← Book details Malamin Bogi Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 9 OF 35

Sashe 9

Malamin Bogi Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

Mai Gari ya jiƙe da gudmi sharkaf ga gwiwarsa ta ƙafa da ya tsunduma a fitsarin Liman, amma dai yanzu a matsayinsa na Mai Gari gashi kuma yana tsoron mutuwa dole zai yi ƙoƙarin yin magana don a samu mafita, tun da tana ganin duka manyan garin ne a ɗakin, idan kuwa fatalwar mai ƙusumbi ta musu fata-fata to gari yana cikin garari.

Su kaɗai suka san gari lafiya lau yake, amma shi Sheik har yanzu tunaninsa wani gudun famfalaƙin tsoron ne ya sa suka yi hijira daga cikin gari zuwa gidansa.

Da muryar kuka kuma muryar a shaƙe kai daga ka ji maganar ka san mai yinta ƙarfin hali yake Mai Gari ya ce

"Ya Sheik, muna buƙatar taimako, muna buƙatar addu'a kar fa a mana ɗauki ɗai-ɗai, ka yi addu',a mana, mu baƙaƙen fata muna cikin wani hali kaima babban malami kana...

Tun Mai Gari bai kai aya ba Sheik ya daure ya yi ƙarfin halin saita ƙalƙalar hausar larabcinsa ya fara cewa

"A'uzubillahi minash shaiÉ—anir rajim, Bismillahir rahmanir rahim" Tun da ya sanu nasarar yin a'uziyyar nan shikenan yake maimaitawa don shi ita kaÉ—ai ya iya kamowa, don haka bai damu da cewa yana ta maimaitawa za su ce wani abu ba. Mai Gari da yake jiran ya fara jin ana zayyano addu'o'in larabci masu yawa bayan gama a,uziyya da bismillah sai ya ji ba a fara ba ana ta maimaita abu É—aya. Can ya ce

"Haba Ya Sheik ka fara addu'ar da muke ji ana karantowa a ƙasar makka mana" Ya faɗa yaba ɗan ɗaga muryarsa da take ta zillo tana rawa, tare da saurin gyara fuskarsa daga inda ya nutsa ta a jikin katifa jin ya danne hancinsa numfashi yana neman gagararsa shaƙa, amma fa duk maganar nan da ya yi Sheik bai ce uffan ba kuma bai fasa faɗar abin da yake faɗa ba, saboda shi a ganinsa ya samu makamar ceton kansa.

Liman da samarin nan jin muryar Sheik ta karaÉ—e É—akin yana faÉ—in

"A'uzubillahi minash shaiɗanir rajim, Bismillahir rahmanir rahim" Cikin muryar larabawa tamkar wanda wani balaraben gaske yake yi, basu san cewa Sheik sai da ya daɗe yana yi wa muryarsa training a kan ƙalƙalar kafin ya zo garin nasu ba.

Liman da samari basa bambance abin da yake faÉ—a, don yadda yake maganar tamkar wata doguwar sura ce yake karantawa sai suka shiga mishi amshi da faÉ—in

"Allahu akbar!" Idan ya faÉ—a sai Liman ya ce

"Attakabir" Sai samari su ce

"Allahu akbar!" Mai Gari ma tuni ya bi yarima yake shan kiÉ—a, don ya lura shi kaÉ—ai ne muryarsa bata fitowa a cikin É—akin, yana tsoron abin ya zama shi kaÉ—ai zai samu.

Sun kwashe sama da awa suna a haka, sannan ne Sheik ya ji ƴar nutsuwa, ya buɗe ido ɗaya ya ƙyallara ya ga dai ɗakin babu kowa, wata ɓoyayyar ajiyar zuciya ya sauke, yana tunanin abin da ya faɗa ne ya sanya fatalwar ta fita daga ɗakin.

