Sashe 28
Malamin Bogi Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read
"Aure ai ba abin wasa ba ne tun da har aka ɗauka babu batun saki, a bar Tasleey ta ƙarasa rayuwarta a gidana" Sunan Tasleey da Sule ya kira a maimakon Tasallah shi ne abin da ya ƙara fusata Jummai, sannan shi ne abin da ya faranta ran Inna ta ji ta dawo tamkar ƙaramar yarinya.
Cikin harzuƙa Jummai ta ce
"Mu zuba mu gani sai na zame muku ciwon ido a gidan nan" Tana faÉ—ar hakan ta juya fuuuu ta bar fadar kamar za ta hantsila.
Mai Gari ya ce ya sallami kowa, ya kalli Inn yana dariyar wasa ya ce.
"Ka ga amarya ran gida, amarya bakya laifi Tasallah amaryar Sule" Wani daɗi Inna ta ji, ta kunce ƙullin hannun zaninta da ta yi ta ɗauko kuɗin kayan miyarta haka ta zaro ɗari biyar ta ce
"Mai Gari ga jaka biyu da rabi (500) Ka ci goro" Sosai ya ji daÉ—i yana washe baki ya ce
"Yaushe za ki tare?" Ta ce
"Yo tun da aure ya É—auru ni kuwa tariyar mai zan jira ai a yau ba sai gobe ba"
Sule ya ce
"Dama akwai É—akina kawai sai ta zauna a ciki".
Lami tsaye ta miƙe ta ce
"Mai Gari ni ina nawa zancen ya kwana tun da ita Jummai an samu mafita?" Kallon sheƙeƙe ya mata ya ce
"Ana batun giwa wa yake maganar ɗan tsako, amma dai ai kin san wanda ya zai je sama ya taka leda ya ci ƙarfin tafiya ko?" ,Takaici ya sa bata sake cewa komai ba, juyawa ta yi sai Inna ta ce
"Yanzu Lami maimakon ki tsaya ki ɗauka mini samirar nan da ledar kayana, ki raka ni gidan in kintsa, amma kya tafi ki barni ai an yi ba a yi ba rufin ƙofa da ɓarawo"
Cike da jin haushi Lami ta ce
"Haba Inna tun yanzu ai a tunanina duk gaggawar asara ta jirayi samu" A faÉ—a ce Inna ta ce
"Ke kika sani ƴar baƙinciki wato kina jin babu daɗi na samu jirgina ya ɗaga na yi aure bayan a gari ga yan mata nan galla-galla da zawarawa masu jini a jika amma ni na tashi na barsu, to ai dama abin rabo ne auren mace da ciki"
Takaicin ta ta danne ta ce
"Haba Inna ai ba batun baƙin ciki ba ne, ai ciwon ƴa mace na ƴa mace ne, ni ma ba zan so ki ƙarasa rayuwarki babu aure ba, gwara ki yi ko a sama mana ƴan ƙanne"
Kallon kallo aka shiga yi a fadar Lami ta sunkuya ba don ta so ba ta É—auki samira da ledar Inna ta yi gaba, ita kuma Inna ta tashi tana ta jin kunyar jama'ar wajen Mai Gari ya ce
"Tasallah babu batun kunya ba a aure kuma ai jahadi kika yi" Ya faÉ—a yana saka É—ari biyar É—in da ta bashi a aljihu.
Inna ta ce
"Haka ne ai da rashin tayi ake barin araha, kuma da rashin kira karen bebe ya ɓata"
Gabaɗaya ƴan fadar aka amsa mata ana mata jinjina, har ta yi gaba Sule ya tashi yana washe baki ya ɗan bi ta suka keɓe ya ce
"Amarya bakya laifi, yaushe za ki zo"
"Ta ce ahaf dag an yi sallar isha'i mana za a rako ni, kar in je in zauna Jummai ta zo ta min tijara a kan kuÉ—in saniyar da na fansa da aurenka"
Haka ya tafi yana wani waiwayen Inna, wasu daga fadar suna masa kallon sha-sha-sha.
Tafe suke a hanya Lami tana barin Inna a baya har Inna ta gaji ta ce
"Lami sai wani cin magani kike, wai ke baki san mata tsoffi ƴan da basa tsufa ba, mu fa nan mu ake yi wa laƙabi da mace daki bari" Cike ta haushi Lami ta ce
"Daki bari kamar wata atamfa?" Inn ta ce
"Yo ai atamfa wataran tana yagewa ko ta mutu a jefar da ita, amma mutane da ƙarko garemu kuma shi namiji ba ya ganin tsufan mace waɗannan matan nasa sai ki ga na je na fiye masa su sau miliyan, duk wannan hayagagar da Jummai take wiyarta in tare ai duk wanda ya daka rawar wani zai rasa turmin daka tasa rawar, dama alƙawarin Malam na ɗauka na ce ba zan yi aure ba amma yanzu na fasa aurena zan zauna yo malam ɗin ma da shi ne ba lallai ya bari a mini arba'in ɗin mutuwa ba zai gallo wani auren, ita ma Jumman kallon raini take min bata san cewa idan makaho ya ce a yi wasan jifa to tabbas ya take dutse ne, amma dai zan nuna mata gani ya kori ji"
Banza Lami ta mata, har ta fara tunanin ma dama duk rawar kan Ibra da rashin jin nasa wajen Inna ya yi gado.
Suna dab da ƙofar gidan Inna Lami ta ce
"To Inna ga kayan ni zan wuce gida, Inna amarya ta ango" Ta faÉ—a cike da gatse.
