← Book details Malamin Bogi Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 17 OF 35

Sashe 17

Malamin Bogi Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

Wata mace ce mai ƙiba ta shigo, tana wani wurwurga idanu, ganin yadda take zazzare ido tana wani soshe-soshen jiki sai Sheik ya ji duk ya tsargu, juyawa ta yi ta rufe ƙofar bai lura ta saka mukulli ba, kuma sai ta cire mukullin, cike da ƙaguwa ya ce

"Mai yake tafe da ke?" Ta ce

"Ina so ka bani maganin da kullum mijina sai ni, sannan ka bani maganin da zan zubawa kishiyata ta mutu, da wanda idan na shafa a hannuna duk inda kuÉ—i yake zai zo wajena" Ganin kamar yadda take magana yanayin ya nuna kamar umarni take bashi ya ce

"Ayya ai ba a kisan kai a wajen nan, kuma kuɗin mutane ai kamar sata ce, zan baki dai wanda mijink... Bai ƙarasa ba kawai sai ya ga ta tashi tsaye idanunta sun juye ta fara dalalar da yawu, gabansa ne ya bada rasss ya shiga faɗuwa tamkar zuciyarsa za ta huda ƙirjin ta fito, gadan-gadan ya ga ta biyo shi, ya ja baya ta matso ya yi wani tsalle sai ya ji ta riƙe masa hiramin da yake rataye a wuyansa, jin za ta sheƙe masa wuya suka shiga kunce.

Idanunsa cikin nata ya gane aljannunta ne suka tashi ba ita ba ce, salati ya hau janyowa yana ji a ransa anya ba zai haƙura da maluntar nan ta BOGI kuwa ba? Da gudu suka yi wajen ƙofa sai lokacin ya lura ƙofar a kulle, idanu ya zaro gabansa yana faɗuwa ganin daga shi sai ita kuma bashi da nutsuwar mata ruƙiyya, kafin ya yi wani yunƙuri sai ji ya yi ta fisge hular gashin kansa, salati ya ɗauka a zuciyarsa kafin ya ƙarasa wani ya kamo wani , yana juyowa ya ga ta tuƙunƙuna hular ta ɗaga rigarta ta totsa hular da gemo da sajen boginsa a bireziya. Kafin ya gama tunanin asirinsa zai tono ta yi wani kukan kura ta shaƙo shi, rasa abin yi ya yi ya buɗe baki ya ce

"Gabaɗaya na ƙofar gida ku shigo a guje ana ruwan kuɗi a ɗakin malam" Ya faɗi hakan ne don a yi saurin kawo masa ɗauki, ya manta da cewa kansa babu hula, haɓarsa babu gemo, gefen fuskarsa babu sajen larabawa...

MAMAN AFRAH
09025576222

💃💃TALLAH TALLAH💃💃

*INA MANYAN MATAN SUKE?*
*Masoyana ina ƙara talalta muku kayan sana,ata kamr su*

*Less, atamfa, laffaya, kamfala, mayafai zannuwan gado, kayan yara, takalma na yara da manya, abayas, huluna na maza, mata, yara frames, sarƙa ɗan kunne zubuna banguls.*

*Akwai kayan maganin mu na kamfanin meera b herbs, maganin sanyi, maganin ƙiba, maganin rage ƙiba maganin rage tumbi, maganin cire tabo ga wanda suk shafa mai ya ɓata musu jiki ko fuska, sannan uwa uba maganin mata.*

*A ƙarshe ina tallata muku FURA dakan mai, wacce muke yi mai garɗi da ƙamshin man shanu, muna yi don biki, ko suna, ko taron naɗin sarauta da dai sauransu muna aikawa ko ina, akwai nono galan galan da bokitai ga masu buƙata, ku nuna min ƙauna ta hanyar siyar abin da nake siyarwa* .

