← Book details Tuna Baya Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 14 OF 51

Sashe 14

Tuna Baya Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

Ni ka ganni abinda Allah bai daura mun ba kenan, shiga abinda babu ruwa na.

Idan ba so kake Aunty tayi sanadiyyar lalata hanyar abincin ka ba''.

Bai yi magana ba, amma yanayin fuskar shi ta nuna maganata tayi tasiri a tare da shi.

Rannan Aunty ta tafi aiki, Elizabeth na wanka ta bar Babyn yana kyankyara kuka, ba tun yau ba ina kallon ta idan har ba Auntyn na gida ba bata wani mai da hankali kan yaron, sai ta bar shi yayi ta kuka har Allah ya gajishshe shi.

Naji baxan iya jure kukan da yaron ke yi ba, domin kuka yake har cikin kwakwalwata.

Na lallaba na leke dakinta naga bata fito ba, na shiga da sauri na sungumi Babe nasa a bayana, na dau towel din da aka nade shi da shi ina jijjiga shi.

Wannan shine babban buri na a rayuwa; in ganni goye da jariri, ina jijjigashi, ina yi masa rawa ina cilla shi ina cafewa.

Rabona da goyon jariri tun ina rainon Jafaru.

Don haka yau na jini cikin wani sabon nishadi.

Shi kuma jaririn da na tabbata ba'a taba goya shi ba, tunda uwar sa ta haife sa, sai yayi tsit daga kukan da yake, yana ajiyar xuciya.

Sai naji tausayin yaron ya kama ni.

Tausayin sa nake, ba don bashi da gata ba, yana da gatan komi, amma ya rasa gatan da yafi komi amfani da muhimmanci a gareshi, watau dumin jikin Uwa, a dai-dai lokacin da yake tsananin bukatar shi.

Na tabbata ba kukan komi yake ba tunda babu yunwa a tare dashi, illa kukan jin sa shi kadai ba tare da kowa ba, balle Uwar da xai laluba ya rungume har ya samu damar tsotson abinda yafi komi dadi a gare shi, wato nonon Uwa.

Ban san sanda Elizabeth ta fito ba sai jin ihunta nayi a kaina tana tafi tana kakabin a kawo mata agaji ''Help!

Help!!

Help!!!

The baby will die'' wato Dan xai mutu.

Nayi saurin sauke mata shi saboda yadda ihunta ya kidimani ya gigitani.

Wai ashe duk wannan ihun da take na goya shin da nayi ne, da gudu ta xo tana tattaba kafafun shi ta gani ko na karya shi?

A sukwane Ejiro ya shigo ta shiga gwada mishi tale-talen da nayi wa Baby har tana daukar filo tasa a bayan ta da xani, yayi tsaki ya fice nima na fice yana yi min korafin ni me ya kaini shiga shirhinta.

Ashe bata bar xancen ba domin Aunty na dawowa da gudu ta kai mata dan ta tana kuka wai baxa ta iya ba tana gani in kashe shi a daura mata laifi, ta gwada mata yadda nayi mishi.

Auntyn ta kira ni tasa ni a gaba, yau ma firji ta sani, wai karambani na yayi yawa, gobe in kara goya mata Da.

Don haka washegari na tashi da matsanancin xaxxabi ko gani bana yi sosai, musamman da yake a watan Fabrairu muke, sanyi yayi tsanani ainun.

Aka kuma sani a firinji, na kwana hancina na yoyo, kuma a cushe ta yadda hatta numfashi ta baki nake iya futar dashi.

S haka na rarrafa na shiga dakin Aunty don ka'ida ne kafin ta fito naa gama da falo, da xarar ta fito sai in shiga cikin dakunan barcin in gyara mata.

In banda rawar dari ba abinda nakeyi duk da riga (sweater) mai kauri da ke jikina, ina yi ina hutawa in na jiyo motsi in yi saurin mikewa, in cigaba.

Sama-sama na jiyo muryar Aunty da ke 'dinning' wato kwararon da aka xagaye da farin labule da makeken tebur, domin cin abincinsu wanda ke gefe guda na cikin falon, tana lissafo kudin aikin ma'aikata na wannan watan, da alama da Maigidan ta take magana.

Yana magana ne a hankali don haka bana jin me yake cewa, sabanin ita da take da karfi, don daga baya ma fada-fada ta koma magana wai babu inda Elizabeth xata, waye xai dinga kula mata da Babyn sai dai in shi xai dinga goya yaron yana tafiya nashi office din, amma ita baxa ta bar aikin ta ba, sabida wani yaro can (unwanted Babe) da yaxo mata ba'a sanda ta shirya haihuwarsa ba.

A fusace kuma cikin fada yace ''ina yarinyar da ke maki aiki da Fulani ta aiko daga KARAYE?

A bata Babyn ta dinga kula da shi, amma wannan matar yau xata tafi...,
Baxan biya wadannan makudan kudaden ba, sabida ba daga kasa nake tono kudin ba.

Idan kuma ganin hakan bai maki ba, to xan dauke shi in kai shi gaban Fulani, tunda ke kika haife shi, kin fi kowa sanin ciwon sa, baxa ki xauna ki kula dashi ba.

Kina kiran shi (unwanted Baby) Mubina, a gareni yaron nan yafi min komai a duniyar nan da abinda ke cikin ta.

Don idan xaki ajiye aikin ki ki bashi kulawar Uwa da ta dace, to, in kuma baxa ki iya ba, to cikin biyun da na baki dole ki xabi daya''.

Ga yadda tayi shiru bata kuma magana ba,maganar nasa ba karamin kada ta su kai ba, jin an ture kujera baya na taho falo nace kafa! me naci ban baki ba, kada suce ina labe, bayan kuma ba haka bane, aiki na ne ya kawo ni.

