Sashe 29
Malamin Bogi Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read
Managar Mai Gari ta katse masa tunani da faÉ—in
",Ai yarinyar nan Allah ya taimake ta ba ƙaramin sa'a ta yi ba da ta auri Sheik amma in ba Sheik ba wa zai iya auren ta?"
Sirikar Sheik ta karɓe da faɗin
"Yo ai dama riƙon mahaukaci sai sarki" Numfashin sa ya samu daidaitawa ya ɗan saka harshen sa ya laso bushashshen leɓansa da ya bushe ya ce
"Kai amma wannan dai sun takurawa rayuwarta, dama ana yi a ce an ɓatar da mashayar jikin mace?" Ya tambaya cike da tsoro don shi yanzu ya kasa bambance komai ma, duk tsoro ya hana shi sakat musamman idan ya tuna cewa yau da ita za su kwana a gida ɗaya kuma a ɗaki ɗaya.
Cike da alhini mahaifiyarta ta ce
"Kayya malam yo aljannu mene ne basa yi, yarinyar nan wataran fa ko rashi ta yi za ta yi fitsari sai ka ji ta ce babu wajen sun toshe mata, sai ranar da suka bushi iska suke buɗewa ai tana wata rayuwa, yanzu dai Allah ya kawo mata ƙarshen wahala, in ma ba malamai irin ku magada annabawa ba waye zai yarda a ce mace an cire mata mashayar ɗa(Breast) Kuma ya yarda bai sake ta ba, kai wani mai aljanun ma ba zai yarda ya aura ba, kai ɗin ma jahadi ne ka yi"
A fili Sheik ya ce
"Yo ai dama kura ma ta san gidan mai babbar sanda, amma su sani rana dubu ta ɓarawo rana ɗaya ta mai kaya"
A zuciyarsa kuma ya ce
"Za ku yi sake reshe kama ganye, wannan dai wayon a ci ne an kori kare daga bakin ɗinya, in ba haka ba kawai kuje fakewa da malami kuna turo mini mutuwa yo mutuwa mana wannan da aljannu suka zama danginta jinin jikinta za a kawo min ita, baku san ni ɗin ma ƙarfin hali ne ɓarawo da sallama ba, babu wani malam kawai MALAMIN BOGI ne'
Cike da murnar kalamansa Mai Gari ya ce
"Ai sai mu je ko? Dama mutane sun kewaye ta in ji mahaifiyar amma kowa cewa yake ai matar babban malamin larabawa ce daga ya zo komai ya ƙare"
Baki Mai Gari ya washe ya ce
"Shi ya sa nake alfahri da shi a garin nan Allah ya tarfawa garinmu nono"
Sheik a ransa ya ce
Ai dama ba wahalalle sai kwaÉ—ayayye, haka kawai garin neman gira in je in rasa ido, ni ban amfani kuÉ—in da na tara ba in rasa abin da kuÉ—i ba zai saya ba, amma ya na iya haka zan ringa tarar aradu da ka, in ta yi ruwa rijiya in bata yi ba masai'
A fili ya ce
"Ai kar ka damu mai gari, mu ko a ƙasashen larabawa bamu san tsoro ba, zan yi ta ba mutanen garin nan magani mata na basu na gyaran aure kai kowa sai ya samu abin da yake nema" Sirikar da Mai Gari suka yi kabbarar jin furucin ta, tana murna ƴarta ta samu mijin nunawa sa'a.
ÆŠaki ya shiga ya É—auko magani ya É—akko dogon carbinsa ya fito, Sirikar Sheik ta ce
"Ai Allah ya kawo mana ƙarshe wahala, yo wahala mana da asubar fari idan aljannunta suka tashi kowa na gidan nan sai jikinsa ya faɗa masa, haka za ka ji saukar doka da dorina"
Gabaɗaya sai ya ƙara kiɗimewa zuwa yanzu ya gama tabbatarwa cewa matsala ya aura wato har tana duka. Tsabar ba ya hayyacin sa sai ya bi bayan su a haka.
