Sashe 16
Tuna Baya Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read
Ya fada ya kara maimaitawa har sau uku, domin kara tsoratar dani ga kowace ce Uwargijiyata (Aunty Mubina).
Bayan tafiyar Tom, na dade ina sake-sake, gami da jinjina abinda na ji a raina, ba a jima ba naji dirin ribda-ribdan motoci, na dau Jawad cikin nustuwa nayi mai wanka na fiddo sabbin kayan shi da ban taba sa mishi ba na kakin sojoji, na saka mashi, na xura mai sabon takalmin shi, rufaffe sak dana sojoji mahadin kayan, na taje yalwatacciyar sumar shi na mulke ta da mai mai kamshi, sai kyalli take ta kwanta lub a dokin wuyan shi.
Na dauko turarukan shi Dune da Caleutta na feshe shi sosai.
Na dura mai kamu na goge mai baki, na bashi ruwa yasha ya koshi yayi gyatsa, ga yadda yake mun rigima nasan so yake in goya shi yadda na sabar mashi bayan cin abinci.
To amma ta yaya xan goya shin?
Uwarsa ta hana balle Uban sa?
Na sashi a kafaduna nayi ta jijjiga shi amma yaki yin shiru, kuka harda digon hawaye.
Ejiro ya shigo ''A'ah Jawad kuka kake, why?
Papa ya dawo'' ya karbe shi ''Nanny Tine, Oga wanna see his son, gashi yana kuka'' nace ''goyon da nake mai yake so, gashi bana son su san ina goya shi, kai dai kai shi hakan, watakila in ya ga Uban yayi shiru''. (An dan jima Ejiro ya dawo) ''kixo ki goya shi yace''.
Gabana ya fadi dam!
Xuciyata ta tsinke, na fiddo 'yan idanuwana hantar cikina na murdawa, muryata abun tausayi nace ''Haba Ejiro?
Meyasa kace ina goya shi?
Idan ya gayawa Aunty fa?'' Ejiro ya kyalkkyale da dariya, yayi mai isarsa ya gaji ''Tine, Oga ke biyan ki ba Aunty ba, shi yace kiyiwa Jawad rainon AREWA, shima dan garin ku ne ya san goyo.
Shi da kansa yace in kiraki, ki goya Jawad yayi barci.
Ya kuma tambaye ki, me kike ba Jawad yayi girma mai ban mamaki cikin watanni biyu da yayi bai ganshi ba?'' Gabana tamkar ana luguden kirjina, doguwar rigar jeans ce a jikina mai kauri, cikin kayan da aka sai min babu kallabi balle mayafi, sai na dauki tawul dina da ke toilet na yafa, Ejiro na gabana ina binshi xungul-xungul kamar wanda...,
...tayiwa sarki karya, har falon yallabai, wanda duk gidan babu kamar sa, haka ko da wasa kafata bata taba taka hanyar ba.
Na makure can gefe.
Ejiro ya russuna gefena.
Ya fito daga wata kofa rungume da Jawad a kafadun shi, ban daga kai ba balle in san kamannin shi, illa ina gani farin tafin kafarsa mai tsayi.
Gaba daya falon wani irin kamshi da sanyin ni'ima ke fita cikin shi mai ratsa kasusuwan jikin dan adam.
Da ya doso mu, xama yayi cikin kujera can nesa damu.
Sukayi magana cikin turanci da Ejiro, ban fahimci me suke cewa ba domin turancin nashi ma na ji shi ba irin na su Tom bane.
Wannan lafiyayye ne ba broken a ciki.
Abinda ya kidima ni, ya kuma sani mance inda nike, shine muryar shi tayi mun bala'in kama da ta BELLO WAXIRI.
Karon farko da naji muryar sa suna magana da Aunty, watannin baya, cikin fada yake magana, don haka ban ji hakan ba sai yau.
Can cikin tsakar kaina na tsinkayi sautin nashi yana cewa ''bakya gaida mutane?'' Nayi firgigit na xabura nace ''ina yini?'' ''Lafiya, yaya kike da kukan Jawad?
