← Book details Tuna Baya Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 41 OF 51

Sashe 41

Tuna Baya Part 1 Complete Hausa Novel · about 6 min read

Ya hade fuskokinmu duk da maganan yana yintane kasa kasa amma na gode Allah da ya mallakamin ke ya hana shi yaso salwantar min dake zubaidah Allah ya fishi,yaso salwantar min jawad dina dani duka,matar shi da 'ya'yanshi saboda san kai irn nasa Allah zubaidah da kin mutu bazan taba yafewa bello ba.hannuna na kai na toshe mai baki amma sai ya juyoni all over muka fuskanci juna,ya janye hannayena a bakinsa ya cigaba da magana.a lokacin nayi zargin kina son bello,in ba hakaba ya za'ayi ki yarda ku kadaice a mota har ku tafi wani huri ku kadai ba tare da abokan tafiyar kuba,kisan Allah zubaidah a lokacin jinayi na tsaneki,domin na tsani a yaudareni, ban aureki ba bisa tursasawaba sai bisa amincewarki,to don me daga baya zaki ha'inceni?ni kadai nasan masifar son da bello yake miki,amma wallahi zubaida nafi bello sonki,idan baki sani ba in gayamiki na fara sonki ne tun randa na fara ganinki,wato ranar da nace ki goya jawad a gabana,sai dai ban taba sanin kece atinen bello yaso aura ba sai ranar da fulani ta kirani a lokacin da za'a kai ki asibiti,da neman alfarma ta na wai na fasa auren ki na barwa bello kece atinen da bello keso a lokacin ne abubuwan dasuka faru ke ta dawo min sabbi (fresh)na tuna tun zuwan ku walimar ya da ya shirya ya canzamani, haka fatima ke gayami itama duk ya canza mata tunda aka fara bikin mu,ita auren nan ya jawomata annoba ban ji haushin bello ba ko kadan ko ba komi so ke damunshi irin wanda ke damuna? zubaidah a kuruciyata bayi sa'ar aure ba banyi aureba sai dana shekaru talatin baya ban tsinci komi cikinsa ba face bakin ciki da dana sani mai iyaka ,ban taba jin ina son wata 'ya mace ba sai akanki nayi jinyar son nan shekaru dai dai har takwas sanna rana daya ace in fasa aurenki?nida bello cousins ne mahaifiyar shi kanwar mahaifiyata ce tare muka taso tun muna kanana sai karatu ya rabamu bello yasha gayamun irin son da yake miki
da kuma kaddarar data fada aurenku,sai a lokacin na tuna komi gashi kun fita tare har kunyi accident ni na zame muku karfe kafa kena bari ku nuna min ku laila da majnun ne,inyaso ni bakin ciki ya kashe ni a lokacin na fita hayyacina na samu fulani nace da ita zan rubuta miki saki sai bello ya aureki tun da na lura kema kina sonshi fulani tace hakan zai zamo rashin adalci a gareki tunda zuciyar bello aka sani ba'asan taki ba amma har in kina son bello zan gane ranar dana shiga dakinki,idan ma ke mayaudariyace in fara tabbatarwa tukuna sabidah zato zunubi ko da gaskiyane.na memi karin haske tace in har ki son bello zaki bashi kanki ko dan ku huce haushin tsohuwar soyyarku damin har dakinta 'yan unguwarku suka je suka gaya mata cewa bello yaje gidan ku ana igobe daurin aure kun shiga dakin awal kun rufe fiye da awa daya a lokacin hankalina ya tashi taji tsoron kar inyi kazamin aure amma bakin alkami ya riga ya bushe an daura auran babban farin cikinta jin cewa ke budurwa ce wannan kadai itace mafitarki itace tayi insisting lallai ayau duk bacin ran da nake ciki in shiga dakinki ingaya mata halin dana tsince ki. ni kaina banso ba amma da nayi tunani mutuncinki a idonta sai na runtse ido na na fadi hakkanan mohd jos yayi min bayanin komi a daren jiya,na kuma gamsu sai dai zubaidah cike nake da zargin kina son tsohon masoyin ki nayi miki katsalana
da cikin rayuwa?illah hadin kan da kika bani a daren jiya farat daya ya tabbatarmin ko ba komi ina da wani kankanin matsuguni ko yaya a zuciyarki you know ni har kullum mai baima dan adam hakkinshi ne nayi mamakin yadda daga daren jiya zuwa yau zubaidah kika zamo RUHI na kasa controlling zuciyata wai na rabu dake wa bello.a yau ina alnihin sanar dake cewa nima kama jawad nima taheer BAZAN IYA RAYUWABA BA TARE DA KEBA!na rasa me zance?tausayin yallabai da kaunarshi da na keji a yanzu,wani abu da bazan iya kwatantawa ba ka taba gayamin wani sentimental ogana a sanda nike YAR RAINONKA kace bana ma karya bana ha'intarka.
88....
toh akan me lokaci dana ke hakan ban ha'ince kaba,ban yima karya ba sai yanzu da nake a matsayin MATARKA,kasan ko matsayin ya wuce ayi masa karya da ha'inci ko yaudara gaskiyane ada naso bello so irin na kuriciya da kasan cewar shi daban da sauran samarin kauyanmu,amma wallahi tun ranar da muka rabu ban kara tuna bello da sunan so ba BELEIVE ME OR NOT YOU ARE THE ONLY ONE I LOVE TODAY AND ALWAYS.ka koyar dani yadda zan so ka yallabai tun ina ficicitata,son da har yakan sani kishin aunty mubina in kuma ji zafi in naga tana yi maka abubuwa mara dadi,in kuma yiwa kaina samun miji kwatankwacika ko mai irin hallayar ka,na duba na tace duk ban gani ba TAHEER wannan ya tabbatarmin lallai ni mai sa'ace dana samu miji kaman yallabai kulawarka da nuna kyautayi a gareni ya dasa wani gyambo cikin gudar tsokar zuciyta wanda yayi ta ruruwa har zuwa dare jiya dana mallaki TAHEER to akan me zan daga ido in dibi wani da namiji a duniya da sunan so ?babu kowanne namiji fanko ne nake ganinsa in na kotantashi da ogana bana jin kona rasa TAHEER zan kuma son wani bayan wannan ingantaccen son da nikewa ogana......

