Sashe 38
Tuna Baya Part 1 Complete Hausa Novel · about 3 min read
Ta shura takalmata ta fice.baba ya tashi sadiya daka zaune duk idon ta ya ciko da kwalla.don inda abinda taki jini a duniya shine kuka na,yace ta tafi ta kira mishi sani a falo ya saura daga ni sai shi sai awal da inna mu amarya.ya barni nayi kuka na ya ishe ni na share hawayena yayi gyaran murya yace toh atine nagode Allah da ya nuna min wannan rana mai dinbin tarihi a garumu duka a yau na zauna nayi tunani abubuwa da dama dasuka faru acikin rayuwarmu ta baya data yanzu da bata kare ba.ta kowanne bangare ubangiji ya rufa mana asiri,yasan zuciyata?yasan meyasa na amince ki auri shi wannan bawan Allah,yasan ba kwadayin abin duniya bane ba kuma neman suna ba illah mutunci da karamci da magajin gari yayi mani,ko ince yake kanyi mani wani abune dazan iya mancewa ba haka shima bello.banki goyan bayan dawowar bello ya aure ki dan taheer ya fishi wani abu ko don kaddara da ta afku a baya ba illah komi ni zanyi arayuwa ina baiwa Allah zabi ne sai naji zuciyata tafi son aurenki da taheer
fiya da bello,wannan shi ya tabbatar mini cewa taheer shine zabin Allah a garemu baki daya, kuma miji mafi alkhary a gareki,don haka duk ma wani mai yiwa abu fassara ta daban ni na barshi da Allah ya ganar dashi,ba wanda ya isa razanani abisa abinda Allah ya zaba a cikin al'amurana haka kema nake so ki amince a rayuwata bazan taba mance da ranar da nace atika taje wanke wanke dan a samu abida za'a tallafi karatun awal da kannesa da abinda zamu ci abinci ita da uwarta suka tozartani akan idonku. ba kuma zan mance ba a washegarin ranar kika kaho min farau farau a cikin koko,kika ce zaki wanke wanke da atika taki zuwa domin asamu abida za'a kaiwa yar uwarki atika daki,da sukayi kutun kutun din da suka raba ki da bello.awal yayi karatu mun ci abinci mu wadata ke kuma kika kari rayuwarki gaba daya a wahalar wanke wanke inba ki manta ba na gaya miki a lokaci ALBARKA NA TARE DAKE ALBARKAR UWA DA UBA,BAZAKI TABA TABEWABA... yasa hankici ya share hawayen da suka cika masa ido nima kuka nake inka dauke awal da amarya da sukayi tsit suna sauraro baba yaci gaba.toh abisa wannan karamci da kika yi mana atine cikin zuri'armu kaf bamu da kamarki,muka mike domin neman na kanmu kurum don mu gina miki rayuwa.mu sayo miki mutunci a idon mijin duk da kika aura.da farko inasan fada miki cewa karfin aikinki da lafiyarki awal ya samu damar yin karatu har matsayin digree na biyu,sani kuma na farko yana kanyin na biyu,tun tuni awal ya samu aiki yana yi a lagos sani kuma yana yi a cikin garin kano abida baki sani ba shine farko fara aikin ki bawan Allan nan N25000 yake bani duk wata a hannu talatu baiwar gidan maimartaba kudin nan baci nake ba tunda dama ni can inada sana'ata,na kuma saba da talaucina don haka wani rayuwar jin dadi dukkamu bai dame muba, dauka nake inbai wa awal ince yasa a banki in hidimar karatunsa ta tashi su dauka a ciki suyi toh hidimar karatun ma daba kullum take tasowaba kuma daga baya suka zo sun daukan alawus na dalibai
dukan su kwana makaranta suke balle ayi wanni zance wahalar kudin mota sai dai abin daza suci, bayan shekara guda kuma bawan Allah nan yazo har nan dakin ya gaidani ya gayami cewa hidimar da kike a gidansa ta karu wai kina girka masa abinci kina kuma kula da yaronsa don haka albashin dayake baki ya ninka shi zai rinka biyan mu N40,000 duk wata ba yadda banyi dashi ba amma ya kafe bazai canza ba,sai na fawwalawa Allah kan cewa aikin naki wata kofa ce ta rahamar Allah a gareni,ya koma biya biyan mu N40,000 duk wata?