Sashe 21
Tuna Baya Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read
Amma ina jin wanda na gansu tare da Alphat ne.
Baki, mai matsakaicin tsawo, shi ya bani kayan daka ambata.
A matsayin tsarabar New Orleans, kasacewa ta aminiyar Aishar su''.
Ina jin sanda yayi dariya ''dadi na dake; fadar gaskiya a duk inda take, bakya karya, bakya ha'inci.
Ina Dan ki, me yake yi a daren yau?'' ''Jawad yayi rigimar shan kamun waken-suya, ya yiwa su Tom rigimar rashina.
Lallai ne a kawo waken-suya gobe, in ba haka ba dukkannin mu ba mai barci''.
Ya dau lokaci, bai yi magana ba, xuwa can ya ce ''yaya karatu ina fatan kina bita sosai?'' ''Ana yi'' ''ba ku bukatar komi nan Canada?
Xan xo unexpected as usual, amma xan gaya maki ina gab da xuwa, don in samu delicious tuwonki, xan samu Zubaidah?
A nan ina matukar kewar abincin ki.
Zubaidah, 'KE KADAI CE XAKI YI GIRKI IN JI NA CI BAN YI TSAKI BA, BAN TURE KWANUKAN DA RAGOWA BA'.
Na lumshe ido a hankali, taushin muryar shi ya ratsa har cikin kwakwalwana, da kyar na iya na ce ''xa'a samu Yallabai, har abin da yafi tuwo, wanda nasan Ba-Hausan bakinka xai soshi.
Wai da gaske ka ce in rabu da Aishah?' ''Idan har xata sanyaki turbar samarin ta ba?
If not, ki gaida ASHSHA IBRAHEEM HARDO''
[10/8, 5:25 PM] A A Dboy: *_POST BY GROUP OF HYPE HAUSA NOVELS BOOK WHATSAPP 08064400100_
[10/8, 5:27 PM] A A Dboy: Tuna Baya 96-100
Kalamin Oga, sun bani mamaki, ta yaya xai ce ba xanyi samari ba?
Alhalin ya ce muna da 'yancin yin komi gidansa tamkar 'ya'yan da ke gaban iyayen su?
Na yi murmushi ''In shaa Allah, xan kiyaye, but please do for me one favour (wato kayi mani alfarma daya) ka gaya min wanda duk yayi maka bayanan da kayi min yanxu, game da su Aisha, I am extremely intrigued!'' Dariya yayi, cikin matsanancin nishadi.
''Xubaidah, kin manta na ce ''XAN KULA DA KE!'' Don haka a ko'ina nake cikin duniya, ina ji, kuma ina ganin duk wani takun sakarki a rayuwa.
Kada ki tsaurara bincike, Zubaidah, ki shafa min gudan raina JAWAD''.
Har na kwanta barci, ina juya kalamin Ogana, mutum ne da wuya ka fahimci inda xancensa ya dosa.
Idan ya murda wata maganar, bana iya warwareta.
Ko ma dai me ke akwai, xan kula, baxan taba yin abinda baya so ba!
''Aishah, Abban Jawad na gaisheki'' ''Ke ma Alphat da Yusuf suna gaishe ki, sai dai wani muhimmin sako daga YUSUF DABO, wanda nike fatan ki amsa da hannu bibbiyu'' ta xaro wani dan karamin (complementary carde da akayi dan rubutu a baya, da farko kamar in ki amsa, sai kuma na amsa din. (Zubaidah!
Luv, so easy 2 say, so easy 2 spell, but we've ever given luv a chance 2 spell itself 2 u) Yusuf .
Na dubeta, cikin tsananin rashin fahimta ''me kenan?'' ''Ma'ana yana SON KI.
Wallahi Zubaidah Yusuf dan manya ne, mai sanin ya kamata.'' Duk sai ta bani dariya.
''Goggo na kada ko kara yiwa kanki karambani irin wannan a kaina.
Ki na so Oga ya kore no ko?'' Why, don me?'' ''Ra'ayin shi ne, ban kuma tambaye shi ba''.
''Shikenan xan wa Yusuf bayani''.
