← Book details Malamin Bogi Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 32 OF 35

Sashe 32

Malamin Bogi Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

"Haba Æ´ar lele ai komai nake hankalina yana kanki, kin sha gaban duk matan duniya ke kaÉ—ai idanuna yake iya gani da kuma hange, haba amarya mai capacity, amarya kin fi quality, mu kwanta...

Banko ƙofar da Mummy ta yi shi ya ankarar da su juyo, zumɓur Zee ta miƙe daga cinyar Daddy, a take idanun Mummy suka sauka a kan cikin wata huɗu na Zee wanda ya yi kufkuf a jikinta kamar ƙaramar ƙwarya...

*BOOK 1 free shiga grp na BOOK 2 500, cmplt doc 800*
*Acc no faiza abubakar 9030283375 opya shaidar biya 09025576222 gobe za mu gama book 1*

*Yau ba samu leƙo inna amarya ba da kuma ango Sheik mai breast*
😂😂😂😂😂😂

*Sai gobe in muna raye*

MAMAN AFRAH
09025576222
[7/17, 7:31 PM] Mom mashkur & Afrah: 👳🏻‍♂️ *MALAMIN BOGI*👳🏻‍♂️

NA

MAMAN AFRAH

First Class Writer's Asso.📝

Daga marubuciyar:

Ƙazamin miji
Bonono Rufin ƙofa...
Ruɓaɓɓiyar igiya
Ƴar zaman wanka
Ƙara'in inna delu
Beelal
Ƴan adaidaita sahu
Ungozoma
Jalli joga
Da sauran su.
*09025576222*

BOOK1️⃣
PAGE 15
*END OF BOOK 1 LAST FREE PAGE*

*BOOK 2 500 naira pay in to faiza abubakar 9030283375 opay*

IMZEEDVENTURE
https://chat.whatsapp.com/GCVmfFguMEf49AFrOjSiMt
Duniyar kayan kitchen da na yara masu kyau da araha!
Kina neman kayan kitchen masu kyau, luxury da adashe, ko kayan yara masu kyau da tsada ko gonjo mai kama da sabo?
To shiga group É—in IMZEEDVENTURE!
Za ki sha mamaki! 🤩Muna da:
✅ Adashe na kayan kitchen
✅ Kayan yara sabbi da gonjo
✅ Kayan gyaran gida da na mata masu kyau
📞 Tuntuɓi mu: +234 707 753 2253
📩 DM: WhatsApp
📸 IG/Tiktok: @imzeed_ventureƊ

*INNA TASALLAH*

Cike da tsoro take kallon sabuwar addar hannun Jummai gabanta yana faÉ—uwa, ta É—auka Sule jarumin maza ne zai yi iya yainsa don ganin ya dakatar da Jummai daga wannan barazana ta mummunan aikin da take so ta yi amma sai ta ga har lokacin yana dafe da mararsa yana ciccira idanu tamkar kwarton da aka kama a É—akin amarya.

Jummai kuwa babu alamar wasa ko kuma yin barazana a kalamanta ko yanayinta kana ganinta ka san iya gaskiyarta take faÉ—a iya abin da yake cikin ranta ne kuwa alwashin da take ci babu gudu babu ja da baya.

Inna a zuciyarta ta ce

'Tabbas Æ´an magana sun ce kifin fadama ba ya gasa da kifin kogi, amma wannan mata tana son kawo min cikas a É—an amarcin da na É—ora rai zan dangwala, tana son shuka min salalan tsiya' ,A fili kuma sai ta ce

"Haba Sule ka yi wani abu mana, kana dai jin abin da take faÉ—a tana neman kawo tsaiko a lamarin kasancewarmu tare, kuma sanin kanka ne Mai Gari ya kashe wannan maganar, kuma maganar ta mutu murus"

,Wani yawu Sule ya haÉ—iye ya lura Inna bata san abubuwan da sukw faruwa a duniya ba, shi da yake ma'abocin sauraren rediyo ne babu abin da bai sani ba saboda yana jin labaran yadda wasu matan suke yankewa maza mafitsara musamman a kan lamarin kishi, bare Jummai da haka nan ma tarar aradu da ka ne da ita bata barin ta kwana.