Tun da na dauko shi yake kyankyara min kuka, sai yanxu Allah yasa yayi barci kunnuwana suka huta'' nayi murmushi kaina a kasa ''ni baya min kuka'' ''me yasa?'' ''Nima ban sani ba'' ''don ke Nannyn shi ce?'' Nayi shiru cikin rashin sanin abin cewa, ya basar da xancen yace ''ina Uwar shi ta je?
Bayan yau Lahadi ba aiki?'' ''Tace mun xata gidan su Mansina, xata nemi Yallabai a waya'' yayi dariya har Ejiro sabida yadda na fadi sakon babu kari, babu ragi da yadda ya gaya mani ''bata san xan dawo ba yau?
Ko don ita bata damu da mijin ta ba, balle dan ta?
Yau watanni biyu bana kasar, na dawo cike da dokin su, amma rana daya an kasa tsayawa domina?'' Duk mukayi tsit, daga ni har Ejiro, ko tunani yayi wannan ba ruwan mu bane?
Yace ''O.K, xo dauke shi ki goya shi'' na mike cikin nutsuwa, na isa gareshi, na mika hannu ya miko min Jawad, sai na hade da hannuwan shi duka biyun, YA ILAH!
Na tsorata, na kidime, na rude nace ''kayi hakuri, ban sani ba''...,
..''kema kiyi hakuri, to goya shi ina gani ko na koya, nima wataran in hutar da ke!''
Na dago ido a rikice na dube shi, alamun mamaki karara a fuskana, Ya Subhanallah!
Yanxu na ga inda Jawad ya debo kyau, tsurar sa.
Wannan wane irin mutum ne?
Saukin kan yayi yawa.
''Ban taho da abinda xan goya shi ba, in munje daki xan goya shi'' ''wannan towel din na kanki fa?'' Da sauri nasa Jawad a bayana, cikin kwarewa nasa towel na daure shi kam da jikina.
Jikina ya bani kallona yake yi, ''daga yau duk sanda xan ganki, in ganki goye da Dan ki a bayanki, ina son ganin mace da goyo, kin ji?'' Na gyada kai, har yanxu a kidime nake, muka fita.
Ejiro yana ta dariya cikin turanci yace ''na so Tom ya ga wannan drama.
Kin ganki kuwa a gaban Oga, kamar wata 'yar mage a gaban Sa (namijin saniya)'', na harare shi ''ban gane 'yar mage a gaban Sa ba?'' ''Ina nufin shi dogo, kuma kato, ke kuma 'yar mutsila'' mukayi datiya ''amma Ejiro Ogan ku ya burge ni, baya kyamar talaka, sannan halayyar shi gaskiyar Tom ne ba daya da na Aunty ba, kwanaki hannu na ya kai ga na Aunty, cikin kuskure garin amsar Jawad, wallahi xabga min tafi tayi wai xan shafa mata muni.
Bata taba tambaya na ya nake da rigimar Jawad ba ko sau daya.
Ko a masu kudi da ilmin, samun mai irin halinshi da wuya''.
Yace ''Amma matar shi bata san da wannan ba, xan iya ce miki bai yi sa'ar aure ba.
Ni xan gaya maki wanene Ogana!
Yau shekaruna sama da biyar tare dashi, ko tsawa wannan bai taba hada mu dashi ba.
Yana treating din mu as perfect human beings; babu maganar bawa da Ubangidan sa, sai mutunta juna da baiwa kowanne hakkin dan uwan sa da ke kan shi.
Bata kyautata masa sam, bata kuma da lokacinsa, bayan kallo daya xaki mata kisan ita ba sa'ar auren sa bace, sai kaddara.
Kullum cikin bambancin ra'ayi suke, kanta kadai ta sani da aikin bankin ta.