Daƙyar ya ɗago daga gohon ya zauna, ganinsa babu towel ɗin nasa, sai ya ƙura ido a mafitsararsa yana son ganin ko an masa shayin, amma sai ya ga yadda take haka take, sai dai ta yamushe a waje guda ta tattare saboda wahala. Har lokacin bakinsa bai yi shiru da abin da yake faɗa ba, hannu ya kai ya fisge towel ɗinsa na wajen Liman, Liman da dama bai riƙe towel ba kasancewae hannuwansa suna matse a matse matsinsa, sai ji ya yi an buɗe masa kansa, hakan ya sa ya ƙara runtse ido haɗe da bada ƙaimi wajen ƙara danna hannuwansa don ganin ba a yi kaciyar nan da shi ba, har lokacin yana faɗin

"Attakabir" Da sauri Sheik ya ɗaura towel ɗin ya ɗan muskuta ya koma kan sallayar da take shimfiɗe, tare da miƙa hannu ya ɗakko hirami a jakarsa yana gyra zaman hularsa da gemunsa, sai da ya zauna yana kallon gabas , ya rufa hiramin yana ta cigaba da a'uxiyya.

Dakyar ya samu nasarar warto suratul fatiha a bakinsa, ya shiga karantowa, sai da ya yi sau uku, sannan yana zaunen ba tare da ya juyo ba ya ce

"Alhamdulillahi, na samu nasarar korar fatalwa, komai ya dawo daidai" Ya faɗa cikin muryarsa ta balarabe. A hankali suka fara tashi zaune kowa yana ɗan ƙyallara ido, ganin babu fatalwa a ɗaki, sannan Sheik yana kan sallaya ya rufa hirami sai suka fara hamdala Mai Gari faɗi yake

"Allah mun gode maka da ka kawo mana babban malamin larabawa da yau ya za mu yi?" Ya faɗa yana kallon gwiwar ƙafarsa, da ta jiƙe, shi kuma Sheik bai ma san inda gudawarsa ta yi ba domin yanzu ba ya ma ji.

Malam Lima cewa yake

"Ai ba ƙaramar sa'a muka yi ba" Ya faɗa yana ɗan satar kallon wandonsa da ya jiƙe ya ce

"Wannan yara an yi yaran banza, yanzu a cikin ku aka samu wani marar imanin ya zage wando ya mini fitsari a jikina?" Ya faÉ—a yana kallon samarin nan da suke sharkaf da gumi. ÆŠaya ya buÉ—e baki zai yi magana Mai Gari ya yi saurin cewa

"Kai ba a son wani tone-tone ku bashi haƙuri" Haka suka bashi haƙuri ba don son so ba, sai don ba yadda za su yi kuma dai ga wandonsa ya fi nasu jiƙewa tun da shi ya yi fitsarin su dai kawai sun shiga lemar ne.

Liman daÉ—i ya ji a ransa ganin girmansa bai zube ba. Nan suka kalli Sheik da ya juyo daga kallon gabas yana gyara zaman towel É—in da hiraminsa, gumin da yake yi tamkar ya dawo daga filin tsere.

Mai Gari yana kallonsa ya ce

"Sannu Ya Sheik lallai ka yi artabu" Sheik a zuciyarsa ya ce

'Artabun yau ka gani, da ka ga na jiya da na sha da ina ga wano zancen ake ba wannan ba' Amma a fili sai ya ce

"Kai wannan ai ƙaramin abu ne, ai ina tabbatar muku kuna zuwa cikin gari za ku ga aljannu sun lafa komai ya daidaita" Da mamaki suke kallonsa jin yana batun cikin gari, Malam Liman ne ya ce

"Cikin gari babu lafiya ne dama?" Shiru Sheik ya yi yana tambayar kansa a zuciyarsa cewa

'To da uban me ya taho da ku da gudu idan ba tashin hankali kuka baro a cikin garin ba?' A fili ya ce

"Dama cikin garin lafiya, na É—auka ai babu lafiya da na ga kun shigo gidan nan a kuÉ—ime" Mai Gari ya ce

