← Book details Tuna Baya Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 46 OF 51

Sashe 46

Tuna Baya Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

Muka bar wannan batun muka koma nasu fa'izah na rarrafo ga fada mata maida auren anti da yallabai na gaya mata a yau zamu tashi kamin mu dawo tana cikin gidan.

Assha ta bani shawarwari nagari masu muhimmanci ga rayuwar aurena,ta kara karfafa min gwuiwa cewar a yanzu ni zubaidah na wuce kishiya ta razanani.

Tace'ki baiwa mijinki hadin kai a komi ku dunkule wuri guda idan tazo ko da ta dawo da halinta in taga ba fuska daga kowannen ku sai ta hadiye tsiyarta ko ni inason jawad ya kasance tare da mahaifiyarshi.

Zubyna ina dada tunatar dake nasihar gwaggonki'gaskia da juriya sune kyawawan sutturar talaka.

Zubaidah da taheer wata ajiya ce daga Allah,haka tarihin soyyrku wani abu ne mai matukar ban mamaki don haka ba uwar jawad ba,ko uwar yallabai ce nan zata ganku ta kyale,zubaidah ki so mijinki.

Maganganun hardo sun dade suna min yawo a kwanya suna amsa kuwwa cikin kaina.

To haka muka fito muka taradda mama,na bata abunda na sawo cikin leda tayi ta samun albarka ita kuma hardo ta ce da kanta zata skt kai sakona wa hajia hafsi.

Banga mansina ba na tambayeta,mama tace ai ta zari mota ta fice.

Assha tace za'a kai gulma ba?

Mama tace'na hanaki irin wadannan maganganun aishah ko ba komi mansina da mubina ba tsararki bane.

Nace 'hkn mama yarinyar nan bata jin magana.

Tace 'sai ki dawo da niyyar kai kawarki daki,mutanen alphat sun kawo kudi ansa ranar aure watanni 3 masu zuwa daidai da dawowarku kenan.

Na rungume hardo na rasa inda zansa kaina don murna nace'munafuka shine baki gaya mun ba?

Tayi gaba tana cewa'ke kinga ki zo ki tafi,ga karfe 5 tana neman yi kada kisa yallabai ya kara tsanata.
107 A hanyarmu ta dawowa Tom ya gyara murya kaman yana son cewa wani abu amma sai yay shiru nace 'wai yaya dai?

Yace 'doguwar magana ce madame dina'' nace' a daure a dan tsakuramun ko yaya' yay murmushi yasha (round) yace 'eh-toh so nake ki gaya wa oga nafa samo mata inason inyi aure shekaru na turawa antinmu.

Na tintsire da daria nace'ya dace kwarai a can bendel koko anan cikin abj?

Yace 'Allah ba zancen wasa ba nan cikin AREWA ba hausa tamkarki.

Ya dace nay koyi da ogana, qualities din shi abun koyi ne ga duk wanda yasan ciwon kansa saidai akwai matsala.

Nace amma a arewa imagine!

Yace karewama musulma,musulmar ma 'yar asalin garin kry,ko zaku bani?

Kaina yay dummm, nace' be serious plz tom bansan ka da wasa ba' yace 'am nt joking antinmu koda cam bana maki wasa balle yanzun da kike matan mutumin da nake girmamawa fiye da kowa' nace 'to wannan maganar tafi karfina mun yi ta tare da yallabai.

Daidai sanda muka shiga gate masu gadi na daga mana hannu yace'nasan abunda ke damun ranki ba zai wuce kasancewana christian ba amma banyi tunanin hakan ba saida nay tunanin wannan kuma yarinyar ta amince dani tuntuni don course mate dina ce.

Nace'thnk twice tom da alamar so kake in maka keke da keke wannan wani al'amari ne da ba zai taba yiwuwa ba sabida banbancin addini abune mai girma, kabilanci ba wani abu bane.

Ya lumshe ido yace 'antinmu idan na musulunta fa?

Ba tun yau ba ina kwadayin addininku saidai tsoron abunda hakan zai haifar ya hanani fito da kwadayin fili.