*Mai so ya min magana a number ta 09025576222 idan ba saya za ki yi ba kar ki min mgn.*

https://chat.whatsapp.com/BcJ4LIJJQlfHRgfiJUnBJo?mode=r_c

👳🏻‍♂️ *MALAMIN BOGI*👳🏻‍♂️

NA

MAMAN AFRAH

First Class Writer's Asso.📝

Daga marubuciyar:

Ƙazamin miji
Bonono Rufin ƙofa...
Ruɓaɓɓiyar igiya
Ƴar zaman wanka
Ƙara'in inna delu
Beelal Da sauransu
Ƴan adaidaita sahu
Ungozoma
Jalli joga
Da sauran su.
*09025576222*

BOOK1️⃣
PAGE 8

Sanye take da doguwar rigar less wacce ta kama jikinta, ta yi ɗaurin ɗankwali wanda ya zauna daram a kanta sai mayafinta wanda yake kala ɗaya da leshin da ta saka, ƙarami ne mayafin yana rataye a gefen kafaɗarta ɗaya. Ƙaran takalmin ta mai tsine wanda take sakkowa da saman benen shi ne ya janyo hankalin Hajiya da take zaune a kan kujera tana waya.

Tana riƙe da wayarta ta ƙaraso tsakiyar rangameman falon, lokacin ya yi daidai da gama wayar Hajiya. Ɗagowa ta yi ta kalle ta, ta ce

"Inyeee ka ga ƴan matan Daddyn ta, kyakkyawar mace kuma matar manya ƴan boko masu faɗa ji, sanann matar masu kumbar susa" Wani daɗi ne ya mamaye zuciyar Rahma tana jin daɗi jin furucin da Hajiya ta mata, tabbas a duniya ta tsani talaka, ta tsani talauci kuma, tana son saurayi ɗan manya wato ɗan gidan masu kuɗi sannan ɗan gayu ko ma dai yaya yake in har za a iya nunawa sa,a shi to tana son shi sosai. Kai ta langaɓae gefe cikin shagwaɓaɓɓiyar fuskarta ta ce

"Ai ni sai na zaɓa sai wanda ya isa ne zai aure ni Mummy bana son duk wani namiji in har bashi da masu gidan rana" Murmushi Hajiya ta yi ta ce

"Da gaskiyar ki ko ni talauci ya yi gabas na yi yamma, kuma ke da kika tashi a gidan naira ai dole sai É—an naira" Murmushi ta yi ta ce

"Bari na je baby nah yana jirana" Hajiya ta ce

"Ya zo kenan" Rahma ta ce

"Eh ya zo" Tana faÉ—a ta kiya cikin takunta na maau aji irin na mata masu ji da kansu.

Yana zaune a wajen da aka tanada don zama a sha iska zaune a kan É—aya daga cikin kujerun wajen, hango ta ya yi ta taho tana tafiya tamkar tarwaÉ—a, tana tafiya tana yanga da wani jan a ji da mata masu aji ne kawai suke yin irin taku. Sulaiman tun da ya hango ta kwacakwam ya mayar da hankalinsa a kanta, dama yana chartin ne da wata budurwarsa, amma ganin Rahma ta taho sai ya yi saurin kashe data ya sauka ma daga kan whatspp É—in gabaÉ—aya.

Ma'aruf yana daga can É—aki ya zo buÉ—e labulen window saboda ya ji É—akin ya É—auki zafi, dama dawowarsa daga makaranta kenan, ya shiga ya yi wanka shi ne zai shirya. Ganin Rahma sai ya ji gabans ya faÉ—i, musamman da ya hango irin kallon da Sulaiman yake mata mai cike da soyayya. Kishi ne ya tsaya masa a rai. Idanu ya runtse yana jin irin yadda zuciyarsa take bugawa.

Da son samu ne yana so ya samu ko da kwatar matsayin da Sulaiman ne ya samu a wajen Rahma, shi in ba ma jarabawa ba da kuma zuciya da baka tursasa ta, ina shi ina kamauwa da son Rahma bayan ya san ko suma yake yana falkowa ba zai same ta ba.

Cike da jin haushi ya rufe labulen dan sai ya ji gwara ya dawwama a cikin zafin É—akin, a kan ya bar windown a buÉ—e yake kallon takaici.

