← Book details Tuna Baya Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 23 OF 51

Sashe 23

Tuna Baya Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

Daga can sassan Yallabai, 'yar karamar na'ura mai kama da karamar talbijin, mai nuna masa wanda duk ya shigo ko ya fita cikin gidansa, haka in baya nan, xata dauka in ya dawo yayi rewinding ya gani.

Ya hasko mishi Peter na jerawa bakin Aunty lemuka da kayan tande-tande, bai taa xaton xagewar Mubina har ta kai ta shigo mishi da abokan cinikin ta gidan auren sunnarsa ba.

Inda duk ranshi yake, in yayi dubu ya baci, dama wai mai hakuri, bai iya fushi ba.

Mubina ta fito daki da takardu a hannu, sai ganin falo tayi wayam.

Ta leka ta taga, sojoji ta gani na ball dasu, har suka fidda su kofar godan ta.

Ta san ba yin kansu bane, suna a bisa umarnin Ubangidan su ne.

Ta ji haushi, amma ai fushin fari ba nata bane.

Ta tuno rayuwar su da Taheer yawon amarci birnin Toronto.

Da yaga wani abokinta sun gaisa ya sambace ta.

Ita da abokin ya hada ya dinga tamaula dasu a harabar hotel din, kadan ya rage auren sati biyun ya tungule, sai da Alhajinta yayi masa kuka.

To wannan taci sa'a kenan da ba'a hada da ita ba.

Ita wannan ba shine damuwar ta ba, abinda ya dameta kawai, yadda xa'a dinga nunata a Bankin su ana mijin ta da take takama 'kidahumi ne'.
[10/8, 5:35 PM] A A Dboy: *_POST BY GROUP OF HYPE HAUSA NOVELS BOOK WHATSAPP 08064400100_
[10/15, 9:14 AM] A A Dboy: Tuna Baya 106-110
106.

Hakannan wannan tamkar baraxana ne ga shirin su da Mansina, sai dai tasan Taheer sarai mutum ne mai tsananin tausayin mace, musamman in yaga tana kaskantar da kanta.

Da wannan ta samu kwarin gwiwar xama ta fece kwalliya, ta cika cikinta da tsatsibe-tsatsiben kayan da'arsu 'yan duniya.

Kwalliya ce da take ganin ko xaben Miss Nigeris ta shigo da ita ba abinda xai hanata lashe xaben.

Wata riga ce da ko a turai ba'a ko'ina ake samunta ba, sai a wani boutique dake cikin birnin Beijing din China, da ta ba Yayanta Yahai dake karatu can sautu.

Wuyanta ya rufe har saman wuyan mutum ruf.

Hannun kuma an wani irin ketashi tun daga sama har xuwa 'armpits' din mace.

Tsayinta iya cibi ne kawai, laushi gareta tamkar kirar (Romania) tasa wando ya taho a matse daga sama ya bude kadan daga gwiwar har xuwa kasa.

Ya sha ce mata bai son kwalliyar ixgar dokin da take mishi don najasa ne, don haka ta hade shi cikin wani tafkeken ribbon mai ciki, kunnenta da wuyanta ta kawata shi da fashion na garari, wato majoricca-pearl, ta kawo turarukan ta duka sexies ta bulbula.

Ana taku tamkar ana tausayin kasa, aka nufi sassan Daddyn Jawad.

Shi har yayi shirin kwanciya, ya yi nafilolin shi ya kare, yana daure igiyar pyjamas dinshi, ta danna kararrawa, ba tare da jiran ya amsa ba, ta dannan kai, abinda ya tsana kenan ''wai ke bakya sallama ne?

Annabi (SAW) ya ce; mafi rowarku shine wanda baya yiwa jama'ar musulmi sallama.

Kullum ki danno min kai ba sallama, ance maki ni kafiri ne xaki ishe ni da kararrawa.
107.

Ta langwabar da kai ta rausayar da 'yan idanunta ''kayi hakuri Taheer, baxan sake ba''.

