← Book details Tuna Baya Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 18 OF 51

Sashe 18

Tuna Baya Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

Tun safe Tom ya markada ayar kunun dana jika tun daren jiya, mai kyan 'yar Katsina.

Nayi kyakkyawa kuma tsaftataccen kunun Aya, Tom ya diba ya kai matsayin karin kumalli.

'Yar boko, tun 7:30 ta fice aikin ta.

Nayi wanka, na kasa shiryawa sai nasa kuka, ina makale da shi shima yayi lamo, a kafaduna.

Sallamar Baban Jawad na ji ba xato.

Ya shigo tare da Ejiro.

Ya jingina da bangon dakin hannuwan shi duka biyun harde bisa kirjin shi.

Kallo yake mana cike da sha'awa ''Maman Jawad, bakya son school, kuma dole kije.

Bana xama da JAHILI duk wani wanda ya rabe ni ko JINI NA ne, koba Jini na ba dole ya nema ilmi''.
[10/8, 5:19 PM] A A Dboy: *_POST BY GROUP OF HYPE HAUSA NOVELS BOOK WHATSAPP 08064400100_
[10/8, 5:23 PM] A A Dboy: Tuna Baya 81-85
''Ni ba makaranta ne bana so ba; Jawad da wa xai xauna?

Baxan baiwa namiji raino ba, ko xasu yarda mu xauna tare?'' Yayi wani irin murmushin da ya fiddo tsabagen kyawun kuruciyar shi, ''tun kamin inyi tunanin kai ki makaranta, na tuna Jawad, da kyakkyawar kulawar da yake samu daga gareki.

Blood is thicker than water (jini yafi ruwa kauri).

Sai dai don Da na guda daya, baxan ki taimakon mace ba, MACE AL'UMMAH wadda in ta ilmantu al'umma da yawa xasu ilmantu.

Kuma mace wadda ta fito daga masarauta na, KARAYE.

Karatun ki, ba ke kadai xai amfana ba har da ni.

Domin Jawad daga gareki ne xai soma samun tabalan ginin rayuwar shi.

Wala'Allah mai kyau ko maras kyau.

Kenan ba xan so shi da mara kyau ba?'' ''To yanxu ina xa'a kai shi?'' ''Kullum da safe xuwa karfe daya da rabi na rana, wato lokacin tasowar ki.

Akwai wata gyatuma 'yar garin Karaye, da mijin ta ya rasu a hadarin mota, bata taba haihuwa ba.

Da akayi wani kakkarfan ruwan sama a Karaye, gidan ta ya rufta mata a ka, ta gurgunce, take bara a kofar gidan Maimartaba.

Na dauko ta na sai mata karamin gida a Wuse, ina sawa ana kai mata abinci da kudi duk wata tare kuma da wata 'yar uwar ta suke xaune.

To ita xa'a ba Jawad har ki taso makaranta.

Tunda nace XAN KULA DA KE, tunda kina son Jawad, to matsayin ki gare ni BA 'YAR RAINO BA, 'yar gari na nake riko sabida Allah''.

Yayi shiru, can ya runtse ido yace ''Atine ke, na bar maki Jawad, matsayin 'DA' ke Uwar Jawad ce da nake biya bata hanyar aure ba.

Tamkar rikon da Halimatus-Sa'adiyyah tayi wa Annabin mu.

Sabida haka ki kula da Jawad kulawar da Uwa xata yiwa Danta, ni kuma XAN KULA DA KE!''
******************
Abu nasu na manya 'yan cuku-cuku, sai gani a aji hudu na firamare, gwajin da akayi mun duk na cinye na side turanci kamar 'yar sakandire.

Shi kansa (head-mastern) cewa yayi anya banyi firamare ba xan maimaita?

Oga kuwa yafi kowa mamaki, ya titsiye ni da tambaya nace Tom ne ya koya mani.

Maganar sunan da xa'ayi amfani dashi yace meye sunana na ainihi?

Ni kaina in xa'a kashe ni ban sani ba.