Bani da kowa sai ku iyayena duk sun mu2 dangi kuwa yanzu bana ce ga inda suke ba,ku taimakamun in auri maryam plsss...

Tausayi ya kamani zuciyata ta haskaka da godia ga Allah na dade ina kimanta tom a musulmi da anyi bawan Allah nagari da jin dadin wannan kari da zamu samu a cikin addinin mu mai dumbin baiwa da daukaka na daga hannu nay godia ga Allah a fili da boye nace 'za muyi maganar da yallabai inshaAllah kada ka damu Tom komai zai tafi daidai nagode inama sha'awar addininmu domin shine kadai tafarki na gaskia da kwanciyar hankali.

Allah Ya tabbatar muna da wannan abun alkhairi.

Yace'ai har Ejiro shima ya yanke shawarar karbar musulunci hannun oganmu, peter ne dai yace yana nan yana tunani domin iyayenshi duk suna raye yana tsoron tashin hankali.

Nace 'Allah nagode maKA, na kara gode maKa.

Da wannan na shiga gida.

Yallabai bayanan nake jin yaje office yin handing over ga mataimakinshi.
108....

Nayi wanka na sallaci magrib na shirya cikin English wears na riga da siket na yana kaina da bakin mayafi mai kauri, takalmana bakake ne rufaffu marassa dunduniya,ina cikin fesa turare yallabai na sawo kai dakin,ya hade cikin suit bakake sai fesa nashi kamshin yake na turaren 'one man show'.

Ya amshi kwalbar turaren hannuna ya shiga feshe mu gaba daya yace'kai wannan turare naki ba dai dadin kamshi ba,ya juyo shi ya karanta yace'pleasures'lallai kina jin dadinki,shin wa ke zabo miki kayatattun turaruka ne?

Nace 'Maman Ashsha ce' Yace' ta kyauta, shiyasa nake sonsu ita da mijinta, tunda ko duk suna son abunda nake so;zubina.

Ina son kamshi zubaidah bana gajiya da ni'imar kamshinki.

Niko sai murmushi.

A yau kam na amince kamshi ma wani abune dake kara dankon kauna,ya daga ido ya dubi agogon dake hannuna yace Ya Salaam, shine kika kyaleni jirgi ya tashi ya barmu?

Karfe goma jirgin Brazil zai tashi gashi har tara tayi.

Nace 'toh laifin wa?

Yace laifinki.

Nace'da nayi me?

Yace'da kika fesa turare mai dadin kamshi har na susuce.

Na tuntsire da daria yace'promise me dukkan ranakun mu a Brazil nawa ne.

Nace 'toh da na waye?

Har abada bani da aikin da ya wuce na ogana.

A jere muka shiga taka matattakalar da zata kaimu falon kasa yace 'ya dace su Tom suyi aure daga yau sun kare aiki a gidan nan zan yiwa kowannen su aure da duk yarinyar da yake so in samar musu aiki mai kyau ko ya kika gani?

Nace'Tom yazo da wani al'amari mai girma na tabbata in ka ji zakayi farin ciki sosai.

Yace'tell me wat's it?

Nace goron albishirin tukunna domin albishirin babba ne.

Yace'me kike so?

Nace'yafi karfin kudinka.

Yace amman baifi karfin lafiyar dana mallaka ba zubaidah kin ganni nan lafiyayyene ko shadi kike so in je karti a ruga zani in kuma lashe,koda yake ke cikakkiyar bahaushiya ce balle ince'' nasa dariya cikin sheshshekar dariyar nan mai ba maigida sha'awa nace'ba komai nake so ba taheer,ONLY U,bana son komi sai kai sai KAUNARKA,da cgb da rayuwa tare da kai har zuwa karshen rayuwarmu....

Yace indan wannan ne tuni kin samu zubina...

Wayyo!

Tom da Ejiro suka kauda kai cikin gigicewa gaskia yau santin amarci na kwasar oga(hehehehe) tafe suke kai kace laila da majnun ne,dukkansu basu ganin abunda ke gabansu balle bayansu sai JUNANSU.

