← Book details Malamin Bogi Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 16 OF 35

Sashe 16

Malamin Bogi Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

"Malam dama mijina ne ko kaɗan ba ya kiran sunana, sai ya kira kishiyata sa sunanta amma ni sai yake kirana madam, kamar wata inyamura mai bashi hayar gida" Ta faɗa cike da takaici don dama ta daɗe tana son ta magance wannan matsalar amma du wajen malaman da ta je sai a ce mata wai soyayya ce da girmamawa, waɗanda kuma take ganin sun cinye mata kuɗi ko an bata maganin ma ba ya yi, amma dai yanzu tun da ta samu balaraben nan wanda aka ce aljannu ma yana maganinsu, to tabbas ta san ta zo ƙare kukan ka.

Sheik a zuciyarsa ya ce

'Mata masu duniya, mata iyayen kishi wato ita ba wata babbar matsala ba ce da ita ma"' Amma a fili sai ya ce

"Allah sarki haƙiƙa na jimanta miki, wannan ba ƙaramin abu bane a ce mijinki yana kiranki da suna madam, kamar dai wata tunkiya, ko kuma bayerabiya mai gasa masara a bakin titi" Ya faɗa yana ɗan mayar da fuskarsa abin tausayi. Kai ta kaɗa irin ka ji dai ji, a zuciyarta tana jin daɗi don ta tabbatar da cewa wannan ba sunan soyayya bane ko na girmamawa.

Yana ɗakko wani ƙullin magani ya dube ta da kyau ya ce

"Wannan maganin ki samu ƙatuwar zabuwa ko kaza ki dafa da wannan maganin, ki juye masa ita duka amma sai ranar bakin girkin ki, kar ki ci ko ƙafar kazar, ki ce masa takanas kika dafa saboda kina son sa don ki faranta masa, sai ya kusa cinyewa ki ce masa kina da wata buƙata in ya tambaya sai ki ce daga yau ya daina ce miki madam, zai buƙaci sunan da zai kira ki da shi sai ki zaɓa ki faɗa masa, daga ranar zai daina kiran ki Madam!" Wani daɗi ne ya baibaye ta, ashe ma aikin ƙarami ne take ta ƙunsar baƙin ciki, kullum in ta ji ya kira kishiyarta da sunanta ita ranta ɓaci yake, ta lura idan ya ce mata madam kishiyarta har wata ɓoyayyar dariya ta cusa haunshi take mata.

Maganin ta karɓa ta ce

"Malam nawa ne abin sadaka" Sai da ya ƙare mata kallo yana son gane tana da halin kuɗaɗe masu yawa ko kuma kuɗi kaɗan take da shi, sai ya daure ya ce

"Ai abin sadaka ba ya kaɗan ba ya yawa" Ita kuma jin haka sai ta buɗe jakarta ƙarama, ta fito da wasu uban kuɗi ƴan ɗari biyar-biyar da ƴan dubu-dubu kuɗin gyaɗar yin ƙuli-ƙulinta ne wanda za a sayo mata buhu guda, mai da ƙarago take na siyarwa, malam sai washe baki yake a ɓoye yana ganin yana zaune a ɗaki zai ci bati.

Amma sai ya ga ta ajiye kuɗin a gefenta tana ta duba cikin jakar, a tunaninsa wani za ta ƙaro sai ya ga ta fito da naira hamsin, sai kuma ta ɗauke kuɗin mai yawan da ta ajiye a gefe ta mayar cikin jakar ta zige zip ɗin, ta ɗakko hansin ɗin da hannu biyu ta zo gabansa tana cewa

"Gashi Malam, Allah ya biya buƙatu, muna godiya babban balarabe na ƙasar larabawa" Tamkar Sheik ya saki ihu haka ya ji, kamar shi Sheik amma ta bashi hamsin. Tsaye ta miƙe bayan ta ajiye tana gyara mayafinta, ta juya tana masa sallama, ko amsawa bai yi ba, duk takaici ya ishe shi, yana jin da na sani dama bai ce mata abin sadaka ba ya yawa ba ya kaɗan ba.

