← Book details Tuna Baya Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 13 OF 51

Sashe 13

Tuna Baya Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

Baki ne ke ta barkowa daga ko'ina cikin Abuja duka ta bangaren Aunty, amma ko kuda na lura babu daga masarautar Karaye, wato dangin maigidan.

A kullum Tom ya daura tukunya ya sauke sau goma.

Ni kuwa shara, wanke-wanke da goge-goge kamar inji don ma yawanci komae da inji ake yin shi.

Akwai wata kanwar Aunty mai suna Mimi har fargabar xuwanta nakeyi domin in ta soma ''ke Black, dauko min kaxa, karbo min kaxa, miko min kaxa har sai kafafuna sun sare.

Ana i gobe suna kuwa kafafun ta tasa a ruwa wai in goge mata kaushi, taje wajen wankin kaushin sun tashi gashi gobe xasuyi luncheon din suna.

Cikin mamaki na dube ta, ba tare da ko dar ba nace ''wannan ba aiki na bane.

An dauko ni shara da wanke-wanken Aunty, amma ba'ace da Ubana xan dinga yin gugar kaushi ba''.

Daga hannun nan da xatayi sai fuuuu!

Ta dauke ni da mari tace bari inje in ji idan ita maijegon ne tace ki dinga yi mun rashin kunya.

Ai dama da ganin idanun nan naki kwala-kwala nasan yarinyar nan ke nan gaba abin tsoro ce.

Ina daki ina ta kuka Aunty ta fado dakin ta soma surfa min xagi, tace daga yau Mimi ta sake sani aiki nayi mata musu, a bakin aikina.

Bayan sunan da akayi shi da sati biyu ga yadda na fahimta maigidan ya dawo, aka sake wata walimar a rockview, wadda Tom ya kawo mana jarida mai dauke da hoton Aunty da Babyn da fuskarshi ke kushe cikin farin showel matar shugaban kasa na mika mata kyauta, nade cikin wata leda mai kyalkyali, cikin mamaki nace ''yaya Baban Babyn bai shigo hoton ba?'' Yayi murmushi mai nuna matukar girmamawa ga wanda na ambata yace ''Ogan mu, ba daya yake da sauran mutane da kika sani ba''.

Tunda aka haifi Dan nan bamu san kalar shi ba, sabida yadda ake kulawa da shi ko kwai sai haka, sai dai mu hangoshi daga nesa a hannun baki masu xuwa, wadanda kallo daya xakayi masu kasan sune jama'ar Aunty Mubina, wato daga matan ministoci sai na manyan ma'aikatan Banki abokan huldar ta, da basu san me ake kira talauci ba.

A wata asabar ce Aunty da Mimi sun baje kyaututtukan da Babe ya samu suna hira, ni kuma ina durkushe gaban t.v ina gogewa, Mimi ta dube ni tayi tsaki tace ''wallahi Aunty ko kadan yarinyar nan bata dace da aikin ki ba kwata-kwata ba ajinki bace, wai baki san ko 'yan aiki yanxu ba kowane irin kwashi kwaraf ake dauka a Abuja ba?

Kin dauko yarinya sai tsayi xankankan da manyan ido kaman ta cinye mutane, ni wallahi duk sanda naga dubeta sai naji gabana ya fadi, sabida tsoron da idanun ta suke bani'' Aunty ta yarfar da hannu, tace ''oho!

Fulanin Sariki ta aiko da ita kema kin san ban isa in maida ta ba, dama kadan ake jira a aibata ni, don ita ke xuge shi wai bai dace Peter ya dinga shiga uwar daki na ba...'' Mansina ta jirkito daga cikin kujerar da take kwance, ta dubesu daya bayan daya tace cikin mamaki.

''Wadanne idanuwa ne suke baku tsoro, kodai suke saku kishi?

Ki dubi idanuwa sparkle (masu walkiya) kuce suna baku tsoro?'' Ni dai jikina na rawa nayi hamxarin fita na barsu batare da naji amsar da Auntyn ta bata ba, bam san yadda suka kare ba.

Sai dai daga ranar na fahimci Aunty ta kara daure mini sosai haka duk wata kafa ta hutu, ta toshe mini ita a gidan.

Baby nada wata daya, watarana ina wanke-wanke kwanukan da aka ci abincin rana, Tom yana tsaye daga can baryar sa yana can kiciniyar daura tukwanen dare.

Wata murya muka jiyo daga can kofar shigowa tana kiciniyar shigo da akwati tare da neman ixinin shigowa falo.

Ba muryar matar ne ya samu fitowa dukkan mu ba illa yaren da take magana dashi.

Ni dai nasan wannan ba hausa bane kuma ba yarbanci ba haka ba fulatanci ba.

Wata yamusashshiyar baturiya ce, da alama ko cikin turwan wannan babu wata wadata a jikinta, tana tura akwatuna masu taya guda biyu (trolley), gashin kanta ja ne irin turawan nan masu jan gashi da ake kira blonde, xatayi shekaru arba'in, Tom ne ya amsa mata yayinda ni kuma na saki baki ina kallonta, shi yayi mata jagora xuwa falon Aunty...,
[10/5, 7:52 AM] A A Dboy: *_POST BY GROUP OF HYPE HAUSA NOVELS BOOK WHATSAPP 08064400100_
[10/7, 7:07 PM] A A Dboy: Tuna Baya 61-65
Can anjima Aunty ta rika kwala min kira na je na tsugunna a gabanta, tace ''kwashe shirgin ki daga dakin ki, ki maida su dakin da ke kusa da shi, wannan falle dayan, Tom xai kwashe injinan sharar da ke ciki, na bayar a sayo maki katifa'' nace ''to'' murya ta abin tausayi.

