← Book details Malamin Bogi Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 8 OF 35

Sashe 8

Malamin Bogi Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

Saurayin nan da Liman ya kaiwa ranƙwashi, zafin ranƙwashin ya saka shi ƙara cukuikuye rigar Liman da gangan, dama shi ne wannan me ƙarfin da aka taho da shi zai buɗe ƙofar gidan, wato ƙaƙƙarfan. Jan rigar da ya yi shi ma ɗaya saurayin yana ta ƙoƙarin ja ya rufe kansa, sai ya zamana gabaɗaya an shaƙewa Liman wuyansa, jin shaƙe wuyan yana barazana ga maƙogwaronsa sai ya lanƙwasa kansa da sauri ya zame kansa daga cikin babbar rigar, hakan ya sa garin ya zame rigar sai kansa ya fita daga cikin bargon da suke tare da Sheik, shi kuma Sheik sai ya ja bargon ya ƙara duƙunƙune kansa, don yana a goho ne duk da yana jin kashin. Samarin nan jin Liman ya sakat musu rigar sai suka cure waje guda suka rufa, tun da yanzu ta ishe su sun rufa tare dama saboda tana jikin Liman ta musu kaɗan.

Malam Liman kasancewar a firgice yake kuma a tsorace kansa yana fitowa daga rufar da yake sai idanunsa suka masa gizo da ganin Kakan Mai Gari wanann marigayin da aka binne a gidan, ya tsago jikin ƙofa yana tahowa sanye da likkafaninsa, ya ɗan duƙa kasancewar yana da ƙusumbi.

A kiÉ—ime Liman ya nayar sa kansa ya cusa a katifa haÉ—e da cewa

"Wallahi marigayi kakan Mai Gari wato mai ƙusunbi ya tatso ta jikin ƙofa ya shigo ɗakin nan"

Ya faɗa yana miƙa hannu a niyyarsa ya samo bargon da ya fito ya shiga, sai ya cafko towel ɗin jikin Sheik, Sheik kuwa jin furucin Liman na cewa Kakan Mai Gari ya shigo ɗaki, hakan ya tuna masa da jawabin da Audu ya masa a daren jiya na cewa Kakan Mai Gari ƙasa ta ƙi karɓarsa da ya mutu, saboda saɓon da yake yi, sai gida aka dawo aka masa kabari aka binne. Kenan wanda ake zuwa maƙabarta ana samun sa yana gefe kabarin da aka saka shi ma a gefe, to ba abin mamaki bane in aja ce yanzu ya taso da ƙafafunsa, wataƙila fatalwa ya yi. Tsabar ruɗanin da Sheik ya shiga yana jin an iska ta fara shiga jikin mazaunansa alamar mazaunan nasa a buɗe suke tantagarya, amma tsoro ba zai bari ya suturta su ba, don shi tunaninsa towel ɗin zamewa ya yi.

Samarin nan jin furucin Liman sai suka rungume juna kamar sa zama mutum ɗaya, haka kowanne yake jin bugun zuciyar ɗan uwansa alamar dai ana cikin fargaba da tashin hankali, Malam Liman da ya samu towel ɗin Sheik ya rufe yana ta ƙoƙarin son ya ga ya samu ko da addu'a ɗaya ce cikin wanda ya iya don yake karantawa ko a zuciyarsa ce amma ji ya yi gabaɗaya ya manta komai a halin da yake ciki yanzu gani yake sunansa ne kaɗai zai iya tunawa. Yana wannnn halin ne ya ji saukar hannun Mai Gari a bayansa, wanda hakan ya sa ya ɗauka hannun marigayi mai ƙusumbi ne wanda ya masa gizo, duk tunaninsa a zahiri ya gan shi, hakan ya sa gumi ya shiga zarya a gabaɗaya ilahirin jikinsa tare da kufcewar wannan fitsari da yake ta dannewa, saboda yanzu an zo wajen da ba ta girma da martabarsa ta Liman ake yi ba, ana magana ne ta ceton rai tun da har yana ganin gawa ta taɓa shi, gawar ma ta marigayi mai ƙusumbi.

