Sashe 18
Malamin Bogi Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read
"Baby mene ne" Ta faÉ—a lokacin da ta mayar da kallonta kan Sulaiman É—in.
Haushi ne ya kama zuciyar Ma'aruf jin Rahma ta kira Sulaiman da wanann sunan, sunan da ko a mafarki zai ji daɗi ta kira shi da shi, shi ya rasa ma yaushe ya kamu da son Rahma abin nan yana ci masa tuwo a ƙwarya ya san dai ko a tsarinsa babu mace irin Rahma, wacce bata san darajar ɗan adam ba amma gashi so yana neman ya kai shi ya baro.
Idanu Sulaiman ya ɗauke jin Ma'aruf yana masa kwarjini, shi dama ya tsani ya zo gidan su Rahma ya ga wannan baƙauyen da bashi da komai sai gidadanci da rashinw wuyewa. Ma'aruf kuwa ji ya yi da a ce yana da dama da ya je ya kora Rahma cikin gida, sai dai bashi da iko da wannan damar.
Sulaiman ne ya yi ƙasa da murya ya ce
"Baby ki sa wannan baƙauyen yayan naki ya kawo min ruwa" Ta kalli Sulaiman cike da jimanta abin da ya ce ta ce
"Ruwa kake so sha bari na kira Mummy ta sanya Æ´ar aiki ta kawo" Yana É—an haÉ—e rai ya ce
"Ni ba na son wata Æ´ar aiki wannan nake son ya kawo mini" Murmushi ta saki cike da kulawa ta ce
"Kar ka damu ai yanzu kuwa" Ma'aruf da ya nufi get zai fita so yake ya je masallaci ya karanta qur'ani ko ya samu sauƙi da salama a zuciyarsa, jin ƙaran wayarsa da take aljihu ya fito da ita, ganin sunan Rahma abin ya bashi mamaki har sai da ya tsaya ya juyo don ya tabbatar da cewa ita ɗin ce take kiransa, don ya san saboda wulakanci irin nata kwanaki cewa ta yi ta goge numbersa saboda bata son take jin maganar baƙauye a kunnenta.
Juyawar da ya yi sai ya ga ita ɗin na wajen take kallo, kamar wasa sai ya ga tana ɗaga masa hannu alamar ya zo, bao je ɗin ba kuma bai cigaba da tafiya ba don ya san wannan kiran akwai wani abu a ƙasa kuma shi bashi da wata daraja da zai rama ko ma mai suka masa, saboda tana faɗawa Daddy shikenan ko kuma Mummy wacce a dole son babu yadda za ta yi ne yake zaune a gidan.
Yana mayar da idanunsa kan wayar hakan ya yi daidai da tsinkewar kiran, yana katsewa ya ga wani kira ya shigo, juyawa ya yi yana tafiya ya É—aga wayar ya kara a kunne yana lumshe ido, a hakan yake tafiya kasancewar gidan babban gida ne, akwai tazara daga harabar gidan zuwa get É—in.
Yana karawa a kunne sai ji ya yi ta ce
"Na ce ba" Ta daÉ—a cike da iko da raini.
Cikin nutsuwa ya ce
"Ina jinki"
Ta ce
"Ka dawo ka ɗakkowa Sulaiman ruwa zai sha" Ransa ne kawai ya yi mugun ɓaci kasanceqar ya san al'adar Rahma ce ta tsani a kashe mata waya sai kawai ya kashe domin ita ma ya ƙunsa mata ɓacin ran da ta sa ya shaƙa.
Yana kashewa ya cigaba da tafiya har ya buÉ—e get É—in ya fita waje.
Rahma ranta ne ya ɓaci kamar yadda ya yi zato, cike da jin kunya ta ce
"Ya ce sauri yake zai je wajen suturar abokinsa da ya mutu" Ta tsinci kanta da sheƙa ƙarya.
Sulaiman banza ta mata ko da ta ce za ta ɗakko masa da kanta sai ya ce ta bari ma ya daina jin ƙishin. Haka dai ranar hirar tasu ta wakana babu wani armashi. Da zai tafi ya shiga mota ya ɗakko rafar ƴan ɗari biyar guda biyu ya bata wai ta sha ice cream. Motar ya shiga direbansa da yake ciki zaune yana jiransa ya tada motar, tana tsaye tana ɗaga masa hannu, har mai gadi ya wangale musu get suka fita tare da haurawa titi.
Tana komawa ciki ta kwashe abin da Ma'aruf ya mata ta faÉ—awz Mummy inda ta ringa faÉ—a ta inda take ahiga ba ta nan take fita ba, tana faÉ—in zai dawo ya same ta, tun da ba ubansa Mai Gari bane ya gina gidan, da har yana zaune ba za a amfane shi ba.
