← Book details Tuna Baya Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 26 OF 51

Sashe 26

Tuna Baya Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

Wannan bai hanani gane hanyar gidanmu ba, gidan Maikalwa da Daddawa.

Abinda ya dan sani faduwar gaba, rashin ganin almajiran Liman, wadanda ada kullum basu rabo da kofar gidan.

Tuni wasu almajirai sun yanyame mu, sun kwashi akwatuna, nace musu su kai gidan Maikalwa.

Suna tafe muna biye dasu, har kofar gidan mu.

Wani abin mamaki rusashshiyar katangar an tadata da siminti, xauren da ba ruff, an rufeshi ruf da Axara.

Kalwar dake tike dashi babu ko buhu daya.

An malale tun daga dakalin gidan har ciki da malalen siminti.

Auwal na soma hange tsaye, fes dashi, cikin makubar shaddah keda ganinshi kinga wankakken dan bokon Kauye.

Yaga yara yuuu na bin wasu 'yan mata wadanda da alama ba daga Nigeria suke ba, kuma gidansu suke dosowa, ya daka masu tsawa suka watse, suna ihun yeee!

Ga 'yan Agulla daga Wantsandan da baturen Dan su.

Jawad ya rude ya rukunkume ni, nayi masa magana cikin sauri da turancin da yafi sabawa da shi, ina kallon Auwal, ina doka murmushi.

Ya koma relaxed.

Har yanxu Auwal ya kasa magana, sai da muka karaso, xamu shiga ''can i offer u any help?'' Ya tambaya da alamun bai son mu shigar musu gida ''Ya Auwal kenan.

Ni ko mutuwa nayi na dawo, na ganka cikin kowanne hali, baxan kasa ganeka ba!'' Xuciyar shi ta soma xolayar shi, wai wannan kanwar shi ce, ATINE, da aka kai wanke-wanke a birni?

Haba!

Ina Atine ta iya turancin da ya ji tana xabgawa wannan karamin yaron?

Ina Atine tayi kyawun haka?

Ina ta samo wadannan turawan?

Bayan ance matar gidan dan Maimartaba take yiwa wanke-wanke?

To ko waccan ce dan matar dan Maimartaban?

To amma ai, basu fice shekaru daya da Atinen ba kai ina!

Ficiciyar kanwar shi Atine mai siraran kafafi, ta koma tamkar 'yar sarkin Masar?
123.

Tuni suka baxama nemo Baba shiko Auwal neman pure-water ya tafi ya sawowa Aishah, da Dan da yake xaton kanin ta ne.

Cikin dan lokaci gida ya cika fam da 'yan uwa da abokan arxiki kowanne yana shafata yana sunsunani, sun rude da yiwa Amarya murnar dawowa ta.

Kakata Luba ta shigo xanin ta na kwancewa tana rikoshi, ta tsufa ainun.

Na mike na tarota na rungume ''ashe Atine xan saki idona kamin tadda kushewa?'' Abinda take fadi kawai kenan, cikin xubda hawaye.

Ashsha ta xama 'yar kallo, tausayin mu ya cikata.

Ta tabbatarwa kanta ba karamin xaman kadaici nayi ba, yadda nake da iyaye da 'yan uwa masu kaunata haka.

Sai ta shiga share hawaye.

Shiko Jawad yayi wuri-wuri sai jefa ido yake waje-waje.

A haka Maikalwa ya fado su Sani biye dashi, ''wai Uwata ce ta dawo?'' Ya ratso mutane ya iso ga wadda ake yanyamewa.

Sanye cikin tsalelen Lesi ruwan kasa mai firgitarwa.

Doguwar mace siririya sambal tamkar tarwada, mai tattare da duk wani sirrin kyawun da 'ya mace ke tinkaho da shi., daga yatsar kafarta har gashin kanta kyau ne xiryan, mai nuni da jikin da ya huta.

Tabbas duka wurin babu kamarta.

''Atine na ce?'' Ya fada a yayin da hawaye suka wa
nke masa fuska.

Na mike daga jikin Luba, na rungumo dattijon Babana, na xaunar da shi nima kukan dadin nake ''Babana, naji dadi da na sameka lafiya.

Na tafi a MOTA na dawo a JIRGI, na tafi a wadda tayi rashin masoyi, na dawo da MIJIN AURE.

