Sashe 3
Malamin Bogi Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read
"Dama ina ɗaki bayan fitarku na yi alwala shi ne nake, gabatar da addu'a domin kawo muku kwanciya lafiya a wannan rana, kowa ya yi baccinsa kun san mu a ƙasar larabawa akwai addu'o'i da ake gabatarwa kullum da dare don samun bacci mai daɗi ga kowa na gari kai har garuruwan da suke kewaye ma, don samun kariya" Mai Gari ji ya yi ransa fari ƙal da wannan batu, ya san addu'a da sadakar ƙuli-ƙulin da ake yi ne a garin ya sa Allah ya kawo musu wannan babban malamin kuma balarabe.
Har za su tafi ya tuna bashi da alwala, tun da wacce ya ce musu ya yi faÉ—a ya yi don ya faranta musu don ya san hakan zai kankaro masa mutunci. Amma saboda gogewa a tsara zance sai ya ce yana son sake alwala, saboda su larabawa suna da yawan sake alwala domin tana kankare zunubi. Haka suka jira shi ya shige bayin a ciki ya yi alwalar ma, saboda gudun cire hularsa wajen yin shafar kai.
Yana gaba suna bin sa a baya sai jan carbi yake bakinsa yana kai wa da kawowa alamar ba ya sake da hailala da salatin annabi S.A.W.
Tun da suka taho mutane suke ta gaishe da shi cikin girmamawa wannan abin ya ƙara ƙayatar da shi, kuma ya sa kansa ya amsa wani gingirigim don jinsa yake tamkar wani basarake ko mai mulki tabbas zai ja zugar mutane yadda zai samu kuɗi.
Sun ƙaraso masallacin inda mutane suna tsaye carko-carko, suna zuwa kowa ya fara darewa ana ba balarabe waje don ya samu sahu kowa yana son tsayuwa kusa da shi. Mai Gari ne a kusa da shi liman sai wani baza babbar riga yake shi ala dole zai jagoranci limanci har da balarabe.
An yi sallah an idar, sai da aka yi isha'i sannan kowa ya watse bayan Mai Gari da jama'ar gari sun yanke shawarar naÉ—a Sheik a matsayin limamin garin, abin ya yi wa liman ciwo amma ya danne tun da ya san babu yadda za a yi a saurare shi tun da yanzu kowa yana ganin Sheik ya zo zai kawo musu waraka daga cutukan da ake fama da su a garin.
Bayan Mai Gari da liman sun raka Sheik gida masaukinsa, Mai Gari ya ce za a kawo masa abinci yanzu nan suka masa sallama suka tafi, liman yana ta muzurai za a ƙwace masa matsayinsa na liman yana ganin hakan zai rage masa kima a idanun mutanen gari.
Mai Gari yana komawa gida ya je wajen matarsa da take dafa kazar da aka kama cikin kajinsa aka yanka, yana hango tukunya a kan wuta ransa ya ƙara ɓaci don ya tabbatar kafin Sheik ya bar garin nan sai ya nakasta masa dukiya sai dai ya ci alwashin sai ya yi ramako don kadararsa da kuɗinsa ba za su tafi a banza ba.
Bayan an gama aka juye a ƙatuwar samira, sai tururi yake, ƙamshi yana tashi Mai Gari sai haɗiyar yawu yake saboda rabon ya ci wani abu mai suna nama har ya manta.
ÆŠaki ya shiga da kwanon da kuma jug É—in da aka sayo shayi a wajen mau siyar da shayi, aka zuba madara haÉ—in kauri, buÉ—ewa ya yi ya saka a gaba yana kallo, a haka matar tasa ta shigo, ganin haka ta ce
"Mai Gari ya haka, kai da za a kai wa baƙo abu ka zauna ka saka a gaba, kana kallo kamar ka samu wata sabon kamawa?" Yawun da ya taru a bakinsa ya haɗiye, kamar zai yi kuka ya ce
"Dama ina kallo ne saboda in kore kwaÉ—ayin da nake ji" Ta ce
"Haba dai dama kallon abu yana kore kwaɗayi?" Ya amsa mata da cewa haka ne. Tana fita ya kasa jurewa, cinyar kaza ya ɗauka guda ɗaya, zafi ne da ita dakyar ya ɗauka, ya kai baki ya ciri tsokar ya cika baki da ita kamar daga sama sai jin takun matarsa ya yi da sauri ya rasa inda zai saka cinyar kazar kuma ba ya so ya mayar cikin kwanon a kai balarabe ya gani an ci ko ma dai ya ce ba zai ci guntun baƙar fata ba, ya san kuwa shi ne a ciki tun da dole a kama wata kazar a yanka a dafa, in ba haka ba jama'ar gari su yi da shi a ace abu ya gagare shi. Da sauri ya kai hamatarsa da yake ƴar shara ce a jikinsa sai ya zamana hamatar a buɗe ai kuwa yana saka naman nan mai zafi ya danne hamatar ya matse ta, ya yi saurin goge hannun a jikin rigarsa. Bidik Asabe matar Mai Gari ta shigo ɗakin ko sallama babu, muduk Mai Gari ya haɗiye naman bakinsa da sauri ba tare da ko taunawa ya yi ba, gashi da zafi duk ya ɗane harshe.
