Sashe 29
Tuna Baya Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read
Yaqi 'yar'uwarta yaje inda za a halakashi,to su duka biyun taga wadda zai aura.da ita da yayarta fulani suka tashi tsaye nemawa bello makarin asirin lami batare da sanin mazansu ba.sune da aike har chadi,hakanan fulani mace ce mai tsananin ruqo da addu'a da tsayuwa akan addininta,tashiga yima bello roqon Allah baji ba gani,itako hajia rabi ta qarfi da yaji tamiqe da son raba bello da atika.duk abinnan da ake yadda zaka tabbabtar mummunan asiri akayima bello,bai taba ganin atikar ba banda ranar da suka fara haduwa da atine,baikuma taba neman ya gantaba,illah sunanta a bakinshi rambadadan kamar shi yarada mata.
14.....
An daura auranshi da atika ranar asabar da niyyar sai ya koma jos karbar takaddunshi na inda aka tura shi qaro karatu yadawo sannan su tafi england tare. dirar shi a jos kuma yariqa tambayar kanshi meke damunshi ne zaice bazai auri atine ba, bayan ita daya zuciyar shi da ruhinshi ke so da qauna?sai alokacin ya tuna wai andaura auranshi da yayarta atika dabaima taba ganiba,hankalinshi yatashi yarasa abinda kemasa dadi,yatuno sallamar shi ta qarshe da waziry inda yace to bello, hankalinka ya kwanta ka auri atika,amma ingaya maka gaskia hakkin 'yar malan mamman bazai taba barinka kwanciyar hankaliba.a daddafe yayi abinda ya kaishi jos yadawo qaraye, kai da ganinshi kaga wanda damuwa da nadama mara iyaka yayiwa ligi- ligi, tamkar ba ango mai shirin daukar amarya sweet 16 ba.
Da daddare a turakar mahaifiyar shi hajia rabi ya kwanta cikin kujera kamar yayi ihu.tayi banza dashi sai data mula tace uwar amaryarka nata aike, baka je ba kun gaisa da atikar takaba.amsar daya bata tabata dariya,wai tambayarta yake wacece atika? tace ah!
Matarka mana da aka daura muku aure sati daya daya wuce.
15.....
Sai ya samata kuka,waishi baice dasu su daura mishi aure da kowa ba sai ATINE. ya zasu tagayyara mishi rayuwa?suna sane da irin qaunar da yake ma atine?
Tausayi ya kama ta, kinsan mahaifi, ta tabbata lalle bello yadawo bellon shi alokacin da bakin alqalami yariga ya bushe.sai ta kira waziry yazo yaga halin da bello ke ciki yana kuka riris kamar ba bello ba duk akan baice su aura mishi wata ba atine ba.bayan zagi ta uwa ta uba da waziry ya sauke mishi kwando kwando bai gaya mai wata kalma mai dadi ba.cikin dare ya rubuta takardar saki uku cif ga atikar inna lami. yana ganin wannan hanya ce mafi sauqi da waziry zai sake nemo mishi auren atinen shi. wayyo! ya qara dagula komai,domin da mallan mamman ya kawowa waziry takardar sakin da bello ya aikama atika waziry asumar shice ta tashi na baqin cikin da bello ke guma mishi.yace ya tattara yanashi yanashi ya bar mishi gida babu irin ban baki da roqon da mahaifiyar bello batayi ba na yagane bello bayin kansa bane duk wadannan abubuwan dayake yi amma ran masu mulki ya baci,don cewa yayi idan bello bazai futar mishi agida ba ita uwarshi zata futa. bello na kuka yace innar shi tazauna shi zai futa.ya kwashe kayanshi yakoma dakin taheer dake gidan mai martaba,wanda a lokacin shi taheer yana washintong aboki nagari muhd jos,yarabu dashi alokacin dayake tsatsanin buqatarsa, ya san da yana nan al'amuran sunzo mishi da sauqi,
16.....
