← Book details Malamin Bogi Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 30 OF 35

Sashe 30

Malamin Bogi Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

*Kamfanimu na MEERAH B HERBS muna da kayan mata masu kyau da inganci, akwai maganin sanyi maganin gyaran breast, maganin hips, na rage ƙiba, na ƙara ƙiba, maganin rage tunbi, da kuma maganun MAN POWER ga matan da mazajen su ba sa uin kataɓus a wajen aikata sunna da sauransu.*

*Mai so ya tuntuɓeni a layina 09025576222*
[7/16, 6:52 PM] Mom mashkur & Afrah: 👳🏻‍♂️ *MALAMIN BOGI*👳🏻‍♂️

NA

MAMAN AFRAH

First Class Writer's Asso.📝

Daga marubuciyar:

Ƙazamin miji
Bonono Rufin ƙofa...
Ruɓaɓɓiyar igiya
Ƴar zaman wanka
Ƙara'in inna delu
Beelal
Ƴan adaidaita sahu
Ungozoma
Jalli joga
Da sauran su.
*09025576222*

BOOK1️⃣
PAGE 14

IMZEEDVENTURE
https://chat.whatsapp.com/GCVmfFguMEf49AFrOjSiMt
Duniyar kayan kitchen da na yara masu kyau da araha!
Kina neman kayan kitchen masu kyau, luxury da adashe, ko kayan yara masu kyau da tsada ko gonjo mai kama da sabo?
To shiga group É—in IMZEEDVENTURE!
Za ki sha mamaki! 🤩Muna da:
✅ Adashe na kayan kitchen
✅ Kayan yara sabbi da gonjo
✅ Kayan gyaran gida da na mata masu kyau
📞 Tuntuɓi mu: +234 707 753 2253
📩 DM: WhatsApp
📸 IG/Tiktok: @imzeed_venture

*MUMMY*

Shigewa ɗakin Daddy ta yi, kasancewar fitilar a kashe sai kawai ta durfafi kan gadon, cike da shauƙin soyayya ta ɗare gadon, sai dai wani abu da ya ratsa ƙwaƙwalwar ta shi ne, jin gadon kamar ma wayam yake babu kowa a ka, ma'ana kamar dai ita kaɗai ce da ta hau gadon yanzu a ka, mamaki da al'ajabi suka haɗe lokaci guda a kwanyarta tambayoyi da tunani barkatai suna safa da marwa a ƙwaƙwakwar tata.

Da yake tun tana dab da zuwa ƙofar ɗakin ta kashe fitilar wayarta, saboda ta fi so sai ta hau gadon zai san da zuwanta, hannu ta kai ta gama zagaye kan gadon amma babu alamar mutum, fitilar wayar ta kunna sai yanzu idanunta suka ƙara tabbatar mata cewa ba ya kan gadon a zuciyarta ta ce

'To ko dai yana banÉ—aki?'

Wata zuciyar ta ce

'Kuma banÉ—akin ne ba zai kunna fitilar É—akin ba, sannan kuma ita ma ta banÉ—aki ba zai kunna ta ba?'

Ƙafafunta ta zaro daga kan gadon, banɗakin ta nufa, bata kunna fitilar banɗakin ba sai ta yi amfani da fitilar wayar, amma sai ta ga babu shi babu alamar sa.

Haka ta rufo ƙofar banɗakin ta dawo ta zauna, nazari take amma kwanyarta ta ƙi bata haɗin kan gano inda mai gidan nata yake, fitilar wayar ta kashe, tana jira ta ga ta inda zai fito.

Daddy kuwa ransa fari tas ya fara haurowa sama, fitilar wayarsa a kashe saboda kar a samu akasin lissafi, saɗaf-saɗaf ya zo ya wuce ƙofar ɗakin Hajiya, ganin fitilar a kashe a zuciyarsa ya ce

'Ka ga sarakan bacci ana can ana fama, ni ai da kike da nauyin baccin nan gaba ta kai ni gobarar titi' Ya faɗa a zuciyarsa yana kama hannun ƙofar ɗakin nasa ya buɗe ƙofar, Mummy da take zaune har sai da ta ji gabanta ya daɗi saboda bata tsammace shi ba, sannan bata kawo cewa zai shigo a duhu bai kunna fitila ko da ta wayarsa ba ce.

Ɗif ta yi tamkar bata cikin ɗakin, Daddy kuwa yana shigowa ya yi wata miƙa yana salati, tare da sakin doguwar hammar biyan bashin baccin da bai yi ba a daren na jiya.

Kan gadon ya nufa kasancewar ba ta wajen da Mummy take zaune ba ne, har ya hau gadon bai san tana zaune ba, sai da ya ja filo ya tada kansa yana sakin wata hammar a karo na biyu, hannu ta ɗan miƙa ta sauke a jikinsa, gabansa ne ya buga da mugun ƙarfi kasancewar bai ma taɓa kawo cewar Mummy ba ce, gabaɗaya sai ya razana, fitilar wayarta ta kunna a takw haske ya gauraye ɗakin, sai a lokacin idanunsa suka yi tozali da ita, duk da ya tsorata da kama shi ɗin da ta yi, kuma ya ga fuskarta ma babu yabo babu fallasa amma kuma sai ya maje ya ɗan saita kansa.

Mummy ita dai haushin inda ya fita da tunanin amsar da zai bata take, amma kuma bata taɓa kawo cewar wai aure ya yi kai bata ma yi tunanin har zai iya fita daga gidan ba.

