← Book details Malamin Bogi Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 20 OF 35

Sashe 20

Malamin Bogi Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

Bare kuma Sheik da yawanci matan dama kissa ce yake faɗa musu, da kyautatawa mijin kuma ko wanda ya ce mata suna gudunsa saboda muninsa da ya je ya yi abin da Malam ya ce na bayar da kuɗi ga budurwa sai gashi ya samu mai son sa har an ɗaura aure, hakan ya sa kowa ya ƙara yarda da maganin Malam. Sanann masu aljannu yana cewa suke karanta nas da falaƙi kullum wanann ya sa suke samun kariya tun da sun yi amfani da ayar qur'ani, idan kuma aljannun wanda ya fitarwa suka aara tashi, sai ya ce dama ciwo na ɗaya rana ne sauƙi sai a hankali.

Duniya ta yi wa Sheik daɗi yana cin karensa babu babbaka, gabaɗaya ya ƙara ƙiba saboda cin kayan daɗin da yake, duk da cewa yanzu Mai Gari yana sanyawa a masallaci ana haɗa sadaka to da su yake amfani wani lokacin ana ciyar da Sheik, sannan wasu ma suna kawo gudunmuwar kaji, wasu zabbi wasu ma dama idan daga rugar da suke maƙotaka da Ƙundun za su zo magani da kaji da nono suke zuwa a matsayin abin sadaka.

Wata rana ana zaune Sheik yana faɗakarwa, Liman sai muzurai yake don shi yanzu bashi da maƙiyi sama da Sheik, tun da an ƙwace masa Limancinsa wanda tun yana saurayi yake yi. Duk da a ganin Liman ɗin Sheik ya fishi ilimi kuma yana karatu irin nasu na larabawa amma dai duk da haka yana jin haushi.

Wani ne ya É—aya hannu ya ce

"Ya Sheik ni ina so a fassara min Assalamu alaikum, kuma a fassara mini karatun cikin suratul fatiha wacce ake karantawa a kowacce sallah, ina so in san me yasa a kowace sallah sai an karanta ta?" Ƙululuuuu cikin Sheik ya bada wani sauti a hankali ba tare da kowa ya ji ba.

A zuciyarsa ya ce

'Na shiga uku yau an ƙure ni?' A fili kuma sai ya ce

"Ma sha Allah, su'alun mai kyau" Ya faÉ—a yana É—an lashe baki.

GabaÉ—aya waje ya kaure da cewa

"Yawwa ni ma ina so in sani" Kowa sai ya ce yana son ya sani har Mai Gari. Da gangan Shei ya tsiri wani tari yake yi ba ƙaƙƙautawa daga tarin ya lafa sai ya ce

"Ma sha Allah ya ikwan... Sai kuma ya sake fara tarin alamar tarin ba zai bar shi ya yi magana ba, nan aka shiga masa sannu aka kawo masa ruwa amma ya ƙi dainawa saboda dama da gangan yake tarin saboda bai san amsar da zai bayar ba.

Ganin haka sai Mai Gari ya ce Sheik ya je gida ya huta, daga haka maganar fassarar ta sha ruwa.

Wata rana da daddare Sheik ya fita daga gida ya saci hanya, gidan wani matashi da yake babu nisa da inda aka sauke shi ya je, ƙogar gidan ko kara ta ba a yi ba kasancewar sairayin yana shaye-shaye idan ya dawo daga yawonsa a buge sai ya shiga ya kwanta. Can Sheik ya shiga ya ga sausayin kwance a tsakar gida a ƙasa yana bacci. Machine ɗin saurayin ya ɗauka ya fito daga gidan, sai da ya ɗan tura machine ɗin ya wuce gidan saurayin, ya tada mashin ɗin dama ko mukulli ba a sakawa mashin ɗin a hakanake tashin sa.