Liman a zuciyarsa yake faÉ—in

'Allahu akbar! Tamu ta zo (Yana nufin mutuwa) Allah ka bamu ikon amsa tambayar kabari, Allah ni nake jan sallah a garin ƙundu ka bani cikawa da imani' Wannan yake ta maimaitawa a zuciyarsa.

Mai Gari kuwa hannun da ya miƙa shi lalumen bargon Sheik yake yi, so yake ya koma cikin bargon Sheik ko ya samu salama a ransa, tun da yana ganin bargon Sheik za a samu tsari kasancewar malamin balarabe ba za a ce ruɗani ya hana shi addu'a ba.

Jin ya sauke hannun nasa a jikin riga, kuma ya san dai Sheik bashi da riga suka shigo ɗakin, tun da idanun Mai Garin a rufe suke ba ya so ya buɗe bare ya ga fatalwar kakansa mai ƙusumbi, son ya fara tunanin ma kar dai mai ƙusumbin ya ce ya zo ya tafi da shi ne. Hannun da ya fara matsarwa a jikin Liman kasancewar rigar Liman ta shadda ce ta ci uban duniyar ta da tsinke, domin daga baya a yage take kasancewar ya ɗora babbar riga shi ya sa ba a ganin yagar, yanzu kuma da samarin nan suka sa ya cire babar rigar sai yagar ta bayyana a bayansa. Hannun Mai Gari ne ya shige cikin bayan Liman ta wanann yagar, hakan ya sa ya shafo bayan fatar jikin Liman.

Liman mutuwar kwance ya yi don zuwa yanzu ma kawai bakinsa ne yake karkarwa kamar wanda zazzaɓi ya yi wa mugun kamu, haƙoransa suna haɗuwa da juna, saboda ya gama saddaƙarwa cewa fatalwar mai ƙusunbi ce ta dama masa baya take shafa fatarsa, ya san yau babu makawa da shi za ta koma lahira

Mai Gari da sauri ya ɗauke hannunsa, saboda fatar da ya taɓa ya ji wani karsansan, alamar fatarsu ce irin ta baƙaƙen fata, ya san ta Sheik tana da laushi da santsi irin na larabawa, shi zai tabbatar da haka tun da jiya ya kama hannun Sheik mai laushi kamar na jarirai, bai san cewa tsabar amfani da allurai da magunguna da kuma sabulai na garan fata ne ya sa take duk a yanayin da ya ji fatar.

Yana ɗauke hannun ya miƙa wani wajen tun da gabaɗayan su a kan katifar suke, duk sun cushe, tun da su biyar a kan katifa ɗaya, yana ƙara miƙa hannun ya sauke a kan ƙafafun samarin nan shafawa ya yi sai ya ji wani gautsin fata, don har ya shafo kaushi da faso a ransa ya ce

'Kai jama'a har yanzu dai ina ta dawurwuri a jikin ƴan ƙasar nigeri'a Allah ka kaini a kan daidai wato in taɓo fatar balarabe' Ya faɗa yana jin tausayin kansa.

Samarin nan kuwa jin an taɓo musu ƙafafu, kowanne sai numfashinsa ya tsaya cak! Tunanin su fatalwar da Liman ya gani ce za ta yi awon gaba da su. Juna suka ƙara ƙanƙamewa kowanne yana ta ƙoƙarin warto addu'a a zuciyarsa domin ya kuɓuta, sai dai a cikinsu babu wanda ya yi nasarar ambatar kowacce addu'a don ruɗanin ya kai ruɗu.

