Sashe 24
Malamin Bogi Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read
"Haba Sulaiman ya za ka yanke wannan ɗanyen hukunci marar ma'ana da madafa? Kai kanka ka san Rahma ta fi ƙarfin wannan bagidajen, kai take so kuma kai za ta aura" Juyowa ya yi yana yi wa Mummy kallon baki fahimci rayuwa ba.
Ma'aruf ya ce
"Mummy dama fa ba son ta... Kafin ya kai aya Mummy ta É—aga hannu ta kai masa wani mummunan marin da ya sa ya ga giftawar taurari.
Sulaiman ne ya fashe da wata dariya da sai da ya komawa kowa madubi abin kallo wato kowa ya tsaya yana kallonsa da mamaki, sai dai yana cikin dariyar sai ya haɗe fuska, ya ɗaga kai yana kallon Ma'aruf da yake dafe da kunci, ya juya ya kalli Mummy sannan ya sauke idanunsa a kan Rahma cike da izza da taƙama irin ta ɗan gidan masu faɗa a ji ya ce
"Rahma ki sani daidai da second ɗaya ban taɓa sonki ba" Idanu ta zaro cike da fargaba zuciyarta ta bugu da ƙarfi, Mummy kuma baki ta saki tana kallonsa da tsantsar mamaki, Ma'aruf kuwa da dama ya san kwanan zancen sai hakan bai ɗaɗarashi da ƙasa ba, bai ba kowa damar magana ba ya cigaba da faɗin
"Na san saboda ina da kuɗi kike sona, da bani da kuɗi na tabbata ba za ki ƙaunace ni ba, tun da dai kika guji ɗan uwanki saboda bashi da kuɗi, bayan ya fini komai na ɗa namiji nagarta kyau da komai, to kin ga saboda na guje ki kar hakan ya dameki, ni dama don kawai a yi soyayar sharholiya don ki sani ma akwai wacce nake so, dama da a ce soyayyarmu ma ta ɗore sai dai ki ji an ɗaura mini aure, ina miki tuni da waɗanda kika yaudara a baya, kika fasa son su saboda kin sameni kika guje su, to ke ɗin ma yau gashi zan nisance ki, dama an ce duk abin da ka shuka shi kake girba, sannan duk abin da ka yi shi za a yi maka"
Yana kaiwa nan ya mayar da kallonsa ga Ma'aruf wanda ba ya mamaku furucin Sulaiman É—in don shi abu ne da ya gama fahimta tun ba yau ba.
Yana kallonsa ya ce
"Ɗan jagaliya ga ƙanawarka nan na bar ta zan je na tafi" Rahma ita mutuwar tsaye ta yi don kuwa maganganun Sulaiman sun ɗaure mata kai, ta kasa furta komai tana a hakan ya nuna mata fuskar wayarsa ya ce
"Kin ganta wacce nake da burin na aure ƙiris ya rage" Ya ce yana nuna mata hoton wata a wayae, sai ya juya ya nuna wa Mummy kawai sai ya fara taku ya fara tafiya.
Ma'aruf ya ce
"Ka je da mugun nufinka, Allah raka taki gona" ,Mummy ta É—aga murya ta ce
"Shege mai baƙin hali, mummunan halinka ya bika Allah ya isa, sai ka samu wanda zai maka abin da ka yi" Juyowa ya yi ya ce
"Kamar yadda kuka sameni na muku abin da kuka yi wa wasu ba"
Rahma juyawa ta yi da gudu ta yi hanyar da za ta sada ta da cikin gida.
Mummy ta ɗaga kai ta kalli Ma'aruf tana surfa masa zagi kamar ta ari baki, tana jaddada masa cewar ya ɗauko ruwan dafa kansa, don ta ɗauki aniyar saita gintse masa ɗan karatun bokon da yake taƙamar yana yi don dole sai ungulu ta koma gidanta na tsamiyata.
Ko fitar da za ta yi fasawa ta yi, ta koma ta hau lallashin Rahma da take ta kukan maganganun Sulaiman duk da abin da ya furta amma sai da ta koma tana faman kiransa a waya amma yake katsewa daga ƙarshe ma sai wayar ta ji a kashe.
Ma'aruf kuwa godiya ya yi wa Allah da ya sa halin Sulaiman ya bayyana ko ba komai ya ceci Æ´ar uwarsa daga mummunan nufin da Sulaiman É—in yake yi a kanta, ko bai auri Rahma ba duk da cewa dama ya san abu ne mawuyaci ya aure ta duba da yadda ita da mahaifiyarta suka tsane shi amma dai zai so ta samu namiji mai sonta da aure ba wai É—an a hole ba.
Tun kafin Daddy ya dawo gidan Mummy take doka masa kira a waya, yadda ya tsinci muryarta ne ma ya sa gabansa faɗuwa, saboda a nasa tunanin ko ɓoyayyan sirrin da yake ɓoye mata ne ta sani. Amma bayan ta shiga faɗa masa akwai matsala a gida sai ya ji ya ɗan samu sassauci don shi ba ya fatan Hajiyar ta ji ƙudurin sirrinsa a yanzu, ya san dai za ta sani amma akwai lokaci!.
Da dare yana dawowa ko ruwa bai watsa ba bare a yi batun cin abinci, Hajiya da Rahma suka saka shi a gaba da batun abin da ya faru, Rahma sai kuka take abin da ya sa hankalinsa ya tashi saboda ba ya haɗa damuwar Rahma da komai. Ransa ya ɓaci duk da Mummy ta cewa Rahma kar su bayyanawa Daddy furucin Sulaiman na cewa dama ba son ta yake ba da gaskiya kawai soyayyar shan minti yake son su yi, kuma sun ɓoyewa Daddy hakan nr don ya ɗauki maganar da muhimmanci ta yadda zai yanke tsatstsauran ra'ayi a kan Ma'aruf.
