← Book details Malamin Bogi Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 10 OF 35

Sashe 10

Malamin Bogi Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

"Haba Mai Gari wanann tambayar ma ai ɓata baki ake yi, ni da na zo taimako ina ni ina bacci, ai ni nan da na gama cin abinci kawai alwala na yi na hau sallaya, nake salloli ina addu'a ban tashi ba sai da aka fara kiran assalatu, shi ne na sake alwala na yi shirin fita masallaci, sai kuma na tuna ku ne za ku zo mu tafi tare, to dai ni ban ji zuwanku da asubar bama don ni nan na yi sallah da nafiloli, wataƙila aljannu sun saka mini auduga ne a kunne shi ya sa ban ji bugun naku ba" Ya faɗa yana kai hannu ya share zufa a goshin sa.

Sosai suka jinjina masa, daga nan suka ce za su je a kawo masa abin kari, nan ya ce wainar ƙwai da dafaffan ƙwai sai a biredi da shayi me kauri. Mai Gari sai da gabansa ya faɗi, jin abubuwan da ya zana, sai dai har da wasu sunayen abubuwan larabci da shi kansa Sheik bai san mene ne ba, ya zayyana sai da Mai Garin ya ce vasu san abubuwan ba sannan Sheik ya ce a barsu dama abincin su ne na ƙasar larabawa.

Bayan samarin sun gama gyaran suka tafi da su Mai Gari. Lokacin ya saka jallabiya, ya ce zai yi wanka, suna tafiya ya gabansa yana faɗuwa, amma haka ya je ya garƙama sakata ya ɗauki ruwa ya tuɓi ya yi wanka a tsakar gidan, don ba zai iya komawa banɗakin a lokacin ba. Yana gamawa ya buɗe ƙofar gidan saboda masu kawo abincin don an ce masa mutane za su fara zuwa neman magani yanzu gidan zai cika maƙil in ya gama cin abinci.

Juyowar da zai yi ya yi arangama da wani ƙaton hanci yashe a tsakar gidan, amma girman hancin ya yi kan mutum da gudu Sheik ya doshi ɗaki towel a hannu don da ya kunce gani ya yi bashi ma da nutsuwar tsayawa ya ɗaura.

Yana shiga ɗakin ya banke ya jingina da jikin ƙofar yana mayar da numfashi, a fili ya ce

"Ko a ni ko a ku aljannun garin nan, wato kun ga ana girmamani hassada da tsana suke damunku, yadda zan ke shan ganimar girki, da kuɗaɗen magani ana biyana yasin babu inda zan gudu, ba hanci da kunne ba kai ko karo zan ke ci da mafitsara kuna jefowa aradu sai dai na gudu ɗaki amma dai arziƙi sai na dagwala a garin Ƙundu" Ya faɗa yana ƙarasawa ya zauna, ya shiga shafa mayukansa, sai da ya gama tsaf a saka kayansa ya samu turarukansa masu ƙamshi ya shafa saboda su kashe warin mayukan bilicin yake yawan amfani da turaruka.

Yana gamawa ya kabbara sallah, sai lokacin ne ya yi sallar asuba, a lokacin kuma Audu yake rafka sallama, gyaran murya ya yi, sai da ya sallame sanann ya amsa, amma da ya leƙo bai ga hancin nan ba, haka ya buɗewa Audu ɗakin ya ajiye masa kayan abincin bayan ya gaishe da shi, ya nuna masa kwanukan jiya ya ɗauka, har ya jiya zai tafi Sheik ya ce

"Mu manyan malamai ba a gutsure mana cinyar kaza ko wani sashe na jikinta, yadda aka ba mutum saƙo ya ji tsoron Allah ya kawo daidai" Da rashin fahimta Audu ya kalle shi amma sai ya ce

"Malam ban gane ba"

Sheik ya ce

"Jiya kazar nan da ka kawo bata da cinya É—aya" Mamaki ne ya kashe Audu jin wai shi da aka bashi abu har lissafawa ya yi, hakan ya sa ya ce

"Wallahi ni ban É—auka ba, sai dai ko a gidan Mai Garin ne da aka dafa suka É—auka suka rabawa yara" Maganar Audu ta nunawa Sheik asalin gaskiya ya faÉ—a masa, don haka sai yayarda ya ce ya tafi.

