← Book details Malamin Bogi Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 2 OF 35

Sashe 2

Malamin Bogi Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

Kamar ya yi kuka haka ya amsa da ceww za a yi bakin ƙoƙari don ganin an ciyar da Sheik ɗin da abincin da ya saba ci, duk da yanzu ya musu bayanin cewa ya yi wata guda a wani gari yana koyan harshen hausa dakyar ya samu ya ɗan iya, a can garin ne ma ya ji labarin halin da garin Ƙundun yake ciki shi ne ya zo.

Sheik ya ga ikon Allah, Mai Gari duk ya rikice saboda tunanin ciyar da wannan baƙo, dan dai babu yadda zai yi tun da yanzu yana yin wani furuci mutanen gari za su ji babu daɗi tun da suna ganin waraka ta zo.

Haka mutane suka yi ta tittiɗowa daga gidajensu suna fitowa tamkar wanda ake rabon buhhunan shinkafa, aka kewaye fadar Mai Gari maza da mata da yara, ana ta kallon baƙon balarabe.

Sai daf da magriba, Mai Gari ya umarci jama'a da su tafi, haka suka tafi shi kuma ya sa aka ɗauki jakunkunan Malam, Mai Gari da kansa ya taso ya kama hannun Malam domin bai taɓa riƙe ko da rigar balarabe ba, bare kuma hannunsa.

Wani irin laushi ya ji hannun Sheik, tunaninsa tsabar zaman ƙasar larabawa ne da rashin aikin wahala, bai san cewa tsabagen shafa mayukan bilicin ne da Sheik ya yi ba da mayuka masu sanya laushin fata duk don cim ma manufarsa ta zama MALAMIN BOGI.

Suna tafiya wasu ƙamshin turaruka suna tashi daga jikin Sheik, wanda wannan ƙamshi shi ne yake ƙara tabbatarwa da Mai Gari cewa yana tare da balarabe ɗan larabawa.

Suna gaba masu ɗauke da jaka suna biye da su, gidan saukar baƙin Mai Gari suka nufa, gida ne na jar ƙasa aka shafe da siminti, ɗakuna uku ne gidan a share ƙal, kasancewar ba a daɗe da wasu baƙi suka zauna a gidan ba.

Ledar tsakar É—aki ce shimfiÉ—e a É—akon, sai katifa mai tudu, nan ne É—akin da Sheik zai sauka.

Mai Gari ya kalli Sheik ya ce

"Ya Sheik wannan É—akin ne za ka sauka a ciki" Sheik da ya ga É—akin a ransa ya ji daÉ—i, amma a fili sai ya ce

"Wannan ɗakin babu shara!" Haka Mai Gari ya sa samarin da suka ruƙo jakunkunan Sheik suka share tas aka goge, sannan Sheik ya shiga yana faɗin

"Alhamdulillah, ma sha Allah" Yake faɗa cikin muryar lanƙwasar harshen larabci.

Bayan su Mai Gari sun tafi don Mai Gari ya ce zai kawo mutane biyu da za su zauna a sauran ɗakunan biyu suke taya Sheik zama, amma saboda ƙarfin hali ɓarawo da sallama ya ce kar a kawo komai ya riƙe ayar Allah ba ya jin tsoron komai.

Ɗakin ya rufe ya garƙama mukulli tamkar dai marar gaskiya duk da dama marar gaskiyar ne wanda ko a ruwa sai ya yi gumi. Hular gashin nan nan ya cire kasancewar zafi yake ji, kansa da babu ɗigon ko gashi ya bayyana wanda yake ƙwalƙwal, hatta fuskar babu wani gashin saje da gemu duk ya ɗaye.