Tana shigowa ta ce
"Mai Gari ga Audun ya zo" Idanu ya É—an runtse jin zafin naman da yake ratsa hamatarsa ya buÉ—e idanun cikin É—an gigicewa ya ce
"Gonar za su tafi yin shuka?" Galala ta saki baki tana kallonsa ta ce
"Haba Mai Gari lafiyarka kuwa? Mu da ba a damuwan muke ba wane irin tafiya gona, kai fa ka ce a kirawo shi zai kaiwa baƙo abincin" Wata ƴar dariya ya saki yana sosa ƙeya da ɗaya hannun nasa ya ce
"Allahu akbar ashe fa haka aka yi ina jin mafarki na yi" Ya faɗa yana tura mata kwanon da jug ɗin gabanta, saboda ya matsu ta fita ya cire naman hamatarsa ko ya samu sauƙin raɗaɗin zafin yaji da na wutar da suka haɗe masa.
Kallonsa take da mamakin jin furucinsa da sauti ta suri kwanukan ta fito daga turakar tasa, tana tunanin ko dai aljannun garin Ƙundu sun fara taɓa Mai Gari. Audu ta ba kwanukan ta juya ta shige ɗakinta gudun tsautsayi ko ɗakin Mai Gari bata koma ba, a yadda ta ga yanayinsa ta fara tsoron ya mata wani abu.
Mai Gari tana fita fa sauri ya ɗaga hamatarsa, naman faɗowa ya yi, amma tsabar raɗaɗin zafin barkono da na wutar bai bi ta kan naman ba, illa barin hamatar da ya yi a ɗage ya karkata bakinsa ya shiga hura iska a hamatar ko ya samu salama. Haka ya dinga yi sai da ya ji sawaba, sannan ya ɗauke naman ya cinye ya taune ƙashin ya haɗiye, fitowa waje ya yi yana ƙwalawa matarsa kira, bakam ta fito daga ɗaki tana ɗan ɗari-ɗari da shi, sai cewa ya yi
"Asabe anya baki cika yaji a wanann dahuwar naman ba?" Shiru ta yi tana kallonsa da mamaki ta ce
"Yaji kuma Mai Gari? Kai da baka ci ba ya aka yi ka sani ko dai baƙon ne ya faɗa ya ce an cika yajin?" Sai sannan ya fahimci ya yi ɓaran-ɓarama cikin wayincewa ya ce
"A'a fa, kawai dai tun ɗazu nake atishawar yajin da na shaƙa garin jin ƙamshin naman" Baki ta taɓe ba tare da ta ce masa komai ba, ƙuri ta yi wa ƴar sharar jikinsa ganin wani abu kamar man miya, fuska ya ɗaurr ganin tana kallonsa gudun kar ta harbo jirginsa, don haushinta ma yake ji da ta zo ɗakin bai kurɓi shayin nan mai madara ba.
Ruwa ya cika a buta ya wanke hamatarsa da klin, don ita matarsa É—akinta ta koma.
A ɓangaren Audu tun da ya je gidan da aka sauki Sheik, ya shiga rafka sallama ganin Sheik ya rufe ɗaki, Sheik kuwa tun daga sallamar ya ji yawunsa ya tsinke don ya gane saƙon abincinsa ne ya zo.
Sai da ya ɗan yi jim sakamakon mayar da mayukan bilicin ɗinsa da yake shafawa, don dama yana shafawa da dare sai ya kwana da su, saboda an ce masa man ya fi bin jikin fata in ana kwana da shi. Ƙofar ya buɗe ya fito yana cewa.
" Man yatahaddas(Waye yake magana?) Ya ce yana ɗan ƙara fitowa . Audu da bai san mai aka ce ba ya juya da gayya zai koma, tun da ya ga ba hausa zai masa ba shi kuma babu abin da ya sani na larabci. Cikin sauri Sheik ya fito ko takalmi babu yana faɗin
"Ya za ka koma gani fa ko ba wajena ka zo ba" Audu juyowa ya yi yana mamakin É—an rikicewar da malamin ya yi ya ce
"Dama abinci ne Mai Gari ya ce a kawo maka" Karɓa ya yi yana ta wasu zantukan larabci da shi kansa Sheik ɗin bai san mai yake faɗa ba, Audu kuma sai ya ji abin ya birge shi, saboda a rayuwa yana spn ya ji yana wani yare da ba hausa ba sai dai bayan hausa bai iya komai ba.
Sai da ya juya zai tafi, malam ya ajiye kwanukan ya bi bayan Audun wannan karon fa hausa yake zabga godiya, saboda tsabagen rowa so yake Audun yana fita ya rufe ƙofar gida, don kar wani ma ya zo yana cikin cin naman shi kuwa ba zai bayar ba. Audu sallama ya masa zai tafi ganin ya kama ƙofa zai rufe Audu ya yi gyaran murya cikin yin ƙasa da murya ya ce
"Malam da kake barin ƙofar gidan nan a buɗe, in son samu ne ma har ƙofar ɗakin da kake ciki, idan ma ba damuwa da sai ka ce a baka masu tayin kwana..." Tun kan ya kai ƙarshen maganar Sheik ya katse shi da faɗin
"Ni bana buƙatar kowa ya zo ni kaɗai ma zan zauna" Ya faɗa a fili a zuciyarsa kuma ya ce
'Aikin banza mutane da shegen kwaÉ—ayi da son samu kuke, wato ka ga an haÉ—o kayan daÉ—i an aiko mini shi ne za ka yi dibara don in ce ka zo ka kwana wato duk wani abin daÉ—i in ke kasawa ina baka, to alharam giya a gidan liman'
Audu ya ce
"Malam wannan gidan da kake gani gidan kakan Mai Gari ne, mutumin nan ya kashe shekaru masu yawa a duniya kafin ya mutu, tsabar tsufa da kuma malamin tsubbu ne mai aiki da aljannu sai da gabaÉ—aya jikinsa ya yi fari gashi..." Sheik ya kalle shi ya ce