← Book details Tuna Baya Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 47 OF 51

Sashe 47

Tuna Baya Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

Nigerian Embassy ta kasar ce tayiwa yallabai masauki a wani estate na baki wai shi Betna Guest Estate,gini ne samansa har kasansa ruf.

Akwai dakin barci guda 2, bandaki 2, balcony wato baranda a saman bene sai katoton kicin da mota da direba ko muna bukatar zuwa wani wuri.

Muna ajje jaka sai shower daga nan kuma sai bacci da mukayi a zaune cikin kujera cikin wani irin luntsumemmen gadon da ban taba tsammanin akwai a dunia ba.

Bamu muka farka ba sai karfe 2 na rana shi din ma kararrawar kukun gidan ta tada mu mai nuna ya kamala abincin rana.

A gaggauce yallabai ya dauro alwala nima hakan muka bada faralin sallar azuhur.

Kamin mu kammala da wanka kuku ya jere komi bisa tebir,a yatsine yallabai ya shiga budewa yana yamutsa fuska alamar ba wanda zai iya ci a ciki.

Yace'bari in je hotel ko zan samo African Food ke sai kici wannan din kamin in dawo ba dadewa zan yi ba.

Nace'toh' suka fita shi da direban da ke waje.

Fitarsu keda wuya na janyo jakata da muka zo da ita na soma sauke kayan girkin da nasa Tom ya hada mun waje daya nayi kicin nan da nan na tada tuwon semovita da miyar agushi,kukun jar fata ne yayi ficewarsa ya bani wuri musamman daya fahimci bana bukatar taimako.

Na bude firji na tadda duk abunda nake bukata wato ganye iri iri da nama nau'i nau'i har dana alade,na ware shi cikin shara ba don na san shi ba sai don kowanne nau'in nama da sunanshi makale jikin dan karfe a kasanshi,na bararraka farfesun dawisu na juye a filas kana danwaken fulawa da mai da maggi da yankakken nunannen tumatur jazur na hada salad da waken gongoni,salad cream da sauransu,kana lemun da na matse daga ruwan tuffa zalla,na kara suga kadan da flavour nasa 'yar kankara na jere a dardumar tsakiyar falon bayan na shimfida ledar cin abinci.

Nay kwaliyya na mike cikin kujera ina jiran yallabai.

Bashi ya shigo ba sai karfe biyar na yamma barci ya soma fizgana kadan kadan,ya russuna ya sumbaceni a kunci nayi harr da idanuna yace'Allah sarki momin jawad na tafi na dade ba tare da niyyah ba gashi ban ma samo abunda nake son ba amman na kawo miki abinci mai dadi wani old frnd of myn ne na gamu da shi a hanya ya rikeni,suna nan zuwa shida matar shi da daddare.

Na mike zaune na bude ledodin daya bayan daya aje bisa tebur,na shiga fiddo foil paper da aka nannade wani irin abinci,haba malam!

Yawuna ya shiga tsinkewa na lashi tausasan labbana da halshena,ya tuntsire da dariya yace'kinsan sunanshi?

Na yarfar da hannuwa alaman oho!
[11/3, 8:35 AM] A A Dboy: *_POST BY GROUP OF HYPE HAUSA NOVELS BOOK WHATSAPP 08064400100_
[11/3, 8:36 AM] A A Dboy:
*TUNA BAYA*
~BOOK 2~
Tuna Baya 111-115
111....

Yace'shi wannan da kike gani kaman cakulet nama ne suka dandake ya koma haka ana kiranshi flamed grilled rebeye' shi kuma wannan shine 'guiltless grilled salmon (kifi ne) nace kifi salmon da nakejin labari?

Yace ki ci bakin ki zai gaya maki.

Ina soma taunawa naji tamkar kunnena ya fice ban kara bi ta kan yallabai ba.

Ina tunanin gyambon ciki(ulcer) ya kamani sbd yadda nake cin abinci a dan tsukin kamar hauka da kwalama kamar sabuwar mayya.

