← Book details Malamin Bogi Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 12 OF 35

Sashe 12

Malamin Bogi Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

"Ku taimaka mini, ya zan yi da gemu shi kaɗai, damuwata gashin kan nan nawa da babu yadda yake salsal su kuwa sun san Sheik da gashi laɓaɓa na larabawa." Yana rufe bakinsa sai ga sauran ma sun fito sai kuma suka faɗo, duk da yana tsoro haka ya lallaɓa ya je ya ɗauka yana godewa Allah a ransa yana jin daɗin cewa ashe dai da sauran shan ruwansa a garin Ƙundu tun da gashi dai asirinsa bai tonu ba lallai akwai damfara.

Shirinsa ya yi tsaf ya ɗauko wani baƙin takalmi sabo a jakarsa ya saka, ya ɗakko turaruka ya shafa ya saka hular gashin ya manna gemun ya saita sajen da yake wani abu ne a jiki da ake ɗayewa mai danƙo daga ya ɗaga wajen sai ya manne kamar a fuskarsa a ka halicce su. Ɗakinsa ya kulle ya fito yana riƙe da wata roba mai ɗauke da ruwa da wani garin magani da aka jiƙa a ciki ya fito daga gidan gabansa yana faɗuwa, yana tunanin yadda za a ƙare da wannan lamari, shi ya sa ko wayarsa bai ɗauko ba gudun masu aljannu su warce ko ma a fasa masa ita.

Tun da ya fito yake hangar mutane jefi -jefi suna yin wata hanya sannan kuma sai wani girmama shi ake ana bashi hanya, wanann ya ƙara masa jin kansa ya ƙara girma, duk da yana cikin yanayin tsoro haɗe da fargaba.

Sheik haka ya doshi cikin garin ya yi inda mutane suke yi da alama nan ne wajen da su Liman É—in suke.Duk da idanunsa sun kumbura saboda fargaba da rashin baccin da bai samu jiya ba, kai har da kukan da ya yi ma.

Tun kan ya ƙaraso yake jin ana ta yin salati, yana kusa ƙarasowa ya ji ana faɗin

"Shikenan ma ga Sheik nan, ga ƙare kukan ka nan, balaraben malami yanzu komai zai zo ƙarshe.

Mutanen gari sun taru suna jiran ya fitar da maganin da zai kori aljannu kuma ya kuɓutar da su Liman. Amma Sheik yana cikin firgici har yanzu saboda abin da ya faru da dare. Yana ganin taron mutane sai ya fara rawar baki da hannun yana murza carbi, yana faɗar kalmomin larabci marasa ma'ana, don shi kansa bai san abin da yake faɗa ba yayin da yake karanta addu'a sai wani ƙaramin yaro ya faɗi a gabansa ya fara rawa ɗari tamkar yana shi ma mai farfaɗiyar ne, mutane suka shiga faɗin suna cewa

"Aljannu yanzu za ku gane shayi ruwa ne" Shi kuwa Sheik ganin yaro ya zube a ƙasa idanunsa sun kakkafe sai ya sha jinin jikinsa gabansa yana tsanata faɗuwa, ya yi shiru don bai san me ya faru ba, amma ya ci gaba da murza carbi yana ambaton maganganu. Jama'a suka fara mamaki da tsoron Sheik suna ganin tsabar maluntarsa ce ta sa yaron ya zube a ƙasa.

Bai bi ta kan yaron ba ya É—aga kansa sama, mutane uku ne a kan bishiyar kukar da mutane gari suke kira da kukar bulukiya saboda tarin aljannun da suke kanta

Hannu ya saka ya kama yaron nan da ya faɗi ya ɗaga shi, ƙirjinsa ya dukan uku-uku ya shiga karanta fatiha da ƙarfin halinsa yana tofawa yaron a fuska, wani gurnani yaron yake, Sheik kuwa ji yake kamar ya sheƙa da gudu amma babu hali. Ɗan ranƙwafowa ya yi yana cigaba da tofa masa karatun idanun yaron a kakkafe ya miƙa hannu bai masa masauki a ko ina ba sai a gemun Sheik.

