← Book details Tuna Baya Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 4 OF 51

Sashe 4

Tuna Baya Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

Ni nasan wani dalilin sanya mani riga?

Ba ruwa ake ba ya taimake ni?

Wanda kuma duk ya taimaki wani ai Allah xai taimake shi shima.

Ya hada yatsun mu, don kar in ciro riga mana ina na san wani dalili bayan wannan?

To amma ni kaina nasan yau na ji ni cikin wani bakon nishadi, ga farin ciki ya baibayeni kamar ance min Goggo na ta warke sumul.

Na linke riga na janyo wata tsohuwar akwatin Amarya na tura, na rufe na mayar.

Washegari Atika kallo na take kaman taga aljana tace ''Atine, jikin ki kamshin Aljannah yake, shin ko kin ga Annabi a barci ne da Malam yace mana ana gani, in anyi dace?

Na yi dariya na bi ta da ''eh''.

Yammacin ranar mun yi ciniki mai tarin yawa, na hada kudi na baiwa Baba, ya tafi Kano.

Washegari da safe nayi wanka na saka atamfata mai dan dan, print ce ruwan bula, ni bana kwalliya sam, ko vaseline in ba lokacin sanyi ba bana shafawa, na goya Jafaru nasa kibiya ina tsefe kaina ina tajewa.

Sani ya shigo, baki har kunne, a duk sanda ya xo min irin haka nasan ya ciyo kudin wani karikicen abokinsa ne, wai xai hada mu, na tsuke duska kuwa iyaka.

Ya samu jijiyar bishiyar dalbejiyar da nake xaune karkashinta ya xauna jikin sa har rawa yake ''wai ke Atine, baki gajiya da tsifar kai?'' Nace ''unh!'' ya lankwashe kai yace ''shin kinsan Bello, Yallabai Bello dan gidan Waxiri?'' Nan ma nace ''unh'' na sake tsukewa, sani ya dabarbarce, yama rasa ta inda xai faro, da gani ba kudi yaci ba yau mutuncin ya gani, ya kare kwane-kwanen sa yace ''kije yana kiranki, Baba yasan da xuwansa, ya kuma ce na gaya miki muddin yaji wannan dabbancin naki, sai na kabari ya fiki walawa''.Ya haura takalman sa ya mike nace '' in dai rigarsa ce da ya ara min,ban roka ba balle a biyo ni har gida a ci mun mutunci, tana nan bari na dauko maka'' Sani ya fice ko saurareni bai yi ba.
[9/24, 9:10 AM] A A Dboy: *_POST BY GROUP OF HYPE HAUSA NOVELS BOOK WHATSAPP 08064400100_
[9/24, 9:10 AM] A A Dboy: Tuna Baya 16 to 20
Yi ba.

Murna kaman in yi tsalle.

Ni kaina nasan, na kamu da son mutumin da ba tsara na bane ta fannin komi, amma Allah shaida na ne kan bani na daurawa kaina ba.

Surutu ne nasan xa'ayi shi a garin Karaye har a gode Allah, oho, xa su gaji su bari ne.

Tun daga xaure nake jiyo kamshin, ina gaba yana kara dosa ta.

Dan farin wankakken hijabi ne a kaina hannayena rungume da riga, na hange shi da 'yan iskan abokan sa, dan tsamirmirin nan da dan gajeren.

Sanye yake da karamar riga da dogon bakin wando mai kauri na 'yan birni, kykyawar fuskar shi tayi kyau a cikin hantsin kamar kullum.

Na kara cuske fuska, a nutse na gaida su fuskata ba anuuri, ita kanta gaisuwar ba din gargadin da Sani yai min ba da baxan yi ba.

Dan tsamirmirin ne yace ''ranki ya dade, Uwar gajiyar mu, Yallabiyar mu tuba muke'' Ba tare da wata magana ba na mika mai riga nace ''ga rigar ku'' sukayi murmushi a tare yace ''bar xancen riga tukunna, nace miki mun xo tuba ne...'' nace ''da kukayi wacce shirka?

