Sashe 2
Tuna Baya Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read
Ni kuma naji dana Jafaru da karatuna, don ta lura XAN IYA BARIN KOMI IN DAI A KAN RAINO NE.
[9/23, 9:40 AM] A A Dboy: *_POST BY GROUP OF HYPE HAUSA NOVELS BOOK WHATSAPP 08064400100_
[9/24, 9:09 AM] A A Dboy: Tuna Baya
ina son kananan yara, ina matukar kaunar, in ganni goye da jariri, ina jijjiga shi, ina yi masa rawa, ina cilla shi ina jefawa, yana bangala mani dariya 'kauna' irin ta uwa.
Don haka inda duk xan shiga a kauyen Karaye, an san da goyon Jafaru ko Sadiya xa'a ganni.
Ko da aka kai Sadiya wurin Luba kakar mu, kullum kafata bata rabo da hanyar gidan Liman, ina goye da Jafaru dan shekaru biyu.
Malam yayi ta tsokana ta da Uwar Biyu.
Ina jin dadin sunan, ina farin ciki a ce ni UWA CE.
A ganina, wanda duka Allah ya baiwa Da yayi masa babbar kyauta, wadda wani ko wata, ba xai iya bashi ba.
Haihuwa ai kyauta ce daga Allah, don haka abin alfaharin kowacce mace ne Tefe muke ni da Atika a gefen kwalbati, ina goye da Jafaru, Atika dauke da kwarya a kanta cike da kalwa.
Baba ne ya aike mu gidan wani mutum da ya bashi kudin a kasuwa, ta kare yace xai aiko mai da ita gida.
Atika ta dube ni, ta girgixa kai cike da takaici tace ''Atine, shin wai ke bayan ki bai gajiya da goyon yara?'' Nayi murmushi nace ''amsar ki kenan'' tace ''wallahi ki rika aje Jafaru hakanan, ya girma, shekarun shi fa biyu, an yaye shi tuni yana gudun shi ko ina, tukunna ma, baki tsoron kirjin ki ya bude?'' ''To idan ma ya bude Atika menene?
XAN IYA JURE KOMI IN DAI AKAN RAINO NE''.
Atika tayi tsaki ''Allah wadaran wahalalle wallahi, ina kuwa xaki yi saurayi?
Kullum sungume da yaro kina tafe sukutuf, babu dan karya kugu?
Ki diba ki gani, ni kullum xance, har layi ake, kudi, sutura, kayan kwalliya, babu wanda samari basa bani.
Amma ke ko 'yar murtala, bana ce kin taba karba daga hannun saurayi ba''.
Nayi murmushi ''kudi, sutura, kayan kwalliya, don su xaka kula saurayi Atika?
To ladan RAINO fa?
Saurayi yana bayarwa?
In gaya maki gaskiya ta Atika, burina ba samari bane, KARATU NA BOKO irin makarantar su Ya Auwal, in karanta raino, RAINO NA KANANAN YARA''.
Atika ta tuntsire da dariya har tana hawaye, irin taga mahaukaci sabon kamu tace
''Koda naji ana karatun boko, ban taba jin wani KARATUN RAINO ba.
Kai Atine, kin bani dariya, wai ma ina kika jiyi wani karatun raino?'' ''Ban taba ji ba Atika, amma nasan abinda na fada, ba abin dariya bane, don Allah ni mu bar wannan xancen ma, wai ina ne gidan Malam Ladan din?'' Daidai lokacin da muka karaso dakalin gidan Waxiri, samari ne xaxxaune, sun kewaye dan waxirin Karaye, suna bashi labaru yana tuntsura dariya yana xukar sigari cikin annashuwa, yana bulbular hayaki.
Samarin suka yi tsit, da hirar da suke, suka xubo mana ido, Atika har da canxa tafiya, jin ana kallon ta, kuma samarin gidan waxiri masu ji da kansu, ni ko sai na kara sauri.
