← Book details Malamin Bogi Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 22 OF 35

Sashe 22

Malamin Bogi Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

Da yake Sheik a wuyansa ya rataya carbinsa, littafinsa yana aljihunsa, Mai Gari ganin gawa tana son cim masa sai ya miƙa hannu ya kamo carbin wuyan Sheik a haka suke gudu, sai da suka zo dab da shiga gari Sheik ya ja wuyansa sai carbin ya tsinke, a nan Mai Gari ya saki carbin, kamar an ce su waiwaya bayansu a tare suka hango gawar bagatatan tana binsu, wanann karon yaron tsirara ya riƙe likkafaninsa a hannu hancinsa toshe da auduga, yana cewa

"Sheik, Mai Gari ku zo ku mayar da ni kabarina ku binne ni" ,Amma bahu wanda ya tsaya bare ya saurare shi.

Tun daga gidajen farko -farko suke cin karo da gidaje a rurrufe, alama ce ta gabaɗaya magana ta ratsa gari tun da dama a tsorace ake da maganar tone kabari bare kuma yanzu aka ce gawar ta tashi zaune, tabbas sai inda mai ya ƙare shiga motar mahaukaci!.

Sun zo tsakiyar gari suke ganin mutane suna ɓullowa ko ta ina, wani babu takalmi wani hula a maƙale a hamata wano ya tuɓe rigar ma yana zangaya gudunsa a haka.

Mai Gari maimakon ya yi hanyar gidansa sai kawai ya bi bayan Sheik, Sheik kuwa ganin gawar yaron tana son cin musu sai ya tura wata ƙofar gida haka Mai Gari ya mara masa baya suka shige, gidan wata tsohuwa ne wacce kp fita bata iya yi, ɗaki suka bankamu suka rufe suna mayar da numfashi.

Sheik ya fito da robar magani daga aljihunsa ya buɗe yake tuttulewa a fuskarsa, Mai Gari ma ya karɓa ya watsa a tashi fuskar sai suka ji da wata muryar yaro an ce

"Ku zo ga likkafaninku, raminku yana can na haƙa muku kabarin" Suna juyawa suka ga yaron ya ratso ta bango, da rarrafe suka fito Mai Gari yana miƙewa sai gida ya yi, Sheik ma ya yi nasa gidan yana shiga ya banke ya zauna ya kifa tagumi, carbinsa ɗaya ya ɗauka ya fara ja yana jin tsoro sosai idan ya tuno wai gawa ce ta tashi da ƙafarta take bin su riƙe da likkafani.

Yana cikin wannan halin ta tuno yadda ya ji wani a maƙabarta ya ce, ya ga wani kabarin yana motsi tunanin da ya fara kar sai gabaɗaya gawarwakin su fito su bazo gari shi bai san ma abin da zai ce ba.

Tun da ya shige ɗaki bai fito ba, ranar haka garin ya tsaya cak baka jin motsin kowa hatta masallaci ma ladan bai kira sallah ba, bare kuma mai gayya mai aiki wato Sheik ya fito ya ja sallah, to shin wa zai ja sallar ma? Bayan mutanen gari kowa yana gida a ɓame ana tsoron fitowa a yi arba da gawa.

Salloli dai Mai Gari sai a É—aki ya samu ya yi alwala a wani kwano ya gabatar sa sallolinsa cikin tsoro. Ranar dai babu watandar kayan daÉ—i yo waye zai dafa kayan daÉ—in.

Ɓangaren Mai Gari ma tun da ya kwasa da gudu ya yi gida, lokacin matarsa ta ji ana cewa gawa ta bazo gari hakan ya sa ta taho za ta kulle gida, ta tura ƙofar kenan hakan ya yi daidai da zuwan Mai Gari ya kai kansa ta banko masa ƙofar a goshi, haka suka shiga turarreniyar ƙofar shi yana turawa yana so ta buɗe masa ya shiga, ita kuma tunaninta gawar da aka ce ta bazamo gari ce, shi kuma tsoro ma ya hana shi furta komai, saboda ko da ya taho ma ya sha haɗuwa da mutane kowa yana ta kansa, babu ma wanda ya lura da shi bare a girmama shi, yo shi ina zai tsaya karɓar girman ma.

Jin yana neman ya ci ƙarfinta sai ta ƙara dagewa ta tura ƙofar, Mai Gari sai cewa ya yi

"Ke buɗe Mai Garin Ƙundu ne" Jin muryar mijinta a rikice sai ta matsa daga ƙofar ko kallonta bai yi ba ya wuce ta ya shige cikin gida a guje, ganin haka bata tsaya rufe gida ba don abin ya girmi tunaninta yadda ta ga Mai Gari yana zabgar gudu ta san tabbas akwai lauje cikin naɗi.

Baya ta take masa sai dai kafin ta je ya shige ɗakinsa ya banki sai ƙaran saka sakata ta ji, nata ɗakin ta nufa, wanda tana shiga ta rufe ƙofar runawa da ta yi sakatar ta cire, sai kujerar zaman tsakar gida ta mata ta saka a bayan ƙofar ta zauna tana haki tana tunanin to ina Balaraben Malamin garin nasu da yake yaƙar aljannu.

