Sashe 5
Tuna Baya Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read
Baba ya shigo da sandunan rake na raba na ba Goggo tace baxa ta sha ba wai ita likita ya hanata shan abu mai xaki.
Muna xaxxaune muna shan rake sai ga almajirai suna shigo da kwalaye muka bisu da ido; kowa yayi shiru sai da suka kare Auwal yace ''shin daga ina aka aiko ku ne Tanimu?'' ''Yallabai Bellon gidan Waxiri ne, yace wai a kawowa mara lafiya, da yamma xai shigo ya dubata in ba damuwa'' ya fiddo wata jaka fara tas, shake da kaya yace ''wai wannan na Atine ne''.
Baba ya mike yace yana ina?
Ba xa'a karbi kayan Atine ba, amma na mara lafiya an gode.
Abinda yayi ma kadai ya isa, Allah ne kadai xai biya shi, don haka ku maida wannan''.
Sani yace ''haba Baba!
Bellon dan wa yake wa Goggo wahala, ba don Atinen ba?
Ba kuma a mayas da hannun kyauta baya''.
Baba ya murmusa yace ''Sani, tunda nace a mayas, to a mayas''.
Sani ya san Baban mu sarai, mutum ne mai kaifin basira, tabbas akwai abinda ya hango.
Shi da kansa ya dauki jakar ya nufi dandalin hirar su, aka sanar da shi Bello ya je kiran Maimartaba, can ya xauna jiran shi.
Inna ta saki baki tana kallon ikon Allah, Auwal na bude kwalaye yana yiwa Baba bayanin locozade ne maras lafiya ke sha don maida kuxari, katon na madara peak da katon din milo kayan shayi ne, Heinz-beans wake ne na gongoni.
Wannan mai kwaya kwayan na cikin kwali sukari ne, shi kuma wannan tang na kwalba lemu ne irin lamurje, ake xuba suga da ruwa a sha.
Wannan na xungura-xunguran gongoni dankalin turawa ne aka sarrafa haka, sai magungunan Guggo da likita ya rubuta da xa'a sallame ta.
Baba bai ce komi ba, sai ma cewa yayi a hada su yadda suke akai karkashin gadon sa, in aure Allah bai yi nufin sa ba, ina xamu nemo su?
Ni kam kaina a duke yake, tsoro da fargaba sun cika ni, ji na nake kamar wata bare a cikin su, kamar kuma wadda ta aikata wani gagarumin laifi.
Ina ganin sanda Inna ta kyafta ma Atika ido suka mike suka shiga daki, Baba da Auwal suka nufi masallaci don bin jam'in sallar Magriba.
Nima na mike na xubawa Amarya ruwan alwala ita da Goggo, nayi alwala nayi sallah na kara nemawa Goggo sauki wurin Ubangiji, na kuma roke Shi, idan tarayyar mu da Bello akwai alkhairi a ciki, ya cire min masifar tsoron shi da ke gallaba na, ya tsayar min da hankali na wuri guda.
Har muka yi Isha, shiru ban ga Atika ba,Amarya ta kare tuwon dawa da miyan xogale ta kira ni in kaiwa Inna, in kuma kira Atika mu ci.Nayi sallama ba'a amsa ba, suna can kuryar daki inda na jiyo sheshshekar kukan Atika, sai muryar Inna kasa-kasa ''kiyi shiru abinki, Atika na kibar asarar hawayen ki a banxa da wofi, su aureshin in gani, ai ba tun yau ba nake gaya miki mutanen nan basu kaunar xaman mu a gidan nan amma kinyi sautun mahaukaciya dani,kin nace a gindin su, ke kenan Atine sama Atine kaxa ke mai 'yar uwa,ai gashi nan ta nuna miki karshen 'yan uwantaka tayi ma kanta miji mai ido
[9/24, 9:11 AM] A A Dboy: Tuna Baya 21 to 25
21.
Ko bakya sonshi tunda naji xancen ke xaki aure shi, wannan shegiyar afiruwar a gidan saraki?
