Sashe 6
Malamin Bogi Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read
Ganin Rahma ta tashi tsaye tana wani buga ƙafa alamar ɓaci, wai Daddy ne zai cigaba da bata fruit, da sauri Yaya Ma'aruf ya ɗauke kai, ganin kayan sun kama mata jiki, kuma ya san shi ba muharraminta bane. Sallama ya musu yana shirin juyawa ya ji Rahma tana cewa
"Daddy ka ce Yaya Ma'aruf ya miƙo fruit ɗin ka cigaba da bani" Ta faɗa lokacin da Daddy ya zaunar da ita kusa da shi yana lallashin ta yana faɗin zai bata har sai ta ƙoshi.
Idanu Yaya Ma'aruf ya runtse jin rainin wayon wannan, ba don yana son ilimi ba, kuma yana da burin ya je garinsu ya kawo musu cigaba daga jahilcin da suke ciki da tuni ya bar gidan nan ya koma ƙauye. Maganar Daddy ce ta katse mata tunani.
"Ma'aruf miƙo fruit ɗin can na ƙanwarka" Daddy ya faɗa hankalinsa yana kan Rahma da take ta zuba masa shagwaɓa, yana mugun son ƴar tasa. Haƙori Yaya Ma'aruf ya sanya ya danne leɓensa na ƙasa yana jin takaicin wanann aiken, amma babu yadda zai yi, kasancewarsa mai biyayya, cike da ladabi ya je gaban Hajiya ya ɗauki tiren, Hajiya tana aika masa wani kallo saboda ita kawai bata ƙaunarsa.
Sai da ya je zai ajiye amma Rahma ta miƙo hannu ta ce ya bata plate ɗin, ya mayar da tiren kicin. Daddy bai ji daɗin abin da ta yj ba amma babu yadda zai yi don ba ya son abinda zai mata ran Rahma. Haka Yaya Ma'aruf ya danne zuciyarsa ya ɗauki plate ɗin fruit ya miƙa mata ashe dai bata riƙe ba, ai kuwa plate ɗin ya kuɓuce gabaɗaya kayan marmari suka yi masauki a jikin fararen kayan Rahma, duk ruwan kankana ya fito jawur a jiki, tana kallon jikinta ta fashe da wani kukan ɓaci, da sauri Hajiya ta tashi har tana neman yin tuntuɓe, tana zuwa vata yi wata-wata ba ta ɗaga hannu ta saukewa Yaya Ma'aruf yatsunta biyar a kumatunsa, kuncin ya safe cike da mamaki ya ɗago idanu yana kallonta Daddy kuma ya miƙe tsaye, duk da ya ji zafin abin da Ma'aruf ya yi na zubaw Rahma kayan marmarin a jiki amma kuma ya ji haushin marin da Hajiyar ta wanke Yaya Ma'aruf da shi a ganinsa abin da ya yi bai kai a mare shi ba, hakan ya sa Daddy ya ce
"Hajiya...
*SHEIK*
Yana cikin wannan halin wandonsa jargaf da fitsari, ya fara ganin wasu ƙananan yara kamar jarirai amma tsaye suke a kan ƙafafunsu suna doso shi, kusan su goma, da alama daga cikin garin suke, abin da ya tsorashi ma babu wani mai sutura a jikinsa su duka tsirara, bai gama tunanin jinsin mutane ne ko na aljannu ba sai ya ji budurwar nan ta ƙofar gidan da take kiranshi ta ce
" Sheik waÉ—annan Æ´aÆ´anmu ne ni da kai, wanda na haifa maka su daren yau, gasu nan zuwa kowanne ka masa kuÉ—uba ka raÉ—a masa suna" Galala yake kallonta, ganin jariran suna dab da zuwa suna faÉ—in
"Baba Sheik" Kawai Sheik ya yanke shawarar ya tsira da rai da lafiyarsa, don da alama wanann yaran suka rafke shi wato suka ɗane jikinsa kowa fisgar inda ya samu zai yi ba lallai su bar shi da fatar jikinsa bama, fakar idanun budurwar yayi kawai sai ya zura da uban gudu, ganin wata kwana sai kawai ya sha kwanar, amma kamar almara sai ya ji ƙarab takun gudu a bayansa, haka ya tabbatar masa da biyo bayansa ake yi, ganin wata bishiya ya yanke shawarar hawa kanta, a nashi tunanin idan ya hau bishiyar in wanda suka biyo shi sun zo sun wuce sai ya sakko in ya so ya gwammace ko gadin gidan wasu ya je ya yi da ya zauna a wannan bala'i da tashin hankali, da shegen kaɗayi da son abin duniyarsa ya kawo shi ciki.