THEN SHOW ME IN ANOTHE WAY(nuna mun ta wata hanyar daban) muka rankaya ga dakin barcinmu,cikin wata irin soyyaya da harshe bazai iya bayyanawa ba wannan kadai ya isar wa yallabai yarda da ya gama mallakar komi na zubaidah to sati guda daga ni har yallabai bamu da lokacin komi bamuda lokacin kowa face na nunawa juna zallar kauna nayi mamakin yadda aunty mubina ta iya barin baban jawad, kasancewarshi irin maxan da ake kira one in million irinsu ne in suna son mace sukan nuna mata basu da komi mafi ,muhimmmanci fiye da ita koda yake gaskiya ne da ake cewa wasu mata sun rako wasu duniya, inban da haka ni ina har zan iya yiwa yallabai laifin da za ya dakeni balle har ta kai ga saki?bana jin ko yankar tsokar jikina zai rinkayi kullum bazan ji ciwo ba balle har takai ga musayar yawu (so kenan)sai yanzu ne na yarda da maganar fatima na
Fatima nace wa wai idan na fara rayuwa mai kyau da yallabai,ko kuda bazan so ya rabe mu ba, yo ni ko sauro zan so ya rabi wannan sabuwar rayuwa da muke a yanzu?ina! kullum daga gidan maimartaba ake kawo abinci safe da rana da dare,baki masu ganin daki basu barina hutawa tun safe har dare danginane ko na yallabai. haka masu neman taimako da yallabai ya saba duk zuwansa garin shima basu kyaleshi ba a kullum zai fita fadar maimartaba yayi gaisuwa a zauna tare da shi har karfe biyun rana ya dawo yaci abinci ya huta zuwa karfe hudu ya fita falon daya tanada musamman dan ganawa da al'ummar karaye yayi tajin koken su har magariba, sai sun yi sallar isha'i tare a masallaci dake cikin gidanmu sannan ya dawo gida shikenan kuma sai Allah ya kaimu gobe,dukkan tsayin daren da wayewarsa na zubaidah ne.
Chapter 41 · 0% Book details