Hawa ya yi ya tafi ƙauyen da malamin wanda Sheik yake karɓar maganin da yake ba mutane, ya same shi ya bashi kuɗi mai yawa daga kuɗin da yake samu, nan malamin ya bashi magungunan amma Sheik ya ce maganin matsalolin mata ya fi yawa saboda sun fi zuwa da matsaloli. Ya bashi kuɗin mayukansa da sabulai da turaren oud da sunayen su a rubuce ya ce zai dawo ya karɓa, dama malamin yana zuwa birmi. Bayan ya karɓo ya dawo gidan saurayin ya akiye mashin, ya tafi gidansa.

Yau ta kama laraba misalin ƙarfe goma Sheik yana zaune a ɗakinsa yana karantar ƙamus mai larabci da hausa, yana ta haddar kalmomin larabci don ya haddace saboda sakowa a magana, duk da cewa ya san ko kwaɓa larabcin ma ya yi ba ganewa suke yi ba, Allah ma da ya taimake shi rubutun larabcin akwai inda aka yi fassarar hausar larabci.

Shigowar mutane ya ji zaure gidan suna rafka sallama kamar dai ma a kiÉ—ime suke, da sauri ya mayar da littafin ya tashi ya hau sallaya, jin suna ta cigaba da sallamar sai ya shiga jan gyaran murya alamar baya rabuwa da bauta da ibadad kowane lokaci.

Jin suna É—an surutai sai ya saurara ya ji suna cewa

"Ai shikenan kuma matsalolin Ƙundu sun fara dawowa, har muna murya an maganace ashe dai da sauran rina a kaba" Didimmm ƙirjinsa ya buga, kafin wani yinƙuri sai ya ji muryar Mai Gari alamar shi ma ya shigo yanzu, ya ji Mai Gari cikin karkarwar murya yana cewa

"Kabarin Hashimu da na wa hallaw?"

Sheik ya ji wani ya ce

"Da kabarin Fatsime" Gabaɗaya Mai Gari ya kwashi salati. Zufa ce ta fara ketowa Sheik jin ana maganar kabari shi dai duk da bai fahimci kurman baƙin ba amma dai ya san shi ne a cikin matsala tabbas.

Haka ya koma ya zauna daɓas sai da ya ji ya ɗan samu ƴar nutsuwa sannan ya buɗe baki ya ce

"Bismillah a shigo" Ya faÉ—a yana janyo dogon carbinsa mai dubu ya fara ja yana mismis da baki tsabar rikicewar da ya yi shi kansa bai san abin da yake faÉ—a ba.

Su duka suka É—oro É—akin Mai Gari ne a kan gaba sai wasu mutum huÉ—u a bayansa.

Mai Gari yana baza malun-malun ya zauna amma kana ganinsa ka san babu lafiya, yana zama ya ce

"Barka dai Ya Sheik" Sheik sai da ya yi yaƙi da idanunsa wajen ganin basu bayyana taoron da yake ciki ba tsumu-tsumu don shi a duniya in dai maganar aljannu ne da maganar mutuwa to ya ƙi jinin maganar nan, ko kabarin mai Ƙusumbi da yake zaune a gidan da shi saboda, kar ya bayar da kansa a ga gazawarsa, don dai ba yadda zai iya kuma yana son samun kuɗi ba ya so ya bar garin wato ya bar cima mai daɗi da kuma samun kuɗi, shi ya sa yake wanann siyar da rai, to in ba siyar da rai yake yi ba kake tunkarar aljannu kai tsaye, bayan shi ƙasurgumin jahili ne ya shiga MALUNTAR BOGI.

Amsawa Sheik ya yi yana É—an washe bakin dole, duk gumi ya wanke masa goshi, saboda lura da ya yi da sauran mutanen nan su a tsugunne suke basu zauna ba, hakan duk yana nuni da ana cikin ruÉ—u da masifa.