A fili ya ce

"Haka kawai shi fa za a dafawa zabuwa ma ai ya fini morewa, ni da na masa silar cin zabuwar haka kawai na ƙare a kuɗin siyan goro, yo siyan goro mana hamsin in ba goro ba mai za a saya da ita" Duk maganar nan da yake cikin hausa sak yake yinta, jin tahowar mutum ya ja bakinsa ya yi shiru, yana mai yin sauri ya jefa hamsin ɗin cikin bahon gudun ma kar a ganta a gabansa a zaci kuɗi kaɗan yake karɓa.

Wani saurayi ne gajere baƙi ya shigo da sallama, malam ya amsa saurayin bayan ya zauna ya ce

"Malam ina da buƙata mai girma"

Sheik ya ce

"Ina jinka" Suarayi ya ce

"Matsalata guda ɗaya duk wajen budurwar da na je bata so na, sai ake cewa ba a son gajarta ta, kuma wai na yi baƙi da yawa shi ne na ce ko za a bani maganin da zan kore baƙin jinin nan daga jikina wato a bani maganin farin jini?" Shiru Sheik ya yi yana nazarin maganar, ya ƙara kallonsa sai ya ga har wani sheƙi baƙin nasa yake, ga wani muni kamar me, hakan ya sa a ransa ya ce

'Ni ɗin ma da kake gani duk bula ce, a toh ni ma ba farin bane mai ne ba don kar a yi saurin gano ni ba da man bilicin ɗina zan ke tsiyayewa ina ɗaurawa a leda ina ba masu buƙata irin taka, to kar a ce ni ɗin ma hakan take gwara in tsaya matsayina' A fili kuma ya ce

"Subhanalla, lahaula wala ƙuwwata illa billa, hasbunallahu wa ni,imal wakil, iyyaka na'abudu wa iyyaka nasta'in" Saurayin gabaɗaya sai gabansa ya shiga faɗuwa jin abin da Sheik yake faɗa, don har ya fara tunanin kar a ce aljana ce ta aure shi, ko kuma a ce ba zai taɓa auruwa ba a haka zai rayu, gashi yana buƙatar aure.

Tun kafin Sheik ya ƙara magana ya ce

"Malam ba dai babu maganin jinyata ba?" Ya ƙarasa kamar zai yi kuka.

Sheik ya ce

",A haba É—an saurayi ai kowace jinya Allah ya saukar da maganinta, mutuwa ce kawai bata da magani" Wani gauron numfashi ya sauke ya ce

"Alhamdulillah"

Sheik ya ce

"Matsalarka tana da magani amma da sharaÉ—i" Ya ce

"Zan bi kowane sharaÉ—i ne in dai mace za ta amince in na ce ina sonta har ta yarda ta aureni" Sheik ya ce

"Zan baka wani ruwa da za kake shafawa a fuskarka tsawon kwana bakwai, amma fa ka tabbatar a kwanaki bakwai ɗin nan ka samu wata ƙwaƙƙwarar sana'a da za take kawo maka kuɗi, sannan a ranar da ka cika kwana bakwai, ka nufi wajen budurwa da kake so kana zuwa kafin ka gabatar da kanka ka bata dubu goma" Idanu saurayin ya zaro saboda shi ko kyautar naira ɗari bai taɓa ba wata mace ba.

Yana kallon Sheik ya ce

"Malam dubu goma? Ni ai bana ba mace kuÉ—i" Sheik a zuciyarsa ya ce

'Ashe shi ya sa ake gudunka, yo ga muni ga cin zanzana, ma'ana ga talauci ka muni wace mace ce za ta yarda, da aka bayar da kuÉ—i ai babu wanda zai ga muninka" A fili kuma sai ya ce

"Wannan shi ne sharaɗin maganinmu" Shiru ya yi sai kuma ya ce in dai da biyan buƙata to zai yi.