Yana ɗan sakin murmushin yaƙe ya ce

"Haba Tasleey ai kin san Jummai a kan gaskiyarta take, haƙiƙa saniya ba tawa ba ce ke ma kuma kin sani"

Wani takaici ne ya rufe Jummai jin wai Sule yana kiran Inna da Tasleey wato ta lura maza basu da gaba basu da baya wato sawun keke ne su, amma in ba haka ba ita yake kiranta Jummai amma Inna daga tarewa har ya sauya mata Tasallah zuwa Tasleey.

Inna kuma wani haushin Sule ne ya kamata tana ji kamar ta hau shi da duka, yana ji za a mata sagegeduwar amarcin amma babu wani kataɓus da ya yi, ita ba ma wannan ne tunanin ta ba yadda maƙociyar yarinyar nan ta bata ƙwaƙwalwar raƙumi ta yi amfani da shi gashi yanzu ana neman sakawa ta shiga uku.

Inna ta ce

"Ban gane a kan gaskiyarta ba?" Ido ya shiga ƙiftawa Inna yana mata alama da addar hannun Jummai, ita ma Inna hannunta riƙe da mazaunai ta ce

"To shikenan saboda ta ɗauki adda sai a ƙi faɗar gaskiya, kana ji fa ta ce wai ni za ka bata in koma ɗakinta, ka taɓa jin wannan ɗanyen aiki ni fa tun da an ɗaura mana aure ni ɗin fa na zama mallakinka ita kuma tana a matsayin kishiyata ne, yanzu kawai sai in koma ɗakin kishiya?"

Jummai ce jin har suna shawara, kenan suna ja da maganarta hakan ya sanya ta fara taku ta zo gaban gadon ta zauna ta miƙe ƙafa ranta a ɓace ita kuma adda sai walwali take, wannan ƙallin da addar take shi yake ruɗawa Sule ciki.

Sule ganin haka ya ce

"Tasleey maganin kar a yi kar a soma... A hargitse Jummai ta katse shi da faÉ—in

"Wane suna ne wannan É—in?"

Da sauri ya gyara da faÉ—in

"Tasallah a bar maganar nan Jummai iya gaskiyarta take faÉ—i"

Inna saroro ta yi tana kallonsa ganin da gaske dai Jummai yake tsoro, duk da ita ma tana tsoron amma tana so ne ta yi yaƙi ta karɓi ƴancin ta.

Inna ta ce

"Jummai kin san dai na yi jika da ke, ni ba na son tashin tashina, tun da Allah ya yi na auri mijinki ki É—au dangana, duk ranar da Ibra ya dawo da kuÉ—inki zan sa Sule ya warware igiyar" Kai Jummai ya É—aga tana wani yatsina ta ce

"Sule ya muke ciki ne? Ka ga yadda na kulle É—aki daga ni sai ku, sannan ga sabuwar adda"

Sule cike da zuga da kambamawa ya ce

"Jummai ikon Allah, Jummai masallacin kura kike ba a ba kare limanci, ƙarfe duka ƙarfe ne amma a cikin ƙarfe akwai zinare da azurfa" Ya faɗa cike da kirari don ganin ya faranta mata ta janye batun ta, don shi yana tsoron mutuwa saboda bai shirya tafiya ba, kar a je ta guntule shi tsakiyar dare ya shiga uku.

Inna jin ta yi sake reshe kama ganye, wato dai amarcin nan ba ciyuwa zai yi ba, sai kawai ta fashe da kukan takaici" Sule bai lallashe ta ba ko bata baki gudun kar ya yi laifi.