Inna ta kalle ta ta ce
"Kin ga Lami kar ki mini fallasa auren bashi, idan ba za ki kai mini gida ba, ba sai kina mini terere a titi ba, amma dai ki sani duk wanda ya ƙona rumbunsa ya san inda toka take tsada" Tana karɓar kayanta ta shige gida, Lami kuwa baki ta taɓe ta yi tafiyarta.
Inna gidan ta buɗe ta shiga, tana murna ta shiga haɗa ƴan komatsanta da ta san za ta buƙata .
Kawayenta guda huÉ—u ta je ta gayyato suna ta mata barka sa fatan alhari don babu wacce ta ce bata kyauta ba. Haka mata biyu suka yi gaba da yara aka je da kayan Inna Æ´an samiru da kayan sawa, sai randunanta da aka É—auka a baro da sauran kaya, aka je dakyar aka shiga da kayan kasancewar Jummai tana tijara, sai da Sule ya tada jijiyoyin wuya.
Bayan an kintsa ɗaki da gadon Inna na ƙarfe, sannan aka rako Inna a ƙafa ana ta rangaɗa guɗa, haka aka shigo da ita aka zaunar da ita a bakin gado.Bayan kowa ya watse , Inna ana zaune ana ta murmusawa ango ya shigo da ledar tsire da pure water, Jummai tana zaune a ɗaki ta kasa ta tsare tana jiran zuwan ango, ita kishiyar tata ma cewa ta yi babu ruwanta ita ma Jummai abin da ya sa ta damu saboda ga babu kuɗin saniya ga kishiya.
Bayan Sule ya shige ɗakin amarya dama ko ta kan su Jummai bai bi ba, ya rufe ƙofa yana washe baki tare da mata kirarin amarya mai daɗin tuwo.
Ƙasa ta sakko suna zaune a tsakiyar ɗakin, ya saka hannu ya buɗe fuskar da ta rufe da mayafi, Inna tana ta kare fuska tana zabga murmushi, Sule saboda ƙarfin hali har da shan magani don abokansa sin zuga shi a kan cewa tsohuwa ma ai mace ce, kuma ita ma tana da tata ni'imar hakan ya sa ya shawo ya yi tatul, don gabaɗaya mararsa hargitsa masa take
Inna kuwa babu abin da ta sha sai maganin zafi wato maganin rana, sai wani abu da wata matashiyar mace maƙociyarta ta bata mai suna ƙwaƙwalwar raƙumi ta ce ta saka a gabanta, gabaɗaya sai ta fi sauran matan ɗanɗano.
Ya fito da pure watern da takardar tsiren ƙamshin ya cika musu hanci Inna tana ganin ita gaba ta kai ta gobarar titi don sai ta ji gwara ma da Ibra ya gudu da saniya tun da gashi ta tsinci dami a kale, ga abinci za take samu ga kuma kayan daɗin amarci, tun da ta ga har da ruwan leda(Pure water) Da har tana jin haushin an katse mata shan mangwaro ashe dai rabo ne yake kiranta.
Sule ne ya ɗakko tsoka ɗaya ya nufi bakin Inna, tana ɗan kauda kai ta karɓa tana jin kunya sai ƙarfin gwiwa yake bata a kan cewa babu kunya tsakanin miji da mata. Tana taunawa ya tulla ruwan guda ɗaya, ya miƙa mata ta kurɓa bayan ta cinye naman, ita ma hannu ta kai ta ɗauki ɗaya tana kare fuska ta miƙa masa, Sule kansa ya ji ya wani ƙara girma don shi har ya manta da a bashi abinci a baki ko dai ya ci ko ya zauna da yunwa duk ɗaya a wajen matan nasa.
Baki ya wangale sai dai kash, naman bai kai ga sauka a kan harshen sa ba sai aka banko ƙofar ɗakin, a tare suka ɗago suna kallon wanda ya banko ƙofar a tare suka zaro ido ganin Jummai sanye da wani tafkeken gajeran wando da wata riga mai ƙaramin hannu, sai wata adda sabuwa dal a hannunta, ƙofar ta mayar ta rufe har da saka sakata, su duka sun tsorata sun fara tunanin ko dai kashe su za ta yi.
Inna bata san lokacin da ta saki naman hannun ta ba, shi kuma ango ya ajiye ruwan hannunsa a take ruwan ya fara malala a tsakar É—akin.
Jummai tana zare ido ta kalli Sule cike da kakkausar murya ta ce
"Sule saniyar da ake shari'a taka ce?" Cike da tsoro yana kallon yadda sabuwar addar take ƙyalli ya shiga girgiza kai alamar a'a
Ta ce
"To wannan ba amaryarka ba ce tawa ce, don haka dole ta bini É—akina muke kwana, in ha haka ba sai dare ya tsala kun sakankanci da cin amarci, zan shigo in datse maka mafitsara" Idanu ya zaro yana saka hannu biyu ya dafe mararsa, don ya san kaÉ—an daga aikin Jummai.
Ta É—ora da faÉ—in
"Ita kuma na sare mata mazaunai" Inna da sauri ta kai hannu biyu ta dafe mazaunan ta tana zare ido gabanta yana faÉ—uwa domin kuwa ta ga samu ta ga rashi.
Tana nuna su da yatsa ta ce
"Shawara ta ragewa mai shiga rijiya"
*SHEIK*
Yana zaro idanu amma bakinsa ya kasa furta ko uffan sakamakon yadda zuciyarsa take zilli tamkar za ta huda ƙirjinsa ta fito.
Tunani yake wace irin baƙar ƙaddara ce a shegen neman kuɗinsa a ce za a ɗaura masa aure da mace mai aljannu, mai aljannun ma wacce aljannu suka raba ta da ido ɗaya, sannan yana ji aka ce an cirewa mai maganin mafitsara amma kuma sai a ɗora masa jakar tsaba gashi nan yanzu kaji suna bin sa.