← Book details Malamin Bogi Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 7 OF 35

Sashe 7

Malamin Bogi Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

'Wuya in ji tsula, yau malamin balarabe na ƙasar Yemen ya ga ta kansa cikin dare' Ya faɗa yana shafo breast ɗinsa da suka sha damƙa a bakin aljannu. Dakyar yake tafiya haka ya je ya buɗe ƙofar gidan sannan ya shiga ɗaki ya saka hularsa ta gashi da gemunda sajensa, yana gamawa ya shiga bayi ɗaure da towel bayan ya kai ruwa, jikinsa ya shiga sallewa da daddaɗan sabulun bulicin mai ƙamshi, ya gama saɓa jikin bai ɗaureye ba, dib ya ji wani abu ya faɗo daga sama, yana dubawa ya ga kunnen jariri ne.

A can ƙofar gida kuwa Liman ne da Mai Gari suka zo da manyan ƙartai za a ɓalle ƙifar gidan a shiga a ga ko lafiya sabon malamin balarabe bai fito sallar asuba ba, kuma an zo an buga masa shiru, sun san dai malamai kamar Sheik ba ya ƙi yin sallar jam'i da gangan ba su da suke ganin an kawowa ƙauyensu waraka daga jahilci, amma har rana ta yi ba a ganshi ba.

Ganin kunnen da Sheik ya yi, hakan ya yi daidai da saƙa ƙafa da wani ƙaƙƙarfan saurayi ya yi ya hankaɗa ƙofar gidan, kasancewar Sheik sakatar ya cire bai buɗe ƙofar ba. Buga ƙofar da ta daki bangon bayin shi ya ƙasa assasa tsoro da ruɗanin da Sheik yake ciki, tunaninsa ya bashi aljannun ne suka kawo masa ziyara, don ya san yadda mutanen garin suke girmama shi, babu yadda za a yi su banko masa ƙofa haka har ta gwaru da bango, towel ɗinsa ya fisgo a inda ya rataye ya naɗa a ƙugunsa ko ɗaurewa bai yi ba, ya bazamo da gudu daga banɗakin takalminsa ma ɗaya can ya barshi a bayin, sannan ga jikinsa kumfar da bai wanke ba, fitowarsa a rikice ya nufi ɗaki ko kallon hanyar ƙofar gidan bai yi ba burinsa kawai ya shiga ɗaki ya kulle, Mai Gari da tawagasarsa su Malam Liman ganin abin da yake faruwa sai suka tsorata, sun san duk abin da zai sanya Ya Sheik babban malami balarabe gudu to ba ƙaramin abu bane, ganin shi da ya san qur'ani da ayoyin Allah, da addu'o'i yana gudun ceton rai ina ga su ƙasurguman jahilai.

A take aka shiga Æ´ar tsere zuwa É—akin Malam inda ya nufa, sai suke ganin nan ne wajen tsira, samari guda biyu sai Malam Liman da kuma Mai Gari aka fara rige-rigen zuwa É—akin Malam Sheik, shi kuma Sheik sai da yana dab da shiga É—aki ya lura da tawagar Mai Gari, ganinsu da gudu a kiÉ—ime sun nufo hanyar É—akinsa alamar kamar an biyo su, sai ya yi tunanin gari ma babu lafiya, tunaninsa su É—in ma daga waje aka biyo su suka taho wajensa kasacewarsa malami basu san a halin da ya kwana ba, basu san shi bacci ma tun na farkon dare bai runtsa ba haka ya kwana tsakanin waje da cikin gida, yanzu ma yana wanka yana son bayan ya yi wanka ya yi alwala ya yi sallah don yadda jikinsa yake sharkaf da fitsari sai ya yi wanka.