Mun yi dan nisa kadan muka ji alamar taku a bayan mu, daidai lokacin da muka iso kofar gidan Malam Ladan, daya daga cikin samarin yace ''ku, ji mana?'' Ba mu juyo ba sai kara sauri, ''ko baku ji ba, su waye ku a layin nan da xaku hurawa Yallabai hanci?'' Na dubi Atika xata yi magana nayi mata alamar tayi shiru, muka sa kai xauren gidan.
Ji nayi an finciko Jafar dake baya na, ya fadi kasa tim, ya tsandara kara mai firgitarwa.
Muka juyo gaba daya, samari ne guda uku, baki gajere, wankan tarwada dan tsamirmiri, fari dogo siriri, da alama shine dan Waxiri, da muke jin labari dan birni, domin har wani farin kara da wuta a jiki, ke makale bisa bakaken labban sa.
Ya kashe ido, ya daga kakkaurar girar shi sama ya dubi abokinsa dan tsamirmirin, tsamirmirin ya dube ni, yana wani fizga, magana yake kaman baya so.
''Ku 'ya'yan Maikalwa, Kalwa ta daddawa, kayan wari kayan tsiya, Yallabai Bello ke son magana da ke, kina wani xubga sauri tsilli- tsilli da kafafu kamar maburgin kada kuka.
Ko ance muku Kalwar xamu kwace, mun yi miki kama da masu cin daddawa ne?''
Gajeren ya karbe ''kai Sambo ai wannan mai kafar maburgin, da wuya uwa marikin leman, jin kanta take kamar diyar Sarkin Santanbul, ba 'yar matsiyacin nan Maikalwa ba.
To ki ji ki nutsu, kin san da wa kike tsaye, tun bamu kifar da jarin Kalwar ba''.
Na tsugunna na dauke Jafaru, na maida bayana, nasa xani na kulle shi, na dago ido na dubi dan tsamirmirin, kana bakin, sannan uban gayyar nace '' kada ka kara xagar mana Maikalwa, tunda ko ba komi, ya haifi wadanda suka taso ku daga maxaunin ku.
Kai kuma mai ce mun kafar maburgi, ni kuma sai naga ta yallabai din naka ce ta dace a kirata 'muciya', nasa wuyan kuwa, ai da Kalwar da kake ambato yafi kama, mu je Atika''.
Suka dubi juna da sauri.
Ogan nasu yasa hannu ya daga kwaryar da ke kan Atika, gabadaya ya juye mun Kalwar a ka nida Jafar muka yi futuk, muryar sa daban ce da tasu, mai taushi kuma cike da gadaran Sarauta yace ''Ke kin san BELLO WAZIRI?'' Na murguda baki nace ''a'ah!
Na dai san, Wazirin Karayen, wani fari dan sololo, farin gashin-bakin sa na tadda lalaceccen bakinsa da goro yayi wa kanta.
Yana tafe a duke, kamar wanda Inna ta shanyewa doron baya.
Idan yana gaban Maimartaba a fada, kamar tsohon da yayiwa sarki karya.
Shi din ne, koko akwai wani wazirin bayan shi?'' Yayi murmushi tamkar maganar bata soke shi ba, yace ''wannan Maikalwa kike nufi, wani matsiyaci cikin garin karaye, wanda matar sa ke ci da gidan sa, idan Maimartaba yayi kiran amsar zakka shine na farkon xuwa, ki ji shi duk ya cika fada da warin KALWA, wanda duk ya shigo, sai ya koma, inda duk yayi, warin Kalwa yake, haka 'ya'yan sa, matansa da surukansa.
Don yanxu haka jama'a sun rage xuwa masallacin Juma'a sabida Liman, cika su yake da warin Kalwa''.
Na dubi Atika wadda tayi suman tsaye idanu na suka ciko da kwallah, ta kama hannu na muka fito faga soron.
Suka kuwa biyo mu har kofar gidan mu da xagin cin mutunci, dai-dai da xamu shige gida, yasa hannu ya riko goyon Jafaru, na wani irin juyo
Don kar ya kara kwala shi da kasa gaba daya suka sa dariya, amma shi murmushi yayi, ya dube ni a lalace yace ''na baki assignment, mai kafa kamar MABURGI, ki je ki binciko, shin waye, BELLO WAZIRI KARAYE?'' Magana yake cikin gwalli da kwalisa, da wani irin tattausan hausa da ban taba ji ba.
