← Book details Tuna Baya Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 45 OF 51

Sashe 45

Tuna Baya Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

Yaja tsaki yace inda mutuwar ne da bai fi ba' ya mike ya zari agogonshi yana daurawa nay hanzarin amsarshi ina tsuke mishi tie hannuna na rawa bansan dalili ba a duk sanda yallabai ke cikin damuwa dimaucewa infishi damuwa,nake jin tausayi na bashi sai ya dago haba na yay mun lallausar murmushinsa yace'ba komi fa yanzu zanje in dawo kodayake ma na fasa dauko kunun muje ki cigaba da yi mun tausa' Wuni guda a washegari na lura yallabai na kin amsa wayar da ake tayi mai akai akai wata ya kashe wata ya kyale har ta tsinke don kanta daga karshe ma ya kulle kwata kwata.

Washegari mun ga text messages har goma da sanyin safiya suna ta shigowa a tare,ina shirin kayanmu cikin trolley katuwa da zamu tafi da ita na rausayar da kai na dubi yallabai yana tazar sumar shi jikin dressing mirrow na dakina ba abunda ya dameshi da wannan mai nacin waya nace 'haba ogana bansanka da wulakanci ba' Yace 'sunan nan ya fita a bakinki inba haka ba zan dinga dalle maki shi.

Nace 'na tuba yallabai amma dai kasan wulakanci ba dadi,don in mu aka yimawa bazamu ji dadi ba?

Yace'in kin ce na amsa sai na amsa ai.

Ya shiga lallatsa waya wai yau ogane ke shara karya,inaji yana cewa jiya tun safe yana dakin meeting da yace zai zo da daddare kuma uzurirrika sun rikeshi,damn too busy,yana nan tafe don gobe zai tashi.

Nace'wai wanene?

Ya dubeni yay murmushin keta yace' wanda kike cewa ina wulakantawa ba wulakantashi nake ba so nake mu tafi mu bar kasar kamin na amsa wayarshi kika takurani na amsa,to so yake ya takura rayuwarmu.

Jikina yay sanyi nace'don Allah abban jawad wa nene?

Yace janar balarabe dango ne shi ke son inje maganar tarewar antin ki.

Na lumshe ido nace'kaje yallabai don Allah.

Yay murmu
shi yace da zucia nawa?

Allah ni da zuciya daya na fadi yace 'toh shikenan Allah Yay miki albarka zubaidah haka nake son ki kasance a kullum wato ki dinga bani hadin kai ina yin abubuwa wadanda suka dace kina dora ni a sahihiyar turba koda ranki baya so idan har kinsan hakan shine daidai don kinga dattijon ya wuce komi a gareni in har ina da iko.

Sai dai rayuwa da mubina sai kin yi hakuri sai kin kai zucia nesa kin santa farin sani ba sai na maimaita maki antin taki ba.

Nace'haba?

In don ni ne wlh zan iya zama da ita menene bata yi min ba?

Amma ba mun zauna a hakan ba?

Zama da anti mubina nace naji na gani,wlh zan iya zama da ita tunda kasan halin mu2m ai sai ka ci maganin zama dashi.

Ya kama baki'Allah zubaidah na?

Na kwantar da kai ina murmushi wlh kuwa yallabai taheer angon mubina da zubaidah yayan faty da abdulraheem,abban jawad!

Ya tuntsire da daria yana cewa'kin ganki bansan sanda dan bakinnan ya bude ba.

Anyway wayonki na bani tsoro zubaidah hakannan ba zan gaji da cewa ba KINA BURGENI!
104...

Koda ya dawo daga kiran Ubangidansa ma ransa a bace yake baice min komi ba nima ganin haka na ja bakina na tsuke.

Can cikin dare yana ta zuga tsaki,ina jinshi nay lamo tamkar mai bacci amma a zuciyata ina ta Allah Ya isa ga duk wanda ya bato min ran miji.

Can anjima ya kira sunana bai zaci zan amsa ba yaji na amsa nan da nan yace'ashe kema ba kiyi bacci ba?

Nace'eh' ya kunna fitila mai haske ya mike yace'zubaidah inason ki fahimci bayanin da zan miki yanzu don ba yadda zanyi ban kuma son mu soma boye ma juna abunda ya shafemu komi kankantarsa.

Ina neman hadin kanki kamar kullum.

Janar ya kirani ya gayamun an maida aurenmu da mubina tunda tuntuni na amsa zan maida ita albarkacinsa da mu2ncin dake tsakanina da wannan family.

Amma na gaya masa a gobe zan bar kasar tare da ke don mu huta gajiyar biki yace ba komi ita mubina zata tare kamin mu dawo nace'a'ah gara a bari in dawo komai zai fi tafiya daidai sai ya shiga rokona Allah da annabi saw ta matsa tana son ta dawo gaban dan ta,kuma ya zaci zai iya nemar wata alfarma a gareni in yi mishi balle wannan kankanuwa?

Balarabe dango Ubangida na ne,shine silar duk wani matsayi da nake kai a yau don haka har kullum nake girmamashi nake darajashi kinsan dai shege kadai ke manta alkhairi.

Tunanin hakan yasa nace dashi na amince ya zartar da duk yadda suke so amman zaman da mukayi a da bashi zamuyi yanzu ba.

Bana jin kaina sai ke don ni da ita dama kar ce tasan kar amma ke sai nake tunanin za a kwareki daga dawowarki ki shiga canjin rayuwa.

Ina gudun bacin ranki ina tsoron duk wani a abu da ka iya kawo mana matsala cikin rayuwar aurenmu.

