Sashe 11
Malamin Bogi Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read
"Ai dama É—an kuka shi yake jawa uwarsa jifa, nima dai kayan marayu ne, don Inna ko kan ki za ki kai kasuwa a yi cinikin ki masu yankan kai su saye ki yasin sai kin siyar kin biyani kuÉ—in saniya" Da wani kuka mai jiniya Inna ta fashe jin ana batun ta sayarwa Æ´an yankan kai kanta ta biya kuÉ—in saniya, Mai Gari ne a fusace ya ce
"Wai shin ni zan yi hukunci ko kuwa ku za ku yi, idan har ku za ku yi babu amfanin zuwanku, kuma nima babu amfanin zumana a wajen nan" Mutanen fadar Mai Gari suka haÉ—a baki wajen faÉ—in
"Wannan gaskiya ne ranka ya daɗe, Allah ja zamaninka mai gudumar dukan talauci" Wani zama ya gyara yana gyara babbar rigarsa, don maganar da ya yi ba iya su Inna ya katsewa hanzari be har da Lami da ta ƙunso nata maganganun amma sai ta ja bakinta ta ƙunshe.
Mai Gari ne ya shiga faÉ—in
"Tasallah yanzu magana tana hannunki amma dai kafin nan sai na fara da Jummai, ke Jummai me ya sa kika cinyewa Lami kuɗi har dubu ɗari biyu?" Ƙeya Jummai ta sosa irin ta mararsa gaskiya sai ta ce
"Tsautsayi zagin mahaifi" Wani kallo ya mata ya ce
"To in har cinye kuÉ—inta tsautsayu ne to ke É—in ma É—aukan saniyarki tsautsayi ne" ÆŠagowa ta yi tana kallonsa da sakakken baki, sai kuma ta kalli Lami da take aika mata harara kamar idanunta za su faÉ—o.
Bai jira cewarta ba ya ce
"Kowa a cikin ku yana da laifi, ke Lami bai kamata ki taka har gidan Jummai ki since saniya a turke, ki ba mijinki ya kai kasuwa ba, mene ne amfanina a wannan garin, da kin kawo ƙaranta ai da na san abin yi" Kai Lami ta sunkuyar tana jin haushin Mai Gari ganin zai ɗora mata jakar tsaba kaji su bita.
Bai ba kowa damar magana ba ya ce
"Yanzu Tasallah kina da kuÉ—in da za ki biya wanann cakwakiya?" Inna kamar jira take ta sakin wani kuka mai É—an sauti tana jin ciwo kayan miyarta da za ta bayar ta ce
"Ya na iya da abin da ya fi ƙarfina, ai dama faɗan da ya fi ƙarfinka wasa kake mayar da shi, ni nan bani da komai amma ga kayan miyar nan da wannan naira ɗarin da na yi ciniki, su kaɗai ne na mallaka, ta karɓi jingina har zuwa ranar da Ibra zai bayyana, idan ya bata kuɗin saniyarta sai ta bani kayan miyata, amma da sharaɗi ko kalwata ko kuka suka yi ciwon kai ba zan yarda ba yadda zan bata kayan miyar nan salin alin ta ajiye kar ta sake ta taɓa" Ta faɗa tana ɗaga robar ta juye kayan miyar a kan tabarma a gaban Mai Gari.
Tsabar takaici Jummai bata yi magana ba, Æ´an fadar ne suka shiga danne dariyarsu, Mai Gari cike da takaici ya ce
"Haba Tasallah a gabana kike mayar da babbar magana ƙarama, ana batun saniya kina batun kalwa da kuka da barkono?" Ɗan karkata kai Inna ta yi ta ce
"To ai kowa da abin hannunsa yake ado, guntun gatarinka ya fi sari ka bani, ita saniya gare ta ni kuma kayan miya ne Allah ya bani"
Mai Gari bai sake bi ta kan Inna ba, ya shimfiɗa sharaɗin za a jira daga nan zuwa kwana uku, a ga ta inda Ibra zai dawo, in ya so sai a san abin yi. Haka ya kashe rigimar ba don ta mutu ba, ya ce idan Ibra ya dawo da saniya ko kuɗin saniya sai Jummai ta karɓi kayanta, sannan ta biya Lami kuɗinta.
Inna wani irin washe baki ta yi, tamkar ba ita ce wacce take wannan kukan ba, dama kukan takaicin za a raba ta da kayan miyarta ne. Haka ta kwashe ta saka a robar tana jerawa Mia Gari godiya, ta tafi gida a ranta tana Allah wadai da halin Ibra mutum kusan shekara arba'in amma bai san abin da ya kamata ba sai tunani irin na yara.
Lami da Jummau kowa a ƙufule da ɗan uwansa ya bar fadar Mai Gari.
Lami tana komawa gida ta samu kishiyarta Sa'a a tsakar gida tana riƙe da ƙugu, shigowar Lami ko zaunawa bata yi ba Sa'a ta ce
"Sannu Lami wato ke kin iya ɗauki ɗam baki ajoye ba ko? A kan me za ki ɗaukar mini gayan tuwo?" Lami wacce take cike da ɓacin ran rashin dubu ɗari biyun ta, da kuma yaudarar da Ibra ya mata a tsawa ce ta ce
"Sa'a hawainiyarki ta kiyayi rama ta, saboda rainin wayo ni da nake da dubu É—ari biyu kuÉ—in adashe uban me zan yi da gayan tuwo, to Allah tsari gatari da saran shuka"
Sa'a hannuwa ta tafa ta ce
"Da ba a san asalin barbela ba sai ta ce daga madina take, kuÉ—in adashen da ko naira biyar bata zo hannunki ba, kika É—auki saniyar mutane kika ba wanann marar imanin ya tafi to ai kin yi saki na dafe.
