← Book details Malamin Bogi Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 31 OF 35

Sashe 31

Malamin Bogi Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

Ranar wata juma'a ne Mummy tana kwance bayan ta dawo daga fitsari, bacci bai ɗauke ta ba, sai ta ji kamar alamar hayowa saman benen, shiru ta yi tana son gano cewa ko dai kunnen ta ne amma sai sai bata kawo komai ba tana dai kasa kunne tana jiran ta bambance, kamar daga sama haka ta ji, ƙaran buɗewar ƙofar ɗakin Daddy mamaki ne ya yi masauki a kwanyarta, zaune ta tashi, amma yau kawai sai ta ji tana son sanin mai ya saukar da shi ƙasa, don zuciyarta ma ta fara wasi-wasi wato shaiɗan ya fara mata biyar ko dai ɓangaren masu aiki yake zuwa, ba komai ya sa wanann zargin ya ɗarsu a zuciyarta ba sai furucin wata ƙawarta da ta ce mata ba a gane gaban namiji bare bayansa, haka ta faɗa mata bayan ta bata labarin cewa ba zai msta kishiya ba kuma shi mata ma basu ishe sa kallo ba.

Da sanɗa ta sakko duk da tana masa zato mai kyau amma kuma dai tana son idan ta yi abin da za ta yi ɗin ta tarar da shi a kan gaskiya. Abin da ma ya sa ta fara wannan tunanin sai tunawa da ta yi da wannan ranar ma da kamar wannan lokacin ne ya dawo inda ya ce mata ƙasa ya sauka ya ji motsi, a nata ganin ai ba kunnen maciji ne da shi ba da za a ce wani ƙaramin motsi ya je kunnensa.

Jinginuwa ta yi a window tana É—an É—aga labule a zuciyarta tana cewa.

'Idan ka ji ana cewa raka no in yi kashi to tabbas kashin ba gudawa ba ne'

A daidai lokacin da ta ɗaga labule Daddy yana dab da shiga ɗakinsa, abin da ya ɗaure mata kai kuma shi ne yadda yake wani sanɗa yana waige-waige, alamomin rashin gaskiya dai sun bayyana ƙarara a yanayinsa.

Gabanta ne yake faÉ—uwa, amma haka ta daure tana kallonsa har ya shige É—akin, kuma a duhu bai kunna fitilar waya ba ko kuma fitilar É—akin. To in har ba babu gaskiya a tare da shi ba mai ya sa zai yi hakan.

Sai da ta bari ya ɗan jima da shiga sai ta buɗe tata ƙofar ta fito, Daddy da ya shagala da yin waya da Zee bai ma san Hajiya ta buɗe ƙofa ba don ba ya cikin nutsuwar da zai ji ƙaran ƙofar. Sai da ta zo za ta buɗe ƙofar ta ji dirin maganarsa sai dai bata ji mai yake cewa ba, mamaki take da wa za su yi waya a doshin asubar nan.

Ƙofar ta murɗa, Daddy da yake waya ya danne wayar da sauri ta ɗauke, idanu ya rufe kamar mai baccin ƙarya. Fitilar ta kunna abin mamaki har da munshari yake saki, wanann ne dalilin da ya sa ya fara jefa masa ayar tambaya a ranta, tana tunanin wane irin sake ne wannan ta yi a cikin gidanta, sai yanzu ne ma take mamakin yadda Alhajin ba ya ƙulafucin ta zo ɗakin nasa wanda a da can baya ba sa ɗaukan wannan tsawon lokacin ba tare da sun kusanci juna ba, amma sai yanzu ta lura da ita da babu ma duk ɗaya, bata san cewa sabuwar fulawa ya samu yake ban ruwa ba.

Yadda ya mata bariki ita ma barikin ta masa, gaban gadon ta ƙarasa ta ɗan buga ƙafarsa tana kiran sunansa, idanu ya buɗe dakyar yana wani ƙanƙance su irin na mai bacci, sai ta ji wani haushin sa ma tun da ta ga zai munafurce ta.

Ɗan washe fuska ta yi tana masa murmushi take cewa ya tashi lokacin sallah ya yi, ko kunya haka ya tashi yana wani murtsuka idanu, duk da ta san ba a ma fara kiran sallar ba, amma dai dama ta zo ne don ta tababtar da baccin makaho, da a ce yana da gaskiya Daddy da ba zai yi baccin ƙarya ba, sai dai ta ci alwashin sai ta gano abin da yake sauka yi a ƙasa.

Ɗakin ta ta juya ta koma shi kuma ya shiga banɗaki, yana suuke ajiyar zuciyar kuɓuta don shi a nashi tunanin ko ta ji yana waya ne, don bai taɓa kawo cewa ta ga shigowarsa ba, bare har ya yi tunanin ta ji yana waya ya san ma ba zai yiwu ta yi shiru ba.

Bata sauya masa ba ko a fuska bata nuna masa ba, sai dai a ɗauki alƙawarin sai ta ƙurewa motarsa gudu. Sai da dare ya yi ta hau ƙawar ya kwana a ɗakinta amma firrr ya ƙi yana cewa shi katifar ɗakin ce ba ya so, da ta nuna cewa ko ɗakinsa za su je, sai ta ga ya ɗan basa da zancen, ita kuwa bata wani nuna masa ta damu ba ko kuma ta damu, sai kawai ta kwanta a nata ɗakin ya mata sallama ya fita ya rufo ƙofar. Yadda ta ga rana haka ta ga dare, tana jiran ta ga abin da zai faru. Har ta fara ganin lafin kanta da kanta cewa ta zargi mijinta kamar daga sama ta ji an buɗe ƙofar ɗakinsa, bizigir ta miƙw zaune daga kwanciyar da take ba tare da ta shiryawa hakan ba.