Tun daga nan ya gane take-taken ta, tunda har ta bashi hakuri, tana wannan lallankwashewar shegiyar tata ta kawota.

Ko dai shi ake so, ko kuma wani dalili nata na daban.

Xa ko tasha mamaki, don shima yanxu kan mage ya waye, ya daina tolerating iskancin banxa.

Ya bar ta nan tsaye, yayi light-up yabi lafiyar ni'imtaccen gadonshi, ya dauki remote ya karo karfin room heater.

Kasancewar sanyi yayi nisa kwarai da gaske, farkon watan April.

Barci mai dadi ke dibarsa, xuciyarshi cike da tunanin hanyar da xai bullowa 'yar yarinya Zubaidah, mai tsananin kunya da kawaici.

Ruhinshi ke hasko mishi ranar da xai mallaki Zubaidah Uwar Jawad, a wannan katafaren gadon da ya narkarda dalolonshi amma bai taba samun nutsuwa a kanshi ba.

Cikin shekarun shi masu tsayi, da aure sai shirme, sai fitsara, sai rashin kamun kai.

Shi dai yana da yaqinin Zubaidah xata xam mai nutsuwa agare shi.

Ya tuna a yau, taki yadda ta dauki Jawad a jikin shi gudun haduwar fatar jikinsu.

Shi ko tashi matar tun kamin a yi auren take nuna mai kulaficinta a fili.

Ba don ya kasance mutum wanda yafi karfin xuciyarshi ba, da Jawad yanxu Dan titi ne.

Yayi Allah wadai da tarbiyar da Mr.

Dango, yawa su Mubina dasu Mimi.

In ba don kaddara ba!

Me ya kai shi hada xuri'a da Balarabe Dango?

Ji yayi ta rungume shi ta baya, ta soma magana cikin muryarta mai kama da an shaqeta.

''Taheer, ina ganin lokaci yayi da ya kamata mu MAI DA BLACK KARAYE.
108.

Iyayenta suyi mata aure, tunda Jawad ya girma xan iya kula dashi yanxu, tunda kaga ba xancen kashi da fitsari, ba xancen goyo da bada madara.

Ajiye baligar yarinya kamar wannan a garemu bai dace ba.

Ka duba fa ka gani ko su Tom na iya lalatata!

Mu xo muna jin kunya, ai gara ayi abi lokacin da ya dace.

Sai muyi mata kyauta ta musamman, ko 'yar mota ce da 'yan kudi, a bawa kauyawan iyayenta, kuma ita ma kanta na lura, ta matsu ta ga iyayenta, ko ya ka gani?''
Ta fada tana kara shige-mishi.

''Kai wannan yarinya, ba dai rainin hankali ba''.

Ya fadi maganar a xuci ne, bai san har ta subuce, ta fito ta shiga kunnen ta ba.

''Dama nasan abinda ya kawo ki kenan?'' Ta kara narke mishi ''bayan wannan, wata da watanni, ina xaman jiran mijina ya dawo, ai dole in nemi hakkina na aure ko?''.

Yayi murmushi, ya mike gabadaya ya sauka bakin gadon, ko kadan tarkonta bai kamashi ba.

Lallai ne da aka ce bacin rai ke danne komi.

Ya girgixa kai cikin matsanancin takaici ''Taso-taso nan Mubina''.

Jikinta a bala'in sanyaye, ta xaro kafafunta ta xauna gefen gadon, kusa da shi.

''Hakkin aure kika ce ko?

To a gaskiya, in gaya maki aurennan, aurennan namu da gyara a cikinsa, a addinance da al'adance.

Shin ina kika taba ganin masu rayuwar aure irin namu?

Addinin Musulunci ya sanar damu cewa idan ma'aurata suka doshi akalla watanni ukku, basu kusanci junansu ba, haka kawai, ba wani dalili, to sai an gyara auren, domin kamar ba aure ne tsakaninsu.

A bar wannan xancen, don ni bai dameni ba, ba shine a gaba na ba.