Allah bani da wannan halin.

Kafin axahar ba sai muka ga Elizabeth ta turo akwati ba tana xumbura baki, Ejiro aka danka wa nemo visa yana tsaye rike da passport dinta a hannu, yace ta bar yafiyar sai jibi wajen visa xasu je.

Ni da Tom har tsalle a muka yi, a daki don murnar tafiyar Elizabeth, Aunty kuwa ta cika fafam, kiris take jira ta fashe don haka muma muka shiga taitayin mu ba wanda ya nuna yasan abinda suke ciki.

Na shiga aiki washegari, da misalin karfe bakwai na tadda Aunty tayi shirin tafiya aiki, tana xaune a luntsumemiyar kujerar falon ta, tana cika tana batsewa wannan sabida tsabar son aikin ko ince sabida son kudin, ma'aikacin banki takwas take masa a office amma ita Aunty tsabar xafin nama bakwai da rabi a bankin su take mata shi kuwa miji ko oho, don shi kan sa Oga tana riga shi fita.

Tom ne ya gaya min cewa Aunty Manajar Banki ce guda don haka nayi mamaki, tace ''ajiye tsintsiyar kixo nan'' da sauri naje na russuna a gabanta ''kina da masaniyar gobe ne Elizabeth xata tafi?'' ''Ban sani ba Aunty'' ''to in baki sani ba gashi na fada maki, don haka xaki dinga kula da JAWAD kamin in dawo don bana son Baban shi ya maida shi Karaye, kina jina?'' Na gyada kai da sauri.
[10/7, 7:07 PM] A A Dboy: *_POST BY GROUP OF HYPE HAUSA NOVELS BOOK WHATSAPP 08064400100_
[10/7, 7:08 PM] A A Dboy: Tuna Baya 66-70
''Daga yau karfe bakwai da rabi nake fita aiki, don haka xaki xo ki dau Jawad kiyi mai wanka, ki shirya shi yadda nurse xata xo ta koya maki, duk kayan shi dakin ki xasu koma bana son rainon Baby.

A rana sau uku xan ganshi, in bashi nono sau uku; da safe kafin in tafi, da yamma idan na dawo da kuma da daddare kafin ya kwanta barci.

Idan kuma na yaye shi, a wurin ki xai dinga kwana.

Ki cigaba da wanka sau uku a rana, kamar yadda na gaya maki farkon xuwanki domin karki shafawa dana datti.

Ayyukan da kike a da, gabadaya an dauke miki Peter xai cigaba da yi, dama shi yake yi.

Dakin barci na kuwa tunda ya hana shi shiga, na dinga gyarawa da kaina koda a karshen sati ne in na samu lokaci.

Don haka ki maida hankali bisa aikin ki na yanxu kadai, KULA DA JAWAD.

Ba'a goya min da, kada a karya masa kafa domin siriri ne.

Akwai gadon shi, akwai abin shan iskar shi duk xa'a kawo su wurin ki.

A rana xaki canxa mai pampers sau shidda.

Ki kwaso kayan ki ki koma dakin ki nada idan Elizabeth ta tafi gobe''.

Nayi godiya na mike na fito duk jikina babu kuxari.

Daga wanke-wanke kuma na koma 'Nanny' babu yadda rayuwa bata yi da dan Adam.

Ta wani fanni kuma ni dama RAINO NA FI SO A RAYUWATA.

Dana gayawa Tom yadda mu kai da Aunty, bude baki yayi cikin mamaki, ya kuma fi mintina biyu bai rufe ba ''Tine, ka lissafa kanka cikin masu sa'a a duniya.

Uwar goyon Babe Jawad?

Xaka ji dadi wurin Oga in har ka ba Jawad kulawa mai kyau.

Yana son Jawad, fiye da komi a rayuwar shi.'' Ina wanka da safe naji ana kwankwasa kofa, na sanya wasu sabbin riga da siket jajaye cikin irin kayan da Talatu ta hada min ne.

Na bude kofar ba tare da na tambayi ko wanene ba, wata macece mai dan jiki gajeriya, tana sanye da fararan kayan asibiti, da alama mai kirki ce tayi min murmushi tace ''kece mai rainon Jawad yanxu ko?'' ''Eh'' ''ni sunana Sister Sadiya Danladi, (nurse) ce, an turo ni musamman domin in koyar da ke yadda ake yiwa yaro wanka, da yadda ake bashi abinci bisa...,
..ka'ida da sauransu don haka xauna ki saurare ni''.

Tayi min bayani tiryan-tiryan har na gamsu nayi mata godiya ta tafi.

Washegari da asuba na tashi, karfe bakwai na kimtsa shiri tsaf, irin wanda take so.

Na je falo na jira ta har ta fito cikin shirin fita.

Na gaishe ta bata amsa ba ta miko min jaririn.

Na sa hannu biyu na amshe shi cike da dukkan kulawa.

''Sai karfe biyar nake dawowa, ba'a soma bashi ruwa ba tukunna, sai yayi wata shidda, yau watannin shi hudu, xaki fara shayar dashi madara yadda sister Sadiya ta gaya miki, an kai miki kayan tun jiya sai na dawo''.

Na xauna bakin gadona na sanya Babe Jawad cikin ni'imtaccen gadon sa, na kura mishi ido kurrr!

Allah gwani tsatstsarka, da ya nufi mummunar mace kamar Aunty Mubina da haifar kyakkyawan yaro irin Jawad.

Fari ne sol, sumar kanshi mai yawa baki wuluk, hancin sa dogo xirit, labban sa jaxur 'yan kaurara, kanana, yana da cleft da kyawawan yatsun kafa da hannu.

Ban taba yi masa wani kyakkyawan kallo ba sai yau.
Chapter 14 · 0% Book details