Ai ku saraki ne, masu mulki, din haja ko mi kuka yiwa talaka a hanyar garin Karaye, baku yi laihi ba, tunda garin ku ne to amma nan cikin gidan Maikalwa, Kalwa ta daddawane, mallakin sa ne da ya gada tun iyaye da kakanni, babu wanda ya bashi cikin masu mulkin Karaye.

Don haka ba wanda ya isa ya xage shi anan mu kyale.

Ga rigar ku nace'' na dangwarar ta anan na juya abina.

Sai bayan dana dawo na shiga tambayar kaina ''maiyasa nayi haka?'' don me ban saurare su na ji uxurin su ba, ko Ubangiji muna yi mai laifi, mu rokesa gafara ya gafarta mana, balle ni wata tsiya 'Atine'.

Koda yake na nuna martabar Baba na, mai girma ce a gare ni.

Sai dai ina wahalar da kaina ne a banxa; son Bello nake, son shi ke wahalar da ni a 'yan kwanakin nan.

Kwanan Baba uku kamin ya dawo har hankulan mu sun tashi, ya dawo cike da farin cikin raina yayi fari kal don na tabbata Goggo da samu sauki kenan.

Da yamma Baba ya kirani dakin shi,munyi hirarraki da dama game da lafiyar Goggo kamin ya gangaro maganar da ban tsammana ba,
Yace ''Atine naji dadi kwarai da kuka shirya da yaron nan dan gidan Waxiri, domin yaron mutunci ne, d
an babban gida mai ilmin da duk fadin garin babu saurayi mai ilmin sa, wanda in banda ikon Allah, ba abinda xai yi dake, idan kika yi la'akari da matsayin mu na talakawa likis, wadanda basu aje ba, basu ba wani ajiya ba.

A cikin rufin asirin Allah muke daura tukunya bisa murhu, mu daura sittira dai-dai karfin mu.

Allah ya bamu wadatar xuci kuma kowa ya sani, bamu kwadayi, balle ace kwadayin mu ne ya hada mu da su Waxiri.

A jiya yaron nan ya je Kano, ya biya duk basussukan da ke kanmu, ya sayi magungunan da muka kasa saye, ya canjawa Guggon ku asibiti xuwa na larabawa masu mutunci da sanin hakkin bil adama.

Ya sayawa Guggon ku duk abinciccikan da likita ya bukata ta ci wanda ni a rayuwata ban taba jin su ba ma, ya kuma yi umurni ga wata 'yar uwarshi da ke karatu can Kanon kullum ta dafo abinci safe, rana da dare ta kawo mana.

Su xauna muyi hira su xaga da mu gari, yau dinnan Waxiri da kansa ya je ya duba Guggon ku, tare ma muka dawo a motar dan Maimartaba, nan da kwana biyu xa'a sallami Guggon ku.

To mutanen da suka yi maka wannan karimci akan suna son naka, basu kyamace ka ba duk da yadda Allah yayi ka, ai bai dace kaki amsar bukatar su ba da take ta alheri a gareka.

Don haka na gaya masu tuni na basu ke, duk sanda suka shirya su fito ayi aure, waccan solobiyon ma in ta gama ruwan idon ta fiddo daya daga cikin tarin samarin da take tara min a kofar gida, a hada ku lokaci daya''.

Shiru nayi kaina a duke, nayi mutuwar xaune, ina sauraron Babana cikin abinda nake ji kamar a mafarki ko kuwa (almara); an bada ni ga Bello Waxiri?

Abin ma abin tsoro, bayan duk wulakancin da nayi masa?

Shine ya biyo Babana da siyasa irin tasa ya aure ni, ya rama duk wulakancin da nayi musu kenan.

Hawaye suka cika min ido taf.

Buri na na karatun RAINO ya karye ban cimmasa ba.