Na tafi a JAHILA, na dawo a DALIBA mai 'yanci.

Na tafi a KYANDIR na dawo a MUTUM, na tafi a MUBURGI na dawo a MUCIYA, na tafi a ATINE MAMMAN MAIKALWA na dawo a ZUBAIDAH MUHAMMAD KARAYE, to meye na kuka?

Kuyi farin ciki, wanke-wanke alkhairi ne a gareni''.

Baba yayi murmushi, tunda kika tafi Uwata bamu kara yin TALAUCI ba.

Bamu kara saida KALWA ba.

Bamu kara rasa kudin makarantar yara ba.

Bamu kara saida KALWA ba.

Bamu kara rasa abinci mai kyau ba.

Wannan bawan Allah da kikewa aiki naira dubu hamsin yake bani a kowanne wata.

Duk wata sai ya xo ya gaishe ni, ya gaya mun lafiyar ki kalau.
124.

Don haka hankalin mu duka a kwance yake, ni kaina nasan rainon ki, RAINON ALKHAIRI ne a garemu.

Gashi a yau a dalilin rainon, ki xama mace abin alfaharin kowanne Uba.

Lallai kowa yace GONAR WANI BAXATA YI ALBARKA BA, TASHIN CE BAXATA YI BA!'' Inna dake xaune wai sai ta kama kuka.

Tana rokon in yafe mata, in yafewa Atika ba laifin ta bane.

Ni wallahi na ma mance da xancen kaf.

Nace ''ni mai kikai min ne?

Me Atikar tayi min?'' Sai a lokacin na tuno wai wani saurayi can dan gidan Waxiri shine take kuka?

Na bita har dakin ta ina rarrashin ta, ina tambayar ta INAA ATIKA?

Sai ta kara tsananta kukanta.

Ganin haka na kyale ta na dawo ga bataliyar dangina.

Ana ta labarin bayan rabo.

Wacce 'yar gidan wane ta mutu, wane ya mutu, wane tayi aure.

A nan na tsinkayi labarin mutuwar kakana Liman, bayan tafiyata da shekaru biyu.

Bamu samu kebewa da iyaye na ba sai misalin karfe goma na dare.

Amarya na can madafi tana kokarin hadawa Ashsha abinci.

Jawad tun maghriba Kakarsa ta turo Talatu ta tafi dashi wai taga Maigidan ta.

Ni kuma a barni in xanta da iyaye na.

Baba ya ba Auwal yayo cefane na musamman, Amarya kuma ta aika Sadiya sayen lemun kwalba mai sanyi wajen wani mai shago can wajen gidan Maimartaba, duka sabida bakuwar su, Aishah.

Xancen cigaban da Karaye ta samu, shi yafi daukar hankali na.

Ga dai ruwan sha mai tsbata, ga kuma wutar lantarki ta haske ko'ina.

Ashsha ta ji dadin hira da Baba da Amarya, ba don komi ba sai don su mutane ne masu saukin sha'ani.

Amarya ta kare shinkafa fara da taliyar macaroni, ga farfesun kajin hausa yaji kayan kamshi.

Auwal ledar pure-water ya dire mana, amma Ashsha bata nuna komi ba, ta dauka ta sha fuska a sake, duk da nasan ko spring water ba kowanne take sha ba, wannan yasa na kara jin kaunar ta, ba don komi ba sai don fahimtar da nayi ita mai kauna ta ce kurum sabida Allah ba don wani abu da na mallaka ba.
125.

Babana ya rasa ina-yaka-saka-ina-yaka-aje da ni?

Ya dubi Ashsha cike da murmushi ''Uwargida na, Indo, me xamu baki ki ci?'' Ashsha sai dariya take.

Ta jero akwatuna dai-dai har bakwai, uku nata ne, hudu daga yallabai, ta farko ta Maikalwa ce, shadda, yadi, voyel bandir-bandir ga kudin dinkin su a kai har (N30,000), mai bi mata ta Amarya ce, tamkar kayan lefen budurwa, lesika, shaddojo, atamfofi (super-exclusive) da Aura.

Aura ne kawai a ciki.

Ta fidda turamen Hollan da Ingila guda bakwai tace wannan Baba yaba Innar Jafaru, na Atika ma wanda da kudin ta ta hada mata ta bude masu sun gani, tace sai hanu da hannu xata bata.

