← Book details Tuna Baya Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 15 OF 51

Sashe 15

Tuna Baya Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

Kaunar yaron ta tsirga mani tun daga tsakar kaina, xuciyata, bargona, kasusuwa har yatsar kafata.

Na fiddo shi daga cikin gadon na rungume shi tsantsan a kirji na, tamkar na tsaga kirji na sanya shi, in haifo shi ya xan mallakina.

A haka barci ya sure mu, motsin shi na ji cikin barcin yana shafa ni yana neman nono kenan.

Na tashi na farke katon din da ke ajiye gefe, na fidda wata irin madarar yara, wannan ta musamman ce.

Hoton kyakkyawan Babie ne a jiki, amma sai naga bai fi Jawad dina kyau ba.

Na debi adadin da Sister Sadiya ta ce min, na duba iya lambar da ta nuna mini a jikin feeder na tsiyayi ruwan dumi da ke cikin flask na hada na jijjiga sosai, ya bar shi ya dan shan iska, na xaunar da shi a cinya ta, nasa mai kan fidar a baki, ya ko kama da karfin sa, kadan yaki shanyewa.

A raina nace kawai a ce baxan ba dan Adam ruwa ba, sai yayi wata shidda?

Don bani da imani ko don me?

Yaran gidan mu ana basu ruwa tun a ranar da aka haifesu, kuma sun rayu lafiya, don haka sai na ba Jawad ruwa.

In Tom xai kawon abinci, yakan hado da wani ruwa da naji yana cewa FORMOSA table water, naje kithcen na dauko mara sanyi, na xuba a murfin fidar kadan, na daura mai a baki, yaro ya kwalkwale ruwa da sauri, na kara cika murfi, ya shanye, na kara mai, ya rage rabi, yana dubana da kyawawan idanun sa ya shiga bangala mani dariya, nima sai naji dariyar ta kamani.

Na sashi a bayana da tawul din sa na goye shi cike da matsananciyar kauna.

Ko Uban wa yace mata goyo na karya kafar siririn yaro?

Ni har bakwaini na goya, na kuma sauke shi lafiya.

Daga goya shi sai barci ya dauke shi, na kwanta rub da ciki da shi a bayana.

A haka Tom ya cimmana, hannun sa rike da bakar leda, bai san sanda ya saki bakar ledar a kasa ba ''lalala!

Ga goya dan kwan gidannan?

Babu goyo, babu goyo, Aunty xata xage ka Tine'' ''Tom mu Hausawa da goyo muka rayu, itama Uwarta ta goya ta, akan me xata ce baxa ta goya nata ba?

Akan wani dalili mara tushe da asali?

Kayi hakuri baxan bari ta gani ba'' ya kyabe baki, daga bisani yayi dariya, nasan mamakin karfin hali da karambani na yake ''is not my own business'' ''me kenan kace?'' ''Nace (babu abinda ya shafe ni), i brought you something special (na kawo miki wani abu na musamman) wanda nasan xaki yi murna dashi''.

Ban ji me yace daga farkon ba, illa naga ya xaro wasu littafai iri-iri daga ledar da ya shigo da ita, duka na koyon karatun turanci da rubutu, irin na 'A for Apple' da sauran abubuwa da sunan su ya fara da A, haka ya tafi har Z, kowanne da hoton abin radau a cikin kala, muka shiga karatu, ko abinci bamu ci ba.

Karfe hudu ya tashi ya kawo min farfesun gudar kaxar gidan gona, da biredi wai inyi maneji kamin ya gama girkin dare.

Nayi sallar la'asar sannan na sauke Jawad, sai ya bude ido, na sake dama mai madara, wannan karon harda nutrient din da tace kar in bashi wai ya wuce sha...,
...shan shi, abinda local yara ke sha ne, na kuma bashi ruwa, na kaishi cikin robar wankan shi na fidda mai pampers, wadda bai yi komai cikin ta ba sai gumi.