To sai kuma aka samu an jefo masa kunnen jariri a banɗakin, bayan ya fito hallaw gashi ya ci karo da su manyan garin su ma sun zo. Da Sheik da Mai Gari aka yi karo wajen shiga ɗaki, shi Mai Gari yana fatan kar Malam ya ƙulla musu salalan tsiya wato ya shige ya banke ƙofar ɗakin, don su tunanin komawa baya ma su fita daga gidan hakan bai zo musu a ƙwaƙwalwar su ba, bare ma sun san tun da aka samu matsala a masaukin malam to garjn ma yana dab da rikicewa, don wani sa'in gabaɗaya aljannu garin suke rikitawa.

Karon da suka yi babu wanda ya lura, kowa ta kansa yake, a haka Malam Liman ma ya totsu suka zama su uku a bakin ƙofar suna ƙoƙarin shiga, ƙofar ta musu kaɗan kuma kowanne ya kasa dakatawa wani ya fara shiga. Samarin nan ma suna jira su ma su shige.

Malam Liman yana kai kansa suka yi gware da goshin Mai Gari, Sheik ne ya fara nasarar shigewa ɗakin, sai dai da takalmin nan ƙafa ɗaya ya shige santsin ledar tsakar ɗaki ya kwashi Sheik, sai gashi wancakal a gefe, yana ta yaƙi da towel ganin bai masa tsirara ba. Su kuea su Mai Gari basu lura da wani towel ɗinsa ba bare su kawo zai yi wani tsirara, don gani suke tamkar a filin ƙiyama inda ake cewa kows ta kai - ta kai yake.

Sheik da rarrafe ya ƙarasa saman katifa, sai Mai Gari da Malam Liman suka mara masa baya, samarin nan ma suna shiga ɗayan ya banka ƙofar, su duka cakuɗe a kan katifar, Sheik ya warto tsohon bargon nan, zai rufa ai kuwa Mai Gari ya ce da wa Allah ya haɗa shi in ba da bargon hannun Sheik ba, nan ya shiga yaƙin warta don ya rufa shi ma, haka Malam Liman ma, ya shiga jan bargon da ya gama shan duniyarsa, kasancewar bashi da ƙwari sai ya yage a biyu, Malam Liman ya ɗauki ɓangare ɗaya, Mai Gari da Sheik suka shiga ɗayan, samarin nan suka totsa kawunansu a babbar rigar Liman...

😂😂😂😂😂

Na ba kaina daria yau Allah sa ju dara amma akwai cakwakiya.

Mu haÉ—u next page akwai gwarama, za ku ji yadda Sheik zai kare kansa saboda rainin wayo, su kuma sai su bada kai bori ya hau.

MAMAN AFRAH

09025576222
[7/2, 4:03 PM] Mom mashkr & Afrah: https://chat.whatsapp.com/EBurrU2vz6OFGbE37xLhPS

👳🏻‍♂️ *MALAMIN BOGI*👳🏻‍♂️

NA

MAMAN AFRAH

First Class Writer's Asso.📝

Daga marubuciyar:

Ƙazamin miji
Bonono Rufin ƙofa...
Ruɓaɓɓiyar igiya
Ƴar zaman wanka
Ƙara'in inna delu
Beelal
Ƴan adaidaita sahu
Ungozoma
Jalli joga

Da sauran su.
*09025576222*

BOOK1️⃣
PAGE 4

*SHEIK*

Suna tunanin samun nutsuwa amma abin ya ci tura!. Abin da yake faruwa shi Sheik ga tsoron kunnen da ya gani a banɗaki ga kuma tunanin yadda ya hango su Mai Gari a sukwane, shi bashi da nutsuwar da za tambaye su ba'asin gudunsu tun da har ya ga suna tseren shiga ɗaki da masu garin to tabbas ya san wataƙila cikin garin yana can a rikice kamar filin yaƙi, kuma ya san kowa shi zai jira, shi ma kuma ga a halin da ya kwana ga kuma a halin da ya falka ko sallah bai yi ba, kenan lamarin garin Ƙundu ba ƙaramin lamari bane in dai a ce aljannu da ranar gari ma sai sun addabi jama'a to lallai akwai sake.