Ya saki daria yace'Tom bude idon jan bakin ne naga yay yawa shine nake gyara mata'' ina!

Tom da Ejiro sukayi waje cikin kunya da gigita Peter ne kadai ya tsaya daga can bayan wundo,Tom yace'sorry oga,daga yau ba mai kara shigowa falon nan bayan sassanmu.

Gaba daya mukayi daria.
109...

Nace 'albishir fa shine Tom da Ejiro sunce zasu musulunta,Tom har ya samo mata 'yar kary' Oga ya fita ya kamo hannun Tom da Ejiro ya zaunar su cikin kujera duk kunya ta kamasu,ya russuna agabansu yace'bansan irin farin cikin da nike ciki ba a yau,Allah Ya taimake ku.

Yanzu muna sauri don haka komi sai na dawo kenan,amman yanzu gobe ku je kry zan wa maimartaba waya in gaya mishi duk abunda kenan za'a kula da komi naku, saidai zan so ya kasance kun nakalci kalmar shahada daga baki na har in dawo daga tafiyar da zamuyi zan ke tunawa da wannan ina kara godia ga Allah kan nasibobi da ni'imomin da yake mun iri-iri, sabida haka kuje maza kuyo wankan shiga musulunci kuyi niyyar shiga musulunci da zucia daya in nakalta muku kalmar shahada...

Ya gaya musu duk yadda za suyi cikin 'yan mintuna sun dawo har da sabbin kaya a jikin su,ya karanto masu niyya suka fada kana ya karanta musu kalmar shahada suka maimaita har sau uku.

Ya fiddo cek ya rubuta musu kudi masu yawa kamar yadda ya saba a duk sanda zaiyi tafiya.

Peter duk yabi ya muzanta daga ni har yallabai ba wanda ya maida hankali a kansa saidai shima yallabai ya bashi kudi daidai da nasun,sauran ma'aikata duk ya sallame su har masu gadi,bayan albashishshikansu na wata 3 ya kara da karamcinsa ninkin ba ninkin albashinsu.

Ya dubi Tom yace 'tom a da,TAUFEEQ a yanzu,da ejiro IBRAHEEM a yanzu,daga yau aiki ya kare a karkashin taheer sai ku nemi sabon ogan ku can a kamfanin siminti na dangote akwai gidaje guda 2 a (maitama) nasa an gina,naku ne halak malak na mallaka maku, komi na hannun Abdulraheem in kun je antinku wannan nauyin yana wuyanta na aza mata shi.

Ya dubeni mukayi murmushi nace'na dau wannan alqawarin' to daga Tom har Ejiro an rasa mai bakin godia sai murmushin kauna ga ogansu,shiko peter sai zazzara ido kawai yake abun tausayi gaba dayan ma'aikatan suka shiga kwararo addu'oin alkhairi ga ogan su.

A filin jirgin saman abj babu bata lokaci muka samu jirgin MEA da zamu hau har lokacin tashinsa ya cika.

Toh muna shiga ana rufe jirgin kamar dama mu ake jira.

Muna cikin bangaren nan mai matsayi da ake kira First Class manne muke da juna tamkar ansa super-glue an manne mu muna ta hirarrakin mu cike da so da kauna,abinki da jar fata ba wanda ke kula da harkar wani.
110....

Ina labartawa yallabai yadda mukai da Tom yana mamaki.

Nace'na ji tausayin peter Allah da kake ta ambaton komi ba tare da shi ba.

Yace'yes ina sane ina son nuna mishi karamci irin na al'ummar musulmi ne,ta hakan sai in kara kwadaitar da zuciyarsa ga son ya rabe mu kin ga dai ban ce dashi ba,amma na nuna mishi sun fishi daraja da muhimmanci a garemu.

Nace shima Allah Ya ganar da shi.

Yace'ameen' Karfe biyar na asubahi agogon mu na nan gida 9ja muka sauka kasar Brazil cikin birnin Rio de Janeiro.

Ban zaci Brazil a yadda naganta ba,ashe jin ta ake ban san tafi yadda ake tsammaninta ba.
Chapter 46 · 0% Book details