Yayi waya gidan su gidan Maimartaba, ya tura Talatu ga MAIKALWA, ta tambayo ta fada mishi.

Washegari ni ce cikin 'suit' da 'skirt' din makarantar firamare ta 'ya'yan masu fada ajin Nigeria, da ke birnin tarayya Abuja.

Na daura Cambas, Tom ya ratayan school-bag.

Abban Jawad yace ''daga yau sunan ki ZUBAIDAH MUHAMMAD KARAYE''.
************
Na cigaba da xuwa makaranta, Direban cefane ke kaini ya dawo dani, sannan mu biya mu dauko Jawad gidan Kulu kullum.

Duk abin nan da ake, Aunty bata san wainar da muke toyawa ba, tana riga kowa fita a gidan, kowa kuma na rigata dawowa.

Shakuwa mai tsanani, irin ta Da da mahaifi, ke kara shiga tsakanina da Jawad.

Tun sanda Yallabai yace kar in sake kai mata shi shan nono, ban sake ba, itama kuma na lura taji dadin hakan.

Bata ko sake tambayar yaya lafiyar yaron ba, balle ni karan kada miya.

Nafi maida hankali kan abincin Jawad dana Abban sa, fiye da karantun kansa.

Sai dai shima ba laifi ina kokartawa.

Jawad yayi wani irin girma da karfi, ya soma rarrafe, sannu-sannu sai mikewa xuwa tafiya.

Bakin shi ya soma budewa, yace min Momi, Baban shi Daddy, Tom Uncle, su Ejiro da ke yawan daukar shi duk Uncle ne a bakin shi.

Aikin da Yallabai xai je yi kasar Canada, bai fito ba sai bayan shekaru biyu.

Bai tafi ba sai da ya kai Jawad makarantar rainon yara 'nursery'.

Ni kuma lokacin takardun jarrabawata na kammala firamare sun fito, nan ma xuke yasa akayi mun sabida haxakar da na nuna a takardun, aka samar mun gurbi a NURUL-BAYYAN INTERNATIONAL ACADEMY ABUJA.

Sau uku Hajiya Talatu tana xuwa duba lafiyata, duk sanda taxo, tana sambarka da rayuwata ta komawa iyayena da labarin yanayin da ta ganni a ciki, na kwanciyar hankali da samun kulawa.

Sai dai tace min shi Baba ne da kansa yace in xauna, kar ta dauko ni ganin gida, har xuwa lokacin da ya tsayar da tunanin shi kan wanda yake son baiwa aure na, domin muddin na xo gida, na dawo kenan ba xai barni in koma ba.

Watan Yallabai daya da tafiya, ranar lahadi, daga ni har Aunty muna gida, yau kuma ku allurar uwa ce ta mosto oho, ta danna intercome naje na iske ta tare da 'yar duniyar kawarya Mansina.

Ta bini da wani irin kallo, wanda nasan baxai wuce mamakin, masifaffar canxawar da nai ba.

Ta kare mamakinta tace in kawo Jawad, Mansina ce ke son ganin sa.

Na lura da irin kallon da Mansinar ke mun, akwai magana.

Jawad na bisa gadona yayi baja-baja da motoci da jiragensa ''Momi wannan helicoptern batir dinta yayi sanyi, a canxa'' nace to Jawad, na canxa batir, nace ''bakuwar Maman ka ce xata ganka, muje ko?'' Ya noke kai, ''Momi sai kin man banbu'' ''wannan abu mai sauki, Jawad, xo ka hau, kai da bayan Momin ka?'' Yayi dariya ya dare bayana, gab nike da shiga jin ana ambatona, ya sani dakatawa.

''Itace mana, mai wanke-wanken nan da aka kawo mani kafin tafiyar ki karatu Scotland, kin mance yadda taxo min; cikin tsummokara da yalayen hakora, kafafu kaman sillen kara, baki kamar bayan tukunyar mai shayi har na sa mata suna 'BLACK' amma dubi yadda tayi haske.

Duk kasusuwan sun ciko da tsoka, ashe dama rashin kyakkyawan abinci ne, da yake na dade ban ganta ba, don daga su har Abban Jawad, ba shiga harkar su nake ba.

