← Book details Malamin Bogi Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 15 OF 35

Sashe 15

Malamin Bogi Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

"Ibra, ka baro garinku ka zo wannan gari baka san matsalolin da suke ciki ba, to ka kawo kanka cilin gagarumar matsala, ko dai ka haɗa kayanka ka koma inda ka fito ko kuma mu shiga fafatawa da kai" Tsuru Sheik ya yi yana jin maganar kamar tana amsa kuwwa amma ya lura shi kaɗai yake ji, idanu ya sauke a kan uban kuɗin da aka saka a cikin fantekar nan masu uban yawa, duk da yawanci ƙananun kuɗi ne amma ya lura akwai ƴan dubu-dubu. Ganin kuɗin nan sai ya ji babu gudu babu ja da baya tun da gani yake babu mai ja da cikar burinsa, wani yawu ya haɗiye yana muzurai, kai ya ƙara cewa

"Ka amince za ka bar garin Ƙundu a yau?" Wannan tambaya ta sanya ya ji wani takaici saboda ga shi dai a kwana ɗaya ya haɗa wannan uban kuɗi babu aikin fari bare na baƙi, to ina ga ya yi watanni, duk da shi a ransa yana ganin in har ya samu dama a shekara goma ma ba zai bar garin Ƙundu ba, tun da ya ga wannan hanyar arziƙinsa. Shiru da ya yi sai kan ya ce

"Shirunka ya nuna ba za ka tafi ba to mu zuba mu da kai" Ana gama faɗa masa haka sai ya ga kuɗaɗen cikin fantekar sun fara ɓacewa, idanu ya shiga zarewa yana son yin ihun kuka amma babu dama, ba ya so ya bayar da kansa a wajen Mai Gari da mutanen gari.

Gabaɗaya cikin fantekar sai robar maganin kaɗai ta rage sai wata tsohuwar naira biyar. Takaici ne ya kama shi yana ji a ransa da a ce shi malamin gaske ne ba MALAMIN BOGI ba da sai ya yi addu'ar da zai ƙona aljannun garin gabaɗaya, tun da gashi yanzu ya ga samu ya ga rashi. Kafin ya gama wannan mamakin sai ya ji an fara tura shi daga baya kamar dai idan mutum ya hau lilo ake tura shi yana yin gaba yana dawowa baya, to haka ya ji, idanu ya runtse tun da shi banda fantekar wannan da ya riƙe babu wani reshe da ya riƙe, illa wuyan rigarsa ne kawai yanzu a maƙale da bishiyar kukar.

Turashin da aka fara sai ya fara ganin kamar zai hantsila ƙasa, suratul nasi ce kaɗai ya samu nasarar wartowa a bakinsa ya shiga karantowa babu sautin yana fita a hankali sai shi kaɗai yake ji, su Malam Liman da suke ƙasa da mutanen gari suna kallon yadda ake shilla Sheik bakinsa kuma sai kaiwa da komowa yake alamar yana magana sai dai kasancewar a can sama yake basa iya jin furucin nasa. Ya daɗe a haka har ya fara fidda rai da rayuwa, hawaye suna safa da marwa a saman fuskarsa. Dakyar ya samu ya daina hangen ƙwarangwal ɗin kan wannan don ya ɓace ɓat, sannan an daina cilla shi yana lilo.

Ganin haka sai ya fara tunanin mafitar da zai wanke kansa ba tare da mutanen gari sun gano ainihin abin da yake faruwa ba. Hannusa ɗaya ya cire daga jikin fantekar ya kaiwa jikin reshen kukar wani uban naushi, har sai da bayan hannun ya fashe alamar ƙumewar da ya yi, ya buɗe murya yana faɗin

"Allahu akbar!" Sai da ya kaiwa reshen nan naushi sau biyar yana ambaton kabbara, duk da azabar da take ziyartar hannun nasa.
Ji ya yi an finciko rigar tashi daga inda take a maƙale, idanu ya waro ganin ya nufi ƙasa gabaɗaya mutane aka dare daga wajen, Sheik fatansa da addu'arsa Allah ya sa ya faɗa a kan Liman ko Mai Gari, sai dai saboda ƙarfin hali yana dab da faɗowa ya buɗe murya yana faɗin

"In sha Allahu balaraben malami ne da nasara a kan ku, garin Ƙundu ya fi ƙarfin ku aljannu" Da wanann kalaman ya faɗo sai gashi wancakar a tsakiyar wajen, ƙatuwar fantekar wannan ta kife kansa, gabaɗaya jama'a aka yi kansa, faɗuwar da ya yi ya ji hular gashin sa tana neman cirewa.

Ga faɗowar da ya yi ƙugunsa kamar zai cire amma dai saboda wannan ce hanyar cutar jama'a da zai yi wajen samun kuɗinsa dole ya daure. Mai Gari ne ya miƙa hannu saman kan Sheik ya cire fantekar yana ta faman jera masa sannu.

Duk da ya jigata kuma idanunsa a rufe amma a haka yake jero kabbara. Jin hular gashin kansa tana nema zamewa ya yi azama ya dafe kansa da hannu, mutane duk an kewaye shi ga hawayen nan da ya yi ga bayan hannunsa É—aya a dauje, da kaÉ—an-kaÉ—an ya shiga buÉ—e idanun kowa ya zuba masa na mujiya ana jiran a ji ta bakinsa.