Jakar kayansa ya buɗe gabaɗaya kayan jallabiyoyi da turaruka masu ƙamshi ne da hulana carbuna, da sauran su, wani zip ya buɗe a cikin jakar kuɗi ya fito da shi ƴan dubu dubu rafa uku, wani murmushi ya saki a fili cikin yin ƙasa da murya da hausa raɗau ya shiga faɗin

"Allah sarki Lami uwar ƴan jaraba ana can ana baloƙoƙo ko ya suka ƙare da mai zubin adashe" Ya faɗa yana tuno cewa matarsa uwar gidan ita ce ta shiga adashe ɗauka dubu ɗari biyu sai da ɗaukanta ya zo mai adashe take mata hanya-hanya Lami da ta gaji ta je gidan mai adashe ranar bata nan ta tafi wani ƙauye sai kishiyarta a gidan, tana ganin Lami ta since saniyar mai zubin adashe, tana fitowa riƙe da igiya bata zame ko ina ba sai wajen mijinta Ibra dama cin kasuwa zai tafi haka ta damƙa masa saniyar ta ce ya kai kasuwa ya karɓo kuɗin ta ɗauki dubu ɗari biyun ta, ta ba mai zubin adashe sauran kuɗin ko mai za a yi sai dai a yi ko ta mutu ko ta yi rai bata tsoro. Ibra ya karɓi saniya bayan ya je ya siyar daga kasuwar ma bai hau motar garin Mai mangoro ba, wato can garinsu, sai ya hau wata motar da bai san garin da ,a ta je ba, wannan ne silar barowarsa gida, da kuɗin ya sayi komai da komai na kayan larabawan da kayan magungunan ƙaryar da ya zo da su.

KuÉ—in ya mayar yana Æ´ar dariya, yana cewa sai ya zama maloniya a harkar maluntar bogin nan, yadda zai wuce raini idan ya koma ya biya kuÉ—in saniyar don yana ganin lokacin ko jirgin sama zai iya saya a yadda ya tsara in komai ya tafi daidai kenan, in ba a samu mushkila ba.

Mayukan bilicin ɗinsa wanda su ne taimakon farar fatarsa, da ƙwayoyi da yake saya na bilicin har allura ake masa ta sanya fari, duk don ya yi ɓadda kama a cikin fatarsa ta asali.

Yanan nan zaune har aka kira sallar magriba, bai ankara ba sai ya ji ana ƙoƙarin turo ƙofa, a kiɗime ya lanƙwasa muryarsa zuwa maganarsa da hausa bata gama kama bakinsa ba ya ce

"Waye?" Mai Gari da suke tare da limamin garin ya ce

"Ya Sheik buɗe mana mun zo mu tafi da kai, za a yi jam'in sallar magriba" Hannu Sheik ya kai ya taɓo tsakiyae kansa da yake salle babu gashi, ya mayar da kallonsa kan hular gashinsa mai haɗe da gemo da saje tana yashe a ƙasa, ba na wannan ba, magungunan bilicin ɗinsa da ya fito da su ya yi ɗai-ɗai da su.

Jin suna ƙara turo ƙofar da ƙoƙarin buɗewa ya mie tsaye babu shiri yana muzurai, a zuciyarsa yana faɗin

'Allah kar ka bari asirina ya tonu ban cika burina ba, wayyo Allah, yau na san matsawar suka gane waye ni ba lallai in fita daga garin nan da ƙafafu ba' Ya faɗa jikinsa yana karkarwa duk ya ruɗe...

Yanzu za a fara don ba zan ce an fara ba, yanzu ne za mu fara ƙoƙarin buɗe labarin ma don ko wuri bamu ɗauka ba, kar ku shagala kuna tare da MAMAN AFRAH wacce alƙalaminta ba ya rubuta shirme na san za ku so labarin nan🥰

*MAMAN AFRAH*
*09025576222*
[6/26, 5:17 PM] Mom mashkr & Afrah: https://chat.whatsapp.com/EBurrU2vz6OFGbE37xLhPS

👳🏻‍♂️ *MALAMIN BOGI*👳🏻‍♂️

NA

MAMAN AFRAH

First Class Writer's Asso.📝

Daga marubuciyar:

Ƙazamin miji
Bonono Rufin ƙofa...
Ruɓaɓɓiyar igiya
Ƴar zaman wanka
Ƙara'in inna delu
Beelal
Ƴan adaidaita sahu
Ungozoma
Jalli joga

Da sauran su.
*09025576222*

BOOK1️⃣

PAGE 2

Cikin muryarsa tabakin balarabe da husa bata gama zama a ciki ba ya fara cewa

"Afwan, afwan, afwan ya Mai Gari a bani minti biyu ina cikin yin wani aiki ne kuka iso" Ya faɗa yana ambatar hailala da ɗan ɗaga murya yadda za su ji sauti. Mai Gari da liman juna suka kalla, suna jin daɗin furucinsa don sautin hailalar sa yake ya musu nuni da cewa wataƙila yana cikin yin wani aiki ne ko addu,a irin tasu ta manyan malaman larabawa.

Malamin bogi kuwa bai yi ƙasa gwiwa ba ya shiga saurin saita kansa, ta hanyar ɗaukan dukan kayan da ya cire a fuskarsa ya mayar, sai da ya saisaita nutsuwarsa sannan ya ɗakko dogon carbinsa hularsa riƙe a hanunsa ɗayan. Har da gyarawa jakankunansa wuri don in ba don an ce sallah za a je ba, to babu mai raba shi da jakar kuɗin nan saboda jin kuɗin yake kamar ransa.

Yana buɗe ƙofar ya fito ƙamshin turarensa yana yi wa su Mai Gari sallama, ganinsu ya yi tsaye a gefe suna ta kallonsa kamar sun ga sabon halitta, shi Liman kawai kanannaɗaɗɗan gashin Sheik yake kallo, ji yake ina ma gashin nan lallausa ya dawo kansa, da ya ji daɗi.

Ƙofar ya jawo ya kulle ya cire mukullin ya saka a aljihu yana mai cewa

"Assalamu alaikum, marhababikum" Ya faɗa yana ɗaga hularsa mai rubutun larabci daga gaban da aka yi da wani golding, shi kansa da za a daɓa masa wuƙa bai san mai aka rubuta a jikin hular ba. Yana ɗora ta a kan hular gashinsa da yake basaja a matsayin gashin sa, sai ya shiga mismis da baki alamar azkar yake. Su kuma amsa masa sallamar suka yi suna washe baki, sun san dai ya musu sallama marhababikum ɗin kuma basu san ma'anarta ba, sai dai sun san ko a hausa ana cewa mutum marhabin, wato dai sai suka saka hakan a matsayin duk barka da zuwa yake musu.

Mai Gari ne ya ce

"Dama sallah za a gabatar muka zo takanas mu tafi da kai" Sheik ya ce

"Laisal mushkila" Kallon kallo aka shiga yi da Mai Gari da Liman, duk da basu san mai ya ce ba sai suka washe haƙora suna haɗa baki wajen cewa

"Ai dama shi ya sa ba a gabatar da sallar ba sai an kirawo ka" Murmushin jin daɗi Sheik ya yi don ya fahimci ba ƙaramin ƙasurgumin garin jahilai bane ya dira, kuma ya ji daɗin hakan, domin hakan yana masa nuni da cewa zai ke cin karensa babu babbaka, saboda dole tun da basu san komai a larabci ba wataran kwaɓawa ma kawai zai ke yi, saboda ya samawa kansa kima a wajensu.

A fili kuma sai ya ce

"Za mu iya tafiya" Turus suka yi don sai suka ji ba za su iya shiga gabansa ba sai dai yake tafiya suna take masa baya, saboda su ba ƙaramin daɗin bayyanarsa a garin nan nasu suke ji ba domin garin Ƙundu yana buƙatar hawa jirgin annabi Nuhu ma'ana suna buƙatar ceto da taimako.

Sheik ya ce
Chapter 2 · 0% Book details