Sashe 26
Malamin Bogi Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read
"Ai sai dai in bana garin nan na Mai Mangwaro"
Sule ya ce
"Daga na bata kuÉ—in ta in na yi noma ai kin zama mallakina ma" Wani farrrr da idanu Inna ta yi.
Mai Gari ya ce
" A yi wa annabi salati"
Jama'a suka ce S.A.W"
Yaraf Jummai ta yanke jiki ta faÉ—i sumammiya.
*MA'ARUF*
Da sauri Ma'aruf ya ɗago kansa yana kallonta, Rahma kuwa sai ƙwafa take a ranta tana cewa Allah ya ƙara maganin mai shishshigi da shiga abin da babu ruwansa.
Daddy jikinsa ne ya yi sanyi jin furucin Hajiya tabbas yana son Rahma amma ba zai kori Ma'aruf daga gidansa ba saboda ya san Mai Gari yayansa shi ne sanadiyyar dawowarsa garin abuja da zama sannan a taƙaice ma shi ne silar arziƙinsa, yanzu yana jin nauyinsa ya kora masa ɗa gida saboda wanann maganar sannan ba zai iya yi wa su Hajiya musu ba hakan ya sa ya ce
"To shikenan Ma'aruf ke ɗauki kayanka mu je in sauke ka a tasha sai ka je gida, idan ka je ka haɗani da Mai Gari in masa bayani" Cike da takaici da kuma da na sani Ma'aruf ya ɗago kai ya sauke a kan ɗan uwan mahaifin nasa, amma abin mamaki sai ya ga Daddy ya faki idanun su Hajiya ya ƙifta masa idanu, duk dabya kasa ganewa cewa gizo idanunsa suke masa ko kuwa dai ya ga Daddyn ya masa wata alama.
Daddy ya ce
"Amma yanzu tun da dare ya yi da safe sai ka tafi" Haka ya buɗe baki zai yi magana Daddy ya dakatar da shi, akwatin ya kinkima Hajiya tana murmushin nasara, na ganin sun jefar da ƙwallon mangwaro sun huta da ƙuda, Rahma har da cewa Allah raka taki gona.
Da daddare bayan kowa na gidan ya yi bacci, Hajiya da ta gama ƙwawar Alhaji ya kwana a ɗakinta ya ce shi ba ya jin daɗin katifar ɗakinta saboda bata da laushi ya fi so ya kwana a ɗakinsa, ta rasa mai ya sa yanzu ya fi son kwana a ɗakinsa, ita kuma kawai bata son gadon ɗakinsa saboda irin ƙaramin nan ne bashi da wasaci sosai, wannan dalilin ya sa sai ta yi kwanciyarta. Yau ma kamar kullum hakan ce ta faru, Alhaji da tun da ya shiga ɗakinsa ya rufe ƙofa ya hangi wayarsa da take kan bed side drower tana kawo haske wani murmushin gefen baki ya saki yana shafa haɓarsa, wajen wayar ya nufa kamar yadda ya yi zato kuwa hakan ce ta kasance sunata ya gani kamar yadda ya yi saving my zee bakin gadon ya koma ya zauna ya ɗaga wayar cikin muryarta mai ɗauki da sinadarin shagwaɓa ta ce
"Haba baby ka barni sai tsoron nake ji ina dakon jiran dawowarka" Ta faɗa tana sakin kukan kissa. Wata ajiyar zuciya ya sauke tana jin ta har cikin kunnenta cikin ƙasa da murya ya ce
"Haba amarya ke kin san sai dai in wani abu ne zai riƙe ni amma ina nan zuwa gare ki, kin san dai daga kasuwa ma a nan na yada zango, to yanzu ma ina so ta yi nisan zango a bacci in lallaɓo in taho" Daɗi ne ya rufe Zee ta ce
"Sai ka ƙaraso" Amsa mata ya yi yana lunshe ido tonowa da ya yi da cewa yanzu idan ya je tana nan sanye da kayan baccin nan nata masu taushi da kama jiki.
