Sashe 42
Tuna Baya Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read
Su ashshah da mamanta da hajiya hafsi sun zo yimin sallama da cewa za su koma abuja mu wuni hira tsokana kam na shata wurin ashshah har na koshi tace gaba daya na canza,nayi jazur nayi bul bul sai sheki nake kamar dafaffen kwan da aka aka bare daga gidanshi shi kuma yallabai tace eh to, although (duk da) yayi duhu sabida karywar kashin amarya kugun amarya,yet da ganinshi ya samu kwanciyar hankali dabe taba samuba sai wani kara zama (fresh)yake kamar ba tsohon gwauroba ashsha shakiyyar duniya mamanta da hajiya hafsi dariya suke khadija diyar hafsi kadai take tare min su kuwa sai kwasar dariya suke nayi musu godiya mai tarin yawa abisa kaunar da suka nuna mani wadda ko yan uwana da muke ciki daya sai hakan.da alqawarin har gida zanbi kowacce su in mata bangajiya.sun bar karaye ba don sun so ba sabida karimcin irin na al'ummar ta da kasaitacciyar masarauta ta mai girmama bako da karramashi washegari aka dauke su zuwa abuja inda kowacce su zata nemi inda ta fito ni kuma na cigaba da amsar baki duk kuma wacce zata tafi da turmin atamfa ingila mai dauke da hoton mu nida yallabai zata tafi da bokiti cike da alkaki da nakiya bakilawa da dubulan
[10/23, 5:20 PM] A A Dboy: *_POST BY GROUP OF HYPE HAUSA NOVELS BOOK WHATSAPP 08064400100_
[10/23, 5:21 PM] A A Dboy:
*TUNA BAYA*
~BOOK 2~
Tuna Baya2 91-100
cikin bokiti cikin dan lokaci mun saba da daukacin dangin yallabai maza da mata musamman abdulraheem dan autan dakinsu jinin mu yafi gamuwa kwarai kusan kullum suna gidana suna min hira da tayani hidimar baki kullum sai yallabai yace wai baba na gaishe ni nayi nayi baba yazo yaki har wasika na rubuta na aikawa awal ya karanta mishi ina rokan shi dan Allah dan annabi yazo inganshi sai yace wai bani da hankali daga kaini gidan mijin kuma sai ya sawo takalmi ya biyo ni .duka jama'ar gidanmu ba wanda bai zo ba masamman sadiya dake ajin karshe a primary sadiya na sona sosai haka nima duk kannena jininmu yafi haduwa,ta kan zauna mu wuni tana bani labarai duk da kasancewar ta mara son magana amma in da nine kyaji bakin sadiya har zaure wajen karfe sha biyun rana fatima ta shigo biye da ita yarantane,sanyetake cikin makubar abaya kirar oman ta yane kanta da gyalen abayar kamar balarabiya,na kauda kai nace fushi nake maman mukhlas tace Allah ya huci ranki maman jawad tun tuni naso in shigo babansu mukhlas ne ya hanani wai in barku ku gama amarcin ku kar in dameki da surutuna, yanzu ma sallama nazo miki,gobe In Allah ya kaimu zamu tashi zuwa inda muka fi wayau mun sha hirar bankwana da fatima saida zata tafi ne ta fiddo katina na taya murnar aure tace inji bello, mun rabu cike da kewar juna,cikin katinan da ta kawo karamin ciki kadai bude na kone su duka a kitchen ga abida ke rubuce.............MR&MRS KARAYE THE RAYS OF THE SUN AT DOWN SIGNIFIES THE COMING OF A NEW DAY.MAY THIS MOMENT SIGNIFY THE BEGINNING OF A SERIES OF NEW BLESSINGS EXCLUSIVELY FOR YOU HEARTIEST CONGRATULATIONSMR AND MRS L.