Sheik a zuciyarsa ya ce

'Shikenan asirina ya tono zai fisge min gemun a bainan nasi, kowa ya gane bogi ne' A fili kuma sai ya fara faÉ—in

"Subhanallahi, ku kuke ganinmu ba mu muke ganinku ba, hasbunallahu wa ni'imal wakil" Duk abin nan da ake yaron ya ƙi sakawa, shi kuma Sheik hannunsa ɗaya yana riƙe da carbin da robar maganin nan ɗayan yana riƙe da yaron, ji yake kamar ya yi kuka, bai yi wani yunƙuri ba kawai sai yaron ya naɗe jikin malam yana cewa

"Ka kaini saudiyya" Sheik a zuciya ya ce

"Ni kaina ko filin jirgi ban taɓa zuwa ba' A zahiri ya ce

"Kai mutum huɗu su zo nan" Ya faɗa yana ƙara miƙa haɓarsa jikin yaron don ba ya so ya ja yaron ya ciro gashin gemun. Samari da mata da magidanta da suke wajen sai aka fara darewa jin malam yana kiran mutum huɗu

Malam ganin yaron yana miƙa hannu wajen wuyansa gudun kar ya shaƙe shi ya kashe shi a banza, inda Sheik yake riƙe da hannunsa ya nutsawa yaron farce ya shiga tsunkonsa da ƙarfu ba tare da kowa ya lura ba, mutane duk sun koma gefe.

Sai aka ji yaro ya fashe sa wani kuka, lokacin ne mahaifiyarsa da ta uso wajen tana kuka ta ƙaraso, kukan da yaron ya fashe da shi sai Sheik ya shiga faɗin

"Allahu akbar! Ya dawo hayyacinsa sun fita" Ya faɗa lokacin har jikin yaron ya saki kamar mai jin bacci yana lunshe idanu, babar yaron ce ta karɓe shi da hannu biyu, tana miƙawa Sheik 3k ƴan dubu-dubu tana cewa

"Allah saka da alkairi, Malam ga abin sadaka" Ko fulaki bai yi ba ya karɓa yana cewa.

"Babu komai ai yi wa kai ne don ma an ce babu kyau mayar da hannun kyauta baya"

Mutane ganin Sheik ya warkar da yaro aljannu sun fita daga jikinsa sai girman Sheik ya ƙaru a idanun su, suka shiga yin kabbara. Kuɗin nan ya saka a aljihu yana faɗi a zuciyarsa cewa.

'Allah kawo dubbanku, da a ce za a ke samun abin sadaka mai yawa haka ai da wuri zan cika buhu da kuɗi' Gabansa yana faɗuwa ya matso daga gaban kukar da su Liman suke ka,reshen kukar ne manya guda biyu a can saman amma ba tsililiko ba, ɗaga reshen Liman ne a maƙale kamar ɓeran da aka tsamo daga ruwa, ɗayan kuma Mai Gari, sai wani lanƙwashashshen reshe wannan matar mai farfaɗiya tana zaune a kan, su kuma suna maƙale da hannuwan su a kan reshen. Sheik ya yi shiru jin wajen babu abin da yake tashi sai kabbara, matan gari an taru wasu ma sai yanzu suke ƙarasowa wajen, a baya idan haka ta faru sai dai kowa ya yi ta kansa, a ringa shiga gida ana kullewa, amma yau ganin balaraben malami kowa sai tsoro ya ragu daga zuciyarsa.

Sheik ya fara tunanin Malam Manniru, wanda yake zaune a wani ƙauye a daji a can wajensa yake bashi magungunan da ya zo don yon bogin da su, har ruƙiyar ma ya koya masa, sai dai ya san yin magani dace ne ga shi maƙudan kuɗi malamim yake karɓa.

