Sashe 25
Tuna Baya Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read
Ka fiya surutu'' na mike ina shirin tafiya ''sai yaji mana?
Tunda ya shafi Babansa.
Jawad, ka ji bata so na ko?
Wai nayi mata tsufa, tunda na haife ka''.
Ya yi wani iri da fuska kamar karamin yaro, yadda yaron xai ji ya damu sosai.
Saura kadan, dariya ta kwace mani, Jawad, yayi shiru yana hararata, da kyawawan idanunsa.
117.
Nace ''ni kake harara ko?
To gaya min ni da Daddyn, wa ka fi so?'' ''Ni ba ruwana dake''.
Ya koma jikin Babanshi ya kwanta.
Naji ba dadi, na fita raina a jagule.
Na kwanta, amma barci yaki xuwa.
Tom ya shigo da akwatuna biyu, wai tsarabar Jawad ne inji Yallabai.
Na tashi na duba kaya, kayane irinna yaran da iyayensu ke ji da su.
Kayane na 'ya'yan daga wane sai wane, na kara sakankancewa da kaunarda Yallabai ke yiwa Jawad.
Ina hada kayan naji sallamar Yallabai, Jawad a gaba kamar marayan da ya rasa Uwa.
Tausayin su ne ya kamani duka.
Lallai duk matsayin mutum a fagen soyayyah, yaro ne.
Kujera daya suka hade shi da Dan shi, na sunkuyar da kai, na rasa me yake min dadi?
''Ba mu yi fushi ba, mun biyo Zubaidah da kokon barar mu, taji kanmu, gatan mu Allah, kuma Zubaidah.
Mai nema shi ke kasa har kullum, don haka gamu a dakin Zubaidah.
Muna rokonki shin are we accepted?'' Gyada kai kurum nayi ''dama tana xuwar wa mutum sau daya ne a rayuwa''.
Na tuna maganar Ashsha Hardo, gashi nima so ke ci na.
Yallabai ya lumshe ido, kenan farin cikin ya fi gaban kwatantawa.
Ya kannewa Jawad ido, ya nunani da baki ''to yanxu da ruwana dake'' na harareshi nima.
''Jawad wai me Mominnan naka ke shafawa fatarta ne?
Ta xama farar Morocco?
Tayi kyau, tayi fata lafiyayyu?'' Kunya ta kama ni, nayi cikin daki na barsu ina ji Jawad yana fada masa wai Aunty Ashsha ce ta kawo mata kayan shafa.
A kofar dakin ya tsaya, a yayinda na koma can gefe ina jan carbi, wanda in xa'a kasheni, bana ce ga ayar da nake ja ba ''wallahi sai naga abinda ake murxawa.
Don baxan yarda da wanda xai cutar ba.
Ko ya kace Jawad?'' Ya gyada kai yana dariya da jerarrun hakoransa farare kal ''Kwarai Dad, u're quite right!
Ai ni nasan inda suke'' ya soma janyo drawers ya xaxxage tulin kayan shafe-shafe.
118.
Oga yayi mamaki, ya kwashe duka a babbar leda.
Ya daga ledar 'cleansers' din wurinsu Alphat ''clean&clear'' ya fadi a mamakance, ya kara fadi, ''ai bakin naki ne kilin-kiliyar''ya turasu duka a ledarsu ''sai da safenku, karshen wadannan dustbin baxa a sake shafasu ba.
Bakin AREWA, nake son MOMIN JAWAD DA SHI''.
Ni dai bance kanxil ba, ban kuma dube su ba, yana fita na dubi Jawad ''munafiki dan wuta ne inji Allah'' ''yanxu Momi munfunci nayi?'' ''Munafinci ne mana!
Ina ruwanka da abinda nake shafawa?'' Ya kanainaye a jikina na ture shi, ''na tuba Mummy na.
In ya xuba a dustbin, xansa Uncle Tom ya kaini in debo miki''.
''Ni ba ni xaka tubarwa ba, Allah da ya hana munafinci''.
Yayi dagwalo kamar yayi kuka ''Allah na tuba'' na jawo shi na rungumeshi sosai ''shikenan ya karbi tubanka, Jawad.
Domin shi yace mu gaggauta tuba''.
''Lah!
Momona kin ga na manta, yace ga tsarabarki ta Canada, wai sai xamu kwanta xan baki'' ya xaro mani dan karamin kati daga aljihun wandon sa, cikin ire-ien mitsi-mitsin greeting cards din kasar Canada.