Nayi mai nuni da ledar dana shirya mai abinci da yatsana sabbab,ya matsa ya soma bude dishes daya bayan daya ya shiga girgiza kai cikin mamaki kamin ya juyo ya jinjina mini yace'wat a surprise!

Shin wai ke mai yasa kike da ban mamaki ne?

Na lumshe ido a cikin murmushi 'ban mamaki har an fika baban jawad?

'Toh ai ke din ce,ke din ce zubaidah wata irin mace mai yin duk abunda zai sa mu2m yasha mamaki.

Ya nade hannun riga ya zauna bisa kilishi ya soma kwasar irin garar da yake so nima ina kwasar tawa,lallai ra'ayi iri iri ne shi kuma haka Allah Yayi sa?

Na lumshe ido cike da sha'awar komi nashi ina mai rokon Allah cikin zuciyata,ya cigaba da bani iko da lafiyar da zan cgb da farantawa taheer har zuwa ranar da muka daina numfashi.

Karfe 8 na dare ina kwance gefen gado inata kallon yallabai dake dressing sassauka cikin farar shirt (DKNY) da bakin wando(tokyo) yay wani irin fes da shi kai ka ce saurayi ne dan shekaru ashirin da biyar komi nashi mai ban sha'awa ne, sai na mike cikin nutsuwa na amshe shi.

Ina fesa mishi turare yay murmushi yace thnk u na shirya nima cikin wasu Pakistan masu ruwan madara kirar india,nay lullubi da yalwataccen mayafin kayan kai kace indiyar gaske ce yace'u look fresh nd beautiful,ni na rasa shigar da tafi maki kyau zubyna,ko don ina sonki ne?

Nace'umh' Adaidai lokacin da kararrawar kofa ta soma kara yace'mu2mina ya iso kenan' Mukka rankaya a tare na bude kofar.

Baturen dogone matarshi 'yar gajera da 'ya'yansu biyu duk mata,suka rungumi juna shi da yallabai itama matar ta kama hannuna a haka muka zauna cikin kujerar reception wadda ta kasance leather seat,farare sol yace da baturen'meet my bride Zubaidah,zubaidah wannan shine Mr.kelvin abokin kasuwanci na,yana daya daga cikin mutane hudu mamallaka kamfanin takalman mu dake Rome (italy) da matarshi Susan dukkanninsu haifaffun Brazil ne, sun zo ne musamman don ke,so ga susan nan,susan ga zubaidah na baki amanarta cikin wata guda da zamuyi honey moon a kasar ku. (yana magana cikin nau'in turancin da kasar ke amfani).

Susan tace 'Zu- bei-dah u're highly wlcm 2 our beloved country.

Muna fatan honey moon mai dadi a gareku cikin birnin Rio de Janeiro.

Muna masu farin cikin gayyatar ku dinner gobe a gidanmu, ko kelvin?

Na kamo hannun 'ya'yanta ina tambayar su sunansu,toh daganan sai hira ta barke.

Basu suka bar gidanmu ba sai karfe goma na dare, mukayi masu rakiya har gindin mota.

Washegari da karfe tara na dare Kelvin ya zo ya daukemu zuwa villa dinsu,muka ci abincin dare tare dasu.

Bayan sati biyu mun gama wasttsake gajiya nida susan muka soma shiga gari tana nuna min wajeje masu ban sha'awa.

Shigata 'safe snorkeling' na daga cikin abubuwan da bazan manta a zamana na kasar ba,domin abu ne mai hatsarin gaske can kasan ruwa,saidai alhmdlh mun fito lafiya.

Cikin sati uku kacal harshena ya sarke da turancin Brazil da nake samu a bakin susan haka fatar jikina gabadaya ni kaina nasan na kara gogewa fiye da da.
112....

A cikin watan gabadaya nida yallabai babu komi a gabanmu daya wuce barje gumin soyayyar mu da ibadodinmu sai ko yawon bude ido.

Wani irin sheki da cika da na soma yi ba yallabai ba har ni kaina abin ya tsorata ni.