Baki ya buɗe ya shiga jan fatila, nasi, falaƙi, yana ta maimaitawa, ya buɗe wannan ruwan ya tsiyaya a marfin ya watsa wajen bishiyar kukar, wata irin kururuwa da su Liman suka ɗauka sai da Sheik ya ja baya kamar zai fita da gudu, sai kuma ya tuna ashe shi ne jagaba a garin. Ya daɗe yana ta karatun nan sai uban gumi yake sharɓawa, ruwan maganin na kuwa sau uku ya watsa, cikin taimakon Allah sai Liman da Mai Gari suka fara atishawa, kawai sai ga su an sakko da su ƙasa, mai fardaɗiyar ce aka sakko ta kamar wanda aka jefo ta, ta zo da rubda ciki, gabaɗaya wajen ya kaure da faɗin

"Allahu akbar! Allahu akbar".Wani daÉ—i ya rufe Sheik yana jin kawai ya warke, shi dai da talauci sai ko ya ga ana yi amma kam sun yi hannun riga da shi da talauci, tun da ga shi har ta ci nasarar warkar da yaro da kuma su Mai Gari, duk da ya san cewa da alama aljanin jikin yaron nan wahala ce ta tsinkon da ya masa ta sanya ya fita.

Mai Gari da Malam Liman sai washe baki suke, su kuma jama'a maza da mata sun dunƙule hannu suna jinjinawa Sheik suna faɗin Allahu akbar!.

Sun san ba ƙaramin aiki ne a sakko da mutane daga saman kukar bulukiya ba, matar nan wasu mata biyu aka sa suka kinkime ta aka ce a kaita gidan ta.

Mai Gari da Liman faÉ—i suke

"Jajirtaccen balaraben malami, garin Ƙundu ya yi babban kamu, sai inda ƙarfinmu ya ƙare dole gari ya kyautatawa Malam kai jama'a ku ce Allahu akbar!" Gabaɗaya wuri ya kaure da kabbara a tare. Sheik bakinsa ya ƙi rufuwa, sai jin kansa yake yana ƙara girma, har ya fara hango yadda zai yi kuɗi a saya kadarori. Yana shafo gemunsa ya ce

"Kar ku damu, mu dama taimako ne muke yi, indai aljannu ne ko ido biyu za mu fafata da su bare kuma a jikin É—an adam, ai na gani duk aljannu ne suka baibaye kukar amma yanzu sun tarwatse" Ya faÉ—a yana É—an murmushi, a take mutanen gari suka fara kawo kuÉ—i suna ba Sheik tun yana zubawa a aljihu har dai aka ara masa fanteka yake sakawa, mutane suna murnar ceton su Liman da ya yi da kuma murnar garin su zai yi lafiya za su rayu babu tsoro.

A cikin kunnesa iska take kawo masa maganganun matan sa suke wajen wata tana cewa

"Ai mun samu wajen zuwa, mun huta kaiwa malamai da bokaye kuÉ—aÉ—enmu suna bamu maganin mallakar miji, da wanda ake yi wa kishiya, shikenan yanzu a wajen balaraben malami za muke baje haja" Wata ta ce

"Ai na faÉ—a miki yanzu malamin nan sai ya rasa lokacin kansa in aka ringa tururuwa"

Duk abin da suke faÉ—a Sheik yana ji har ya fara hango yadda zai ke tsula musu kuÉ—in aiki.

Ana cikin haka kamar an ce Sheik ya ɗaga kai, sai kuwa ya sauke idanunsa a kan kukar bulukiya. Wani kan ƙwarangwal ya hango ajiye a saman kukar, sai ƙaho a jiki, da sauri ya sunkuyar da kansa, yana haɗiye wani yawu muduk. Carbinsa ya shiga ja da sauri-sauri dama robar ruwan maganin tana cikin fantekar kuɗin, gabansa ne ya shiga faɗuwa ya tuno furucinsa da yake cewa ko ido da ido za su fafata.

Liman ne ya ce
Chapter 12 · 0% Book details