← Book details Malamin Bogi Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 34 OF 35

Sashe 34

Malamin Bogi Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

Rahma ta kasa jurewa, wajen sha biyun rana da ya fita ta je ta cewa Mummy za ta tafi Ƙundu ta je ta faɗawa Mai Gari halin da ake ciki, don ita abin ya mata ciwo tamkar dai wanda aka ce Daddy babu aure ya yi wa Zee ɗin cikin.

Tana fita Mummy ma ta rufe ƙofar ta kwanta ranta yana ƙuna tana tunanin mafita da kuma yanda za ta yanke shawara.

Rahma mota ta ɗauka ta saka jakarta a ciki, direba ta sa ya tuƙa ta suka doshi garin na Ƙundi wanda rabon ta da ƙauyen har ta manta kuma ta san dai Mai Gari yayan Daddy ne kaɗai yake iya sanya Daddy ya yi ko ya hana shi.

*SHEIK*

Cike da tashin hankali Sheik ya yi cilli da bulalar hannun sa, yana kai hannu biyu ya taɓa ƙirjin yana faɗin

"Innalillahi, na shiga uku ya zan yi?" Ya faɗa a hankali yana kallon amaryar tasa da ta zube a ƙasa kamar wacce ta suma.

Mai Gari da ya ji Sheik yana cewa su maido da nonon da suka É—auka, kuma dai sai ya ji Sheik É—in ya yi shiru wannan dalilin ne ya sa murna ta cika Mai Gari don a tunaninsa Sheik ya sa aljannu sun maido da nonon amaryar, baki ya buÉ—e yana cewa mahaifiyar yarinyar

"Kin ga abin da nake faɗa miki ko? Ai balaraben malami mashayar ɗa ba ko mutum sukutum aka ɗauka sai Sheik ya dawo da shi bare wani nono ai abu mai sauƙi ne fitar da wando ta ka" Ya faɗa yana dariya mai sauti, duk matan tsakar gidan a kunnen su aka yi wannan magana, a take aka fara ƙusƙus kowacce tana cin alwashin ta samu wajen zuwa neman maganin damuwarta.

Mahaifiyar amarya ta washe baki tana jin daɗin sa'ar sirikin da zai zama silar warakar ƴar tata. Duk maganar nan da ake a kunnen Sheik da ya jiƙe jagaf sa gumi ƙirji da tudun breast.

Maganar Mai Gari ce ta katse shi da faÉ—in

"Ya Sheik sun maido ko?" Sheik yana kallon ƙirjin sa ya buɗe baki dakyar ya ce

"Ina ta fafatawa dai da su suna gab da maidowa" Ya faÉ—a yana hawaye da jin da na sanin wannan maluntar BOGIN

Ya cigaba da karanta qulhuwallahu wacce ita kaɗai yake iya tunawa zuwa yanzu, yana tofawa amaryar don yanzu bashi da ƙarfin dukanta ma.

Yana yi sai ya ga ƙirinta ya fara tasowa kamar almara sai ga tudun ƙirjinta ya dawo, a rikice ya kalli nasa ƙirjin ganin bai ɓace ba kuma dai natan ya dawo das dashi.

Da sauri ya tsugunna yana yin ƙasa da murya ya ce

"Haba aljannu kar mu yi haka da ku, ni na yafe nonuwan nan domin Allah ku raba ni da shi" Amma atishawar amaryar tasa ce ta tabbatar masa da cewa aljannun sun sake ta.

Ƙuri ta masa da idon ta ɗaya tana washe baki, fuska ya tamke yana ganin duk ita ce silar shigarsa matsalar da yake ciki.

A wayince ya shiga kare ƙirjinsa gudun kar ta gani, ya janyo hiraminsa ya yafa a kafaɗa yana dibara wajen kare ƙirjinsa.

Magana take masa yana amsawa a daƙile, ya buɗe ƙofar ya fito ta biyu bayansa tana tafiya dakyar alamar ƙarfin jikinta bai dawo ba, mahaifiyarta ta rungume ta cike da murna, kowa na wajen ya zo ana kallon yadda Sheik ya sa aljannun suma maido mata da nonon ta, sai dai babu wanda ya lura da ƙirjin Sheik bare a ha ajiyar da aljannun suka masa.

Mahaifiyarta tana ta masa godiya, tana cewa yanzu ai za a kawo masa ita gidan, amma buÉ—ar bakinsa sai ya ce aljannun sun ce ba yau za ta tare ba idan ta tare yau za su haifar da gagarumar matsala a garin.

Jin haka sai Mai Gari ya ce a dakata da tarewar yau, shi kuma Sheik ya yi hakan ne saboda rufuwar asirin sa, don ya san matsawar aka kai amarya to tabbas ita ce za ta fara tona masa asirin ajiyar da aljannu suka masa a ƙirji, bare kuma shi da rayuwarsa gabaɗaya sirri ce yana sana'arsa ta MALAMIN BOGI.

Daga nan masallaci suka wuce ya ja su sallar isha'i basu lura da yadda yake ta kare-karen ƙirji ba. Ana gama sallah ya ce zuwa zai yi ya kwana yana lazumi saboda matsalar garin, amma ya faɗa ne kawai don yanzu tashin hankalinsa bai wuce ƙirjinsa ba, so yake ya ce ya ga ta yadda zai yi da breast ɗin ƙirjinsa.

Bayan ya je gidan ko ta kan abincin da aka kawo bai yi ba, É—akin ya bankawa sakata, ya yi saurin cire hirami ya jefar ya kama riga ya cire.