Maganar da kika yi, na wadda kika kira, Black!

Wadda ainihin sunan da Ubanta ya rada mata , ZUBAIDAH!

Kin yi gaskiya, akwai abin dubawa a ciki.

Dama na dade ina tunanin abin, don haka ne gwanda da kika tunasar da ni.

Zubaidah ta isa aure kwarai, shekaranjiya dana lissafa ya kama nan da wata uku xata cika shekaru ashirin da daya.

Ta xo mana nan shekarunta goma sha uku, na kai ta Primary tayi shekaru biyu ta xarce babbar makaranta daga aji biyu (JSS 2), a yanxu tana shekarta na karshe.

Bai fi wata uku ba xata xana (Secondary School Certificate) din ta.

Allah ya bata mijin aure tuni, da ta kammala xan shirya masu birthday a can KARAYE, ita shekara 21 Jawad 'seven'.

Idan xaki muna maraba da ke.

Harma kawar ki, data fi mijinki muhimmanci a gareki, MANSEENAH IBRAHEEM HARDO.

Xancen su Tom, kada su lalatata!

Allah ya kare, wannan yarinya mai sanin darajar kanta, addininta, iyayenta, mutuncin ta na talaka, wanda bai aje ba bai ba kowa ajiya ba.
110.

Ta yarda ta saida mutuncinta ga KIRISTOCI, tayi shiru bata gaya min ba.

Kuma in gaya maki gaskiya, yaran nan baxa su taba cin amanata ba...

Suna kaunata, kaunar dake bakya mini, suna kula dani, kulawar da ke bakya mani, suna kyautata mani, kyautatawar da ban samu daga gareki ba.

Suna kaunar Da na, da bani da kamarsa a duniya.

Don haka nima bani da kamarsu, baxan taba xargin su da abinda xuciyarki ke tunani ba.

Ba don kudina suke xaune dani ba, sai don na nuna masu suma suna da 'YANCIN KANSU, talaka nada 'yanci a gidan mai kudi, 'yancin da xaiyi abinda yaga dama, daga cin abinda yake so xuwa amfani da motocin sa, kwana a gidansa shiga dakinsa, ba tare da wani kyama ba.

Na nuna masu everybody have right to education.

Ba sai dan wane ba, ba sai wanda Uban sa yake wane a Abuja ba.

Don haka baxa su taba xalintata ba.

Baki san wani abu bane, wani kiristan yafi wani musulmin tsoron Allah.

Yafi wani musulmin rikon amana.

Tom, tamkar Uba yake ga Zubaidah.
[10/15, 9:14 AM] A A Dboy: *_POST BY GROUP OF HYPE HAUSA NOVELS BOOK WHATSAPP 08064400100_
[10/15, 9:15 AM] A A Dboy: Tuna Baya 111-115
111.

Shi ya koyar da ita A,B,C,D, ya koya mata yadda xatayi rayuwa cikin masu kudi, yadda xatayi magana cikin turanci tamkarsu, yaya xa'ayi ya nemeta?

Yaya xa'ayi ya bari wani cikinsu ya bata ta, bai gaya min ba kada ki karayin wannan tunanin game da bayin Allahn nan, domin kin masu KAXAFI.

Dole Zubaidah ranar da ta kammala makaranta, ranar xan sadata ga iyayenta, tare da mijin aurenta amma yanxu tunda kince kin lura tana son gaini iyayenta, karshen satinnan xan kaita ta gansu, ta dawo ta kammala jarrabawar sai ta koma ga iyayenta suyi mata aure.

To amma Mubina?

YAYA XAMU YI DA JAWAD?

XAMU BARWA MIJINTA NE, KOKO XAMU KYALESHI, KEWARTA TA KASHE SHI, KO RASHINTA YA SANYA MISHI CUTAR DA BAMU DA MAGANI?

IN GAYA MAKI GASKIYA BAXAI IYA RAYUWA BA TARE DA ITA BA!
Chapter 23 · 0% Book details