Hannu biyu Mai Gari da Liman suka saka suna ƙoƙarin tada shi zaune, duk fa haka bai yi wasa dafewar da ya yi wa hular gashon kansa. Mai Gari ne ya buɗe baki ya ce

"Sannu Ya Sheik, Allah ya maka alam nashra" Ya faɗa cike da tausayawa. Cike da ƙarfin hali Sheik ya ce

"A haba kar ka damu Mai Gari ai mu Allah ya riga ya bamu, duk runtsi ba zan bari a cutar da garin nan ba sai inda ƙarfina ya ƙare" Liman ne ya ce

"Kamar ya Sheik kai da ka sha wahala amma kake kiran sai ƙarfinka ya ƙare?" Sheik a zuciyarsa ya ce

'Ka ji masu hana ruwa gudu, waÉ—annan basa mutuwar tsakar É—akinsu, wato zani zai kuncr mini a kasuwa' A fili kuma ya ce

"Ai ni nan na hangi wani bala'in tashin hankali, gingimeman yaƙin duniya na uku ne aljannu suka shirya tsakanin su da mutanen garin Ƙundu, gabaɗaya so suka yi su tarwatsa ku, su yi muki bazata, cikin ƙoƙari don ba na so ku firgita hankalinku ya tashi, shi ya sa a zuciyata na ringa addu'a a kan iska ta kai ni saman kukar, domin daga can ne aka shiryo dakarun yaƙin, shi ne ma kuka ga na tashi a saman iska, to a can ma ku abin da idanunku yake gani da ban abin da yake faruwa da ban, kuna ganina a rataye amma bakwa ganin gwagwarmayar da take faruwa, yaƙi ne ake tafkawa suna kawo sara fa suka da wuƙaƙe da adda ta aljannu a ƙarshe duk na ƙwace makaman na ci su da yaƙi hatta wanann hannun nawa haɓar wani aljani na yi ta naushi da shi kun ga yadda na ji ciwo, ku za kuke gani ina naushin kuka amma ni ina ganin aljani ne mai ka bakwai, ganin dai zan musu lahani duk suka watse don duk na jinyata su, saboda baƙin talaucin da suke ciki ma, na raba musu kuɗin da kuka tara mini, domin na ji suna cewa za su bazo garin duk wasu kuɗaɗe su kwashe" Gabaɗaya maza da matan wajen suka yi wata kabbara tamkar a filin sallar idi.

Suka ce "Allahu akbar" Wata ɓoyayyar ajiyar zuciya ya sauke jin ƙaryar da ya zabga ta kuɓutar da shi, a take Mai Gari ya saka ƙasan babbar rigarsa yana sharewa Sheik ƙasa a bayan rigarsa ganin faɗuwar da ya yi duk ya kwashi ƙasa.

Cike da tausayawa yana miƙa hannunsa kan hular Sheik daga ƙeya yana karkaɗe masa ƙasa, Sheik kuwa sai ƙara danne hular yake gudun afkuwar matsala, Mai Gari ya ce

"Lallai garin Ƙundu ya yi dace mai shahada da sadaukar da kai ga mutanen garo domon ceton rayuka, in ba haka na ta yaya za ka amince da garin nan har haka?, Ni da ya kamata a ce ni zan yi wannan sadaukarwa" Sheik cike da lanƙwasa kuryarsa ya ce

"Ina ai in har ina garin nan babu wata matsala da za ta tunkaro ku in ƙyale ta, saboda mu can a ƙasashen larabawa haka muke yi bare ni da na baro ƙasata don in zo in taimaka muku" Gabaɗaya sai aka shiga jinjinawa Sheik bisa namijin ƙoƙarin da ya yi, haka ya ƙara girma a idanun jama'a kowa yana yaba masa.

Haka aka yi yuya guda don raka Sheik gida ya huta saboda faɗa da aljannu. Amma a ransa baƙinciki ne fal na yadda aljannun suka ɗauke masa kuɗin da ya tara, yana murna ya samu kuɗi ashe dai da sauran rina a kaba.

Har cikin gida aka rako shi ana girmama shi, da zai shiga É—aki Liman ya ce

"Sheik Allah gafarta malam ga robar ruwan maganinka, da naira biyar ɗin nan, ita da ka rage ta a cikin fantekar ko maganin aljannun za a yo da ita" Ya faɗa cike da girmamawa yana miƙa masa don an ba mai fantekar fantekar ta. Sheik kamar ya yi kuka ya ce

"Eh ai ina sane na rage ta, ka san har hawayen tausayin garin nan na yi a saman kuka na ji tausayinku sosai" Ya faÉ—a yana danne takaicin da yake ji a ransa ga zafin da hannunsa yake yi.

*DA YAMMA*

Ƙofar gidan Sheik ya cika da jama'a maza da mata, masu karɓar magani, saboda ya ce ba za a ke bada magani a titi ba saboda kowa abin da zai nemi magani sirri ne a wajensa bai kamata ake faɗa ba, hakan ya sa aka yi dogayen layi biyu na maza da ban na mata da ban, aka ce idan mace ɗaya ta shiga sai namiji ɗaya ya shiga.

Wata mata ce ta fara shiga gidan da sallama, Sheik ya amsa, yana mai mata umarnin ta shiga, shiga ta yi ta samu waje daga can nesa wajen ƙofar ɗaki ta zauna, shi kuma yana daga kan sallay ya lanƙwashe ƙafa sai wani ƙaton baho a ajiye daga can bayansa.

Gyaran murya ya yi ya ce

"Mai yake tafe da ke?" Matar wani daÉ—i ne ya cika mata rai jin muryarsa, sai yanzu take tabbatar da maganar mutanen gari da ake cewa maganarsa hausar ma bata fita, ba ma wannan ba farar fatarsa kaÉ—ai ji take kamar wanda ta je garin makka. Cike da É—an diriricewa irin tana magana da balarabe ta ce
Chapter 15 · 0% Book details