Nayi mai wanka da wani irin tsadaddan sabulun Babies dana gani cikin kayansa, bayan na xuba duk wani abu da sister tace in xuba.

Ina sanya mai kayan sanyi Tom ya shigo dauke da tray, nace ''da ka koma dashi, wannan ya ishe ni sai ko 'dinner' naji kana cewa ko?'' Yayi min tafi ''Yauwa, haka nake so Tine, ka dinga rike duk abinda na fadi cikin turanci, da haka xaka saba.

Daga sati masu xuwa, ka daina magana 'in Hausa'.

Sati na xagayowa, na soma yara turanci da Tom, ya dinga kunna min labarun BBC, labarun kasa da sauran su, suna yi da babban turanci yana bani bayani cikin sassaukan turanci, rubutu kuwa na iya rubuta su Ant, Ball, Cup.

A satinne ta kara tura ni saloon, da wurin gyaran akaifa, don wai taga alaman yakushi a wuyan danta, bayan shi ya yakushi kan sa.

Wannan karon da Tom ta tura ni.

Wani yammaci bayan ta fita, na gama dirkawa Jawad abinci na goya shi, na tadda Tom da Ejiro a kitchen, suna ta kiciniyar kwabin coconut-sandwitch da beef burger, abin ya burgeni, ya kuma bani sha'awa, ganin komi da inji suke yi, ba wahalar komi sai ta tsayuwa.

Nan na xauna kallon su har suka kare.

Na tabbatar abin ya xauna a kaina, ko yanxu akace inyi yadda sukayi, xan iya.

Daga ranar duk sanda suke girki, in dai Maman Jawad bata nan, sai in goya shi inje in xauna inyi ta kallon su, muna hira ana kara min bayanin komi.

Watarana nace da Tom don Allah ya samo min waken suya (soya-bean), ya tambaye ni abinda xan yi dashi nace wani kamu ne muke sha a kauye.

Kullum sai inyi kamun waken suya mai tsabta, in shige da shi dakina in kulle, inyi ta durawa Jawad, shiko komi na bashi ya shanye shi tas.

Bama bari yayi awanni biyu ban bashi abinci ba da ruwa, ba ruwana da wani kididdige, shiyasa yake yawan fitsari da kashi, in fidda in wanke shi tas, in canxa masa.

Cikin watanni biyu kacal da dawowar shi hannu na yaro ya shiga wata irin kiba da wayo mai ban mamaki.

Wani marece Tom yake ce da ni ''Tine ka iya raino mai kyau, hannu ka mai albarka ne.

Dubi yadda Babe ya koma daga xuwan shi hannun kam yaro dan siriri ya koma Bouncing Baby''.

Washegari ranar naga sun fiddi na'urorin gidan, dukkan ma'aikatan sun kasa xaune, sun kasa tsaye aiki suke cikin kuxari da xafin nama tamkar anayi masu allurar kuxari.

Ga wani nishadi na babu gaira babu dalili, tattare da kowannen su.

Maman Jawad ta iske ni har daki na tana daga shi da kyar, don wai bata iya daukar shi yanxu kada ya sata ciwon kirji.

''Yau Abban Jawad xai dawo daga tafiyar da yayi Kasar Canada, idan ya nemi Dan sa, ki je ki kai masa, ki tabbatar kin gyara shi sosai, in ya nemeni ki ce ina gidan kwamishina Mansina ce ke fama da mura, amma xan neme shi a waya''.

Na amsa da ''to''.

Ina sallah, nayi sujjadar karshe ina sadar da bukatu na ga Lillahi, Tom ya shigo, ya xauna ya xauna har ya gaji ya tafi, can kuma ya dawo ''Tine pieous (wato mai Ibadah), ni xani (lecture) sai biyar xan dawo.

Mun gama shiryawa Oga Spanish-Lunch, idan xai ga Jawad xai neme ki da kansa, ba ruwan shi da matsantawa irin na Aunty''.