Yana hawa bishiyar yana jin wani santsi dakyar ya samu ya haye sai da ya hau can sama, ya samu waje ya zauna, sai ganin jariran nan ya yj sun tasho suna gudu suna kiransa, haÉ—e da wanann budurwar mai fitila, suka zo suka wuce bishiyar, wata dariya Sheik ya fashe da ita marar sauti a zuciyarsa ya ce.
'Ashe aljannu ma ana iya guje musu, ka ga sakarkaru wato ni ina saman bishiya ku kun wuce kuna kirana, wannan shi ake kira hotiho!'
Yana kallonsu har suka yi nisa kifta idanun da zai yi sai ya neme su ya rasa a fili ya ce
"Ai indau zan samu cikar burina to da in fallasa kaina a gane MALAMIN BOGI ne gwara kullum in ke kwana a saman bishiya, a to don na ga wajen zama ni sai in ke kwantawa ma a kan bishiyar in kr baro musu gi...
Jin an zungure shi daga bayansa shi ne abin da ya dakatar da shi daga maganar da yake, cike da faÉ—uwar gaba ya É—an waiwaya, jariran nan ya gani su duka suna kan bishiyar da yake muryar É—aya mai amo a cikin su ita ta katse shi da faÉ—in
"Baba Sheik muna ta nemanka ashe dai ka zo gidanmu" Jin an ambaci gidansu sai lokacin hankalinsa ya kai ga kallon bishiyar da yake kai a nan ya ga bishiyar kuka ce wato matattarar aljannu" Hawaye ne suka taru a idanunsa, ya tashi dakyar jikinsa yana karkarwa, rigar wuyansa ya É—akko ya É—aure tsantsa, bai jira komai ba a fili ya ce
"Innal hamda, wal ni'imata laka wal mulk, la sharikala, Allahu akbar! " Yana gama faɗar haka ya yi tsalle ya diro daga saman bishiyar nufinsa sai dai su tsera, da aljannun yaran, amma abin mamaki maimakon ya ji shi a ƙasa sai ya ji shi ya dira a kan hannaye, yana dubawa ya ga wannan jariran ne su duka suka masa ɗaukan makarar mamaci.
Babu damar guduwa ya zubawa sarautar Allah ido, don shi kansa ya san riƙon ma ba na jarirai bae, tamkar wanda aka tara ƙattan maza.
Suna tafiya suna faÉ—in
"Mama mun ɗakko miki Babanmu" Sheik kuwa sai ruwan ido yake tamkar an buɗe famfo. Suna zuwa ƙofar gidan suka samu wannan dai budurwar, shi bai san wane irin tunani zai yi ba ma.
Tana ta musu sannu da kawo Babansu ta matsa gefe suka shige da Sheik yana ji yana gani, suna gama shiga, ta rufe ƙofar gidan ta saka sakata.