Tun da ya buɗe kwanukan ƙamshin wainar ƙwai ya cika ɗaki, ya cinye tass ya sha shayin bayan ya saki gatsa ya ce

"Bari in yi shiri na san yanzun nan masu buƙatar magani za su fara zuwa, ni ko buhun hatsi ma zan ce Mai Gari ya bayar a kawo min? Saboda in ke zuba kuɗin sadakar magungunan da zan ke bayarwa" Ya faɗa a fili yana ciro hular kansa ya shiga taje ta da brush kumb ta kwanta sosai ya ɗauko wani mai me sheƙi ya shafa a take ta shiga walwali. Ajiyewa ya yi a gefe ya buɗe inda kuɗinsa yake ragowar kuɗin saniya, ya shiga ƙirgawa, yana cikin hakan sai ya ji tashi hayaniya an shigo gidan, sai ya ji ana masa wani kira kamar na ƴan farauta ana cewa

"Sheik ka fito gari babu lafiya, aljannun mai farfaɗiya sun tashi, ƙartai goma aka tara suka riƙe ta amma ta watsar da su" Gaban Sheik ne ya harba da ƙarfi wai me farfaɗiya, kuma ƙartai goma ta watsar kenan yanzu shi kuma in zai mata maganin ya zai yi?.

Bai yi magana ba kuma dama É—akin nasa a rufe, sai ya ji wani ya shigo yana cewa

"Innalillahi wallahi matar nan mai farfaɗiya ta ɗaga Mai Gari da hannu ɗaya hannunta na dama, hannun hagun ɗin ta ɗaga Malam Liman, Sheik ka fito da gaggawa ,a ta hau saman kukar bulukiya da su" Gabaɗaya idanun Sheik sun ciko da ƙwalla, hankalinsa ya tashi gabansa ya hau dukan uku-uku. Dakyar ya yi ƙarfin halin faɗin

"Ya subhanallahi, mai farfaɗiya a yi haka kuma, ki ɗaga Mai Gari da Malam Liman, jama'a gani nan zuwa" Ya faɗa yana zufa, sai dai abin da ya bashi mamaki wanann hular tasa wacce ita ce rufin asirinsa, wacce ya cire ya taje gashin ya ajiye a gefe yana lissafin kuɗi, babu ita babu dalilinta, wato hula dai mai gashi da gemo da saje ta yi ƙafa don bai ganta ba.

Hankali a tashe ya kai hannunsa biyu saman kansa yana shafo tsakiyar kansa zuwa fuskarsa, hankali tashe, jin ya shafo ƙwal kwabon kansa da kuma fuskarsa da babu saje babu gemu lallai yau akwai cakwakiya, ya ake so ya yi wajen fita zuwa ruƙiyyar.

Wani ƙaramin mudubi ya ɗakko a jakarsa ya duba fuskarsa yana ganin tabbas idan ya kuskura aka ganshi a haka ya kaɗe har ganyensa, don za a gano ba balarabe ba ne.

Wani mai ƙarfin hali ne ya takarkare ya ce

"Sheik ka fito su Liman rai a hannun Allah, tana hawa kukar nan ɓacewa za ta yi, don idan aljannu suka ɗauke ta sai ta yi wata biyu ma ba a ganta ba" Ya faɗa a ruɗe ganin Sheik bai fito ba.