Kin ganshi ba maxauni ba, sai yayi watanni biyu baya kasar ya dawo tana gidan kawayen ta ko office dinta, ba abinda ya kai wannan aikin muhimmanci a gareta, a shirye kuma take don ta rabu da komi, domin tsira da shi, wata ran in sun soma...,
Haurawa har mu mukan ji, amma an fi jin nata, don bata da sirri ko kadan.
Allah ya hore masa iyaye, ta raba su, 'yan uwa da duk wani abokin arxikin sa.
Abokan aiki kadai ta barshi da su'' nace ''to ku ina ruwanku kuke sa masu ido, in suka kore ka naga inda xaka je kayi aikin kuku kana karatu a bati''.
***********
Washegari Aunty ta tafi aikin ta kamar yadda ta saba, wato karfe bakwai da rabi, sai 10:00 Oga ya fito shima cikin shirin nashi ofis din, Tom rike da suit-case din shi.
Shi kuma ya tarayo falmaran din Australian-Suit din da ke jikin shi a kafadun shi.
Da kanshi yayi sallama dakin da nake, sai da na amsa ya murda kofar suka shigo ciki duka.
Rungume nake da Jawad a kirjina, yana tai min kiriniyar sa irin ta lafiyayyun jarirai ina shan dariya.
Nayi saurin tashi xaune na xube a kasa na gaishe shi, ya karewa dakin kallo tsaf kafin ya xauna a gefen gadon, ya dauki Jawad yayi mai 'kiss' a kuncin shi, yace ''Yello my bouncing beautiful baby, how a do u do today?'' Tom yayi dariya ni kuwa na sake nutsuwa, ''ke bakya daura kallabi ne, kullum kuma kai ba kitso, me yasa?'' '' Bani da kallabi, kitso kuma waye xai mun ranka ya dade?'' Yayi murmushi, ''xam kawo miki kallabi da atamfa har da shadda a dinka maki xane, don na lura kina takura cikin wadannan kayan wanda na tabbata tsarin Mubina ne, kina so?'' ''A'ah ranka ya dade'' ''meyasa?'' Na tuna sanda take ce da Talatu (ki xabo mata kayan sawa, wanda ba'a daurawa, idan naga xani a ciki, Ubanta xan ci).
Ni kuwa duk wani abu da xa'a ci mutuncin Ubannan da bani da kamar sa, ina gudun shi, ina nesantar shi ina kuma rokon Allah yayi mun katangar karfe da shi.
Ya lura tsoron Mubina nake ji bai kara maganar ba.
''Ina so ki gaya mun tsakanin ki da Ubangijin da ya halicce ki, me kike bawa Jawad tun xuwanki?'' Ban ji tsoro ko shayi ba, don na lura ba halin su daya da matar shi ba ''Kamun waken-suya ne da ruwan da aka ce kar in bashi sai yayi wata shida.
Rannan yana shaquwa, naji tsoro na bashi ruwa, data tsaya kullum na bashi ruwa da sauri yake shanyewa, amma bana bashi na famfo sai irin wanda naga Aunty tana sha''.
''Good (da kyau) Nanny Atine, xan sa a kawo buhun waken-soya.
Da yamma Tom xai kai ki wurin Yarbawa masu kitso, su dinga yi miki weekly (duk sati) kin ji?'' Na gyada kai, na sake kaskantar da murya nace nagode..,
[10/8, 5:11 PM] A A Dboy: *_POST BY GROUP OF HYPE HAUSA NOVELS BOOK WHATSAPP 08064400100_
[10/8, 5:19 PM] A A Dboy: Tuna Baya 76-80
Ranar wata litinin bankin Omega an rufe shi, sakamakon gagarumar satar da suke xargin Akantocin sun masu, Aunty na gida kenan, Yallabai kuma bai fita Ofis da wuri ba, suna karya kumallo, take gaya mai wai cikin da take dashi ya bare tun sati biyu da tafiyar sa.
Ya kalleta kawai, ''ko kuma kin barar ba?
Ke dai Musuluncin ki akwai question mark (?) a cikinsa, mtsw!