Mubina tace bata yarda mu yi har wata 3 ba ita tana zaune ni kuma na gaya mata in har zamanta zai takuramin ne,to tay zamanta sai na dawo to amma ga abunda dango yace shine duk na rasa ma ta inda zan bullo ma al'amarin.

Har abada bana fatan Allah Ya nuna min ranar da zan bata maki rai zubyna,domin kina faranta mini kina dada damani irin wanda ban taba samu ba a tsayin shekaru na masu yawa a aure.

Ban taba sanin dadin aure ba sai a kanki babu wani gurbi da zan iya hada sonki dana kowa a zuciyata believe me wlh i'll nvr betray u'kina ji na momyn jawad?

Nace cikin sanyin murya mai kwantar da hankali 'wlh kaji rantsuwa ta 'yan musulmi kenan har raina bana bakin ciki da dawowar anty har kullum ni mai farin ciki ce da duk wani cgbnmu ai ba burgewar mu bace ace jawad ya tashi baisan mahaifiyarshi ba bai saba da ita ba bai san kowa nata ba wannan kwara ne a gareshi ko Allah sai Ya tambayemu.

Akan me zan takura da zaman anti?

A gidanta fa na zo na tadda ita tare da mijinta da dan ta,da dadi ba dadi suna zauna tare na zamo annoba na tarwatsa iyali na aure mata miji.

Shin har akwai wanda aka takurawa tamkar ta?

Babu.

Nasan babu haramci a ciki,amma idan anti bata yafe mun ba,na tabbata bazan taba samun kwanciyar hankali ba.

Don haka ka dawo da anti ba don ni ba ba don babanta ba,sai don kasancewar ta UWAR DAN DA KAKE SO FIYE DA KOWA.

Wata rana jawad zai nemi uwarsa,idan yaji abunda muka taru mukayi mata zai ga beken mu duka,niko mai bakin ciki ce da duk abunda zai bata ran mohd jawad.

Na roke ka ka dawo da maman jawad ta hakika...

Na soma sharen kwallah.

A fusace ya dago fuskata yace ''who tell u?

Wane wawan ne ya gaya maki idan mubina bata yafe miki ba zaki ga farin ciki ba?

Karya ne!

Ba kyamun karya kada ki fara akan wannan shin dama ita ta rike ki da amanar ne?
[11/3, 8:33 AM] A A Dboy: *_POST BY GROUP OF HYPE HAUSA NOVELS BOOK WHATSAPP 08064400100_
[11/3, 8:35 AM] A A Dboy:
*TUNA BAYA*
~BOOK 2~
Tuna Baya2 106-110
106.....

Washegari da safe na shirya cikin abaya mai salki kirar Bahrain na yane kaina da gyalen abayar.

Tashin dare zamuyi don haka naga ya dace in je in ga assha wadda tayi mun waya cewa ta dawo shekaran jia zata zo,nace tay zamanta ni zan zo nace da yallabai zan leka in gaida maman assha da sauran jama'ar da sukayi mani halarci wurin biki yace adawo lapia bayan ya dankare mun jaka da dubban nairori yace in kaiwa maman assha wani abu duk da suna da shi bai dace inje haka ba irin wahalar da tayi a wurin auren mu, nace hakane.

Tom ne ke ja na cikin mota ta wurin awal kirar Pg .506 fara sol.

Nace ya fara biyawa dani shagon turare hakan kuwa akayi.

Na sayawa maman ashssha collection din DESIRE DUNHILL da BOUCHERON ita da hajia hafsi da niyyar in danka hannun ashsha tasan yadda zata yi ta kai mata, mutanen nan sun nunan min kaunar da mahaifiyata zata nuna mun don haka nake son su nima tamkar iyayena.

Aka shiga lale dani a gidansu ashsha,ta fito a guje ta dafe ni sai mama tace 'ke don Allah shashashar banza sai kinji mata ciwo bakya ganin duk surorin mai juna biyu sun bayyana a tare da jikin nan nata?

Ashsha ta sake daka tsalle ta rungumeni mukayi ta juyi kaya kaya tamkar wasu akuyoyi kafin mu dire a daki,mansina dake gefe in banda kallona ba abunda take a ranta ko cewa take Allah sarki mubina lallai taheer yay aure yanzun dole ya mance da ita irin wannan tsaleliyar mace haka?

Na gaida mansina ta amsa a lalace ban damu ba muka afka daki nida aminiyata muka shiga surutun bayan rabo kaman ma kashe kanmu don suru2 tace'wai ya aka kare da uncle bello ne?

Kinsan Allah ranar sayan baki saida wani fitsari ya kullemin mara don mamaki?

Nace'mamaki har kin kai ni?

Ni kam ji nayi kamar an zuremin jini, inda Allah Ya rufan asiri idanuna cikin mayafi suke da kin gansu kwal kwal a waje.

Tace'ni ko sai naga cewa ya saduda ne ya hakura ya gane rashin dacewar hakan duk ya bani tausayi Allah shaida ne kan bello na sonki.

Na kyabe baki nace 'oho masa ni kam ina mai neman tsari da duk wani mai adawa da soyayyata da yallabai kai assha!

Don Allah kiyi aure! (hehe su atine ansan dadin auren) ashe haka auren so yake?

Tay tagumi tana dubana tace'ba sai kin fada ba zubaidah fatar jikinki kadai ta fada komi na jikinki ya fada,kin ko ga wani irin shining da kike daa haske hadi da taushi da fatanki ya kara?

Nace'oh shine mama ke tsammanin ina da juna 2?

Bata sani ba ko wannan watan nayi al'ada assha tace 'to bayan nan fa?

Nace'kai anya zai yiwu?

Kwata kwata fa sati 2 fa kenan.
Chapter 45 · 0% Book details