Ran Daddy ne ya ɓaci ya ɗaga waya ya kira Ma'aruf, sai gashi ya shigo da sallama, Hajiya sai aika masa harara take tamkar idanunta za su faɗo. A ƙasan kafet ya zauna yana ɗan sunkuyar da kai ya shiga gaishe da Daddy. Rahma sautin kukanta ta ƙara saboda Daddy ya yi hukuncin da ba zai yi wa Ma'aruf daɗi ba.
Daddy ko amsa gaisuwar bai yi ba ya ce
"Ma'aruf mai ya kai ka shiga sabgar da ba ruwanka? Mai ya sa ka bari haka ta faru a kan mai za ka yi yadda ka yi ka raba Rahma da mijin da za ta aura?" Baki ya buÉ—e zai masa bayani cikin nutsuwa amma sai Mummy ta dakatar da shi ta hanyar É—aga masa hannu ta ce
"A cikinmu babu mai maka ƙarya don haka ba bayaninka ake nema, ko kuma kare kanka, hujja kawai ,a ka bayar" Shiru ya ratsa falon saboda ya rasa ma mai zai ce.
Daga haka Mummy ta inda take shiga ba ta nan take fita ba, har Daddy yana ce mata wataƙila shi Sulaiman ɗin ya dawo su shirya amma Mummy ta ce ai ba zai taɓa dawowa ba.
Tashi ta yi ta fita, jim kaɗan sai gata da akwati niƙi-niƙi tana zuwa ta dangwarar da akwatin a gaban Ma'aruf ta ce.
"Alhaji ni dai daga yau na bar zama da wanann mai nufin mutane da sharrin a gidan nan, dole ya koma ƙauye don ba zai zauna yake korewa ƴata samari ba, idan su basu yaudare ta ba shi ai ya yaudare ta da kalamai ya ya gusar mata da abin da kowace ƴa mace take taƙama da shi....
*INNA TA SALLAH*
Tun kafin su ƙaraso fadar Mai Gari take hango rawanin Mai Gari take aikawa rawanin harara, ji take gabaɗaya har Mai Garin ma haushinsa take ji, a nata ganin ai shi ma ba zai ce kwana uku ba, tun da ya san a magana ta gaskiya ba lallai Ibra ya dawo ba a kwana kusa ma bare kwana uku ai dama sai ya ce daga wata uku zuwa shekara uku, wannan shi ne magana ta adalci.
Zaunawa ta yi ta ce
"Lami miƙo min saitin samirar wanann" Lami tana muzurai ta miƙa mata samira. A gabanata ta ajiye tana jiran abin da uban gayya wato Mai Gari zai ce domin ita ko arziƙin gaisuwa bai samu daga gare ta ba saboda tana ganin ai bai kamata tun da ya san ba ita ta ɗauki saniya ba yake mata aike kamar ta ci bashi.
Gyaran murya ya yi ya ce
"Tasallah ya za ki zo ki mana gurum da tsoffin kwanuka a gabanmu? Duk tunanina ma ko kaji ne kika soyawa fada kika taho da shi don in ke ci ina gabatar da shari'a cikin adalci, amma sai na ga an miƙo miki shafal da su samirun babu wani nauyi sai wata uwar lamba duk sun kwankwatse" Wani kallo ta masa ta ce
",Ai da kana son cin kaji sai ka aika mini zakara da kaza tun jiya da yamma, ka ga zuwa yanzu da na gama soyawa sai in taho maka da su" Ta faÉ—a tana kawar da kai gefe.
Ƙwafa ya yi bai ƙara maganar naman ba don ya gane magana Innar ta faɗa masa.
Ya cigaba da cewa
"Ko gabatar da kanki baki yi ba kika yi gurum da ke" Idanu ta É—ago ta ce
"Wai Mai Gari shari'a za ka yi a kan saniya ko kuma dai cin fuska za ka mini a gaban jama'a sanin kanka ne babu wanda bai san sunana ba Tasallah nake matar Malam kaka a wajen Ibra, mai ake neman sani kuma?" Ta tambaya tana kafe Mai Gari da ido.
Taɓe baki ya yi don ya ji hashin yadda ta bashi amsar ya ce
"To ina maganar mu ta kwana?"
Shiru ta yi sai kuma ta ce
"Yo tana inda ta kwana mana, a inda ka tsayar da ita ranar nan ina ganin ai bata motsa ba" Cike da jin haushi ya ce
"Tasallah kar fa abin naki ya fara wuce gona da iri, ana batun saniya amma kina mayar da abin wasa kamar ana maganar tsuntsuwa"
Ta ce
"To mai kake so in ce in ban faɗi haka ba fisabilillahi, yaron nan an bashi saniya ya tafi bai shawarce ni ba ban san ma ua bar garin ba, amma sai tuhuma ta ake kamar tsohuwar ɓarauniya ina dalili"
Mai Gari ya ce
"Abu ne da ya zama dole, in ba a faÉ—a miki ba wa za a faÉ—awa yanzun nan kika gama gabatar da kanki har da inkiyar kakar Ibra, kin ga kenan ba laifi ba ne don mun nemi ki a cikin laifinsa"
Kallon Jummai da take muzurai ta yi ta ce
"To fa! Allah ya dawo da mu ke dai wannan mata baki da haƙuri a ce a kan saniya ɗaya kina azalzalar mutane" Jummai kamar jira take dama ta ce