Mai Gari ya ce

"Ya Sheik abu ne na gaggawa, garin Ƙundu babu lafiya, wannan ƙaiyen da muke maƙotaka da su ne maƙabartar su ta cika, to shi ne idan aka yi rasuwa sai su kawo maƙabartar garin nan su binne, yanzu wani yaro ne ya mutu a garin sun zo ya za su binne shi aka samu gawa biyu an tono su daga kabari, kuma an ce masu haƙar kabari da suka zo suka tona kabarin da za a binne yaron lokacin da suka gama kabarurrukan da aka tone lafiya lau ba a tone suke ba, sai yanzu da suka zo suka tarar da hakan, kuma sun ce ɗaya gawar da aka tone ta yi motsi bayan ta shekara nawa a binne, yanzu dai sun bar gawar yaron a maƙabartar kowa ya gudu" Mai Gari ya faɗa yana ɗago kai ya kalli Sheik.

Tun da Mai Gari yake bayani ƙirjin Sheik yake fat-fat-fat, ya yi wani tsumu-tsumu tamkar an tsamo ɓera daga ruwa, dama sunkuyar da kansa ya yi idanunsa suna kallon ƙasa don kar su fallasa asirin zuciyarsa na tsoron da ya ji ya kunyata.

Sheik ya ɗago da kansa idanunsa tamkar wanda aka tada daga baccin sa yake mafarkin tsoro, ya yi wujiga-wujiga, ruwan da yake gefensa a kwano ya ɗauka ya kurɓa, bayan ya ce musu da sai ruwan roba da na leda yake sha, ajiye kwanon ya yi ya ɗago carbinsa yana ja tsabar ya ruɗe ma ba ɗaɗɗaya yake jan carbin ba, wani lokacin ƴaƴa goma wani lokacin biyar kawai ja yake babu ƙaƙƙautawa, sai da ya ji zuciyarsa ta daina bugun da in ya yi magana za a harbo jirginsa na tsoro ya yi ta maza ya ce

"Subhanallahi, subhanallahi, subhanallahi, wannan aikin aljannun garin ne yanzu abin har ya kai a tono gawa a kabari kai abin ya girmama, yanzu ya za a yi?"

Ya tambaya har lokacin tamker ana fisgo maganganun daga bakinsa. ÆŠaya daga cikin mutanen ne ya ce

"Ya Sheik yanzu dai ka yi gaggawar zuwa maƙabartar nan ka rufe kaburburan da aka tone, gudun kar a yi bori da sanyin jiki su cigaba da tone sauran kaburburan maƙabar nan, tun da hatta yaron nan da ya mutu yana nan ajiye a makara ba a binne shi ba, an bar sabuwar gawa ajiye a maƙabarta" Nannnauyar ajiyar zuciya ya sauke wacce ta kasa ɓoyuwa a ɗakin ya ce

"Tabbas wannan iblisan aljannu ne, da ifiritai" Mai Gari ne ya zaro ido duk da yana ganin za a magance matsalar garin amma jin wannan sunaye na aljannu ya ƙara rikita shi ya ce

"Yanzu waɗanann aljannu ya za ka yi ka fitar da su daga garin nan, bayan ƙauyen ya yi lafiya amma kuma yanzu za su dawo mana da hannun agogo baya"

Sheik ya ce

"Kar ku damu, na taho daga ƙasarmu ne don in kawo ɗauki ga mutane masu neman taimako babu gudu babu ja da baya" Ya faɗa yana miƙewa tsaye, ganin haka sai suka fita suka bar shi, gabaɗaya ji yake kamar ya rufe ido ya gan shi a garinsu MAI MANGWARO ji yake kamar dai ya bi wata hanyar ya bar garin ba tare da sanin kowa ba, sai dai wata zuciyar tana tuna masa irin badaƙalar da ya baro a garinsu, da basussukan da ake binsa kuma dai bai akiye ba bai bayar ba ajiya, ya san tabbas in ya koma zaman banza ne zai cigaba da yi, amma tun da ya samu sana'a a nan dole ya jajirce.
Chapter 20 · 0% Book details