Kowa gabansa faɗuwa yake, shi Malam Liman sai yanzu yake jin da na sani da sun juya baya sun koma cikin gari, amma gashi sun shigo wannan gida mai ruɗani bayan sun san cewa wannan gidan shi ne kan gaba wajen matattarar aljannu amma kuma ƙarfin gwiwar tasu shi ne Sheik to shi ma babu yadda yake, sun lura a ruɗe yake ruɗun ma iya ruɗewa, bayan shi suke ganin zai kawo musu ɗauki amma sho ma kamar dai yana neman ɗaukin ne.

Mai Gari kasancewar shi kaɗai ne a cikin yankin bargon da ya shiga, duk da a katifa ɗaya suke amma sai yake jin tsoro yana ƙara baibaye shi, ya so a ce bargo ɗaya suke da malam balarabe mai jar fata kuma babban malami wataƙila aljannun sa yi sassauci a lamarin. Samarin nan guda biyu sai numfashi suke ƙasa-ƙasa kwata- kwata a ruɗe suke.

Ya Sheik shi idan ya tuna da kunnen da aka jefo masa a banɗaki sai ya ji cikinsa ya murɗa alamar gudawa, yanzu haka yana ta fafutuka wajen danne wata guntuwar tusa da take son ta fito masa wacce yake da tabbacin matsawar ta fito kashi zai iya kuɓuce masa. Wannan dalilin ne ya sa yake ta mutsu-mutsun dannewa, don ya san matsawar ya saki tusar to su Mai Gari za su ji wari kuma hakan kamar zubar da kimarsa ne a matsayinsa na bababan malami, shi ba ma wannn ne matsalar ba yadda suka biyo shi suka cika masa ɗaki, ya san cewa yanzu kowa shi yake son ya kawowa ɗauki bayan shi kansa ta kansa yake. A daidai wannan lokacin kuma ɗaya daga cikin samarin nan ne ya ji ɗayan ya janye masa inda ya rufu don haka ɗan jijjiɓin yaƙi ya kaure a tsakanin su biyun, shi ɗayan so yake ya rufe har ƙafafunsa, shi kuma ɗayan an janye masa don kansa ma yanzu a tantagayyar waje yake, wannan ya sa yake ganin va zai yarda ya ɗauki dala ba gammo ba. Hakan ya sanya suke ta jaye-jaye da rigar Malam Liman wamda fitsari ya cika masa mara, duk fusgar rigarsa ɗaya da suke barazana ne ga mararsa da take cike da fitsari, hakan ya sa ya damƙe baki, a zuciyarsa yana faɗin

'Lahaula wala ƙuwwata, kar ku mini haka ƴan samari, ina zan kai wanann abin kunyar a ce limamin gari guda amma ya yi fitsari a wando, ku taimake ni kar ku kunyata ni' Ya faɗa a zuciyarsa yana wani damƙe idanu tare da haɗe ƙafafunsa waje guda yake fafutukar matse su.

Ɗayan ne ya fisge rigar da ƙarfi ya zungura kansa wanda kan nasa yake a saitin mazaunan Malam Liman, Malam liman ana zungurar mazaunansa ya ji guntun fitsari kaɗan ya kufce masa da sauri ya sake haɗe ƙafafun don ya lura in bai yi da gaske ba sai an saka shi ya saki fitsarin nan duka.

Hannu ya miƙa ya sakarwar kan wannan saurayin wanda yake kusa da mazaunansa, ya sakar masa ranƙwashi a zuciyarsa yana faɗin

'Shegun yara, kamar da ubanku muka haɗa kuɗi muka sayi rigar, sai ja kuke kamar kun samu guga a rijiya' Ya faɗa a zuciyarsa yana jin da a lafiya ƙalaw ake ko iyayensu ba za su yarda su shiga rigarsa ba saboda yadda yake da kima ana girmama shi, a matsayinsa na Limamin garin.
Chapter 7 · 0% Book details