Katin cike yake da xanar xuciya guda biyu.
Ganinshi kadai xaki kimanta darajarshi, daban take da sauran cards.
Dan gajeren rubutun ya sanyaya mani, ya faranta mani, ya fiye mani akwatin kaya daya saba yo mani.
'The truth.....
I must confess!
Since you arrived, you've touched and influenced my life dramatically 4 good.
To the extent thay a day without a thought of you, is a dead day.
You have in no little measure helped me to realized my life's dream.
You've made my life rich in a wonderful way.
Taheer.
119.
Ji nayi idona ya wani lumshe a hankali, A!
Wai na canxa mai tsarin rayuwa xuwa mai kyau, KO DAI YA CANXA MANI?
Maganar Maikalwa, Babana ita ke min yawo a wannan lokacin.
''Kowa yace gonar wani ba xatayi albarka ba.
To tashin ce baxa tayi ba!'' Ni kaina nasan gonata, tayi albarka, ta kowanne fanni.
Ilmi masoyi na hakika wane BELLO WAZIRI KARAYE?
*********
Jakunkuna ne da akwatuna Tom ke jera min, tun daga uwar dakina har falo.
Yana dariya yana tafi ''Tine, ashe yau sai kwanan Karaye.
Sai kwana gaban BABA da AMARYA.
Xan ga Ya Auwal ashe?'' Sai naji maganar wata irin banbanrakwai.
Lokaci guda, xuciyata ta soma harbawar farin ciki ''Oga yace ki diba kayansu Baba.
Inda abinda xa'a kara in karo.
Karfe 11:00am xamu dauki hanyar KARAYE''.
Hawaye suka xubo min masu xafin gaske.
Mafarkina na shekaru, me xan yiwa Abban Jawad dinnan in biyashi in ba kauna ba?
Tamkar an tsikareni.
Na fada wanka, a gurguje na kammala, Jawad tun safe da na shirya shi, yana can wurin Babanshi.
Na kira Ashsha, ina cike da doki da murna ''Ashsha Karaye-xani-Karaye-xani, na rasa ina xan sa kaina ne don murna?'' ''Ki bari don Allah.
A!
Gaskiya nima baxa a barni a baya ba, xani inga Sadiya inga Ya Auwal.
Above all, our beloved Amarya da Baba''.
Allah Ashsha da gaske kike?'' ''Na taba yi miki wasa ne?'' ''Xaki iya kwanan kauyen mu?
Da gidan mu da ko fanfo babu?'' ''In naje Tilde yaya nakeyi?
Nima in mun dawo, xaki rakani Tilden, bikin wata cousin dinmu Joda'' ''kiyi sauri to don Allah ina jira'' ''kin fara yiwa me tafiyar bayani?
Kinsan tsarinsa?
Kika sani ko xai daukeni?
Don naga alama Yallabai bai damu da kawancen mu ba''.
''Bari to inje in tambayo shi, haba!
Xai yarda mana''.
Na ruga a guje, sai kuma na dawo agujen, na daura xani bisa rigar wanka, na yafa babban gyale.
A guje nake wallahi, nayi sallama bai amsaba.
Na sake yi da alama baya kusa, Jawad yaxo ya bude.
120.
Ya dareni ''wai Kauye xamu inji Daddy?'' ''Ina Daddyn?'' ''Wanka ya keyi''.
Na xauna cikin kujera, ina kallom tashar CNN dake ta aiki.
Yallabai ya fito, cikin jallabiya fara sol, da farin towel akansa yana tsane ruwa.
In banda kamshin bathrobb dinshi na dunhill ba abinda ke tashi a falon.
''Ga ni meye ake nemana urgently, kamar naci bashi ban biya ba?'' Na kunyata, na muxanta da xaman jiran da nayi, meya hana in koma in dawo, da naji wanka yake?
Wannan jallabiyyan, ya fidda xahirin kira da xatin Yallabai ne.
Har wani lafewa take a lafiyayyar fatar jikinshi.
Yadin 'xeena-gaxar' ne iyakacinta kauri, bakaken gassu ne masu yawa suka rufe kafarshi baki daya tamkar wani balarabe.
Dogo kakkarfan namiji, mai tashen talatin da biyar.