Kirji kaman danmalele, kugu uwa an tatsile kuliya bisa kwalta, ke kuma a gidan manomi, waye Jibo?
Ai baxa ta sabu ba.
In dai akwai boka, Mallam da bori a duniya BELLO BAXAI AURI ATINE BA, sai ke, ko kuma duk ku rasa''.
Muryar Atika ''wallahi Inna ni in baki sa ya soni ba, sai dai in mutu ba aure, wallahi shikadai nake so Inna, duk cikin samari na babu kamarsa, mai kyau ne dan birni kuma mai ilmin bokon nan irin na radiyo, ke baki ganshi ba fa...''nace naji ya isa, Atika, ASIRI FA GASKIYA NE, wallahi kin ji na rantse miki daga Atine har Amarya sai sun bar mana gidan nan, sai sun...
Na gyara murya na kwarara sallama sukayi tsit, ya tsumma cikin mai, Atika ta leko jikin ta a sanyaye idanun ta sun yi ja tace ''au, ke ce, baki shigowa?
Tun yaushe kike tsaye?'' Nayi murmushi ''abincin Inna ne na kawo, ke kuma in kin gama kukan kixo muci namu''.
Na kwanta rigingine ina tunanin maganar su Inna, wata xuciyar tace dani in fadiwa Goggo da Amarya.
Nasan Inna bata da imani ko miskala xarratin duk abinda ta furta xata yi, to sai tayi shi hankalin ta ke kwanciya, amma sai nayi wani xuxxurfan tunani sanda Liman ke ce mani.
''A kowane hali kika tsinci kanki, ki rike Allah, ki sanyawa ranki cewa yana tare dake a duk inda kike''.
Akwai kuma sanda yake yi mani nasihar munanan aiyuka masu kai mutum wuta, yace ''ku guji munafinci.
Cikin kaba'irai shima babba ne, wanda Allah (SWT) yayi wa ma'abotan sa tanadin wutar jahannama, inda yake cewa ''Innal munafiqina fid- darkil asfali minan nar'' ya kuma ce ''fa bash-shir hum bi adhabin azeem''.
Atika tace dashi a lokacin wai ''MEYE MUNAFUNCI?'' Yace ''shine; - Yi da mutane(cin naman mutane) -Hada husuma tsakanin mutane -Daukar xancen wani ka kaiwa wani -Zunde, yafice da kifce duka munafinci ne -Xama da mutum da xuciya biyu.
Saboda haka sai naja bakina nayi shiru.
Da dare Bello dan gidan waziri yazo duba Goggo na shi da abokinsa, sun shigo har cikin gida shi da abokin mai suna Muhammad ya gaishe da mutanan gida sannan aka raka shi dakin Goggo ya duba ta, ya cika su da alkhairi tana ta godiya, daga nan dakin Inna ta suka shiga nan ma tayi ta masa godiya ya ajiye mata kudi mai yawa, ta ce an gode Mamman Allah ya saka da alkhairi, sai kuma tayi sauri Tace ashe abokin na ka ne Mamman ko?'' sukayi dariya ''Mama ai nima Mamman din ne, a can Jos, Muhammad nike, ainihin sunan Muhammad Bello'' ta jinjina girman sunan tasa musu albarka tace ''Ka dinga hakuri da Atine, sai a hankali xaku saba, tace tsoron ka take, kuma dama dai halin ta wani iri ne sai Goggonta'' kai ya dukar cike da kunya Muh'd din ne ya amsa ''to Mama''.
Suna fita tana kwallan kira tace in dau kudinnan in mayar mai baxata amsa ba, ba kuma ta sigar rashin da'a ba.
A dan filin da ya xama xauren mu, jingine suke jikin buhunan kalwa, basu ko damu da warin kalwar ba, na russuna na gaida abokin da alama mai barkwanci ne yace ''naki in amsa Atine, ya xaki gaida Muh'd Jos, baki fara gaida Muh'd.
Karaye ba?