***********
Mansina, ta dawo Indonesia ranar lahadi wurin karfe 9:00pm, bata xame ko ina ba sai gidan aminiyarta.
Mubina xaune bisa 'carpet' din falonta, ta barbaxa takardu da 'yar karamar 'computer laptop' a gabanta, kai da gani kasan lissafin Bankinne da baya karewa.
Mubina ta tare ta da murna, amma da ganin fuskarta, ta san labarin ba mai dadin ji bane.
''Me kike yi?'' Abinda Mansina tace da ita kenan tun kamin ta samawa kanta maxauni a falon.
''Wallahi sabon Manajan mu ne ya hada ni da aikin lissafa abinda muke bin wani 'foreign trader' amma nake jin na kammala''.
''Game da taryar mijinki fa?'' ''Wai mara mutuncin nan (Baban Jawad), cewa yayi xai dawo?
Yaushe?'' Tayi xugum tana dubanta kamar ta makure ta don haushi, ''wato Mubina duk abinda na gaya maki, kinyi watsi dashi.
Don ke naje Indonesia da kaina.
Don in gyara ki, mijin ki ya soki, amma kina nan kina bobbotsaren taki.
Jiya a labaran BBC naji sun taso daga Canada, me kika tanada?'' ''Yo in ma nayi kwalliyar yabawa yake?
Inna yi shegen shaye-shayen ya san an yi?
Kin ganni nan, gobe idan na bar gida sai goma na dare.
Akwai aikin lissafin da xan yi...
''Na ji-na ji, Banki uwar ajiyar kudi, kina da labarin 'yar rainon ki, na shekararta ta karshe a makarantar su kanwata Aisha?
Aisha na koya mata karuwancin kwacen miji?
Mubina ki kama kanki, ki fidda 'yar rainon nan daga gidannan.
Ga magungunan gyara na hado maki kiyi amfani da kowannen su a yau, (kuji sai kace wata uwar ta, Takori), ba Taheer ba, ko Sarkin Karaye kika danawa wannan tarkon, sai dai uwar shi ta haifi wani, amma ba shi ba kara kallon wata diya mace da sha'awar aure.
Sauran dubarun na bar maki, kiyi amfani da hikimar ki ta diya mace, ki lallameshi cikin hila da kissa ya sallameta, ki karbeshi da murnar ki, ko kin samu ya taya, in ma bai taya ba, kada ki kyaleshi, ai hakkinki ne''.
Da haka sukai sallama, xuciyar Mubinah tamkar tafasashshen ruwa.
''Black, a Nurul-Bayan?''
To me xata yi mata ta huce?
A doke dai, yanxu sai dai su kirbi juna.
A xage, sai dai tayi ta kare, ba xata daga ido ta dibeta ba balle ta tanka mata ba.
Abu mafi a'ala ta Mansinar ce da tace ta lallame shi, ya sallameta hakannan.
Washegari, bakwai na safe a Omega tayi mata.
Wai tayi ta kammala abinda xatayi xuwa shidda na yamma ta dawo.
Tun karfe goma na safe, ina ji a radio saukar shigaban kasa da ministocin sa da sukayi mai rakiya xuwa kasar Canada, domin kulla cinikayyar man fetur tsakanin kasashen biyu.
Shi kuwa Yallabai dama ya je da biyu ne, rakiyar shugaban kasa da karbar ragamar kamfanin su na carpet wanda a da yake mallakin su su hudu, wanda a yanxu ya xama nashi shi daya bayan wasu kudade masu yawa da ya biya sauran share-holders mamallaka kamfanin.
Sun sauka ne a filin jirgin saman Abuja, karfe biyu na rana.
Na rubuta komi, na baiwa Tom, ya nemo mu yiwa Oga abinda xamu burge.
Sai gashi harda garin masara da tsaki daga wurin Kulu da Gasara mai kyau.
Jawad na gefe a kicin din yana ta fama da bindigar roba, na tankade gari tas, na ware tsakin nayi kyakkyawan tuwon masara miyar xogale, da aka wadata da toxon Saniya.
Sannan dambun tsakin masara da dambun shinkafa, wanda yaji kayan hadin su green beans, cabbage, carrot da sauransu.
Maimakon nama, da yankakkun kananun hanta nayi amfani.