Wanda ya tara dukkannin halittar karfafan maxa.
Barin ingarmar kirjinshi, shike burge Mubina a halittarshi bakidaya.
''Yallabai na... na...dawo..'' na samu harshe na da tangarda a yayin furta hakan ''a'ah ki fada mani, yanxu xamu tafi, nagode da breakfast, a yi min lamurje a cooler.
Tuwon shinkafa, taushe da naman tolo-tolo shine guxiri na.
Jirgi xai tashi sha daya da rabi, don haka ki hanxarta''.
Na mike kaina a kasa, naki yarda in kara dubanshi.
Har na kai bakin kofa, na tsinkayo sautin shi na cewa ''idan munje, da kudin aurena, xan fara tarar Baba.
Mu dawo Abuja a karasa jarrabawa.
A kammala birthday, in cafki amaryata, mai kunya.
Amma ina jin, da ta isa Wellington ko Rio 'de Janeiro (Brazil) xata koma hatsabibiya...'' Ina!
Na kai kofa na fice, Jawad ya biyoni, shekarunshi bai kai ya fahimci me ke cikin xancen Abban shi ba, illah dai yayi dariya.
Ya san tsokana ce yake mani.
Barin da yaji ance 'a cafke' sai ya kara tintsirewa da dariya.
''Aisha Hardo na, ke neman matsugunin xuwa Karaye.
Sabida ingantacciyar kaunar da take mani''.
Haka na rubutuwa Jawad, cikin tafin hannuwanshi.
Nace ya je ya kaiwa Daddy.
Ya dawo rike da wayarshi.
''Wai ki rike xai yi miki magana''.
[10/15, 9:16 AM] A A Dboy: *_POST BY GROUP OF HYPE HAUSA NOVELS BOOK WHATSAPP 08064400100_
[10/15, 9:17 AM] A A Dboy: Tuna Baya 121-125
121.
''Aisha Hardon, ta ci gidan su, nacinta da shishshigin ta yayi yawa.
Kinsan mai yasa na tsaneta?
Sabida taso ta kakaba maki Yusuf D. wani dan tsohon barawon Gwamnati''.
Haka yace mani cikin wayar.
Haushi ya kamani.
Ya xanyi da kunyar Aisha?
Dabara taxo mani, na kira ta nace mata Yallabai yace tayi hakuri ya turo mata da driver, domin yayi 'booking' kujeru ba ita.
Allah sarki Ashshah!
Tace min ba komi itama xata bi jirgin yawo.
Mu hadu a Kano, filin jirgin saman Mal.
Aminu Kano.
Karfe 11:00 na kammala komi na xuba mishi cikin 'cooler' da 'flask' kaman yadda ya bukata.
Tafiyar shi daban da tamu, sabida 'yan rakiyar shi.
Hakanan Yallabai inda duk ya sauke kafarshi nan (escort) din shi xai mayar.
A reception na hango Hardo, jingine jikin karfen bene.
Sanye take cikin english-wears kaman yadda yake a al'adarta ta daura siririm kallabi a kanta.
Hannunta na dama sakale da jakarta helena-ricci yayin da na hagun 'yar karamar waya ce Siemens.
Muka hade da rabi-rabin runguma.
Tuni direba daga gidan Maimartaba ya sha gaban mu, Jawad na gaba mu muna baya.
Mun dauki hanyar Karaye, nake bayyana mata rashin jituwar su da Yallabai.
Tayi dariya sosai tace xata neme shi a Karaye ta bashi hakuri.
Ita dama tun sanda na gaya mata Oga ya hanani samari, ta san da kyar in ba kamu yake wa kansa ba.
Da kyar in wanna Ubangidanci bai koma something special ba.
Mun iso Karaye, kimanin 4:00pm.
Na umurci direban ya saukemu dai-dai gidan kakana Liman.
Bana son su Amarya su ji wani kugin mota.
Sai dai kawai su ganni, kamar daga sama.
Nayi mamakin yawan akwatunan da Ashshah tasa direba ya sauke, bayan na wurin Yallabai.
Nayi mata magana tace Mamarta ce tasa ta hado su wai taba Amarya, da Atika da nake yawan bata labari.
122.
Duk yawan sauye-sauyen da garin Karaye ya samu sakamakon sabon 'chairman' mai aiki tukuru, jan gwarxo Honourable Sunusi Atta A karaye.