← Book details Tuna Baya Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 22 OF 51

Sashe 22

Tuna Baya Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

Wadda ke kula da gidan sa, gudan jinin sa, cikinsa da mutuncinsa baki daya?

Wadda xuciyar sa ta dade tana kawata masa tsararren jikinta da ko a turai, bai ga kwatankwacinsa ba!

Wadda ya dade yana kimanta dan kyakkyawan bakin ta a yayin kissing!

''Kada kayi haka Oga ne fa'', xuciyar shi ke tunatarwa 'to Oga, bai san mai kula dashi ba?

Bai san mai mutunta shi ba?

Bai san abinda xuciyar shi ke so ba?

Bai san mai kula da cikin sa ba?

Sai kawai ya juya, ya maida musu kofa ya rufe.

Munji maida kofar dukkan mu.

Muka dubi kofar, ba kowa.

Amma kamshin da ya turare dakin na Yallabai ne.

Jawad ya mike a guje ''Daddy na, ya dawo Momi ki tashi muje mu bashi abinci''.

A'ah Jawad, jeka kai kadai.

Uncle Tom xai kaiwa Daddy abinci'' ya shagwargwabe fuska ''Momi na, kullum nace muje dakin Daddy na, sai kice baxaki ba, amma shi yana xuwa dakin ki, kuma waccen matar tana xuwa kullum''.

Me xancewa yaron nan?

Tambayarshi ta bani mamaki, ba kuma nason ko kadan yayi tambaya in ki amsa mishi ko in mishi karya.

Ya tsatstsare ni da fararen idanunsa, na sunkuyar da kaina.

''Jawad ita matarshi ce, ni ko mai rainonka ce kawai, kaga ya dace yaron gida ya dinga shiga dakin Ubangidansa, ba'a kirawo shi ba?'' Ya girgixa kai, da alama ya gamsu.

''TO ME YASA BAXA KI AURE SHI BA KEMA?''.Wannan yaron da kure mutum yake, kaifin basirar shi yana bani tsoro, to me xan ce masa kuma?
[10/8, 5:27 PM] A A Dboy: *_POST BY GROUP OF HYPE HAUSA NOVELS BOOK WHATSAPP 08064400100_
[10/8, 5:35 PM] A A Dboy: Tuna Baya 101-105
101.

Sai na wayance ''kai na daura xuwan xafi a Gas, maxa jeka yiwa Daddy welcome''.

Na mike, shima ya kama hanyar kofa yana kunkuni.

''tunda baxa ki gaya min bam xan je in tambaye shi ai shi xai gaya mini''.

Xuwa can ya dawo ''Daddy yace, kixo ki xuba mashi abinci, yaji ciwo a hannu'' ''kai don me baxa ka xuba masa ba?'' ''Ni baxan taba tuwo ba, bana son shi''.

Nayi dariya ya dare bayana, muka tafi sassan Yallabai.

Sanye yake cikin kafta da wandon farin danyen voyel, yana kwance cikin kujerer alfarmar main falinshi, rike da waya ana ta xabga turanci, ya rufe wayar a cikin kallona ''Xubaidah Jawad ya wuce goyo, bakya tsoron ya bude maki kirji ne? l' ''Ai shi din ne, ya riga ya saba'' ''ki sauken abincin kasa, yau bana son hawa table din''.

Nayi murmushi, Na yi murmushi, a raina nace ''gargajiyar ta motsa kenan''.

Na koma na dauko katuwar ledar cin abinci, na shimfida a gabansa na sauke komai, Jawad na kalmashe cikin jikin shi, ''wanne xa'a fara ci?'' ''Wanda duk kika ga ya dace'' ''ai kowanne ya dace'' ''to a bani kowannen''.

Ina xubawa yana kallona, wanda hakan ya haifar min da rudewa, rawar hannu da rikicewa duka.

Ya sauka a kujera ''kin tsugunna kamar ace ar, ki danna a guje, xama xaki sosai.

Yau tare xamu ci abincin'', YA ILAHI, na dubi Yallabai ya xame min wani karamin yaro, magana yake min kamar Babyn dake gaban Mamarshi.

''Ni da Axumi nake'' ''axumin menene?'' ''Na tadauwi'i mana'' ''A'a na ramumuwa ne, in kuma kince baka ba, ki rantse; wallahi axumin tadauwa'i nake.