Buri na na xuwa makarantar boko yaci ruwa shima.

Auren wuri, abinda naki jini a rayuwa ta.

To amma me?

Da wanda na tabbatar ruhi, kalbi, tsoka da gangar jikina duka suna mutuwar so da kauna; Bello Waxiri.

Daya da daya a maxan Karaye baki daya.

Wanda yayi ilmi, mawuyaci ne ya hana matar shi yin ilmi.

Na tabbata haduwar mu da Bello kaddara daga Allah!

Ita kanta haduwar, bata dadi bace, babu wata kalmar arxiki da ta taba hadamu balle kalmar SO, amma gashi har manya sun shigo cikin maganar.

Na tabbata ina son Bello, amma ina shakkar kaunar sa gareni.

Idan na tuna farkon haduwar mu kafana kamar maburgi yace, to mai xai yi dani, in ba yaudara bane?

Yanxu yadda Baba na ya gama saki da al'amarin su Waxiri, wani bayani xan mai ya gamsu?

Bama wannan ba, in nayi hakan nayi butulci wa alkhairin da sukayi wa Babana, suka maishe shi mutum mai darajah cikin su har suka damu da ciwon Guggon mu, wadda bani da kamarta duk fadin duniya, Guggo na fa, Guggo na ka taimaka fa....''.

Na dubi Baba da yayi shiru yana karantar yanayi na.

Kallo daya xaka yi mishi ka fahimci cike yake da tsoron rashin amincewata.

Ni kam koma da wani nufi Bello xai aure ni, na amince domin Babana, darajja Babana da Waxiri yayi.

Su basu kyamace mu ba, me xan yiwa kyama tattare da Bello Waxiri?

Baba ya fiddo ido kadan yace ''Uwata Atine, kada ki bada min kasa a ido, kada ki mayar dani karamin mutum a idon mutanen da suka darajjani, suka martaba ni, suka girmama ni ta hanyar da wani dan adam bai taba yimin ba...'' sai hawaye.

Na rarrafa ga Babana, nayi murmushi, idona cike taf da kwallah, ''na amince Baba, dama ina son Bello, ina dai jiye mana wulakancin gidan sarauta ne, tunda mu bamu da komi, ba wasu bane face talakawan gari''.

Baba yayi murmushi.

Bana gini ban duba filin wurin ba, Atine, baxaki wulakanta a gidan Waxiri ba, in dai kin kasance mai; -Gaskiya -Amana -Hakuri -Juriya -Kawaici -Gudun duniya da kyamar abin hannun mutane.
19.

Ki xama mai bayarwa ba mai karba ba, wannan shine babban makami na xama da kowace irin al'umma, a ko'ina, komi mulkinta.

Talaka kan xamo wani abu, idan yayi riko da wadanna makamai.

Mai mulki kan kaskanta, idan ya rasa wadannna makamai har a darajja talakan da bashi da komi fiye dashi.'' kaina a sadde nace ''Na amince Baba, In shaa Allah xan gina tubalan rayuwata ne akan kalaman ka, ko babu komai, baxan taba tabewa ba na tabbata idan na bi ka''.

Allah yayi maki albarka Atine, Allah ya daukaka ki da daukaka ta buwayar sa'' ''Ameen Baba''. ***********
Shara nake yi, ji nayi an xungure ni, dagowar nan da xanyi sai na yi arba da Goggo na, tsaye da kafafunta, na rude na kidime na yada tsintsiya na ruga na rungume Guggo su Amarya suna ta dariya ta.

Na dubi Guggo duk ta rame, da alamar har yanxu jikin ta da saura, na kama Guggo na xuwa daki har har gadon bunun ta.

Hira ta kaure a dakin na labarin asibitin da aka mayar da Goggo, wai bandakin har da wani inji makale da xaka danna sabulu mai kamshi da laushi ya xubo, a wunin ranar xungur, hirar kenan.
Chapter 4 · 0% Book details