A razane yake kallon ƙirjin nasa ganin wani baƙiƙƙirin ɗin breast ne, musamman da suka haɗu da farar fatarsa da ta sha bilicin, sai baƙin su suka ƙaru, kamar a jikinsa suke tun asali haka suka yi, ya rasa ma ya zai yi da su.

Ya fara tunanin mafita cewar yake yafa hiraminsa a wuya yana dabara yadda zai ke ɓoyewa ba tare da kowa ya gani ba, har zuwa lokacin da Allah zai yanke masa wahala, don shi bai taɓa jin an ce namiji yana da breast ba in har ba mata maza ba. Ya san mata maza ne suke da breast sannan suna da HQ da kuma mazantakar namiji a jikin su, amma dai bai taɓa jinw wanda shi ba mata maza ba kuma aljannu su fito masa da breast rana tsaka tashin hankalin ya yi yawa.

Haka ya kwana ranar da zulumi sai bacci ɓarawo ne yake ɗauke shi.

Washe gari aka kawo masa wata mata Æ´arnuwar Mai Gari an ce masa bazawara ce sakin wawa, an kawo ta ne a mata magani saboda tun da suka rabu da mijin har yau ta rasa mashinshi ni, shi ne ake tunanin ko mijinta na farko ne ya mata asiri.

Sheik tun da ya ƙyalla idanu a kanta ya ji yawunsa ya tsinke, sannan a ransa yana tunanin ina ma a ce wannan ce aka ɗaura masa aure da ita ba waccan mai ido ɗayan ba, yanzu kuma da kunya matsayinsa na balarabe ya ce ya ga baƙar fata yana so, domin ita ma farar bafulatana ce gashi har kafaɗa ga shi tana da cikar halitta wacce ita ce ta sanya Sheik ya rasa nutsuwarsa don sai ya ji ko fatar jikinta ne yana so ya taɓa.

Saboda wannan dalilin na ba ya son ya daina kallon ta ya ce maganin na kaana uku za a yi, sai wanda suka kawo ta suka koma garinsu ita aka barta a gidan Mai Gari a kan cewa idan an gama maganin ta koma.

Da yamma motar su Rahma ta yi wa garin Ƙundu dirar mikiya, a ƙofar gidan Mai Gari motar ta tsaya, tun kafin ta fito ta hangi Sheik yana tsaye da wasu mutane, gabanta ne ya yanke ya faɗi ganin wani balarabe fari tasss da shi yana sanye da baƙar jallabiya ga gashin kansa kwance lufff kamar na jarirai. Sajensa da ya ƙara ƙawata fuskarsa shi ne abin da ya ja hankalin ta cikin sauƙi, gemunsa da ya tashi ziyat a habar shi kaɗai ma abin kallo ne.

Ta shagala da kallon Sheik bata san lokacin da ta sauke wata nannauyar ajiyar zuciya ba. Sheik bai ganta ba saboda hankalinsa ba a wajen motar ma yake ba, dakyar ta samu ƙwarin gwiwar fitowa daga motar.

Abin yana bata mamaki ya aka yi aka samu balarabe a wannan kwaraɓaɓɓan ƙauyen, ko ita da take bahaushiya ba don wannan damuwar da suke ciki ita da Mummyn ta ba, babu abin da za ta shigo ƙauyen nan ta yi.

Direban ne ya bita da akwatin kayanta wanda ta ɗakko kala uku da kuma su madara kwanfiles da sauran abubuwan buƙata saboda ba za ta iya cin cimar garin ba, kuma dai a yadda ta yi fushi da Daddy tana so ta ɗan nesanta kanta da shi, sannan sai ya zo har garin an magance matsalar wannan dalilin ne ya sa ta taho da kaya.

Mai Gari ganin Rahma ya cika da murna, har ya kasa zaune da tsaye ganin ƴar ɗan uwansa da ya fi ƙauna. Mutane suna ta mata sannu amma ko kallo basu ishe ta ba, tana ta waiwayen inda za ta ƙara ganin balaraben nan amma bata ga inda ya yi ba.

Direban komawa ya yi a cewarta za ta masa waya ya zo ya ɗauke ta, in buƙatar hakan ta taso.

Da suka yi sallar isha'i Sheik yake cewa Mai Gari ya fara sha'awar saka kayan hausawa babbar riga da Æ´ar ciki, Mai Gari ya yi mamaki ganin dai Sheik bai saba da saka kaya in ba na larabawa ba, amma ganin ya ce tana so sai ya ce za a siyo shaddodi da yadika masu tsada a É—inka masa.

Shi kuma Sheik ya yi hakan ne saboda ya fara ɓoye breast ɗin ƙirjinsa, sannan yana so idan ya je wajen malamin da yake karɓo magunguna ya bashi kuɗi a siyo masa bireziya saboda ya fara suturta ƙirjinsa tun da yana ganin bra ɗin za ta sanya ba za a lura da tudun ba kuma musamman idan ya saka kayan hausawa da babbar riga.

Rahma ta faÉ—awa Mai Gari gabaÉ—aya damuwar da ta kawo ta, Mai Gari dama ya san cewa É—an uwan nasa ya yi aure amma kuma bai san cewa bai sanar da iyalinsa ba, don haka sai ya nunawa Rahma zai kira shi ya masa magana za a san abin yi a hukunta Daddy, ta ji daÉ—in furucin shi ma kuma ya mata hakan ne don ta fita daga damuwa.
Chapter 34 · 0% Book details