Cike da tuhuma ta ce

"Alhaji daga ina haka?" Ta tambaya tana kafe shi da idanu don gani ta harbo jirginsa musamman da ta ji wani ƙamshin turare da ba nashi ba, yanayin ƙamshin mai sanyin ya sa ta ji tamkar ma turaren na mata ne, sai dai ba za ta yanke hukunci ba, kai zuciyarta ma ba za ta bari ta zargi Alhajin ta ba, saboda ta bashi yarda, ba ma wannan ne abin yin ba, sai alƙawarin da ta sanya ya ɗauka na dole, a kan cewa ba zai mata kishiya ba.

Cike da iya sarrafa harshe ya ce

"Ni ke ce ma kika bani tsoro kawai sai ki zo cikin duhu ki zauna? " Sai ta ji gabaɗaya ma ranta ya ɓaci kasancewar tana tambayarsa yana tambayar ta.

Rai ta haÉ—e ta ce

"Kai É—in ma ai a cikin duhun ka fita, da ka dawo ma a duhun ka dawo"

Gabansa ne ya bada rass jin furucin ta, tunaninsa ko dai shuka ya yi a idon makwarwa wato Mummyn ya ga tafiyarsa ko kuma dai Rahma dama ta gan shi ƙyale shi ta yi ita ce ta faɗa mata, wani gumi ne ya karyo masa, ya san in her Rahma ta ganshi amma ta nuna bata ganshi ba sai da ya fita ta bi sawunsa to tabbas babu abin da za ta ɓoye wa Hajiya. Jarumta ya ara ya ce

"Haba Hajiyata ai ni na fita a duhu ne saboda kar in kunna haske ki hango daga É—akin ki, ki ce na bar miki idanuna basu runtsa ba wato ban yi bacci ba, kuma da na dawo ma wannan dalikin ne ya sa ban kunna hasken ba" Ya faÉ—a zuciyarsa cike da zulumin Allah tarkonsa ya kama tsuntsu.

Wani daÉ—i ne ya baibaye Hajiya don yanzu kam na gane komai ma saboda soyayyarta ya yi, wani farrrr ta yi da idanunta ta ce

"To yanzu dai ina ka je?"

Hannu ya kai ya shafo gashin kanta da babu hula ya ce

"Kawai fa ina kwance na falka nake jin motsi a ƙasa shi ne na sauka na duba, ashe ma dai kunena ne don ban ga komai ba"

Murmushi ta yi tana cewa

"Kai kam baka son abin da zai taɓa iyalinka"

Murmushin jin daɗin samun nasara a kanta ya yi, don ya san tabbas matuƙar ta gano shi to akwai gagarumar matsala ko da kuwa ganin budurwarsa ne bare kuma a ce matar aure, auren ma kuma a ɓoye ba tare da sanin ta ba duk da cewa ya san ita ce ta ja koma mene ne, a ce mace ta ce ita ba za a mata kishiya ba, wannan son zuciya ne da dannewa namijin haƙƙinsa tun da Allah ya halatta masa.

Washe gari tun da sanyin safiya Hajiya take famar a je a sallami Ma'aruf da kuɗin kota ya kama hanyar ƙauye, Daddy kuwa da ya gama shirin fita ya ɗauki Ma'aruf ɗin suka fita tare, bai zame da shi ko ina ba sai gidan Zee a nan ne yake gabatar da Zee a wajen Ma'aruf tun da ita dama ta san shi a bakin Daddy.

Daddy ya ce ya zauna a ɗakin baƙi kafin ya gama sama masa admission a wata ƙasar inda yake ganin zai dace da cigaba da karatun sa. Ma'aruf ya yi mamakin jin cewa Daddy yana da wata matar bayan ya san babu wanda ya sani kuma ya san akwai matsala ko dai ya ce tashin hankali duk ranar da ƙwan ya fashe za a yi ɗan jijjiɓin yaƙi.

Ya ji daɗin cewa Daddy za fitar da shi ƙasar waje karatu, wannan ya nuna cewa Daddy har yanzu yana riƙe da zumunci kuma, zugar Hajiya da Rahma bata yi tasiri ba kuma dama bashushe ya ce hassada ga mai rabo taki ce.

Zee ta karɓe shi hannu biyu shi kuma yana girmama ta duk da cewa ya girme ta amma kuma, tun da dai matar Daddy ce babu wani batun girmansa tun da idan ana dara fitar da uwa ake.

Daddy ya kammala masa komai na tafiya, inda zai tafi China nan da kwana uku, murna kamar zai yi mai, ashe da rabon ya shiga jirgi. Ana jibi zai tafi ya je Ƙundu ya musu sallama, duk da a tsaitsaye ya yi saboda bai gama shiri ba, har ya je ya dawo basu haɗu da Sheik ba.

Ranar laraba misalin ƙarfe biyu jirgin su ya tashi, Zee da Daddy ne suka raka shi airport yana ta farinciki saboda shi yana son karatu.
*(A page 15 buk 1 zai ƙare mai buƙatar book 2 zai biya ɗari biyar*

Haka rayuwa ta cigana da tafiya, Rahma tana fantamawar ta, sai samari take yi kala-kala ƴaƴan masu faɗa a ji, don ita ta ƙi jinin masu ƙaramin ƙarfi ƴaƴan malam shehu. A ɓangaren Daddy kuwa har yanzu yana ta cin karensa babu babbakaa, domin babu ranar da za ta zo ta faɗa bai kwana a gidan amarya ba, ita kuma Mummy da yake hotiho ce bata taɓa lura ba, saboda idan ta je ta hangame baki sai bacci bata taɓa sanin abin yake wakana ba.

Sannan basu da masaniya a kan tafiyar Ma'aruf karatu su duk tunanin su yana can ƙauye, don Mummy takan ce Ma'aruf ana can ƙauye an kama sana'ar sayar da rake.
Chapter 30 · 0% Book details