Gwiwarsa ya ja bargonsa yana ƙamale a kafaɗarsa idanunsa a rufe, ya miƙa hannunsa bai masa masauki a ko ina ba sai a kan mazaunan Ya Sheik, laushi luɓus ya ji, hakan ya sa ya miƙa ɗaya hannun ma ya zamana hannayensa biyu a kan mazaunan don yana son tabbatar da cewa tabbas a kan fatar Ya Sheik ya sauke hannunsa, amma fa duk abin nan da yake bai san cewa a kan mazaunan Sheik ya sauke hannu ba. Sheik kuwa jin an taɓa masa mazaunai a lokacin ya ƙara gane mazaunansa a tantagarya yake babu rufi ba ma wannan ba lalumen da Mai Gari yake yi nema yake ya wuce gona da iri a wajen Sheik domin kuwa hannunsa yana neman taɓo mafitsarar Sheik, Sheik wanda tunaninsa ya fara bashi cewa fatalwa ce take lalumen jikinsa sai ya ƙara tsorata ya shiga ruɗu, da tunanin kar dai fatalwar mai ƙusunbin tana so ta tsinke masa mafitsarar ne gabaɗaya ma, wani sashen na zuciyarsa yana bashi cewa ko dai shayi ake son a masa(Kaciya,sallatu) Idanu ya zaro bai san lokacin da ya buɗe baki ba gabaɗaya ya manta sa ƙalƙalar sa yake yi ta larabci wajen yin magana, wato yadda ko hausa yake sai ka ɗauka ɗan koyo ne.

Wanann karo da hausa sak irin yadda bahaushe yake magana babu gargada ya ce

"Wallahi na rantse da Allah an mini kaciya, don Allah kar a cire mini mafitsara" Ya faɗa a fili ɗakin har yana ɗaukan amsa kuwwa. Don ya fara tunanin kar a je ko dai a tsinke masa mafitsarar ko dai a je garin masa kaciyar a yanke fiye da rabin mafitsarar a bar masa ƴar guntuwa. Yana faɗa wani hawayen tausayin kansa ya cigaba da zubo masa domin ya fara tuno matansa su Lami da ya baro a ƙauyansu ya san duk inda fatalwar kakan Mai Gari ya gabce masa rabin mafitsara, ko ta cire masa gabaɗaya to in har ma bai mutu ba kenan, ya san shikenan sai dai kowacce ta ce ya bata takardar saki, tuno da wannan kuma ya san yana son matansa sai ya ƙara ware murya duk da yana cike da tsoro ya ce

"Wallahi ina son matana, ba zan sake su ba wani ya aura" Mai Gari tun maganar da Sheik ya yi ta farko wato inda ya ji Sheik yana batun kaciya da cire mafitsara, bai san lokacin da ya É—auke hannuwansa salin alin da sauri ya koma wajensa da ya taso ya kifa kansa yana ambaton

'Lahaula wala ƙuwwata ' A zuciyarsa, don shi ya san dai ya ji an yi magana amma ko za a saka masa wuƙa a maƙoshi ba zai gane ga wanda ya yi maganar ba, sannan ruɗanin da yake ciki bai bari ya gane cewa Sheik ne ya yi maganar hausa sak ba, babu ƴar ƙalƙalar larabcin.

Malam Liman jin ana ambaton kaciya sai ya fara tunanin ko dai fatalwar ta yanke shawarar yayyanke musu mafitsara ne hakan ya sa ya saki towel ɗin da ya rufe kansa da shi, ya mayar wajan matse matsin ƙafafunsa a nufinsa ya yi shirin ko ta kwana, saboda kar a masa sakiyar da ba ruwa.

Gabaɗaya kowa da zaman jiran tsammanin da yake, Sheik ya yi ƙarfin halin jan bargon ya rufe mazaunansa, yana jin da na sanin zuwa garin ma baki ɗaya, sai dai shegen kwaɗayi da son abin duniya ba za su bari ya bar garin ba, ya yi wa kansa alƙawarin zama daram sai ya ga abin da ya turewa buzu naɗi.
Chapter 8 · 0% Book details