Sashe 4
Malamin Bogi Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read
"Audu ni fa ban tambaye ka tarihin Kakan Mai Gari ba" Ya katse masa hanzari. Audu ya ce
"Ba tarihi nake baka ba, abin da nake faɗa maka ya danganci zaman ka a gidan, wato duk jikinsa sai da ya yi gashi farin gashi, ko da ya mutu aka binne shi kullum sai raminsa kabarinsa ya buɗe wataran a gan shi a wajen kabarin, to a ƙarshe dai sai rami aka masa a cikin gidan nan aka binne shi, ka ga wancan zagayen da aka saka langa-langa to kabarinsa ne a ciki, kuma gidan nan matattarar aljannu ne, tun daga ranar da ya mutu cutuka suka baibaye garin Ƙundu, aljannu suka addabi jama'a mutane ɗai-ɗai ne basu da aljann... Gaba ɗaya Sheik ya jiƙe sharkaf da gumi, tsabar ruɗun da ya saukar masa a zuciyarsa, hatta jikinsa ya ɗan fara karkarwa amma bai bari Audu ya fahimci hakan ba, idanunsa duk sun faɗa tamkar wanda ya yi sati bai ci abinci ba, bakinsa ya haɗa kalmomi yana shirin faɗin wani abu sai ya tsinkayi maganar Audu yana faɗin
"Ni zan koma sai da safe"
Tsabar rowa da Sheik yake da ita sai dai ya ji duk da haka ba zai gayyaci kowa a taya shi kwana ba, musamman ma da ya san ya riga ya cewa Mai Gari shi kaɗai zai kwana ya riƙe ayoyin qur'ani.
Har Audu ya juya cikin haÉ—o jarumta ya ce
"Kuma baƙin da ake saukar da su a gidan fa?" Audu ya ce
"Basa yarda su kwana su kaɗai, sannan duk da haka suna faɗawa ƴan garinsu kaima ina ga abin da ya sa Mai Gari bai maka bayani ba saboda ya ga kai babban malami ne" Kai ya shiga gyaɗawa kamar ƙadangare, a haka Audu ya tafi ya bar Sheik, dakyar ya iya kara ƙofar kamar dai ya jinginata amma bai rufe ta da ƙarfi ta rufu ba, bare a yi maganar saka sakata.
Yana juyowa daga zauren idanunsa suka sauka a kan kewayen langa-langar da aka ce kabarin tsohon nan ne, ƙwiiiiwitttt wata tusa da bai shirya fitowarta ba ta ƙwace masa, tsabar tsoratar da ya yi amma dai zai yi iya yinsa ya ga bai kunyata kansa ba, wajen cikar burinsa na zama Malami a garin, tun da neman kuɗi ya fito dole ya jure.
Kwanukan ya ɗauka ya shige ɗaki ya rufo ƙofa, amma bai kulle ba, domin ya tsorata da furucin Audu na cewa akwai kabari a gidan, sannan akwai aljannu. Duk halin da yake ciki yana buɗe kwanon kaza sai ya manta komai, romo ya dangwala ya ɗanɗana wani ɗanɗanon farin maggi da na daddawa ya ziyarci harshensa, tuni ya tashi yana wata rawar larabawa yana juyi a tsakiyar ɗakin, gijif ya faɗa kan katifa a reran tsabar murna, ya tashi ya dawo gaban kwanon, ƙuri ya yi wa kazar yana ɗakkowa yana ɗorawa a kan marfin, tsaf ya irga sai ya ga babu cinyar kaza guda ɗaya, tsaki ya ja a ransa yana ayyana don maita sai da suka taɓa masa, amma dai zai sanar da su cewa su a ƙasar larabawa idan za a ba malami kaza kai da ƙafa kawai ake fitarwa amma ba a cire wani sassa ya faɗa saboda ƙarfin hali.
Tas ya cinye ya shanye wannan ruwan shayin mai uban yawa, dam ya ji cikinsa yana sakin gyatsa, ta window ya miƙo hannunsa ya wanke, da yake akwai ruwa a ɗakin.
Sai da ya gama danne-dannensa a waya, sannan ya cire hularsa da saje haɗe da gemu ya ajiye, rigarsa ya cire daga shi sai gajeran wando, kan nan sai sheƙi yake, magungun ƙwaya na bilicin ɗinsa ya sha, ya kwanta, ya yi ɗai-ɗai a kan katifa, a take ƙoshin da ya yi da kuma samun ɗaki mai iska ya sanya bacci ya yi awon gaba da shi, ko addu'a bai yi ba, shi ya sha'afa ma da maganar da Audu ya faɗa masa.
Yana cikin bacci ya fara mafarki da Æ´an garin a mafarkin suna cewa
"Sheik, wannan gidan... uhm... ka dai dinga karanta ayatul kursiyyu da suratul Jinn a kai -a kai. Saboda kowa ya san gidan…†Duk a mafarki ne amma sai da gabansa ya faɗi
Cike da ruÉ—ewa ya ce
" Mai gidan yake? Sheik ya tambaya yana jan carbi da azama.
"Dama... Uhmm... Komai lafiya ne. kawai gidan yana da...†Ba a faɗa masa mene ne a gidan ba ya farka daga nannauyan mafarkin, gabaɗaya ya haɗa gumi gabansa sai faɗuwa yake.
Lalume ya hau yi a jakar kayansa, ya É—akko wata rigarsa wacce ta fi jallabiyar da ya cire tsawo, zai saka amma sai ya kasa saawa kasancewar ta wuyan rigar yake Æ™oÆ™arin sakawa, ganin bashi da nutsuwar sakawa sai ya rataya ta a kafaÉ—a, ko sallaya bai shimfiÉ—a ba ya zauna a Æ™asa ya kalli gabas yana karanta “A'uzubillahiâ€Har sai da numfashinsa ya fara daidaita.