"A'a gari lafiya ƙalaw dama zuwa muka yi, mu ga ko lafiya mun zo da asuba kiranka a yi sallah amma aka gaji da bugawa shiru, to shi ne muka samo samarin nan muka ce su ɓalle ƙofar a duba lafiyarka, da aka tura ƙofa kuma sai muka hango ka taho a guje da takalmi ɗaya a ƙafa jiki duk kumfa, wannan dalilin ne ya sa mu ma muka ga tun da har kana gudu to akwai gagarumar matsala gwara mu bika mu tsira ka ji dalili amma gari kowa yama sabgar gabansa lafiya" Wata ɓoyayyar ajiyar zuciya ya sauke, yana jin wani mugun haushin su, da suka firgita shi, shi a nashi tunanin garin ne a ruɗe suka taho ashe dai shi ya ruɗa su.

Cike da ƙarfin gwiwa ya sheƙo wata sheƙeƙiyar ƙarya don kar a ga gazawarsa ya ce

"Ai nake faɗa musu ina cikin banɗaki ina wanka, nan na ga wani aljani mai ƙaho bakwai ya tsaga bango ya fito, yana fitowa ta sheƙe da dariya yana cewa, wai yanzun nan za su saki manyan aljannun da za su rikita gari, kai har cewa ya yi mai gari ma ɗauke shi, za su yi, wannan dalilin ne ya sa ina nuna shi da yatsa wani hayaƙi ya tashi da shi sama, ya bi iska ya ɓace, to ni kuma tuno halin da garin zai kasance shi ne na fito hankali a tashe domin na kai muku ɗauki cikin gari, ganinku a guje kun shigo ya ƙara sanya hankalina ya tashi, saboda bana son jama'a su shiga damuwa, sai yanzu bayan na gama addu'ar nan na gano ashe dai aljanin nan ne ya shiga jikina ya haifar da tsuma da ruɗu da tsoro, don kar in taimaka muku, shi ne fa muke rige-rige tsakanin ni da ku wajen samun maɓoya" Ya faɗa yana dafe goshi alamar damuwa.

Mai Gari har da ƙwallar farin ciki ganin ba ƙaramar ƙauna Sheik yake yi wa garin nasu na Ƙundu ba, sannan ba ƙaramin taimakon su yake yi ba, bai san cewa Sheik kasuwanci ya zo yi a garin nasu ba, don ba a aikin banza a ko ina.

Cike da girmamawa ya ce

"Allah saka da alkairi Malam ashe kana ta fafutuka ne a kan garinmu, silar haka har aljani ya shiga jikinka ya saka muke tsere, bawan Allah dama na yi mamakin ganin muna ta neman mafaka tare da kai ashe dai ba da kai muke nema ba, da aljani ne" Ya faÉ—a yana kallon Sheik.

Liman ya ce "Ai ni na yi mamaki dama, malamai ai magada annabawa ne" Sheik ya ce

"Ina ai ƙaryar aljani in ji tsoronsa, su kansu sun sanni" Ya faɗa amma yana ɗan rage murya saboda tuno kunnen jaririn da aka jefo a banɗaki.

Liman ya ce

"Allah mai baiwa, ku dai Allah ya baku" Sheik aka wani gyara zama gudun kar towel ya kunce ya ce

"Ai aljanin ya yi niyyar hanani yin addu'a ma lokacin da fatalwa ma ta shigo hatta bakina sai da suka so riƙe mini, yanzu ma sai da na sha fama na hau sallayar nan, so suka yi kar in yi addu'a" Gabaɗaya suka ce

"Allah ya fi su"

Nan dai aka sa samarin nan su fita da katifa su gyara ɗakin, a nan ne ma Mai Gari ya ƙarewa Sheik kallo ganin idanunsa luhu-luhu alamar ko dai kuka ko rashin bacci ya ce

"Ya Sheik ka ga idanunka kuwa, hatta fuskarka a kumbure take" Sheik tuno artabun da suka sha jiya da jarirai da aljannu har ya hau bishiyar kuka, sai ya É—an yi gyaran murya ya ce
Chapter 9 · 0% Book details