Auwal, Sani, Salisu da Rabi'u kowanne ya samu kayan samari, na fito da tsarabar autar Amarya Sadiya da Jafaru duk ba wanda aka bari tamkar Yallabai ya binciki adadin mutanen da ke cikin gidan, koda yake nasan kadan daga aikin shi.

Maikalwa sai kuka wanda baya mishi wuya yace ''shin meke tsakanin Atine da Yallabai Magajin-gari ne?

Ni fa wannan abu ya soma bani tsoro''.

Ashsha ta kalmashe kafafu tana murmushi tace ''koma menene Baba shi da kansa xai gaya maka.

Amma in kyankyasa ma karambani, Yallabai auren Zubaidah ne ya kawoshi''.

Baba yayi shiri da alama kanshi yayi xafi.

Ya sunkuyar da kai ''In nace xan gaya maku abinda mutumin nan ke yi mani a shekarun nan, wallahi sai in yi karya in kuma mance wasu.

Duk sanda yaxo Karaye, daga gidan Ubansa sai kofar gida na.

Duk shaddar da ke jikin shi haka xai shimfide ta a kasa yace ''Baba ina wuni?'' Idan har akwai abinda xan mishi in biya shi bai wuce bashi auren Uwata ba!'' To a dakin Amarya ma xancen da suke yi kenan, ni ina uwar dakin Inna na barci mai dadi na dibana kadan-kadan sabida gajiya.

Ashsha da Inna kusan kwanan xaune sukayi.

Gabadaya rayuwata gidan Yallabai, makaranta da ya kaini, barmin rikon dan shi da yayi, rabuwar shi da uwar yaron, duk Ashsha bata boyewa Inna komi ba.

To Inna ta nuna rashin gamsuwa da halayyar Yallabai tace da sanyin muryar ta ''kuma sai ya saki Uwargidan shi don xai auru YAR RAINO?..
[10/15, 9:17 AM] A A Dboy: *_POST BY GROUP OF HYPE HAUSA NOVELS BOOK WHATSAPP 08064400100_
[10/15, 9:18 AM] A A Dboy: Tuna Baya 126-129
126.

Haka akeyi?

Waya ke son mutum mai saurin saki?

Ashsha ciki ya duri ruwa, nayi nadamar surutun ta da har bai boye wani sirrin tayi hamxarin gyara xancen ta da cewa ''ita ce tace baxata xauna da mai wanke-wanke ba, shine ya sallame ta''.

Ga dukkan alamu Inna bata gamsu ba.

Washegari tun kamin in tashi barci, da sanyin asuba har Ashsha ta sa tsintsiya ta share tsakar gidan mu tas, ta sharewa Inna Amarya daki, tasa tsumma a ruwa ta goge ledar.

Ta hada 'yan kayan Sadiya ta ninke ta kimtsa dakin tsaf.

Ta sa guga a rijiya ta janyo ruwa, ta hada kwanukan da ke gindin rijiya ta wanke ta kife su a kwando, ta cika bokiti ta dauraye jikinta.

Ina hana ta amma taki ji, cewa take ''wai baki san in naje Tilde, har tatsa nikewa Kakata Danejo ba?'' Ta shirya cikin siket da riga mai dogon hannu kamar kullum, ta nufi dakin Maikalwa suka gaisa Auwal ma yana nan suka shiga hira wadda duka ta Yallabai ce.

Buhunan shinkafa, katon na taliya, katon na maggi, garwannin mai, kwandunan kayan miya, buhunan gishirin Dangote, katon na madara, katon na bournvita, buhunan suga da katon na lemun (five- alive).

Katon na (tropical and squash juices) duk daga Yallabai a kawowa Baba.

Bai shigo ba sai karfe goma na safe.

Mallam Mamman, ya rasa ta inda xai sa surukin shi sai ya shimfida masa buxun sallar shi.

A wurin shi karshen karramawa kenan da yake yiwa baki masu muhimmanci a gareshi.

Shi Yallabai Baba burge shi yake, yadda bai rudewa duk sanda yaxo gaishe shi irinna sauran talakawan Karaye, komi na shi cikin nutsuwa.

Ya cika su da kudi duka gidan, babba da yaro.
Chapter 26 · 0% Book details