Sa'a ta ci gaba da cewa
"Shi ne za ki ɗauke mini gayan tuwona ki fice da shi, na san a gyalenki kika duƙunƙu ne tuwon kika je maƙota kika yi kwaɗo da mai da yaji kika cinye" Galala Lami take kallonta sai dai takaicin da yake cikin ranta ya fi wannan wanda Sa'a take takalarta faɗa da shi don ta san ita da Sa'a basa jituwo ko kaɗan, haka ta tashi ta shige ɗakinta tana jinta tana jera mata Allah ya isa amma bata ji za ta iya biya ta su yi ba, don ita a halin da take ciki ko yunwa bata ji bare har ta saci gayan tuwo ta san kawai neman masifa ne irin na Sa'a.
*WASHE GARI*
Sa'a ce a tsakar gida tana shanya kayan wanki, Lami tana bakin ƙofar ɗakinta tana zaune ta kifa uban tagumi, bata da buri illa ta ga Ibra ya dawo da kuɗin wannan ko saniya amma shiru malam ya ci shirwa.
Wata uwar sallama ake rafkawa a zauren gidan, da murya wacce hausa bata gama ratsa ta ba, alamar yare ne yake maganar. Wani takaici ne ya turnuƙe Lami ta taso rai a ɓace ta zo bakin zauren ta tsaya ta ce
"Tunde sai aka yi yaya kuma? Ya za ka zo da safen nan ka ishi mutane da rafka sallama" (Tunde inyamuri ne da ya zo daga Lagos yana zaune a garin Mai Mangwaro yana da gidansa da matarsa ɗaya da ɗansa, sai kuma shagonsa da yake a ƙofar gidansa nasa).
Kallon Lami ya yi ya ce
"Ba wajenki na zo ba wajen mijinki na zo" Ya faɗa cikin hausar sa da bata gama kama bakinsa ba. Ambaton mijinta da ya yi ya ƙara sosa mata mikin takaicin Ibra da ta kwana da shi, cikin takaici ta ce
"Baya nan ya ɓata, hijira ya yi da saniyar mutane ba a san duniyar da yake ba" Idanu ya zaro ya saka hannu a lajihu ya fito da takarda wacce rubutu ne rututu a jiki ya ce
"In na yarda shegiya nake, kalli basukan da mijinki ya ci" Ya faɗa yana nuna mata takardar. Kallon sheƙeƙe ta wa takardar ta ce
"To ai ka yi ta banzar ni da ba boko na yi ba ina zan san me aka rubuta" Yana zaro idanu ya ce
"Idan ma ɓoye mijinki kika yi ki fito da shi, don yau ba zan bar nan ba sai da kuɗina, shinkafa kwano uku wake rabin kwano, sabulun bilicin da ya sha karɓa, da mayukan bilin har allurai da nake masa na sanya fari bai biya ni ba wallahi ko a ni ko a shi jiya ya ce zai dawo daga kasuwa ya biyani yanzu ki ce wai ya yi hijira"
*SHEIK*
Kukan zuci ya shiga yi wanda ya fi na fili ciwo, ya san tabbas yau watan tonuwar asirinsa ne ya kama in ba haka ba hular da ita ce kaɗai rufin asirinsa kuma ita ce take fito da asalin kamarsa da larabawa a ce babu ita. Shiru ya yi yana nazarin yadda zai kuɓuta amma iya tunaninsa bai tuno komai ba, don babu mafita, kansa gabaɗaya ya kulle. Ga abin da ya fi ɗaga masa hankali ma shi ne yadda samarin sukemta azalzalarsa a kan ya fito ana jiransa.
Cikin É—aga murya ya ce
"Afwan ya shabbab, gani nan ina zuwa, ina yin shirin ko ta kwana ne, saboda aljannu dubu saba'in ne a kan matar nan mai farfaɗiya" Ya faɗa yana ta safa da marwa a ɗakin ya haɗa uban gumi yana ganin yau dai ƙarya nema take ta ƙarewa ɗan kada, saboda ya lura yana cikin tsaka mai wuya.
Kamar zai yi kuka a hankali ya ce
"Allah ka taimake ni, Allah kar ka bari in kunyata" Ya faÉ—a yana ciccira ido a É—akin, fani yake kamar zai ga hular amma babu niyya wai ango ya kwana da wando.
Wata dabara ce ta faÉ—o masa ya buÉ—e baki ya ce
"Gabaɗaya ku fita daga gidan nan, gani nan fitowa saboda maganin aljannun da zan fito da shi yana da ƙarfi, wataƙika idan na fito guguwa ta taso ta haɗe gidan da ƙura... Tun bai kai ƙarshen maganar ba, samarin nan kowa ya yj ta kansa, sai lokacin ya ɗan ji sawaba, kamar ƙiftawar ido da fitar su Sheik ya fara ganin labulen windown ya fara kaɗawa da ƙarfi kamar dai ana iska mai ƙarfi ne,
Idanu ya zaro cikin taku biyu ya koma jikin bango ta raɓe, bakinsa yana karkarwa ya fara addu'a, kawai sai ganin hular gashin nasa ya yi tana reto a saman ɗakin, kai ya ɗaga yana ta kallonta, a ransa yana jin daɗi da ya ganta sai dai ba a nan gizo yake saƙar ba yanzu tunaninsa ɗaya ya za a yi ta zo hannunsa. Bai ankara ba ya ga an wurgo dogom gemun jikin fuskarsa sai kuma sauran sajen da hular gashin suka ɓace, kamar zai yi kuka ya hau faɗin