Mansina gaskiya na gaji da auren nan, nayi kuskure da nayi tunanin Taheer shine Mr Right dina.

Wani irin kidahumi ne, ban taba samun shi da irin ra'ayi na ba kwata-kwata, har yanxu baya sona.

Ya dauki son duniya ya axa akan wanna figaggen Dan nashi, a sabili dashi yarinyar nan ke daura xannuwa irin nawa.

Idan nayi magana, yace nakasa rainon Da na tayi mun ai ta cancanci hakan.

Duk tsarin xama da nayi mata, ya rusa.

Ya bata irin damar da ya baiwa su Tom a gidan nan, suna binda suka ga dama.

Kinsan munyi fadan tafiyar nan da xai yi Canada, yace sai dai a tafi da ita, sabida Jawad, bai saba da ni ba.

Ni kuwa da in shiga jirgi da mai raino, gwara nayi xamana wallahi, tunda na dauko ta shiga duniya, in fita kunya, ya sanya mata kahon xuka sai da yasa ta koma kasar su.

Wallahi Mansina ina tunanin aure na da Taheer, ya kusa xuwa karshe, tunda ba shine autan maxa ba.

Baxan xauna ina kare kuruciyata da mutumin da bai san ciwon kansa ba, bai san darajar da yake da ita ba.

In kin ganshi yana dariya, to da wadannan barorin nashi ne da yake gani tamkar abokansa.

Ba abinda yafi bani takaici irin naga Tom, yana tuka motar da mijina yake hawa wallahi ji nake kaman inyi aman xuciyata.

Kin san ma abinda ke daure min kai?'' Mansina kai kawai ta girgixa ma'ana ''A'ah sai ta fadi''.

''Ni dai nasan Taheer ba manemin mata bane, ba kuma wani mabukaci bane cancan.

Amma sai yayi tafiya har ta tsayin watanni biyu ya dawo ba wata mu'amalar kirki.

Karshe ma nice mai nema, yana yanga yana jan aji, sai ya gama kwalani a kasar wulakanci tukunna, a kare da yi mun tsaki da juyan baya.

Duk wani kyale-kyale na, bai burge shi.

Duk gyare-gyaren da nake, bam gamsar dashi.

Sabida Allah Mansina ina xan iya jure wannan rayuwar wulakan ta kai?

Ya tafi nima in tafi, ba mai neman wani, ba so balle kauna ginshikin aure?

Da haushi ya ishe ni kwanaki, dan cikin da naga yana ta bare- bare akan sa naje aka kifar da shege, tunda na gane Akuya ya maida ni, in ta xubo masa 'ya'ya su yana kaunar su nice banxa.

Da nayi mashi karyar ya xube, sai cewa yayi Musulunci na akwai question mark(?), gorin so kala-kala ni dai wallahi na gaji.

Ba don har yanxi ina son shi ba, wallahi da tuni na kama gabana.

Duk abinda Ubana yayi masa, bai gani ba, ya manta, da baxar Uban wa yake taka rawa, bada ta Ubana ba?

Idan yau nace ya bar kujerar sa, wallahi ta xauna.

Don dama shekarunsa basu kai ba, Babanane ya shiga ya fita yasa shugaban kasa ya bashi ita.

Sai dai ina ji a jikina Mansina, baxan iya rabuwa dashi ba.

Shikadai ne a duk maxan da nayi hurda dasu kamin nayi aure, da xai kusance ni in san da namiji ne da ya san menene kauna?'' Ta karashe fadin maganar cikin murya mai ban tausayi.

Tsaki Mansina tayi sabida haushin da ta bata tace ''kina amfani da kayan Indonesian da naki kawo maki kuwa?'' ''Har na Uwar Indonesia ma, nace maki ko ohon sa.

Ni fa nasan ala tilas yake bari na kwana cikin gidan sa, don baxan ce aure ba''.

Mansina murmushi take tana karawa.
Chapter 18 · 0% Book details