Yana cikin wannan halin sai ya ji ƙara daga ƙofar ɗaki "Gum, gum, gum!"
Sheik ya yi firgigit! Ya miƙe yana ƙoƙarin lalumo wayarsa sai kawai ya kara ta a kunne yana faɗin
"Wayyo Mai Gari a kawowa Sheik É—in yemen É—auki" Ya faÉ—a cikin raÉ—a, sai lokacin ma ya tuna bashi da number Mai Garin ashe.
Wata iska mai sanyi ta fara ɗaga labulan windown, sai ya hangi wani haske kamar walƙiya ya wulga, sai ya ji ana buga katako.
Sheik ya miƙa hannu ya ɗakko wani littafi da yake yashe a tsakiyar ɗakin, duk tunaninsa ba qur'ani ne saboda tsabar ruɗun da yake ciki, buɗewa ya yi yana karantawa, kawai yana girgiza kai yana cewa
“Wallahi ni dai ban taɓa ganin irin wannan ba a ce ba damina ba ana walƙiya Allah mun tuba" Ya faɗa yana ɓarkewa da kuka marar sauti, sai dai har yanzu bai ji yana da na sani a kan fitowa harkar maluntar bogi ta cutar mutane ba.
Yana a haka sai ya ji kamar ana tafiya, ma'ana ya fara jin taku a tsakar gidan, bai san lokacin da ya yi cilli da littafin hannunsa ba, shi da yake kallon gabas sai gashi ya juya zuwa yamma, bakinsa yana kaiwa da komowa, wannan karon, babu ƙalƙalar larabcin bogin nasa hausa ce sak yake yi babu lanƙasa, shi kansa bai san mai yake faɗa ba. Yana cikin wannan hali ya ji wani sauti ana cewa
"Sheeiiiik Ibra mun san kai ba malamin gaske bane na bogi ne, to ka sani muna sane da zuwanka wannan ƙauye" Shi da yake zaune ya kalli yamma, bai san ya tashi ba sai ganinsa ya yi a tsaye ya kalli kudu ƙafafunsa, suna barazanar kasa ɗaukansa, saboda karkarwar da suke, tunaninsa ɗaya wai aljannun ne suka san da haka ko kuma shi tsohon da aka binne ne ya yi fatalwa? Tun da gashi har sunansa na asali an kira shi da shi wato Ibra.
Wannan yasa Sheik ya buɗe ƙofar ɗaki da sassarfa, ya fito yana kwalalo ido kamar wanda ya yi fashi aka kama shi. Ya yi gigin barin gidan da sassarfa.
Cikin sanÉ—a ya fito daga É—akin daga shi sai gajeran wando, da rigarsa rataye a kafaÉ—a,
Yana fitowa ya ji gidan ya ruɗe da surutai kamar ana wani gagarumin taro, bai tsaya wata-wata ba ya durfafi hanyar ƙofar gida, sai lokacin ya tuna lokacin da ya ɗauki wayarsa ta kawo haske ya ga ƙarfe biyu da rabi na dare, amma da bala'in da ya fara fuskanta a gidan gwara ya fita. Cike da tsoro ya buɗe ƙofar gidan, shiruuu garin tamkar babu kowa sai carar zakaru da yake tashi da kukan dabobi lokaci zuwa lokaci.
Yana fitowa ya kalli, gabas da arewa ya ɗaga ƙafa zai fara sheƙa gudu ya tuna kansa babu hularsa ta gashin larabawa mai haɗe da saje da gemu, sannan ƙafarsa babu takalmi, uwa uba a tuɓe yake bashi da riga don bashi ma da nutsuwar saka rigar da take rataye a wuyan, amma dai ya san ba ƙaramin abin kunya bane ya tafi cikin gari a haka a zo a ganshi da kai a ƙwalƙwale, kai sunan zuwansa a haka mutuwa kusa don batu ne wannan na tonuwar asirinsa, yana a wannan halin na cewa ko ya koma ya yi shigarsa ta balarabe, in ya so ko gidan ne sai ya ce a sauya masa, duk da bashi da hujjar da zai faɗa a sauya masa tun da shi dai ba zai ce yana tsoron aljannu ba, a wannan yanayin ne ya ji an ce
"Sheik, baby nah ina jiranka mu je mu kwanta" Idanu ya zaro yana mai juyawa inda ya ji sautin wato ƙofar gidan da ya fito, wata budurwa ce tsaleliya riƙe da fitila mai haske, tana sanye da sari na indiyawa"
Ga birni ga ƙauye, shi dai ba zai koma gida ba tun da ya san dai budurwar nan aljana ce, sannan ba zai je cikin gari a haka ya bugawa mutane gida ba, tun da gidan kusan shi ne na ƙarshe a inda yake, ganin ta doso inda yake sai fitsari ya suɓuce masa, ya fara sakin wata tusa mai ƙara a kai- a kai...
MAMAN AFRAH
09025576222
[6/28, 6:21 PM] Mom mashkr & Afrah: https://chat.whatsapp.com/EBurrU2vz6OFGbE37xLhPS
👳ðŸ»â€â™‚ï¸ *MALAMIN BOGI*👳ðŸ»â€â™‚ï¸
NA
MAMAN AFRAH
First Class Writer's Asso.ðŸ“
Daga marubuciyar:
Ƙazamin miji
Bonono Rufin ƙofa...
Ruɓaɓɓiyar igiya
Ƴar zaman wanka
Ƙara'in inna delu
Beelal
Ƴan adaidaita sahu
Ungozoma
Jalli joga
Da sauran su.
*09025576222*
BOOK1ï¸âƒ£
PAGE 3
*ƘAUYEN MAI MANGWARO*