A yau ba muje ko'ina ba muna falo,muna kallon shirin film din America na (around d world in 80 days) wanda jackie chan da steve coogan ke gabatarwa.

Ya dubeni kuri yace 'na dade ina zargin jikin nan naki zubi, ko aiki na ya samu karbuwa ne?

Ya dace muga likita koko sai mun je Wellington jibi?

Nace' susan ma haka tace amma ni ina al'ada ko shekaranjiya nayi wankan sallah.

Yace toh wannan farin fa kau da kike na menene?

Ban yarda da kayan shafar nan da susan ta sa kika sake ba,kwaso in gani.

Nayi dariya na mike na kwaso kit dina na dire mishi, yay dube dubensa daya saba bai ga wani sabon abu ba yace'ke ban yarda dake ba Allah dole a gobe mu ga likita.

Nace'duk yadda ka ce maigida haka za'ayi.

Washe gari munga wata kwararriyar likita wai ita Dr.anna Branthwaite ta dubani thoroughly tace ita bata ga ciki ba.

Yallabai yay dumm!

Kamar an aiko mai da sakon mu2wa yace'toh canjin jikin fa?

Komi nata ya canza ta kara haske kuma ta kara girma sosai.

Sai ya baiwa likitar dariya nima na murmusa tace'ya danganta da sauyin da ta samu na abinci da ruwan sha da hu2,koko ince albarkar kasar mu ta amsheta.

Duk mukayi murmushi.

Mun bar Rio de Janeiro zuwa Wellington ranar lahadi,hakika nida susan munyi kewar juna ba kadan ba,tayi alqawarin zuwa 9ja musamman domin ni har kuka tayi lokacin da zamu shiga jirgi.

To a Wellington a hotel muka sauka hakannan rayuwar bata canza ba,soyayyar ce dai ziryan da yawuwwukan bude ido.

Kar kiso kiga zubaida a wannan lokacin ba shakka ta zamo hatsabibiyar da ogan ta ke tsoro da kyar in bata mance yadda ake daura zani ba.

Jikinta mulmul fatarta kamar ka taba jini yay tsartuwa sabida tsabar hu2.

A dan tsukin kuma na koma lalaci,haka karfin da nake baiwa abincin yallabai duk sai ya raunana.

Komi nasa a baki na babu taste ina tsammanin abincin su ne ba dadi sai na daure na shiga dafawa da kaina duk da haka bata canza zani ba.

Na lura a dan tsukin yallabai na kebewa yay ta hira a waya yana kyalkyatar daria abinsa.

Rannan cikin kunnena naji yace'hakuri zaki kara mubina ni kaina duk hankalina yayo kanki to amma kinsan dole nida ke mu hadu mu dinga tarairayar zubaidah don anan din ma ba cikakkiyar lafiya ce da ita ba wai komi taci bata jin dadinshi balle mun komo wadannan asibitocin namu marassa kula?

Nakejin wani abu ta gaya mishi naji yace'a'ah dukkanmu bama tsammani don an dubata a Brazil sun ce babu.....

Can anjima kuma yace eh toh hakan za'ayi nagode da shawararki don Allah ki kara hakuri muna nan tahowa cikin watannan in Allah Ya yarda.

Ji nayi kaina ya shiga juyawa wani abu ya zo ya tokareni a kahon zuci,NAMIJI...sai a bar shi da ban takaicinsa.
113....

Wato duk inda suke sunan su daya,'yan uwan juna ne halin su daya.

Nayi daki bana ko ganin gabana na zauna bakin gado nay tagumi sai hawaye sharr!

Yanzu ni bani da sirri kenan sai anti tasan yadda tai ta kalallameshi ta ji,wai har cikin ma in ina da shi sai an ji,to idan ma gulma ce kuma zamannawa ya tsole mata ido kowa ya murza kanbunnashi na ga mai dawo mata cikin watan wai shi yallabai baisan kaidin mata bane?

Ya karaso yana cin biscuit'digestive' ya zauna dab dani ya sauken tagumi yace na tsani ganinki cikin tagumi,any matsala?
Chapter 47 · 0% Book details