Bayan a dalilin shi kika ganni?'' Nayi shiru, kaina sadde ina dan murmushi ''Atine, kuma sai aka dawo da ajiya mai ita bai ce akawo ba, kin kyauta kenan?'' da kyar cikin 'yar siririyar muryana nace ''wane ajiya ne?'' ''Rigar sanyin Dan Karaye mana''.
''Wane dan Karaye?'' ''Au, baki san shi ba?'' ''Da na san shi baxam tambaye ka ba'' ''to dago dubar ni, in nuna maki Dan Karaye''.
Kamar wata doluwa, wai sai na dubeshi har ga Allah, ni da xuciya ta daya nake magana.
Ashe tuni har ya canxa wuri sai muka hada ido hudu da Bellon da ke rikita ni.
Idanuwan shi lumsassu ne, kuma manya tamkar nawa, bakin xanen idon shi har wani kyalli yake na musamman cikin hikimomin Ubangijin halitta.
Wani irin kallo ne da shi mai jan hankali da ban sha'awa, ban iya na dauke kwayar idanuna ba kaxalika shi din.
Dan Karaye, kokari yayi ya sarke kwayan idanun mu sarkewa mai ban mamaki.
Ke da gani kinsan ya saba yiwa mata, ba ni ce ta farkon ba.
Kallon da ko kin ki Allah, dole ki fada a tafkin kaunar shi...
Ni naga Bello mai kyau ne, amma ba wannan ne ya raxana ni ba; tsabar kwarjini da cikar xati, Ingarman namiji ne tako'ina, Bello Waxiri bai da makusa.
Dogo ne hakika, mai ginannen kakkarfan jiki, ga wani lafiyayyen saje da ya aje tun daga gefen kunnuwansa har xagayen lafiyayyen bakin shi, lebba gare shi masu sulbi da sheki bakake sidik.
Shi ba fari ba shi ba bakii ba gashi nan dai ruwan kasa mai daukar ido.
Sanye yake da Jabba (kayan sarauta) kufta da wando na wani rantsatstsen yadi ruwan madara, wani irin budadden takalmi ne a kofar sa, wanda ya tona asirin lafiyayyun yatsun shi da sullubebiyar kafar shi tamkar bai taka kasa, gashin kansa baki wuluk sai sheki yake kaxalika bakar daran dake kanshi, gassun ta na reto a wuyan sa.
Ta ko'ina nasan Bello ba tsarana bane.
Koda yake nima wai ina da kyau inji Goggona?
Oho.
Tafin Muh'd., har tsakar kan mu, gabadaya muka juyo muka dubeshi, idanuwan mu jaxur; so kenan, ke aiki a tsakanin mu.
Dan Jos yace ''a'ah Atine!
Daga cewa ki dube ni, in nuna miki Dan Karaye, sai ki dulmiya gabadaya?
Ya dace in kauce hakannan, don naga Dan Karaye bai son fadin son a gabana.
To an ce dai kallo in ya wuce daya, biyu haramun ne na barku hakannan''.
Bello bin shi yake da ido kamar ya ga mahaukaci sabon kamu yace ''Atine na aiko miki da sako kika ce a maido mun kayana?
Don sunyi kadan, ko don har yanxu kina jin tsorona?'' na harare shi kasa-kasa ''na ji ne daga bakin da ba xai mun karya ba'' ''ni wallahi bana tsoron ka, da ina tsoron ka ashe da ban rama xagin Ubana da akai ba''.
Yayi murmushi a karo na biyu ''to tunda baki tsoro na, kuma ki na son in yarda baki tsoron, shin yaya sunana?'' '' Dan Karaye mana''.
''Ai kin ji tsoron kenan, wannan ba suna bane don ko ke 'yar Karaye ce, amman ai Atine ce, don haka ya sunana?'' ''Na manta'' ya sake murmusawa ya kashe xancen ta hanyar russunawa ya tura min jakar daxu gabana ''Atine, ba'a maida kyautar miji, don haka kada in kara baki abu ki maido manni, kina ji na?''
Ya dan fiddo ido na kara tsorata don haka ya saki, ya koma xolaya.