A hankali ta lallaɓo ta zo window sai gashi ya fita, tana nan tsaye ta ji ya buɗe ƙofar falon ƙasa, shi ma don idanun ta biyu shi ya sa ta ji kuma saboda ta kasa kunne. Gabanta ne ya tsananta bugu tana jin faɗuwar gaba don zuwa yanzu ta tabbatar da cewa wajen ƴan aiki yake zuwa, tun da dai babu abin da zai fitar da shi da dare, windown da ake hango harabar gidan ta zo ta leƙo sai kawai ta hangi Daddy ta cikin hasken farin wata yana ta sauri, kallonsa take hawaye cike a fuskarta don a halin da take yanzu gani take ko rantsuwa za ta yi cewa biyan buƙatarsa ce ta wajen ƴan aiki ta fita da shi.

Sai dai akalar tunaninta ya sauya ne a lokacin da ta ga ya nufi ƙofar fita daga gidan ta baya, a sannan ne ƙirjint a ya shiga bugu da mugun ƙarfi,, ji ta yi hankalinta ya tashi, da sauri ta bar jikin labulen bayan ta ga fitarsa, a kiɗime ta juyo ta kunna fitilar ɗakin, haske ya gauraye ko ina, ƙaramar lokar jikin madubi ta janyo inda take ajiye mukullai, dakyar ta samu mukullin ƙofar fita daga bayan gidan, jikinta yana ta ƙyarma, saboda jikinta ya bata akwai wani gagarumin abin da yake faruwa.

Ko ƙofar ɗakin bata rufe ba, haka ta fito fitilar wayarta a kunne, da matakala bibiyu take sauka daga saman benen, ƙofar falon ma a buɗe ta bari ko takalmi babu a ƙafarta, ita fatan ta ɗaya shi ne Allah sa dai ba wai fira yake da wata macen ba, shi ne ba ya zuwa sai dare ya tsala saboda gudun ɓacin ranta, amma wace mace ce za a ce tana fitowa daga gidansu a wannan daren, sai dai in mutuniyar banza ce, haka take ta saƙawa har ta zo wajen ƙofar, ganin ƙofar a kulle , zargin ta ya zama gaskiya, mukullin ta saka ta buɗe ƙofar sai dai bata da nutsuwar rufe ƙofar, amma sai ta laɓe ta leƙo, daga can ta hange shi tsaye da alama wani yake jira, tana hango shi tana jin tsanarsa a ranta, wato su iyalansa suna nan suna bacci shi kuma lokacin ne safiyarsa ta waye.

Wani machine ne ya tsayar ya hau, suna fara tafiya sai ga wata mata a mota, nan Hajiya ta tsayar da ita ko tsoro ma bata ji, matar kasancewar ta likita kuma sama da gidan su Mummy take, ta fito ne za ta je karɓar haihuwar wata mata, haka ta ɗauki Mummy ganin kamar ba a hayyacinta take ba machine ɗin ta nuna mata a kan cewa ta bi bayansu, ganin sai kuka take tana mata bayanin abin da ya sa ta biyo bayan mijin nata.

Ta tausayawa Mummyn, sun ɗan tsaya daga ɗan nesa ganin machine ɗin ya tsaya a ƙofar wani gida, Mummy ta mata godiya bayan an buɗewa Daddy ya shige ta fita daga motar ta ƙarasa a ƙafa. Ganin katangar bata da wani tsayi a ranta ta ce

'In ka ji kana ba za ka iya ba to bai same ka ba ne, ai ni yau sai na ga ƙwal uwar daka' Ta faɗa a zuciyarta tana komawa daga can bayan gidan ta kama katanga ta ɗare, haka ta ti dabara ta dira amma fargabar abin da za da tarar sai ya sanya bata ji buguwar da mazaunanta suka yi ba.

Tashi ta yi ta yi saurin laɓewa ganin ana hasko fitila, sai da ta dakata mai gadin ne ya zo ya yi ɗan haske haske ya juya bai ganta ba, da alama bai fuskanci cewa gidan aka diro ba.

Ƙofar falon ta lallaɓa ta tura a hankali jin ba a saka mukulli ba zuciyarta tana ta ayyana mata cewa

"Namiji ba ɗan goyo ba ne, tun da ta yarda da mijinta ashe dai saka reshe kama ganye ta yi, sai dai ta ɗaukarwa kanta alƙawarin za a yi kan mai uwa da wabi, domin ta lura tsugunne bata ƙare ba amma sai ta nuna musu tun kafin a haifi uwar mai sabulu barbela take da farinta, tun shi Alhaji ganin hadarin nesa zai sa shi yin wanka da kashi, don ta lura wadatar biki ne tsarki da romo, tun da har ya iya zuwa wajen wata mace za ta nunawa matar cewa abincin wani gubar wani ne, don abin nasu aikin banza ne shafa lalle a ɗuwawu'

Ɗan hasken da ka bari a falon wanda yake kawowa yana ɗaukewa hasken mai kalar blue, ganin falon shiru hakan ya bata tabbacin suna sama, saman ta hau tana jin cewa yau duk sai sun baƙunci lahira, a ɗaki na farko ta fara jin magana ƙasa -ƙasa muryar Zee ta ji tana cewa

"Haba kai kuwa gaskiya yau ka makara baka fito da wuri ba, ka san dai ai bana iya bacci sai da kai, sai ka je ka tare a gidanka ni ka barni da kewa" Mummy ji ta yi kamar ta fasa ihu, Daddy ta ji ya ce
Chapter 31 · 0% Book details