Koba komai zai shawo mai kan atine da babanta da waziry kanshi daya fahimci bayin kanshi bane. to amma muhd yana lagos alokacin da anininshi na farko a aikin soja gashi ko numbar wayarshi baya da ita,innar shidaya data rage mashi a dunia ta rasu,bata tsaya taga matsayin da muhd jos keson kaiwa a aikin sojaba,Allah kenan. ya nemi yayanshi taheer a waya,ya zayyana mishi duk halin dayake ciki,tare da neman shawarar mafita a gareshi,taheer yace shi don me yanemi aure tun farko bai gama karatu yafara aiki ba?sai yace SO baruwanshi da wannan, SON ATINE,yafiye mashi komi muhimmanci a rayuwarshi.shima taherr din don bai taba fadawa a son mace bane,taheer sai yayi dariya yace bama zantaba insha Allahu me ake dashi,tunda ko zaisa mutum problem dashi da iyayanshi?taheer yace naso inga wannan atinen inga shinme yadauki hankalinka gareta haka brother?
Abin mamaki kuma illiterate?imagine:
Ya runtse ido,jin zafin taheer yakira atinen shi JAHILA .sai yace shawara ba cin fuska ba yalla'bai taheer ya tuntsure da dariya yace kayi haquri bawai ina nufin haka bane,inadai mamaki ne. amma inaga kabi takan mai martaba na tabbata zai fahimceka fiye da baba waziry,itama kuma atinen kanemeta kabata haquri,inhar tana sonka nina gaya maka zata fahinceka bakuma zata kullace kaba.to bello shawarar taheer yabi, sai da aka kwana biyu ya doshi sarki da alfarmarshi na asake nemo mishi auren atine, yana kuka da idanunshi da alqawarin wannnan karon bazai basu kunya ba,su ceci rayuwar shi su tausaya mishi,inya rasa atine baisan yaya rayuwarshi zata kasance ba. mai martaba yayi murmushi,karo na farko da bello yanemi wata alfarma agaresa yagaza yimashi,yace wai ido da kunya don mallan mamman yana talaka bazai dunga mai yawo da hankaliba koba komi ya girmeshi inya qara dosarshi da wannan magana yazama dattijon banza,da kyar in mutuncinsa bai zube daga idanun talakawan shiba.
Sabida haka inhar muhd bello kanason albarkarmu atare dakai, ka haqura da atine! ka haqura da atine!!sai da ya maimaita mishi wannan har sau biyu.
18....
Bello yayi kuka kukan da wani namiji bai taba yiba a rayuwarshi wai don yarasa mace,kukan dabai taimaka ba ko kadan wajen rage azabtuwar da ruhinshi keyi da qaunar atine.jiyayi ya tsani kansa,ji yayi rayuwarshi batada sauran amfani,to amfanin me gareta batare da atinen daya kallafawa rai ba? meye matsayinshi a zuciyar atine yanzu? (mayaudari) in fact!
Har abada ma zata sake son shi?inya tuna haka sai komi ya dagule mishi,yashiga juyi da watangaririya akan gado, har saiya fidda hawaye zaiji sanyi sanyi. ranar da hawaye suka zuba, tamkar zararre yake komawa. inda duk ya diba cikin dakinsa a kowace kusurwa atine yake gani tana cewa 'sunan ka dan qaraye mana?
Idan ya mike ya isa gareta saiya ci karo da bango,ya dunqule hannu ya kai mishi duka ya rikice da kuka.rannan a halin fulani ta riskeshi ,ya riqe kirjinshi yana ta juyi da kiran sunan atine,tausayi ne yakamata ,
Ta zauna nasiha mai ratsa jiki kan muhimmanci yadda da kaddara kuma biyyaya ga maganar iyaye don samun rabo kyakkyawan rabo a gidan duniya da lahira ga badaya.sai yace wai shi kirjin shine ke ciwo,ji yake tamkar zuciyar shi ta tsage, yayi ya daina ji ya kasa.sai tasa habar mayafinta ta share hawayen da suka cika mata ido.
19......