Mai Gari da ya waiwayo ya ce
"Subhanallahi Ya Sheik kana lafiya kuwa, baka saka takalmi ba" Cike da wayincewa ya ce
"Ashsha duk saurin zuwa nemowa amarya lafiya ne"
A ransa ya ce
'Lallai akwai lauje cikin naɗi, yau dai na yarda cewa dalili ne kaɗai yake sa a leƙa gaban sirika'
Takalmin ya É—akko, lokacin da suka doshi gidan, sai haÉ—uwa da jama'a suke a hanya ana girmama Sheik basu san cewa ba ya gane abin da suke faÉ—a ma, shi hankalinsa ba ya jikin sa musamman da suka kusa shiga gidan suka ringa jin wani kururuwa da iface-iface.
A zaure suka tsaya, Sheik zuwa yanzu ko magana ba ya iya yi ta fito sosai sai jan carbi da yake ta faman yi yana addu'a a ransa cewa, Allah ya É—ora shi a kan aljannun nan, shi yanzu so yake ya cigaba da bayar da magunguna amma batun aljannun nan ba so yake yi ba.
Sai tashin hanyaniya da suke ji ta mata a cikin gidan, jim kaÉ—an sai ga sirikar Sheik É—in ta dawo tana cewa
"Bismillanku ai gata can ma jikin ya matsa, amma abin mamaki sunan Sheik take ta faman faÉ—a" Sheik da ya ji faÉ—uwar gaba an ce ana kiran sunansa sai ya yi zaton ko dai sunan sa na asali ta faÉ—a wato Ibra tun da ya san su aljannu babu abin da basu sani ba.
Da É—an diriricewa ya ce
"Ya subhanallahi wane sunan daga ciki?"
Ta ce
"Sheik kawai take cewa, amma idanunta a rufe"
Æoyayyar ajiyar zuciya ya sauke, ta shiga gaba suna biye da ita, duk mata ne da alama Æ´an taron bikin ne da kuma kai amarya.
Ɗakin da take karaɗin ihun ne wanda sai da aka rufe daga window ake leƙen ta.
Mai Gari ne ya ja ya tsaya yana mai cewa
"To Ya Sheik a fito lafiya" Ɗiff Sheik ya yi yana jin faɗuwar gaba tana ratsa dukkanin gaɓoɓin jikinsa da zuciyarsa, amma haja ya daure ya gyaɗa masa kai yana mai faɗin
"In sha Allah"
Haka sirikar tasa ta buɗe masa ƙofa ya shige, har da rufo ƙofar.
Tana kwance reran sai wani gurnani take tana surutai da ihu.
Gabansa yana tsananta bugu ya haÉ—iye wani yawu ya ce
"A'uzubillahi minsh shaiɗanir rajim" Ya faɗa da ƙarfi saurin yana karaɗe ɗakin, kamar aljannu jira suke ya yi magana sai ta ɗifff kamar an ɗauke wuta, murmushi ya yi a ransa yana faɗin
'Ashe dai ku É—in ma matsorata ne kamar ni, yanzu kuwa za ku faÉ—awa Æ´an garinku don wallahi sai na mori faÉ—uwar gaban da kuka sakani sai na baku wuju-wuju, mu zuba mu gani' Ya faÉ—a a zuciyarsa yana ajiye maganin da ya taho da shi, carbinsa, da kuma hiraminsa ya naÉ—e hannun jallabiyarsa.
A can tsakar gida kuwa jin ta yi shiru sai aka shiga ƙusƙus kowa yana murna, ana yabawa lamami daga ƙasar larabawa.
Mahaifiyar ta ta ce
"Kai jama'a aiki ga mai ƙare ka, ashe dai duk ihu suke bayan hari ka ji dai ya fara maganin su"
.