ÆŠakin da Sheik ba a can ya sauka ba can aka nufa da shi, suna shiga suka zaune da shi yana ta kallon ikon Allah, da suka ajiye shi suka fara kama jikinsa kowa yana mamula, guda biyu sun kama breast É—insa suna sha wasu kuma jikin fatarsa da babu riga, a zuciyarsa ya ce
'Wai ni Ibra yau ni ɗiyan aljannu suke mamular fatar jikina da bakinsu marar haƙori, har da masu sha mini mama, na ga ta kaina duk tsorona amma yau an ƙure mini gudu' Ya faɗa a zuciyarsa hawaye suna zuba shaaaaa.
Yana nan zaune suna ta faman tsotsarsa, idanunsa a rufe don ya lura duk idanunsu babu ƙwayar ido a ciki. Idanun a rufe ya ji kamar daga saman matar nan ta ce
"Ka raɗa musu suna ka zo mu kwanta dare ya yi" Cike da faɗuwar gaba ya buɗe, ya ganta zaune a bakin wani gado mai kyau. Haka ya ringa kai bakinsa wajen kunne jariran yana musu gwalan gwalantun larabcin da bai san mai yake faɗa ba bare ya san addu'a ce ko mene ne. Abu ɗaya ya sani duk wanda ya gamawa gwalan gwalantun sai dai ka ji daga ƙarshe ya ce, Mamuda, Lawwali, Amiru a haka ya gama raɗawa kowa suna. Yana gamawa suka tashi suna masa bye-bye suna cewa sai sun dawo, haka budurwar nan ta miƙo masa hannu, wannan karon a zuciyarsa ya ce zai gwada sa'arsa don yadda ya ga za su kaɗaice a gado da aljanna yana tsoron wani abu ya wakana a tsakaninsu ma'ana ta je ta masa cikin gaske, tun da yanzu ma gashi tana cewa ƴaƴan can nasa ne.
Ganin ta fara wani abu kamar mai shirin yin dambe sbai san lokacin da zuruf ya tashi tsaye ba, sai kawai ya ga ta fara sawaya ta koma tsohuwa tukuf, a guje ya fito daga ɗakin, ɗakinsa ya shige, yana haki yana shiga ya banke ƙofa ya saka sakata, kan katifa ya faɗa ya ja wani tsohon bargo da ya gani a kan katifar, da gari lafiya ƙalau ne ya san, sai dai ya cewa ƴan garin larabawa basa shiga tsohon bargo, amma yanzu da yake neman mafaka yake gani yake ko cikin kashi aka ce ya shiga babu musu zai shiga kashin in da hali har wanka sai ya yi da kashin..
Tun da ya rufa da bargon nan yake ta faman gumi amma bakinsa sai warto addu'a yake wacce bai san wace iri ba ce shi dai fatansa ya tsira dafa halin wannan, sai ya ji a ransa zai bar garin Ƙundu a gobe amma in ya tuna irin kaji da shayi mai kauri da zai je sha to tabbas sai ya ji zai jure komai.
Tun da ya rufa shi ba a kwance ba, shi ba a durƙushe ba kawai dai ya yi goho ya nutsa kansa a katifa, a haka yake ta jin ife-ife da guje-guje wani lokacin ya ji an buga ganga wani lokacin a ƙwala masa kira, fitsari ya yi wajen kala biyar, har sai da aka fara kiran sallar asuba, sannan ya ji komai ya lafa, can kafin shigar masallaci ya fara jin tashin muryoyi a ƙofar gidan, yana ji ana ta bugawa, amma ya ƙi fitowa ma don shi yanzu babu wanda zai kira shi ya je, gani yake aljannu ne, duk da yana ganin rashin fitarsa masallacin asuba barazana ne ga maluntarsa, amma dai a halin da yake duk ya yi wurjanjan, da kuma jiki da fitsari jargaf in ya fita ya buɗe ƙofar abun kunyar sai ya fi na ƙin zuwa masallaci.
Sai da ya ga rana ta fito tangararau ya tashi ya fito har lokacin rigarsa tana ƙugunsa a ɗaure, ya since a zuciyarsa yana faɗin