← Book details Tuna Baya Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 37 OF 51

Sashe 37

Tuna Baya Part 1 Complete Hausa Novel · about 6 min read

Wasu dumammun hawaye suka zubo min na faki idon kowa nasa hankici na daukesu amma duk da haka yallabai ya gani domin kuwa juyowa yayi kawai ba zato, bayan tun da muka taso yake ignoring hada ido dani abin daya rada mani a cikin kunnuwana ya gigitani,ya kuma kara dugunzuma zuciyata ranar bakin cikin a gareki ko?
68....
niko ranar farin cikin daban taba tsintar kaina a cikiba zubaidah,na dago na dube shi da idanuna da suka kankace,in tambayeshi abinda yake nufi da ranar bakin ciki? sai flashes aka shiga zuba mana a hakan haka masu video suka maido hankulansu a kanmu suna tsammani wata hira ce muke yi mai dadi a tsakanin mu basu san zuciyoyinmu tamkar madaci suke ba duk jijiyoyin jikina sun saki,shin menene makomata a zuciyar abban jawad yanzu?

Allah ya isa tsakanina da kai Bello!mun dawo gida ranar asabar ce ina gidan su ashshah muna shiri tawo wa karaye inda daga can ne za'a dauki amarya. tom yazo ya taddamu abakin gate muna shirin shiga motocin da zamu tafi a cikinsu da jaridun punch weekly trust da new nigeria baice komi ba ya mikawa ashshah ,kyawawan fuskokinmu nida yallabai a wurin dinner,a gefe kuma kyakkyawan yaron mune jawad headline na new nigeri cewa yayi INDA YAR RAINO A GIDAN MINISTER TAHEER USMAN TA ASIRCE SHI TARABA SHI DA UWAR DA DANSA DIYAR BALARABE DANGO TA AURE SHI BAYAN TA ASIRCE YARON TARABA SA DA DAN DA UWAR DATA HAIFESHI JAMAA AYI HATTARA DA DAUKAN YAR RAINO.....
69 cikin harshe turanci,sauran shafukan dauke suke da cikakke tarihinas wanda aunty mubina ke fadi da bakinta,yadda tasa akai min wanka aka dirje yalayen hakorana da amosani da kircin kaina ta sayamin sitturu ta dankamin amanar yarota jawad da yadda rana daya taheer ya canza mata saboda ni ta kuma tsinci labarin daurin auran mu a kafafen yada labarai sauran jaridun ma duk kwatankwacin abin da suke dauke dashi kenan da sauran labarun kaskanci da wulankaci a gareni,hajiya hafsi da maman ashshah sukayi murmushi tace kadan daga aikin iyalan dango ashshah ko ashariya ta antayo ta mulmulo ta yarfar a take ta fidda waya ta kira yallabai ta gaya mai duk abinda ya kenan har tana karanto headline din shima ranshi ya baci sosai amma ya taushe ta yace muyi hakuri bai da ikon hana yan jarida buga abin da suka gadama illah zai nemi yahai ya jawa mubina kunne kuma zai tsaida saida jaridar.