Sheik ya san muddin saurayin nan yake bada kuɗi budurwa ba za ta ƙi son sa ba duk da ba duka aka taru aka zama ɗaya ba wasu ƴan matan basu da son kuɗi.

Ruwan da Sheik ya tsiyaya masa a ƴar kwalba ya karɓa, ya ce masa na farin jinin ne da kuma wanke shi da munin mata su daina ganin muninsa, godiya yake kamar zai ari baki, bai san cewa ruwan ma a randa Sheik ya ɗuro shi ya ajiye, don ya lura in ya ce maganin da ya saya wajen malam zai ke bayarwa ba lallai ya haɗa kuɗin ya ƙara komawa ya karɓo wasu ba, wanda ya san zai iya warware matsalarsu ba tare sa magani ba sai ya basu maganin BOGI.

Yana karɓa ya tashi zai fita ba tare da ya bada kuɗin sadaka ba, ran Sheik ne ya ɓaci ganin zai fita ya ce

"ÆŠan samari babu abin sadaka ne ?" Juyowa ya yi cike da girmamawa ya ce

"Ai a gari aka yi sanarwa cewa a zo nan a karɓi magani an samu baƙo daga ƙasar larabawa na ɗauka ba a biyan abin sadaka" Cike da jin haushi Sheik ya ce

"Hankali za ka taka aljani burubutu a gabanka dama su ne masu karɓar kuɗin sadakar" Da sauri sairayin ya ja baya yana mai ɗakko dubu biyu hannunsa yana karkarwa ya ajiye a gaban Malam ya juya cike da tsoro ya buɗe ƙofar ya fita.

Yana fita Sheik ya É—auke dubu biyu.

Wani tsoho ne ya shigo yana dogara sanda, saboda tsufa har ya ranƙwafa, dakyar ya zauna, yana sauke numfashin gajiya hannunsa yana karkarwar tsufa jikinsa duk ya yi yaba sannan kansa da gemunsa duk furfura. Sheik kawai kallonsa yake ya rasa ma mai zai kawo tsohon nan shi da ya dace ya zauna a gida yakenta sallah yana neman gafara ya jira zuwan mutuwarsa.

"Bakinsa yana karkarwa ya ce

"ÆŠana balarabe, na sha wahala a waje wajen bin layin shigowa, yanzu ma ganin an bige ni a turarreniya shi ne wata mata ta bar min layinta na shigo, ka san ai namiji É—aya sai a mace É—aya aka ake shigowa, shi ya sa ka ga na shigo" Har lokacin Sheik yana mamakin abin da zai kawo tsohon.

Daurewa ya yi ya ce

"Baba maganin basir kake so ko maganin ciwon baya?" Tsohon ya ce

"Haba ɗan nan balarabe, ni nan maganin maida tsoho yaro za ka bani, wato maganin ƙarfi ka gane?Ƴan mata ne guda biyu zan ɗauka a rana ɗaya dukansu kowacce budurwa" Mamaki ne ya mamaye Sheik dakyar ya danne harshen sa ganin bai yi magana da yaren hausa sak ba ya ce

"Budurwa fa Baba?"
Tsoho ya ce

"Rass kuwa ba ma budurwa É—aya ba Æ´an mata biyu ake saka mini su a lalle gobe za su tare ka ga kuwa aiki ya ganni dole in nuna musu basu auri tsoho ba"

Shiru Sheik ya yi ya rasa ma abin da zai faÉ—a masa, kawai ya É—akko wani garin magani ya ce ya saka a ruwan wanka ranar da amaren za su tare. Godiya kamar wanda aka bashi maganin da tsofa zai barshi.

Dubu goma ya ba Sheik amma sai da Sheik ya kama shi ya iya dogara sandar ya tafi.
Chapter 16 · 0% Book details