Rahma kuwa ƙarasawa ta yi tana ɗan murmusawa, ta samu kujerar da take kallon ta Sulaiman ta zauna, idanun da ya kafe ta da su, hakan ya sanya ta sakar masa da wani shu'umin murmushi mai bayyana haƙora, yadda hakoranta suke a jere reras kamar masara sai ya ji ya ƙara mutuwa a kanta, ya san za a saka Rahama a sahun farko na kyawawa.

Cike da murya irin ta mayaudarin namiji, irin muryar da dama ta saba da yi digiri a yaudara ya ce

"Sannu da zuwa sarauniyar matan duniya, alkairin Allah yana lulluɓe da ke, ina so ki sani mutuwa ce kawai za ta raba mu, don na san na gama dacen mace ta kece raini ta nunawa sa'" Ya faɗa yana kafe ta da idanunsa wanda har aai da ya sa ta ɗan sunkuyar da kai tanaƴar dariya kaɗan.

Hannunsa ya miƙaya ajiye wayarsa a kan teburin da yake a tsakiyarsu ya ce

"Da a ce zan mallake ki da kuwa na gama dace a duniya, ke ni bana jin zan sake bacci a duniya, don an sallame ni, a baya in jin tamkar wanda na rako maza duniya, in na ga suna da budurwa mai aji kuma ana nuna musu kulawa da soyayya ashe dai ni É—in ma zan samu rabona"

Sai da ta É—ago fuskarta ta sauke idanunta a cikin nasa sannan ta ce

"Ba kai kaÉ—ai ne ka yi sa'a ba ni É—in ma har kullum ina alfahri da kai, yanzu daga zuwana ko gaishe da kai ban yi ba amma kana ta zuba mini yabo" Ta faÉ—a don kaf ta rasa inda za ta saka ranta, tana son ta ji ana yabonta ko ana koÉ—a kyawunta sai take ji kamar duk duniya babu kyakkyawa kamar ta.

Idanu ya lumshe ya buÉ—e su tarrr a kan nata idanun yana jifanta da wani kallo na mayaudara wanda duk macen da akw mata sai an sace zuciyarta ya ce

"Ke É—in ce kin cancanci haka, ke É—in ce duk kin rikita mini lissafi, bana iya kallon kowace mace sai ke, bana son kowacce mace sai ke, har abada na gama zamar mace sauran duk kallon maza nake musu" Wani mugun daÉ—i take ji

Tana kallonsa yana kallonta, hannunta da ta ɗora a kan teburin ya miƙa hannunsa ya ɗora a kan hannunta, Ma'aruf da fitowarsa daga ɓangarensa kenan sanye yake da farin yadi ɗinki tazarce yadin marar nauyi, ya yi matukar karɓar jikinsa, Sulaiman ganin Ma'aruf ya fito ya yi saurin janye hannunsa, ita kuma da yake ta ba Ma'aruf baya bata san ya fito ba, kuma ita bata ma ɗauki cewa taɓa hannun nata wani laifi ne da har za ta janye hannunta, tun da tana ganin yanzu dan ma saurayi ya taɓa hannun mace ma wani abun ƙarama bane, tun da yanzu har wajen hoto saurayi da budurwa suke zuwa, kuma a kama hannun juna, har ma da abin da ya fi hakan, kuma a ɗora a status mutane su gani babu mai cewa an aikata haramun sai dai ake cewa sun yi kyau, idan aka samu wanda ya ce hakan bai dace ba, sai a ce ai saurayin da za ta aura ne, ko a wane hadisi ko ayar aka bayyana haka? Kawai dai ƙarshen duniya ne duk da ba duka aka taru aka zama ɗaya ba.

Ma'aruf zuciyarsa ce ta fara tafasa shi fa dama ya lura cewa duk mazan nan da suke son Rahma ba wai son aure suke mata ba duk mayaudara ne. Wani mugun kallo yale jefaw Sulaiman daga nesa, Rahma ce ta lura da Sulaiman hankalinsa ba ya kanta baya ta waiwaya ta ga Ma'aruf ta yatsina fuska ta ce
Chapter 17 · 0% Book details