CONEL BELLO waxiry kamar kullum yau ma naji tausayin bello na alqawartama raina sanya shi a cikin addu'o'ina na fatan alkhari a rayuwa ga yan uwana musulmi na kone katin na kama harkar gabana
satin mu biyu kenan cif da aure komi na tafiya dai dai ta fanni na da yallabai,ranar da muka cika sati biyu da kwana biyu yallabai yace inshiga sallama gidanmu don jibi zamu koma abuja.nace har wajen fulani zan shiga in gaisheta in kuma dauko jawad don tare zamu koma na lura yaji dadin hakan amma sai yace jawad bazai tafi tare da muba.nace don me? ya daura hannusa bisa lebbanshi yace "c'mmmon maman jawad tun can bakya mun musu why now? ban son musu ya soma shiga tsakaninmu tun yanzu kingane?
Ina mana shirye shiryen tafiya wellington da rio de jeneiro ne haney moon kama yadda na alqawarta tuntuni,kin mantane?so nike in mai dake hatsabibiya yadda nake so wannan amarcin bai ishe niba,kenan jawad zai takura abbanshi?na bude baki zan yi magana,ya kammala rufe duk abinda nayi niyyar zan fadi cikin launin soyayyar shi mai ratsa zuciya da bargo.sai muka koma cin karen mu babu babbaka.har nike tambayar kai na shin ni ko taheer wa yafi son wani?
Ban sani ba.
Nakira abdulraheem da yamma awaya nace don Allah duk yadda zai yi ya nemo min kayan ciki rago a gyare,zuma farar saka babban gongoni zaitun guda biyar da turaren bakhour shima biyar ya hado min kudin zanbiya, karfe takwas nayi ya kawo min duk abinda na lissafo mishi ya gayamin kudin duka naira dubu biyar na bashi washegari da sassafe na dau kayan cikin daga deep freezer nayi kitchen nasa apron na kunna cooker na tada lafiyayyen farfesun anta, koda, huhu, tumbi, saifa da sauransu nan da nan na kammala na juye a cikin kyakkyawan warmer sabo ful na koma daki na hada yan abinda nake bukata tafiya dasu cikin akwati ukku abdulraheem ya fiddasu yasa acikin boot din mota.
94....
Zuwa shadaya nayi wanka na shirya cikin atamfa super holland mai kalar ruwan bula mayafi da fararen jaka da takalmi yan china ina janyo kofa zan fito abdulraheem na shigowa yana tami tsiyar wai kamshin farfesun surukar har kasan bene ya karbi katuwar jakar leda dake hannuna ya shiga kitchen ya dauko filas din da alamun jin dadi tattare dashi
Yace yallabai yace mu fara zuwa can cikin gida (gidansu) dama shi tun sassafe ya fita donya samu maimartaba suyi sallama kamin ya shiga fada shike driving din mu cikin karama prelude dinshi da yallabai ya saya mishi daya fara karatun jamia gidan maimartaba sarkin karaye babbane sosai mai rassa daban daban har bazan iya fasaltawaba muna ta wuce soraye bayi na tsugunawa suna gaidamu sai acan kuryar gida muka tadda kayataccen sassan uwargida fulani falo uku muka wuce kamin mu tadda ita tana kishingide bisa tuntu wanda akasari a yanzu anfi samunsa a gidan sarauta Koko gidan manya masu hannu da shuni kyakkyawar dattijiya da alamu wayewa ainun cikin fararen idanunta cikin 'ya'yanta kaf babu wadda ya debota sak kaman yallabai.a tare muka yi sallama sai ta amsa cike da murmushi tace oyoyo da zubaidah ta mike ta kamo hannuna ta zaunar dani a gefen damanta. muka hada ido da yallabai dake can gefe kwance cikin kujera three seater yana faman lallatsa waya muka yiwa juna lallausan murmushi kuma atake kunya da nauyin fulani suka taru suka lullubeni.
95....