Wai duk kwalisa irin na bello,bellon da bai barin ko gashin baki tare da shi,amma shine ya koma haka duk kasumba babu kyawun gani?wai yau bello ne da kaya a cukurkude,bellon da ko karin hular shi d
aban ne da na sauran maxa!ta tausaya mashi iyaka.da kanta ta samu waziry ta nuna mishi matsalar bello bata ayi fushi da shi bane. lallashi da ban baki yake nema,yace shima daga baya yayi tunani,tuni ya yafemishi,amma aurene bazai kuma nemo mishi ba ko xai mutu ba auren.
bello yasan babanshi kaifi daya ne, daga ranar karaye ta fitan mai rai,ya tafi ingila shekaru ukun da aka tura shi.acan ne suka shirya da muhd jos. inda wanda yasan azabar son da bello kewa atine to muhd jos ne don kullum suna tare,bacci wanna daki daya suke yinsa,duk hirar bello atine, duk rabin zancesa ATINE ne,amma ya alqawarta ma ranshi ya hakura da ita don mutuncin iyayen shi a idon karaye,kamar yadda suke fadi lokacin da taheer yafara aiki a abuja yace da bello tunda maganar ta kare toh lallai ya auri fatima ko don ya farantawa iyayensu, wayyo! bello bai tsallake maganan yaya taheer, ina! kwandala wannan da zai batar haka kawai ko ta fannin karatun shi TAHEER ne,
20.....
ya daukewa iyayensu hidimar karatun kannen shi duka, musaman shi bello da yake dan gaban goshin sa.
A lokacin fatima kammala diplomarta a bayero. duk wasu hidimdimumshi a ingila taheer ne,ko sadaki bai bari kwandalarsa ta yi ciwon kai ba kamar ba kawarsa da suke ciki daya zai aura ba. to shi ko shegene yace bai son kanwarsa sai wata daban atine?
Sai dai fa wannan shine bakin cikinsa na karshe a rayuwa,don ya tabbatar yarasa atine har abada!aurenshi da fatima da fari kamar ba aureba za'ace,don second, minti, awa ko dakika bai wucewa bello bai ambaci ATINE BA. sai gata wai yau a matsayin matar da yaya taheer zai aura?
**********
Bello Waziri tunda yaji zance Yayansa Taheer ne zai auri Atinen sa nanfa hankalisa ya tashe gaba daya ya birkice tamkar mahaukaci, suna dakinsa na gidan mai martaba shida abokinsa muhammad, muhd shine mai tausarsa akan yayi hakuri ya danne zuciyarsa shi kuma ya dage akan bazai bari wani ya aure masa Atine ba, muhd yana nuna masa irin halaccin da taheer da iyayensa suka yi masa baikamata akan mace ya rufe idonsa ya manta alkhairi ban amma ina sam Bello yaki yarda da wannan batu na abokinsa, hardai Muhammad daga karshe shima yaji haushi yace to
[10/20, 10:27 AM] A A Dboy: *_POST BY GROUP OF HYPE HAUSA NOVELS BOOK WHATSAPP 08064400100_
[10/23, 8:00 AM] A A Dboy:
*TUNA BAYA*
~BOOK 2~
Tuna Baya2 21-30
21...
"Badani za ai wannan dibar albarkar ba.tunda kai baza a baka shawara ka dauka ba,tokayi duk abinda kadama .'do whatever you want!
Sai dai nagaya maka gaskia,...abinda aka yishi cikin fushi sai anyi nadamar aikata shi.wannan cin fuska ne,yaya kake behaivng as a lunatic?
Zan tafi, kayi duk rashin mutuncinka kai kadai amma banda ni..:.......................
Kai muhd, bahaka ake yi ba nima nasan yarinyar ce atinen bello ya npema. abinda yasa ban ce komai ba don banji bello yaqara yin zancen ta ba.tunda haka ne ku kiramin shi baban jawad!
Gabadaya suka dube ta, fulani ce,mahifiyar su yallabai.ashe tun dazu tana tsaye tana sauraron su kunya da nauyi sun lillibe bello, shi kanshi ya san baiyi dai dai ba.to amma ya zaiyi?ya zaiyi?hawaye suka zubo mishi sharrrr.......suna diga tafin kafar muhd jos.muhd ranshi yayi masifar baci,kamar zaiyi kuka yace
"Ranki yadade kiyiwa Allah kiyiwa darajar annabi,kada kishiga maganarnan.in bello na hauka kowa ma sai ya haukace?
Idan har kika gayawa yallabai komi zai dagule,maganar auren Zubaidah ta wargaje.......
22.....
Nizan iya rarrashin bello.fulani tayi murmushi muhammad ka san SO?