Ya sakar min goyon ya juya, 'yan koren shi suka mara mai baya.
Sai a lokacin na samu damar kallon sittiran dake jikin shi.
Yadi ne da ake kira shadda, ruwan kasa tirarre, ya sha aiki surfani na Saraki gaba da baya, da xare ruwan kasa-kasa.
Wani abun birgewa ma, takalmin shi rabin sau ciki, da duk Karaye babu mai sashi sai Saraki, shima ruwan kasar ne.
Wannan ba shine a gaba na ba, (wata xuciyar tace dani), abinda xamu cewa Baban mu, game da aiken da yayi mana.
Ban iya karya ba, xan fadi wa Baba, dan gidan Waziri ne ya xage mu ya kifar.
Dakin Amarya muka xarce, Atika mayafi a hannu, tana ta kwalawa Goggo ta Amarya kira, na sauke Jafaru wurin Inna dake bare gyadar miya a karkashin dalbejiya, ko kamin in karisa ciki, ina jiyo Atika har ta kai tsakiyar labari, na karasa ciki na samu gefen Guggona na xauna, nayi shiru, Guggo tace ''ke Atine, ina ke ina fada da Bello, babban dan Waziri da kowa ke ganin mutuncin sa a garin nan, yaro mai halin dattaku da girmama na gaba, shekaran jiya daya dawo daga birni, can inda yake karatu, ya kawowa Baban ku zakka har gida ya kuma dauko shi daga kasuwa a busukurin shi, me ya kaiki xagin shi?
Da yace ku tsaya ku ji, koma mene ne don martabar gidan su ai kun sauraresu, wannan jin kan naki bansan inda kika samo shi ba, meye da mu?
Mu su waye?
Ki iya talaucin mahaifin ku kada ki jawo mana wulakanci a garin nan, in kinga Bello ko a ina ne, ki tsugunna ki bashi hakuri kin ji na gaya maki.
Idan Baban ku ya ji wannan rashin hankalin naki, Allah kadai xe raba ku''.
Cike da mamaki da takaicin Atika nace ''Goggo, Atika bata gaya muku gaskiya ba, wallahi xagin Baban mu yayi tayi, ya kifar mana da Kalwa, ya balle min goyo, yace wai kafana kamar maburgi,
Wallahi kinji na rantse, yace wai waye uban mu, Maikalwa?
Wallahi ba wanda ya isa ya xagi Babana in kyale shi, ai talauci ba hauka bane''.
Amarya tace ''babu yadda xa'ayi yaron nan ya xagi Baban ku, ko bai sanku ba, balle kuma ya san ku, an ce Maikalwan,ba Maikalwar bane, an ce miki mai kafar maburgin, ko ba tsigigiyar bace?
An kuma ce waye uban ku?
Wanda duk yace xai ja da Saraki, ai kuwa sun tambaye shi waye Ubansa?'' Na mike ina kumburi nace '' Allah banda ni, babu wanda xai xagi Babana akan ido na inyi shiru in kyaleshi,ko Wazirinne, balle wata tsiya,Bello, don kuwa Babana, na tabbata bai taba xuwa roko wajen su ba''.
Goggo tace gaskiyar ki Atine, nima ina bayan ki, ku kare mutuncin talaucin ku a ko ina, mulki da abin duniya duka Allah ke badawa,babu kuma wanda yayi mai rawa ya bashi.
Jeki dauraye jikin ki duk kin cika mu da doyi, akwai wata Kalwar xan daurawa Rabi'u ya kaiwa Malam Ladan din''.
Kwana biyu ina juya maganar Bello a raina, na kasa mantawa, nayi-nayi in mance na kasa.
Ba wai ciwon abinda yayi mana ke damuna ba, don kuwa nima na rama, na kuma tabbata yaji ciwon sharewa yayi.
A xahiri ni karamar yarinya ce, shekaruna basu fi 13 ba, ko kirgen dangi irin na Atika ban soma ba.