Sai da ya ɗauki kamar minti talatin ya fito ya nufi ɗakin Mummy yana zuwa ya tura ƙofar ɗakin, tun kafin ya shiga ɗakin kunnuwansa suka yi arba da munsharin da take sakin tamkar an shaƙewa raƙumi wuya, kasancewar tana da nauyin bacci har ya ɗan tsaya amma ko motsi bata yi ba ta yi shame -shame.
Ƙofar ya jawo mata a hankali, ya rufo, ɗakinsa ya koma ransa fari ƙal, yana zuwa ya ɗauki wayarsa da kuma mukullin ƙofar baya wacce yake bi ya yi ɓadda kama ya tafi gidan Zee.
Zee ƙawar Rahma ce amma ba ƙawa ta jiki sosai ba, sun yi aure da Daddy ba tare da sanin Hajiya ba kasancewar tsananin kishin Hajiya ya saka ta sanya shi ya mata alƙawarin ba zai mata kishiya ba, yanzu kuma da tafiya ta yi tafiya yana son ya yi auren amma babu hali. Don ba za ta bari ba, sun haɗu da Zee ne watarana ta zo wajen Rahma, bayan ta fita shi kuma yana ƙoƙarin shiga get ɗin gidan, hakan ya sa ya ɗauke ta a motarsa ya kaita har gida, daga nan ya karɓi lambar wayarta.
Komai a ɓoye ya yi hatta bikin Zee Rahma bata san an yi ba, saboda lokacin ta je hoto Kaduna gidan wata ƙawar Mummy.
Ya fito cikin dunu da yake gabaɗaya ƙwayayan gidan an kashe su, sannan shi ma ya kashe na ɗakinsa, yana lallaɓawa zai sauka daga matakalae kasancewar a sama suke, kamar daga sama ya ji an buɗe ƙofar ɗaki, da sauri ya ɗauke sawub takalminsa yana saurin ƙarasa sauka daga matakalar. haske ya hango an kunna fitilar harabar wajen, jin ƙaran tafiya ya yi saurin laɓewa, yana nan a laɓe sai ya ga Rahma ta sakko tana sanye sa doguwar rigar bacci hannunta riƙe da waya ta kunna fitilar.
Gabansa ne ya faÉ—i saboda ya san matsawar ta ganshi sai ta gane shirin fita ne a jikinsa, don bai yi kama da mai bacci ba, kuma ya san idan ta ganshi tamkar a kunnen Hajiya sai ta faÉ—a mata.
Fitilar falon ta kunna ta nufi frige ta buɗe ta ɗakko ruwan roba ta rufe, fitilar ta kashe ta haura sama, sai da ya ga duhu ya rasa saman alamar ta kashe fitilar kuma ya ji ƙaran buɗe ƙofa da rufewa, alamun ta koma ɗakin ta.
Ƙofar falon ya buɗe ya fita ta ƙofar bayan gidan ya kulle ta, machine ya samu ya tsare ya hau ya nufi gidan amaryarsa. Yana zuwa ya ƙwanƙwasa mai gadi ya buɗe masa ya shiga, yana zuwa part ɗinta ya ta buɗe ƙofar ya shiga ta rufe, yana kafe ta da idanunsa sai wani bubbuga ƙafa take wai ya ƙi zuwa tana ta jiransa, a rayuwarsa shagwaɓa da ɓacin da take masa shi yake rikita masa lissafi.
Kimanin wata biyu da yin aure suna cin amarcin su suna cin karensu babu babbaka, yana fitowa daga gidan Hajiya in ya ce zai tafi kasuwa gidan amarya yake zuwa, sai a shelaƙe zai je kasuwar, sai dai yaransa ne a kasuwar, sannan da wuri yake tashi ya koma gidan amarya, a can sai dare zai dawo gida kullum da uzurin da yake ba Hajiya, ko Ma'aruf bai sani ba, abu ɗaya ya sani shi ne Daddyn yana sanya shi ya ajiye shi a gidan amma bai san mai Daddy yake a gidan ba.