Jummai ta sheƙe da dariya ta ce

"Wato an ga samu an ga rashi, to ai sai ki tashi ki koma ɗakin mijinki, wato ni kenan ɗakin mijin ki Jummai" Cewar Jummai tana ƙara bushewa da dariya

Kai Sule ya shiga gyaɗawa kamar ƙadangare, alamar eh, Inna ta kalli Jummai ta kalli sule wanda zuwa yanzu ya fara motsu-motsu da harhaɗa ƙafafu wanda ba komai ba ne ya haifar da hakan sai maganin da ya sha ne yake tambayarsa.

Cike da sanyin murya ya ce

"Tasleey au...

Ya dakatar da maganar tunowa da ya yi Jummai ta yi magana É—azu.

Yana sauya akalar maganar ya ce

"Tasallah ki tashi ku je ku kwanta" Wani haushinsa ne ya kama Inna tana ganin saboda tsabar shi saunan namiji ne kana da amarya amma ka ba mace saboda namijin hotiho ne shi.

Jummai ta miƙe tsaye tana wata hamma, ta je saitin ƙofar ɗakin ta tsaya, ganin Inna bata taso ba, sai ta saka addae a jikin bango ta karta alamar wasawa ta yi, tsabar ruɗewa a kuɗime Sule ya miƙe bai san ya aka yi ba sai ganinsa ya yi a gaban Jummai, sai da ya ganshi a gabanta ya tuna cewa ashe ba shi ne za a tafi da shi ba.

Inna kuma karta addar a bango sai ya sa ta miƙe tsaye har zani yana neman kwancewa ta gyara, Jummai ce ta ce

"Sule ko har kai za a tafi ne?" Yana wayincewa ya ce

"A haba da girman kujerarki ai da Tasallah ne za ku tafi" Ya faɗa ransa yana ƙuna gabansa kuma yana faɗuwa a lokaci guda, don shi duk abin da za a ce an haɗa da rai to tabbas ba ya son maganar mutuwa.

Inna tana yin yaƙe ta ce

"Eh da ni ce" Dariyar cin nasara Jummai ta saki a ranta tana saka hannu ta buÉ—e sakatar ta saka Inna a gaba suka nufi É—akinta suna fita Sule ya yi zaman Æ´an bori yana ambatob Lahaula wala quwwata.

Kai ya dafe da hannu biyu a fili yana faÉ—in

"Kin cuce ni Jummai, sai da na gama ɗora rai zan kwashi garaɓasa kika mini shigar sauri, yanzu a ce sai da na gama bankar magani abokaina suka gama zuzuta maini amarcin zan kwashi ganima amma ki zo ki min haka" Ya faɗa idanunsa suna masa jawur.

Inna kuwa ɗakin Jumman suka shiga, warin fitsarin yaran ne ya ankarar da Inna cewa an shigo ɗakin ƙazama Jummai, don yaran sun isa su daina fitsarin kwance ma.

Cike da umarni ta nunawa Inna gado, haka Inna ta hau gadon tana jin tsinkon da marar ta take mata. Amma babu yadda ta iya haka ta hau ta kwanta, tana tuno tsiren amarcin ta da kuma ruwan ledar da aka kawo mata na amarci. Jummai wuri ta samu ta ajiye addar ta hau gefen Inna ta kwanta, sai yanzu Jummai ta ji sauƙin zafin ranta da yake mata raɗaɗi tun lokacin da aka ɗaurawa Inna auren, ga kishi ga rashin saniya, yanzu kuma tun da Inna ta dawo ƙarƙashin ta sai take ji daidai yake da saniyarta ce a kusa.

Sule a nan tsakar ɗakin ya yada zango, don ko gadon ƙarfen Inna bai samu hawa ba, haka nan tsire ma bai samu shiga ba saboda yanzu amaryarsa kawai yake buƙata amma babu hali, don da alama Jummai da gaske take ba za ta bar Inna a ɗakinsa ta kwana ba, tun daɗewa yake jiran dawowar Inna ya ɗauka Jumman za ta barta ta zo amma dai har har yanzu shiru, kamar maye ya ci shirwa ba amo ba labari, tun da dai babu niyya ango ya kwana da wando.
Chapter 32 · 0% Book details