Mai Gari ya ce
"Yo dama mai zai gagara ai da kike ji da gani ƴarki ta yi babar sa,a saboda yanzun nan za ki ji ya fitar da su, ke hatta nonuwanta dole su dawo mata da su" Wannan maganar da suka yi a kunnen Sheik da yake suna a ƙofar ɗakin ne.
Sheik jin haka sai ya ƙara ƙaimi, ya leƙi da window yana cewa
"A samu murÉ—uga-murÉ—ugan bulali, guda biyar wannan dole sai sun ci ubansu" Ya faÉ—a da muryar hausar larabcin sa.
Da sauri Mai Gari ya saka samari suka ciro a dalbejiyar ƙofar gidan, aka miƙawa Sheik, nan da nan sai ya hau karatun suratul fatiha ita kaɗai ya karanta har lokacin dai bata ƙara ko motsi ba ta yi ɗif kowa bata cewa komai sai dai yanzu ta buɗe idanunta sun yi faral kamar na gawa.
Ganin hakan ya hau zagarta da bulala, yana faÉ—in
"Za ku fita ko sai na koya muku hankali, sai na nuna muku kudu ba arewa ba ce matar malamin ƙasar yemen za ku ɗaukewa mashaya, baƙin ciki kuke min, kar in angwance" Ya faɗa yana tafka mata bulala. Sai da bulala uku ta karye duk ya burɗa mata jiki.
Ya ɗaga ta uku zai zabga mata sai gani ya yi ta miƙe a fusace, yanayin yadda ta iyo kansa sai da hanjin ciknsa sa ya kaɗa, bulalar ta riƙe bai ankara ba ya ji ta warce, ja ɗaya ta yi wa bulala sai ga Sheik ya saka yana zare ido cike da tsoro, gabansa yana bugawa, ɗagawa ta yi ta tsula masa, tsabar yadda zafin ya shige tsalle ɗaya ya yi sai gashi a gefen gado, taku ɗaya ta yi sai gata a tsakiyar gadon, ta ɗaga bulalar tana rama dukan da ya mata, amma saboda gudun kar a gano lagwansa bai yi ihu ba, ko wani furuci da zai sa a gane halin sa yake ciki.
Mai Gari ne cikin laga murya ya ce.
"Aikin ka yana kyau Sheik kar ka bar su sai sun dawo mata da abubuwan nan masu muhimmanci a jikin mace(Breast)"
Sheik dakyar ya mayar da kukan da yake ƙoƙarin ƙwace masa ya ce
"Ai sai sun maido... Bai ƙarasa faɗa ba ta buge masa baki tana zare ido yana kallon ta ya san ba a hayyacin ta take ba.
Shammatar ta ya yi ta ya fito daga lungun gadon sai ga shi a tsakiyar ɗakin, farɗo ta ya yi yana ɗaukan ɗaya bulalar ya zabga mata sai ta zube a kan gadon idanunsa ƙurrr a ƙirjin ta ya ga wayam babu breast kamar ƙirjin yara.
Baki ya buÉ—e yana karanta qulhuwallahu ahad, yana zabga mata bulalar yana cewa
"Ku maido da nonon da kuka É—auke, ku maido da shi aka ce... Bai rufe bakinsa ba mai zai ji?
Wani abu ya ji kamar an hura masa iska a ƙirjinsa, kafin ka ce kwabo sai ya ga tudu nan da nan sai ga breast ɗin duka biyu a ƙirjin Shaikul yemen. Idanu ya zaro cike da fargaba a zuciyarsa ya hau cewa
'Ƙirjin ta nake nufi fa aljannu, ƙirjinta nake nufi ku mayar ba ƙirjina ba na shiga uku ni Ibra jikan Inna' Ya faɗa yana kai hannu cike da tashin hankali ya shafo ƙirjin, breast ne ya ji tamkar ƙirjin mace....
*BOOK 1 free BOOK 2 500 shiga grp cmplt docment 800 za a biya ta asusun faiza abubakar 9030283375 opay. Saura page 2 a gama book 1*
*MAMAN AFRAH*
09025576222
💃 TALLAH TALLAH💃