Washe gari sai da gari ya waye tangararai aka fito sallah, saboda ƙarfin hali irin na Sheik ya baro wata baƙar rigar jallabiya tana ta sheƙi ta ƙara haska shi, ya sheƙa uban turaren oud, ya fito yana jan carbi, yana muzurai don kar a kawo masa raini, a haka ya ja sallar, bayan an idar ya zauna a mazauninsa bayan ya juyo ya fuskanci mutanen masallacin ya ce

" Alal haƙiƙa jiya mun haɗu da wani ibtila'i, wanda aka samu wani aljani marar imani ya shiga jikina don kawai yana son ya rikita wanann gari ku shiga halin ha,u'la'i, saboda sun san ni kaɗai ne zan kawo mafita a wanann gari, sun san ni zan magance duk wata matsala da za ta tunkaro gari, shi ya sa suka tura mini wani ƙasurgumin aljani ya shiga jikina, sai da daddare na ƙure karatun qur'ani a wayata sanann na hau yi wa kaina da kaina ruƙiyya, a nan ne da ya buɗe baki ya yi magana na gane ashe ba ni bane aljani ne" Kowa ya yarda da maganar Sheik sai suka ji dk ya fara basu tausayi don sun yarda da abin da ya faɗa.

Mai Gari da yake da shi suka yi gudun famfalaƙin da Sheik sai ya kalle shi da mamaki ya ce

"Yanzu dama Sheik duk wannan abin da muka yi na gudun ceton rai ba kai bane?" Wani yawu Sheik ya haÉ—iye jin kamar dai tambayar ta yi kama da tambayar tuhuma ko rashin yarda.

Cikin son ya kankarowa kansa mutunci ya ce

"Ashsha Mai Gari, haba kai kuwa ni ne zan yi gudu saboda gawa? Ko ana ha maza ha mata ai ba zan yi gudu ba, sannan kuma ina horar mutane a kan rashin dacewar tuhumar malaman su musamman malaman larabawa ko abu suka yi ba daidai ba, ba a tambayar mai ya sa" Shiru Mai Gari ya yi sai ya ce

"Ni ma duk mamaki ne ya cika ni, ni ina ta gudun gawar yaro ashe ina tafe da aljani" Ya faÉ—a yana ji babu daÉ—i.

Haka dai Sheik ya yi ta kawo maganganun da zai kama zuciyarsu, ya ringa faÉ—ar maganganu masu shiga rai, saboda cewa ya yi ma ko joya da suka ji shiru bai fito ba aljanin ne da bai sake shi ba shi ya sa bai fito jan sallah ba, basu san abin da ya hana su fitowa ba shi É—in ma shi ne ya hana shi fitowa wato tsoro.

A ƙarshe dai ya ce musu wannan yaron ba mutum ba ne, aljannu ne suka ɗauke gawarsa wanda ya taso ya shigo gari aljani ne ya yi shigar yaron, sai washe bari aka ga gawar yaron a ƙofar maƙabarta, haka dai Sheik ya ari jarumta aka binne yaron.

Bayan sati uku, komai ya kankama, a inda mata suke tururuwar zuwa wajen Sheik karɓar magani, gabaɗaya a sati rana biyu ce ta maza amma kwanaki biyar duka mata ne aka warewa suke ziyartar Sheik ɗin.

Hatta ƴan mata suna layi a wajensa, maganin farin jini, maganin karɓar kuɗi a hannun saurayi, maganin samun bazawari marar mata, haka suka yi ta zuwa suna karɓar magani, Sheik kuma kasuwa ta kankama yana ta damƙar kuɗaɗe.

A wata ranar laraba ne Sheik ya yi arba da wata budurwa da iyayenta suka kai masa ita ya mata ruƙiyya tun da ya ɗora kansa a kan yarinyar nan ya ji ya kamu da son ta, yana so ya aure ta amma kuma yana tsoron su mutanen gari su zargi wani abu ko ma wani ya harbo jirginsa, a ga shi yana balarabe ya ce yana son baƙar fata, amma dai ya fara ƙagauta da zama babu mace ya baro matansa biyu.

Shiru ya yi a fili ya furta

"Ba za ta saɓu ba bindiga a ruwa, in baro mace tana gugar mace har mata biyu amma in zo ina zaman gwauranci, shi ma Mai Garin ban da sakarai ne ka bar baƙo babu mace haba ko da na ce ni malami ne ina kwaana sallah da salatin annabi S.A.W ai ni ma ba dutse bane kuma ba katako bane da zan ƙare kullum a cire aljannu da bayar da magani, ina nan ina zaune da abu sanƙamƙam a jallabiya" Ya faɗa yana jan wani dogon tsaki.

Bayan kwana biyu da yamma ya ce zai yi lazimi ya dakatar da ba maza magani dama ranar maza ce, shi kuma ya fi son ranar mata saboda wuni yake yana wadaƙarsa yana kallon su shegen son mata.

Kuma maza basa bada kuÉ—in sadaka da yawa, amma ya fi morar kuÉ—in mata.

Yana kishingiÉ—e bayan ya gama kallon film a wayarsa, wanda ya sauke a youtube, wayar da ya cewa su Mai Gari wayar babu komai sai karatun qur'ani.

Ɗan baccin da ya ɗauke shi ne yake mafarkin ya auri budurwar nan da ya ɗora rai. Bugun ƙofar gidan ne ya falkar da shi, ji yayi ana ta rafka sallama, ya taso ya leƙo, jin ana hayya- hayya, wata matashiyar mace ce aka shigo da ita maza ne ƙattai uku sun riƙo ta tana togewa, dakyar ake janyota sai kamce saniya, da wata mata tana share hawaye da alama mahaifiyarta ce, sai da Sheik ya kalle ta ya gane ido ɗaya ne da ita.

Aljannunta ne suka tashi, ɗaki aka sakawa Sheik ita duk da yana jin ɗarɗar haka ya shiga mata ruƙiyya kafin a gama ruƙiyyar ta haɗa shi da ƙasa sau uku, yana cikin bayan ya fitar mata da aljannun sai ta miƙe ƙafa ta ƙura masa idonta guda ɗaya har sai da ya tsargu, ko kuɗin sadaka bai karɓa ga burinsa kawai su fitar masa ita.
Chapter 22 · 0% Book details