Tuwon shinkafa mai sulbi da miyan taushe, wadda ta ingantu da kayan hadi cikin tsokar kaxar gona.
Na hada kunun xaki da gasarar yaji kayan yaji da kayan kamshi.
Lemu da na hada kayan marmari kala-kala har kala biyar wato abarba, lemun xaki,Inab, tuffa da strawberry, shi ne na karshe.
Na adana kowanne a flask dinshi daban.
Na kama Jawad yana ihun in barshi yayi wasan sa, nayi mai wanka, na shirya shi cikin wani irin 'suit' kalar 'brown' da fari ta ko ina kamshi yake.
Yayi dariya a yayin da nike fesa mashi Dune ''Momi na, kullum Daddy yaji ina kamshi, sai yace Allah ya sakawa Momin ka alkhairi'' na ce ''na ji''.
Tun haduwan mu da Ashsha nayi sittiru ba kadan ba, kowanne bana banxa ba.
Dama kuma Abban Jawad bai rageni da komi ba ta fannin tsadaddun sitturu.
Kuma nafi son in sa nashi in yana nan, bakin shi baya shiru da yaba mani, ya kan ce wai ni bana raina abinda aka bani.
Wannan ya tabbatar mani duk kyautar da yayiwa matarsa, baya burgeta.
Nayi wankan rana na kamar yadda na saba.
Atamfa Super-Holland kalar ta orange da blue, duk cikin kayana, itace tsohuwa, domin akalla ta doshi shekaru uku, itace a jikina.
Dinkin mai kama jiki, dan caras iya cibi, xaninne ke karawa har kasa.
Banyi daurin kai ba, don ba damu na yayi ba.
Xagayo da dankwalin na yi wuya na sai shacin fuskata kawai xaka iya gani, wadda na san haduwarmu da Ashsha, gabadaya ta canxan, tsari da fasalin halitta na ya koma irin nata.
Tace wai turare in ka fesa shi yana sawa kaji ranka da dadi, don haka na dau daya cikin turarukanta ''GUCCI'' na feshe ilahirin jikina dashi.
Na kuma ji dadin.
Jawad yayi dariya ya sakalo hannayen shi xuwa wuyana ta baya ''Momi na, kinyi kyau.
Idan Daddy na yaxo xan ce ya baki turare, yau kin fesa turare'' ''ni kuma in ka fada, in fada masa kutufo da ka rinka yiwa Uncle Tom rannan''.
Ya kyalkyale da dariya ''ai bai ji xafi ba, bari ma in tambaye shi Uncle Tom!'' ya shiga jerawa Tom kira, sai gashi a sukwane, hannuwan shi dama da hagu rike da tumatir da tattasai ''lafiya?
Irin wannan kira haka Master?'' ''Nothing actually.
Dama tambayar ka xan yi, wannan kutufon da nayi maka kaji xafi?'' Tom yayi tsaki ya juya ya fice, sai kuma ya dawo ''Tine, danki bashi da dama''.
Momi na baki tambaye ni ba, karatun da kika biya min jiya da daddare, na rike'' ''To na tambaye ka yanxu, yi in ji?'' ''Sai mun kwanta akan carpet'' ''ni kuma bana son kwanciya, sai barci ya daukeni'' ''To Momi ki xauna akasa, in kwanta a cinyarki, sai kifi jin in ina karatun sosai''.
100.
Na sauka kasa daga kan kujera, ya kwanta duka a jikina, ya soma karanto ''Suratul A'ala'' ina shafar kanshi, in yayi kuskure, in gyara mashi.
Ya dade yana kallon mu, admiringly, baya son katse mu, baya son daina kallon wadannan fuskokin guda biyu.
Wadanda ke faranta masa, su wanke duk wani bacin rai da ke tare dashi, wadanda da ganin su kasan ba abinda ya dame su a rayuwa, face kauna da kulawa da junan su.
Sabanin shi da xuciyar shi ke cike da kuncin rayuwa, duk a dalilin rashin dace da samun mata ta gari, thoughtful and caring tamkar mai rainon Jawad.
SHIN MAI XAI HANA SHI AUREN ZUBAIDAH MUHAMMAD KARAYE?