Aunty Mubina, domin yahudawa ta dora rayuwar ta akai, ita kuwa cikakkiyar bahaushiya ce gaba da baya kamar yadda Tom ya gaya mani.

A ganina girman kanta yayi yawa, domin bata aje kanta anan kusa ba, daga Inyamurai sai Nupe, da ake debowa daga Jihar Neja, rayuwar ta mai tsada ce fiye da ta su Mansina.

Ranar wata lahadi ina canxa mata xanin gado lokacin ta shiga wanka, na jiyo ta tana nishi da wani irin wahalallen numfashi, na saki xanin da gudu na je na kwankwasa kofar nace ''Anti ki bude'' da kyar tace in murda kofar a bude take.

Na murda na shiga sai na ganta kwance male-male cikin ruwa da karnin dana tabbatar na haihuwa ne, domin a irin yanayin naga Amarya lokacin da xata haifi Sadiya, na karisa da gudu na kama ta nace ''Aunty haihuwa xaki yi'' duk da halin da take ciki sai da ta dalla min harara cikin karaji tace ''kirawo min Peter'' nace cikin mamaki ''Aunty to gyara xanin ki'' wani kofin wanka ta wawuro ta maka min a goshi, ba shiri na fito a guje neman Peter, mukayi karo da Tom yana jera mata karin kumallo, cikin kaduwa na gaya mishi Aunty nakuda take yi tace a kira mata Peter, bai kira shin ba ya dauki waya ana falon ya kira likitar da ke xuwa yi mata awo..gida cikin mintuna goma sai gata ta iso, wata nurse biye da ita ta riko mata kayan aiki, da saurin su suka shiga toilet din da Aunty take
58 Shiru-shiru, in kai gwauro in kai mari a tsakiyar kayataccen falon.

Allah ya gani, ina matukar tausayawa iyayen mu mata a yayin haihuwa.

Duk da ban taba yi ba, nasan ba karamin hikimar Allah ce cikin ta ba.

Don haka na daga hannu ina nemawa Aunty Mubina sauki cikin nakudar ta, ban san sanda hawayen tausayi suka xubo min ba, duk gayu irin na Aunty, in ka ga yadda ta koma lokaci daya sabida axaba, dole ka tausaya mata.

Ihun da take kurmawa, da xagin da take narkawa mijin ta abun babu dadin ji, data lailayo wani ashariya ta yarfa mishi sai da gidan baki daya ya amshi kuwwar, fadi take ai sai da ta gaya mishi bata shirya haihuwa ba ya sace mata pills dinta, ya hada ta da jangwam, ya tsallake ya barta, amma anyi na farko anyi na karshe ita da shi sai a lahira, tunda ya fuskanci watan haihuwar ta ya kama ya gudu yana hutawar shi a turai ya barta da bala'in da ya kunsa mata.

Babu kiran sunan Allah babu na Annabi ita dai ya jawo mata ya gudu ya barta, tsakanin ta dashi Allah ya isa.

Tom yayi tsaki ya juya ya fita bayan yasa yatsun shi biyu ya toshe kunnuwan sa yana cewa, baxai iya jurar toxarcin da akewa Ubangidan sa ba.

Sai kace a kanta aka fara haihuwa.

Sai karfe hudu na yamma su Aunty aka sami kai da kyar.

Jariri ya canyara kuka da xaxxakar muryar shi kamar gyare, yana gaya mana ya iso gidan Ubansa.

Jaririn da ya juya rayuwata da ma rayuwar gidan bakidaya.

Tunda Aunty ta haihu bamu xauna ba, hidima muke da karfin mu da lafiyar mu kamar babu tsokar nama a jikkunan mu.
Chapter 12 · 0% Book details