Ina kwashe kayan ina hawaye don ba karamin sabawa da dakina nayi ba, duk da cewa shima wancan dakin cikin bangaren Auntyn yake, amma babu toilet, don haka nakoma na tambayeta ko da wane toilet xan dinga amfani?

Ta kunduma min ashar tace ai talaka wai iya samun wuri ba, a gidan Ubanki ba a filin Allah kike kashin ba?

Kamar ince da ita ai in ma a filin Allahn ne, akwai kasar da xamu haka mu bixne, nan kuwa fa?

Da tangareren shine abin takawar ku?

Sai da taga dama tace in dinga shiga dakin muna amfani dashi mu biyu.

Daga baya Tom yake gaya mani mai raino ce baturiya Aunty ta dauko bada sanin Oga ba, sabida a gobe ne xata koma aiki, tuni ta so ta dauko ta tun Babyn yana sati biyu sabida hutun da aka deba mata ya cika.

Yace Oga yayi-yayi ta aje aikin nan ta kula da yaron taki, nonon ma da take bashi, wanda ba kullum ba, ba karamar badakala a ka kwasa da ita ba kafin ta yarda ta dinga ba shi sau uku a rana, sai da yayi karar ta gun Baban ta tukunna.

Don tana tsoron Baban ne yasa take bashi amma ita tana ganin rainon yara bai dace da ita ba wannan lokacin da take kan gabar kuruciyar ta, haihuwar ma Allah ne ya kaddari yaron mai numfashi ne a doron kasa, amma bata shirya mata ba, ba kuma kokarin da bata yi ba don xubar da cikin abin ya ci tura, karshe dole ta hakura, don har kasar waje ta je a fitar mata sun tabbatar mata ko dai ita a rasata ko mahaifar gabadaya, sabida cikin ya girma sosai a lokacin shiyasa ta hakura.

Nace ''amma da aka haife shi ai gashi nan tana son shi, ko kuda bata bari ya taba mata shi''.

Yace ''wannan ne kuma bani da tabbas a kai (tana son shi ko bata son shi?)'', Tun xuwan Elizabeth bama jin dadin xama da ita, kwata-kwata ta maida mu 'yan aikin ta sai kace itama ba 'yar aikin bace.

Ita aikin Baby kawai take wanda nake ganin kullum ta sa shi cikin wani keke ta tura mai fankon fida a baki (kan fida kawai babu fidar da turawa ke sarrafawa don hana yaro kuka) ko ta dau keken goyon jarirai ta hada da bayanta ta kulle, bayan ta sanya shi a ciki, tana harkokin ta ko kallo bamu isheta ba.

Wani xubin kuma sai ta sashi cikin wani irin lilo mai kamar gado tana cillawa a hankali, hatta madarar da take bashi a kididdige take, sai ta auna, ko kusa ko da wasa bata bari wani cikin mu ya je ko kusa da shi.

Duk abinda Tom ya dafa sai tace bai yi mata ba, ya sake dafo mata wani.

Wata rana kuma taje kasuwar Wuse (Wuse-Market) ta sayo kaguwa da dodon kodi taxo ta soya, yawancin abincin ta kwari ne, in ta so kuma ta aiki Peter manyan gidajen cin abinci dake cikin Abuja ya sayo mata abincin kasarsu, wanda duk rabin su tsutsotsi ne da ganyayyaki.

Ranar da na fara ganin ta tana loma da tsutsotsin nan, wuni nayi ina kwarara amai sabida kyankyami, daga ranar kuwa ko plate ta taba bana kara cin abinci da shi, ita kanta ma tsantsamin ta nakeyi.

Gata da kaxanta a toilet, sai ta cire auduga (pad) batacciya ta ajiye a kan bahon wanka, sai dai ni da abin ke daga min hankali in dauke mata.

Ko ta jika kaya taki wanke su sai sunyi tsami haka tun xuwanta bandakin mu yake wani irin xarni.

Ni dai na ji an ce turawa suna da tsafta, amma wannan ko a cikin kaxaman turawan ma ta daban ce.

Ko brush tayi bata san tasa ruwa ta wanke kumfar daga cikin sink ba haka xata barta ta bushe, ko kuma ni in wanke mata.

Gata da fadan tsiya, Tom boyi-boyin ta, Peter dan aiken ta, ni kuwa 'yar aikin ta, Ejiro da baya sakar mata fuskar har da xata raina shi, shi ta mayar makiyin ta, kullum cikin bata shi take a wajen Aunty, don dai Auntyn tana son aikin sa ne kawai da tuni tasa an sallame shi.

Tsaye muke ni da Tom a kicin kowa na aikin sa, yayi kwafa yace ''nifa xaman matar nan ya ishe ni Tine'' nayi dariya nace ''da yake kai ka ajiye ta ba?'' yace Allah ba xancen wasa ba, kiga kullum sai na gama abinci taxo tace bai mata ba, in sake, an gaya mata aikin ta nake, Allah ko Oga na ban taba yi mai girki yace bai mishi ba, sai wannan matar, who the hell she thinks she is, tana 'yar raino ina kuku, matsayin me ta fini?'' Nayi murmushi da ya kara kular da shi don ni kadai nasan hakurin da nake da Elizabeth, shi nashi shafar mai ne ''kome yake yi daurin gindi ta samu daga Uwargijiyar ta, amma da baxa ta yi ba''.

Tom ya kuta yace ''ban ga dama ba ne, na rantse da tuni da bar gidannan...,
...don Oga bai san da xaman ta ba, a tunanin shi Aunty na tafiya da Babyn wajen aiki ne'' nace ''akan me xaka fada mishi?

Ina ruwan ka da sha'anin su, kai dai kayi aikin ka na kuku, a biyaka ba shikenan ba?
Chapter 13 · 0% Book details