Sai nayi kus, na xauna can gefe a darare.

Al'amuranshi masu ban mamaki ne, komi nake yi ya sani.

Tunda ya fara cin abincin bai kara magana ba.

Sannnu-sannu, daga gyan-gyadi barci mai nauyi ya dauke Jawad.

Duk abinda ke wajen nan Yallabai ya ci kowanne, ko ba'a fadi ba.

Shiru ga mai cin abinci santi ne.

Da gani ya bala'in yunwatu, don ma dai yana da jure yunwa.

A turai yafi son yayi Axumi, duk bayan kwana daya, don bai son abincin su bai burgeshi.
102.

Na yi murmushi, a raina nace ''gargajiyar ta motsa kenan''.

Na koma na dauko katuwar ledar cin abinci, na shimfida a gabansa na sauke komai, Jawad na kalmashe cikin jikin shi, ''wanne xa'a fara ci?'' ''Wanda duk kika ga ya dace'' ''ai kowanne ya dace'' ''to a bani kowannen''.

Ina xubawa yana kallona, wanda hakan ya haifar min da rudewa, rawar hannu da rikicewa duka.

Ya sauka a kujera ''kin tsugunna kamar ace ar, ki danna a guje, xama xaki sosai.

Yau tare xamu ci abincin'', YA ILAHI, na dubi Yallabai ya xame min wani karamin yaro, magana yake min kamar Babyn dake gaban Mamarshi.

''Ni da Axumi nake'' ''axumin menene?'' ''Na tadauwi'i mana'' ''A'a na ramumuwa ne, in kuma kince baka ba, ki rantse; wallahi axumin tadauwa'i nake.

Sai nayi kus, na xauna can gefe a darare.

Al'amuranshi masu ban mamaki ne, komi nake yi ya sani.

Tunda ya fara cin abincin bai kara magana ba.

Sannnu-sannu, daga gyan-gyadi barci mai nauyi ya dauke Jawad.

Duk abinda ke wajen nan Yallabai ya ci kowanne, ko ba'a fadi ba.

Shiru ga mai cin abinci santi ne.

Da gani ya bala'in yunwatu, don ma dai yana da jure yunwa.

A turai yafi son yayi Axumi, duk bayan kwana daya, don bai son abincin su bai burgeshi.
103.

Ya kammala, na tsiyaya mishi ruwan lemun SANA ya fara sha, sannan wadanda nayi ''Zubaidah, kada ki kara yi min haka, ya baki fara bani wanda nake so ba, xaki bani farin ruwan banxa?'' ''Na tuba Yallabai'' ''baki tambayeni ciwon da naji ba, ko Jawad bai gaya miki bane?'' ''Ai ban ganshi bane shiyasa, amma ya gaya mani'' ''kin ganshi, ai a ido ne''.

A karo na biyu, tamkar wata doluwa, sai na kai idona ga idanun Yallabai.

Wai me yasa maxa suke shammata na irin haka?

Su dulmiyar dani a tafkin kaunar su?

Babu ko tantama nasan irin wannan kallon cikin idanun BELLO WAXIRI.

Babu komi cikin kwayar idon Baban Jawad, face fitinannen so.

Sun juye, sun rikide xuwa 'luv colour'.

Wani abu ne ya tsirga min tun daga kirjina har xuwa yatsar kafata, na ji wani irin yarrrr!

Nayi saurin sauke idona.

''Kina da maganin wannan?

Zubaidah!

Xaki bani?'' ''Ni... ni.. ni.. bana da maganin komi''.

''To tashi je ki, tunda bakya badawa, ki binciko mani komi kankantarsa''.

Har na kai bakin kofa yace ''xo ki fice min da Dan ki'' na dawo da sauri kafafuna se karo suke da juna, shin yaya xanyi in dauki Jawad, alhalin gabadaya cikin kirjinsa yake?

Ganin na tsaya cak, na kasa koda motsi, ya san tunani na.

Ya fidda yaron daga jikinshi, ya kwantar dashi a kujera, na matsa na russuna na kai hannuwana ga Jawad ''iye, ashe gaskiyar Jawad kin sa turare mai dadi, to nima gobe xanxo a sammi ni''.