Wannan furucin ya sake sanya shi diriricewa yana ƙara shafa sallallan kansa ya ce

"Gani nan zuwa ai ƙaryarta ta sha ƙarya"

*Mu haɗu a gaba don jin ya SHEIK zai yi wajen fitowa babu hula, shin ina hular tashi? Ko dai aljannun ne suka saci don su ga ƙarshen ƙarya?*

Yanzu muka fara ku dai ku biyo ni don jin ya za ta kaya✍️

MAMAN AFRAH
09025576222

*Dan Allah masoya ina neman alfarmar addu,arku gareni da bakunanku masu albarka, Allah kaɗai ya san bakin wani, ina nema domin Allah🤲 ko a zuciya ne ki mini addu'a NGD sosai ana tare😍* 🤝
[7/4, 4:00 PM] Mom mashkr & Afrah: https://chat.whatsapp.com/EBurrU2vz6OFGbE37xLhPS

👳🏻‍♂️ *MALAMIN BOGI*👳🏻‍♂️

NA

MAMAN AFRAH

First Class Writer's Asso.📝

Daga marubuciyar:

Ƙazamin miji
Bonono Rufin ƙofa...
Ruɓaɓɓiyar igiya
Ƴar zaman wanka
Ƙara'in inna delu
Beelal
Ƴan adaidaita sahu
Ungozoma
Jalli joga

Da sauran su.
*09025576222*

BOOK1️⃣
PAGE 5

*ƘAUYEN MAI MANGWARO*

A fadar Mai Gari dakyar aka dakatar da Jummau daga kukan da take tana ta faÉ—ar cewa yau sai an biya ta saniyar marayu. Ita ma Lami tana faÉ—in sai Jummai ta biya ta kuÉ—in adashen ta, tun da ita ma saniyar ba ita ta siyar ba don haka sai dai ta biya ta kuÉ—inta in ya so idan Ibra ya kawo kuÉ—in sai ya bata, sai dai Mai Gari ya tsawar musu sannan suka yi shiru.

Isowar Kakar Ibra Inna Tasallah fadar Mai Garin na Mai Mangwaro tana sakin É—an kuka tana face hanci shi ya dakatar da kowa aka É—ago ana zuba mata na mujiya, wuri ta samu ta zauna har lokacin tana É—an matse hawaye ita takaicin ta É—aya jarin kayan miyar nan idan ta bayar ina za ta samu?

Mai Gari ne ya yi gyaran murya ya fara magana kamar haka yana mai cewa

"Tasallah shin kin san kiran da na aika aka miki?" A maimakon ta bashi amsa sai ta ƙara gudub kukan nata, kasaƙe ya yi yana kallon ta, sai da ta ɗan tsagaita kukan ta ce

"Yo na sani mana Mai Gari, ai Idrisu da ya je ya kwashe komai ya faɗa mini, to zuwa wajenka kuwa ai ya zame mini farillah tusa a masallaci, in da sabo na saba a kawo ni ƙara wajenka, yau a ce Ibra ya cinyewa yarinya me tallah ƙosai, gobe a ce ya warci sandar rake a dandali, har ta kai ya fara kame kajin mutane yana yankewa ya cinye, yau kuma saniya sukutum ya gudu da ita wallahi albasa bata yi halin ruwa ba"Ta faɗa tana rungume robar kayab miyar ta tamkar wani ya ce zai ƙwace.

Jummai ce ta yi tsoma baki ta ce

"Wallahi in har ya saba cin ƙasa ya kiyayi ta shuri, in har tun yana ƙarami yana wartar kayan jama,a ana ƙyalewa kawo samartakarsa, to yau ya taɓo gidan rina don ko sama da ƙasa za su haɗe sai kin biyani saniyata" Haɓa Inna ta dafe ta ce

"Haba Jummai kema kin san alamar ƙarfi tana ga mai ƙiba, in ba tada zaune tsaye ba, ni yanzu a kan kuɗin ƙafar kaza ma sai a harbe ni, bare wata saniya, ni ban ci nanin ai nanin bata ci ni ba ko?" Ƙirji Jummai ta buga tana hayayyaƙowa Inna kamar ta kai mata duka ta ce
Chapter 10 · 0% Book details