Daga can daki jawad ya fito yana mutstsikar ido da alama yaji ana ambatar suna mai kamar ZUBAIDAH ne,to ashe dai MOMIN ce da gaske.. da gudu ya karaso muka yiwa juna tsatstsaurar runguma kamin ya fara kukan,can kuma ya sake rungumeni ya daga rigata ya tura kansa tamkar mai gudun kar na sake gudu na barshi a karo na biyu.daga fulani, yallabai abdulraheem kallon mu suke cike da sha'awa muka gaisa da fulani a mutunce ina cike da tsananin jin kunya ita ko babu ruwanta labaru ta shiga bani na rigimar jawad domin rashina tace shikenan sai ku tarkata ku tafi nima kunnuwana su huta haba!
Yaro kamar dan jar fata shi baza ayi masa fada yaji ba sai sokanci yayi ta naushe 'ya'yan jamaa mutane basu jiba basu gani ba ina na taba ganin irin wannan jarababben maigida? gaba daya mukayi murmushi jawad daga cikin rigata yace bake ce kike kulleni a daki ba kina sawa suna min gwalo tace an kulle ka din ai sai kabi uwarka can inda baza kullekaba a daki ba amma ni nan kullum kulle da kwado don bazan iya masifarkaba?
Abdulraheem ya tuntsire da dariya niko murna tamka in rungume fulani jin jawad dina zai tafi tare damu don nima ko ina nake hankalina baya kwanciya ba tare da shiba,ni kadai na iyawa da rayuwar jawad ni kadai nasan likes anda dislikes din shi,kenan ni nafi kowa iya zama dashi ni nafi kowa sonsa .amma sai naji yallabai yace a ah wannan auren naku na zobe ne fulani jawad ya sake ruban yashi da igiyoyi tara ba inda zashi na fada miki na dauki hutun shekara har na wata uku (annual leave)
96 Zami tafi Brazil nida Zubaidah, don haka can gidan ba mai kula da shi sai su Tom.
Kafin hak ma Jawad ya dawo Qaraye kenan, Makarantar Primary Abdulrahim zai Kaishi gobe...' Na kai hannu na dafe kirjina da karfi daya fara bada wata irin karar razana, dam dam dam, na daga ido na dibi Abban Jawad ammn shi din yaki mu hada ido, idanunshi na bisa wayar shi ko ajikinsa, banga abinda ya dame shi ba.
Sai na dauka wasa yake, irinnishadin nan daya kanyi na tsokanata lokaci-lokaci.
Fulani tace anya!
Jawad zai iya rayuwa cikin yaran karkarar nan?
Ya dubeta da dukkan idanuwa yace "nidin ina nayi primary?
Abinda na ke so kenan Jawad ya koyi rayuwa cikin kauyen shi KARAYE, ya tashi da dabi'u irin nawa naa kauyen shi KARAYE, bana son wadannan dabi'un nasa, inason ya san me nene talaka?
Ba abun kyama bane, dashi da su daya suke.
Jin dadin da yake ciki da gatan da yake samu yayi yawa, 'he has no experience far life', komi yake so yana samu, komi yace ana yi masa wannan ba TAHEER bane.
Don haka zai zauna a nan gobe a kaishi makaranta yana so ko bayaso, zamu dinga zuwa ganin shi akai-akai, kana jina ko Jawad?" Jawad ya fashe da kuka mai tsima rai, ya san Babansa a kullum yana nufin abinda yake cewa ne balle in ya hada da Fulani, baya maganar wasa tare da ita yace "don Allah momina kar ki bari Daddy yayi mun haka, Allah bazan sake naushin yara ba, bazan sake kinji ba, bazan sake dukan kowa ba, zanci abincin ki da masar ki Fulani na daina cewa ki sai mun icecream...Uncle Abdul na daina cewa ka sayo min pizza...." Nima tuni hawaye sun kwararo sharrr! na sunkuyar da kaina ina sharewa.
Na sake rungume Jawad dina, na kasa furta ko kalma daya miyan bakina sun kafe kat da al'amaran Oga na.