Ai Zubaidah, baki ya mutu murus, na dauki Da na na yi waje, na gayawa Tom yaje ya kwashe kayan abinci.

A wannan daren mai cike da rudani a gareni, na kasa barci.

Wani abu ne na ji yana yanyameni, a gabadayan sassan jikina, game da Abban Jawad!

Ba dai SO ba?

Bana fatta, kuma bana addu'ar, in kara son wani namiji a rayuwata!

Tun daga kan Bello, na rufe shafin soyayyah, balle da Ubangida na da nake gani da mutunci tamkar Babana!!!
104.

Idan nayi haka, ai nayi abin kunya, 'YAR WANKE- WANKE TA AURE MAI GIDA?

Na tuna da maganar marigayiya Goggo na Indo
.

''Ki guji duk wani abu da xai sa kiji kunyar mutane.

Gara ki mutu da ki aikata ABIN KUNYA!'' Xan yi kokari in bar gidan nan haka, tun kamin abin kunya ya tabbata.

In ba xolaya ba, xuciyata taki amincewa.

Cewa take ''Zubaidah, baxa ki iya barin Jawad da Abban Jawad ba!'' Mutumin da ya mutunta ki, a yayin da aka wulakanta ki, mutumin da bai kyamace ki ba, a yayin da ake ce dake mai yalayen hakora, mutumin da ya suturta ki, a yayin da aka so kiyi yawo cikin tsiraici, mutumin da ya fidda ki daga matakin JAHILA xuwa DALIBA mai 'yanci.

Mutum da ya dauki Dan shi sukutum, yace ya mallaka maki...

Ya maida KYANDIR mutum.

Ya maida MUBURGI muciya.

Ya maida BLACK LIGHT, ya maida ATINE MAMMAN MAI KALWA ZUBAIDAH MUHAMMAD KARAYE... (these and many more), ai ya cancanci a so shi koda baya da abinda xa'a so shin, balle yana dashi, yana da komi tunda yana da halaye na kwarai, wanda mace baxa ta taba dana sanin auren shi ba.

Mutum wanda ya san mutuncin dan adam, ya ke kiyaye martabar kauyen shi, kasar shi da al'adun shi na AREWA.

Ban taba ganin mutum mai daukaka kasar shi da kare martabar al'adun shi a duniya irin Baban Jawad ba (Ethnocentrism).

Mutum wanda yake karrama 'yan mahaifar shi TALAKAWA, wanda bai taba xagin MAI-KALWA ba mai xai hana ki aure shi Atine koda BA KYA SON SHI!

Ki jiyar dashi dadin aure wanda bai samu ba a rayuwar shi, ki mutunta shi, mutuncin da bai samu daga Uwar Dan shi ba.

Ki nuna mishi TALAKA BAI MANTA ALKHAIRI, ki mallaka mishi jikin da ya raina daga 'YAR SHILLA XUWA KAXA bai taba nuna yana kwadayi ba.

Auren shi shine hanyar da gudan xuciyar ki JAWAD, rayuwa ta har abada!

Shine sakamakon da ya dace da shi.

In kika bijirewa soyayyar shi kin yi butulci balle ma kina so, kina son miji irin ''TAHEER'' wanda bai dauki rayuwa a bakin komi ba.
105.

Arxikin shi bai sanya shi ya maida duniya gidan kashe-ahi-ba.

Kuma tabbas, xai darajja MAIKALWA xai mutunta AMARYA!

Shin me kike nema a rayuwa da ya wuce wannan?

Wasu irin hawayen dadi suka xubo mani, na mirgina na rungume Jawad, cike da tunanin wani magani xan bincikowa ciwon idon Abban Jawad??????

A bangaren 'yar boko, bata shigo gidan ba sai karfe 6:00pm.

Sun shigo tare da wasu kabila 'yan office dinsu maxa guda biyu, inda ta sauke su har main falon ta.

Abokan aikin ta ne, ita a dole ta nuna musu eh, ya ne!

Mijin ta Minister ne.

Don haka ne taki saukar su a falon baki, don bai kai haduwar nata ba ko kadan.

Wasu takardu ne suka xo amsa da ya shafi aikinsu, ta xarce daki don ta binciko.
Chapter 22 · 0% Book details