Sannan da dare ma sai ya lallaɓa ya je su kwashi soyayya ita Hajoya tana can kwance basho bata san wainar da ake toyawa ba.. Don haka amarya bata san bakin uwar gida ba saboda kullum ita ce take da miji safe rana da dare ma su kwana, sai ya yi asubanci ya koma, don a mota mai gadi yake mayar dashi da yake a gidan akwai motar Zee ɗin.
Ido biyu suka kwana suna bankar amarci tamkar ba za su rabu ba, Daddy ji yake yanzu kaf duniya babu abin da Zee za ta buƙata ya ƙi yi mata saboda yana samun yadda yake so daga wajenta. Tare suka shiga suka yi wankan su, ganin ƙarfe huɗu da wani abu ya ce zai tafi gudun samun matsala, dakyar ya samu Zee ta bar shi ya fito, mai gadi ya ɗauke shi kamar kullum a motar ya nufi gidan da shi a ƙofar bayan ya ajiye shi, ya buɗe ya fita ya buɗe ƙofar gidan ya shiga ua mayar ya kulle.
A can cikin gidan Daddy kuwa Mummy ce ta tashi zaune, tana murtsuka idanu, tare da sakin doguwar hamma ta rufe bakinta, ta sakko daga gadon ta nufi bayin cikin ɗakin nata domin yin fitsarin da ya tashe ta, da ta fito har za ta koma kan gadon sai kawai ta fasa, ji ta yi kawai tana son jin ɗumin mai gidan nata, ita da ta ma manta rabonta da shi saboda ita a nata hankalin yanzu sai ta shafe tsawon lokaci basu kasance tare ba, tana ganin ai sun girma, bata san cewa shi namiji ba ya girma da buƙatar sunnar aure, haka nan namiji ba ya tsufa da haihuwa. Wayarta ta ɗauka ta kunna fitilar bayan ta kashe fotilar ɗakin nata da ta kunna, duk da ta san ana kiran sallag zai ce masallaci zai tafi amma dai ta san kafin lokacin sun kashe arnan soyayya ya haɗa alwala da wanka, tun da ta ga ƙarfe huɗu ta wuce.
Ɗakin nasa ta dufafa gadan-gadan ta kama hannun ƙofar ta murɗa tare da tura ƙofar ta buɗe...
*SHEIK*
A kiÉ—ime ya É—ago yana kallon Mai Gari ya ce
"Aure kuma Mai Gari ni Sheikul Yemen, balaraben malami daga ƙasar larabawa?" Ya tambaya lokacin yana nuna kansa da yatsa.
Mai Gari ya ce
"Haba Ya Sheik kar ka manta ka sauka a garin nan don ka ceto garinmu daga halakar da shi da aljannu suke yi kuma yanzu wata gagarumar matsala ta taso a ce kana tambaya mai kamar tuhuma?"
Wani yawu Sheik ya haÉ—iye yana son nuna musu ba haka bane, cike da wayincewa ya ce
"Haba kai kuwa ina ni ina wannan babban al'amari ina so ne in san shin wa kuka samu ya mata ruƙiyya har ya gano wanann baban al'amari na aurena a tare da ita?"
Mai Gari da bai zaci waÉ—annn tambayoyin ba ya ce
"Sai an mata ruƙiyya za a gane haka, ita da kullum bata cikin hayyacinta ita fa koyaushe aljannunata suna tare da ita, ga shegen leƙen asiri da tone-tone, ai gwara ma da ta zaɓe ka to ai kai ne maganin iskancin nasu idan suka je maka leƙen asiri su ganowa kansu maganin su"
A zuciya Sheik ya ce