Na rungume Jawad a kafaduna da ya soma kokarin tashi daga barci nace ''yauwa!

Dama tuntuni ina so na tambaye ka Tom, tun da nake, ban san dan aiki yana da 'yancin xuwa makaranta ba, har ya fita sanda yake so, ya dawo sanda ya ga dama?

Imagine!'' Ya kyalkyale da dariya sosai yace ''Ogan mu, mutum ne da baya dannewa dan Adam hakkin sa ko kadan.

Mutum ne mai masifaffen ilmin boko.

Ba kowadanne iyayen gida bane irin Ogana ba.

Bai xama da wanda bai ilmi, shi ba maxauni bane haka matar shi da muke xamanta bata faya xama ba.

Mu biyar ne duk maxa, ita ta kawo mu ba shi ba, amma yace lallai tunda munyi sakandire, mu tafi makaranta.

Xama a karkashinsa baya nufin bamu da 'yancin sauran abubuwa masu muhimmanci a rayuwar bil adam musamman ilmi.
[10/7, 7:08 PM] A A Dboy: *_POST BY GROUP OF HYPE HAUSA NOVELS BOOK WHATSAPP 08064400100_
[10/8, 5:11 PM] A A Dboy: Tuna Baya 71-75
Ni da Ejiro, muke kuku, don haka muke karantar catering, Peter da Joseph da ke kula da gida, tattalin gida suke karanta, Samson da ke kula da shukoki yana karantar ilmin tsirrai (Botany) a Jami'ar Abuja.

In daya nada darasi, daya baya dashi, xai yi aikin gida kamin daya ya dawo koda ba aikin sa bane, wanda yawanci, mu ke cinye abinda muka dafa domin ita bata cin abinda ya hau wuta, sai na gongoni.

Shi kuma Oga, asalin shi kauye, bai son wanna tsarin, in yana nan xai bamu odan muyi masa tuwon semovita miyan danyen kubewa da busashshen kifi, yace kunun aya yace kunu xaki.

Wallahi idan kinga abinda yake ci, sai ki raina mishi.

Matsayin shi; Minister of Foreign Affairs, (Ministan huldar Nijeriya da kasashen waje).

Sun yi artabu da Aunty akan xuwan ki, domin a da, Peter ne yake mata dukkan ayyukan da kike yi, Oga yace bai lamunta ba, katon na miji ya dinga mata hidima, ya gayawa mahaifiyar shi cewa a sama mata 'yar aiki mace, kuma karamar yarinyam haka sunyi artabu akan cewa da yayi ke ki dinga kula da Jawad, tunda ta dage baxata bar aikin ta kan rainon yaro ba, domin Aunty ta dauko raino daga Brussel can cikin kasar Belgium (Elizabeth) da xai rika biyan ta tsabar kudin Amurka dubu dari da hamsin a kowanne wata, shi kuma ya dage, wanda ba dan AREWA ba, ba kuma dan masarautar sa KARAYE
KARAYE ba, baxai rainon mashi dan jinjirin shi a duniya ba.

Ita tana ganin Bahaushe kaxami ne, sai kace ita ba bahaushiyar bane. ('Yar asalin garin Xaria ce).

Ki saki jikin ki da Oga mutum ne mai saukin kai, xaki ji dadin xama dashi fiye da Aunty, domin suna tare ne amma halin su daban-daban.

Sai dai kada kiyi mata abinda bata so ko kadan, xata ci miki mutunci daga ke har shi, don bata darajashi sam.

Talaka da dabba a wurin Aunty basu da maraba balle kuma dan aikin ta.

In kinga yadda shi kuma yake jan mu a jiki, yana jin damuwar mu, kamar kannen shi da suka fito ciki daya, wadanda ta haramta masu xuwa gidannan sam, kiyi taka tsan-tsan da Aunty, ''bata da mutunci''.
Chapter 15 · 0% Book details