Ashsha ranta ya baci da wannan shirmammen matakin da yallabai ya dauka don tana gani bai dauki abin da muhimmaci ba, shiko yanayi komine cikin hankali domin ubangidansa ne har gobe,ba zai tozarta duk wani da ya shafi mutuminan balarabe dango ba ta sake danna wayar yayarta mansina dake tare da aminiyarta a lokacin a honolulu tun da akasa ranar bikin zama nigeria ya gagari aunty mubina do haka suka tsirga birni honolulu mansina na cewa hello ashshah nacewa ki gayama kawarki ta sayo jaridar sabuwar nigeria da ragowar data kai musu wani article suka buga taga yadda muji ya dace da mata,mata ta dace da miji ba ladi ba duwaiwai da marsandi ba ta kuma dunga iya bakinta a komi inba haka ba wataran zata yanka wuyanta.ai abin kunya har ya wuce nata? tana (portugalese trained)amma ta kasa rike mijinta tana zaune cikin gadan har idon shi ya afka kan YAR RAINON da take ambato,ina ajinta,ina wayewarta sanda tayi saken da har yaso YAR RAINO to ta nemi fidda yar rainon yayi mata saki wukakanci bayan ya dankara mata dan banza duka kuma
ki gaya mata wadda tayi dominta batamawa, mijinta ya tausheta da kalaman kauna.tace ayi mata godiya sabida hoton data kaiwa yan jarida, ya balain birge jamaa har itama ya burge ta,dan ta jawad ko data ke ikirarin anyi asiri an rabasu. bayan a zahiri sakaci da shashancin tane ya rabasu, yace ya gaisheta,wai meyasa bata zo bikin momisa zubaidah da daddyn sa ba?koda yake tuni taba shi amsa da cewa kunya ce ta hana ta zaman kasar ta tattara yanata yanata ta tafi can wata uwa duniya da ba'asan da ita ba balle ayima dariya.gaba daya suka kwashe da dariya banda ni da mamansu,tace ashshah!ta dago ta sakar mata dakuwa tace ungo naki,ba gaba suke da kuba, bana son rashin kunya?tace haba mama,ai kunyar mara kunya asarace .na kifa kaina jikin kujerar bayan motar da nike zaune, na soma kukan da bazan iya fassarawa ba. ban taba facing humiliation kaskanci irin na yau ba.shin auren sunna ya taba zama abin kunya?wata zuciyar tace ba auren bane abin kunya, matsayin wanda na aura ne, haka bello ma ya gayamin,sai naji zuciyata tayi bakikkirin,lokaci guda na tsani auren, na tsani abban jawad din ma kansa na rinka ganin maganganun bello suna dawowa suna warwarewa suna neman zama gaskiya zubaidah da wannan abin kunyar ai da kin baro naki daga nesa,mai kaunar ki da gaskiya tun kina yar sam tsami tsaka tsami.....sai wasu hawaye sharr!

Ban sani ba ashe suna diga kafar hajiya hafsi wadda take daura dani,ta kai hannu bisa kafaduna ta rungumoni jikinta tana cewa har bazazzagi ya isa ya girgiza ba kano?har barazana jarida ta isa ta karya miki gwiwa diyata?ai haka take so ta takaitaki to meye abin kunyar a ciki? cewa nake manzon mu mai tsira da aminci yaron nana khadija ne,ta nemi daya aureta sabida gaskiyar shi da amanar shi,kenan kina da qualities da za'a so ki akai wanda har yafi nata ai ke abin tinkaho ne zubaidah ki shiga gidan auren ki da karfin gwiwarki sai nayi murmushi mun isa karaye yamma lis,awal ne ya fara amsa jaridar hannu ashshah ya dubawa
[10/23, 5:14 PM] A A Dboy: *_POST BY GROUP OF HYPE HAUSA NOVELS BOOK WHATSAPP 08064400100_
[10/23, 5:18 PM] A A Dboy:
*TUNA BAYA*
~BOOK 2~
Tuna Baya2 71-80
A dakin amarya inna luba ta fizge jaridar tana cewa rangadi, cancadi.atinen goggo ce wannan? kai amma wanda ya dauki hotonan gwani ne na gwanaye dai dai sanda baba ya shigo yaci farar shadda mirror yar ciki da wando da babbar riga fara sol yana ta fara'a suka gaisa da kowa sai auwal yace inna don baki san meke rubuce jiki bane, kyawun hoton kadai kika sani tace to karanto min inji kunne na biyu su dacta hafsi da sauran jama'ata suka mike suka hau sama inda aka yi musu masauki tun fara bikin,maman ashshah na cewa kai auwal da tsurku ka ke,ina ruwan inna da shirmen su?awal ya karanta tiryan tiryan yan fassarawa,tun bai kai karshe ba inna luba tasa kuka.raina ya kara baci basan sanda nima na fashe da kukan ba,cikin rishin kuka tace ai gashi nan tun ba'a je ko ina ba kin jawa kanki abin gori atine,tun farko ai sai da na fada,amma da yake ni tsohuwa ce ba'a mai dani a bakin komi ba ba wanda ya saurareni. yanzu da bello kika aura wa zai ce dake kin yi abin kunya?
Chapter 37 · 0% Book details