Daddy sai bayan magriba ya dawo gidan, ko da aka zo cin abinci Mummy ta kwashe komai ta faɗa masa na tsinka Rahma da Ma'aruf ɗin ya yi a gaban saurayinta, duk da Daddy ya san abin da Rahmar ta yi bata kyauta ba sai dai ba zai iya tsawatar mata ba saboda soyayya da kuma Hajiya ya san ba za ta bari a ga laifin ƴarta ba kasancewar ƴar tata ƴar ido ce. Ma'aruf dama sai dai ya ci abincinsa da ban saboda Hajiya da Rahma wai basa iya cin abincin idan yana waje zuciyarsu tana tashi, wai suna jin yana warin ƙauye, kuma kawai tsabar rainin wayo ne.
Sai da aka yi ishasha'i ya dawo don karatu suke tsakanin magriba da isha'i a masallaci, Daddy ne ya kira shi yana masa faÉ—an rashin gaskiya, Ma'aruf ya ce
"Haba Daddy ni ne fa gaba da Rahma amma sai ta aike ni kuma a gaban saurayinta, kuma ma saurayin fa zan É—akkowa ruwa, duk Æ´an aikin gidan nan, yanzu fa ko Yayan da ka ce take faÉ—a min ta daina Ma'aruf take kir...
Daddy ne ya katse shi da cewa
"Haba kai kuwa ana ga yaƙi kana ga ƙura, ana maganar baka je aike ba kai kana maganar bata ce maka Yaya.
Hajiya ce ta katse da cewa
"An ƙi a ce maka Yayan ubanta ne kai da sai ta girmamaka" Kai ya sunkuyar don ya san Daddy kawai yana tsoron Hajiya ne amma ai ya san shi ne da gaskia, haka ya masa faɗan ya tashi ya fita ya koma ɓangarensa.
*BAYAN SATI UKU*
Zaune take a lambu ta ɗora ƙafa ɗaya a kan ɗaya tana zaune ne bisa kujerar roba sai ta ɗora ƙafafunta a kan wata kujerar, jarida take dubawa sai kayan maƙulashe a kan plate a gabanta tana ci.
Tun da fa shigo lambun yake kallonta da yake idanunta a kan jaridar bata san da tahowarsa ba ma, sanye yake da riga blue mai ƙaramin hannu sai jeans baƙi sai ƙamshin turare yake mai daɗi.
Rahma da ta jiyo ƙamshin iska ta kawo mata ta lumshe idanu, don ƙamshin turaren ya mata, kasancewae sabo ne ya saya ƙamshinsa ya sha bamban da wanda yake shafawa. Sai da ya zo dab da ita ta ji ƙamshin ya ƙaru alamar ma ƙamshin ba iska ce take kawowa ba mai ƙamshin yana dab da ita. Murmushi ta saki, saboda ta san sun yj waya da Sulaiman ya ce zai zo su fita su shaƙata kuma ta faɗa masa tana zaune a lambu, a tunaninta shi ne ya zo zai tsokane ta take son ya rufe mata ido ko dai wani abu makamanci haka.
Cike da shauƙi ta ce
"Barka da zuwa Babynah" Gaban Ma'aruf ne ya faɗi yana tunanin ko dai addu'ar da ya kwana yana yi a kan Allah ɗora shi a kanta ta amince da shi, ita ce ta karɓu.
Ta cigaba da cewa
"Ƙamshin turarenka ne ya sanar da ni ƙarasowarka, zuciyata tana maka marhabin, tana maka tuni cewa da kai kaɗai za ta rayu!" Kaɗan ne numfashin sa bai bar gangar jikinsa ba, tsabar irin yadda maganar ta dake shi, a hankali ya fara taku a dawo gabanta, sai lokacin ta ɗago fuskarta daga kallon jaridar tana murmushi mai ƙara mata kyau da kwarjini.
A kan kyakkyawar ƙafarsa da take cikin baƙin takalmu ta fara yi wa idanunta masauki, ko a mafarki bata taɓa zaton Ma'aruf bane, cikin murya mai taushi, wacce take damfare da nutsuwa ya hau faɗin
"A nawa ɓangaren ma haka ne, da ke kaɗai za ta rayu, kuma zuciyarta ta janyo linzamina ne zuwa wannan wajen, don ta bayyana miki asirin da yake cikinta, tana fata da addu'ar mu rayu a tare har mutuwa...
Waɗannan kalaman sun sauka a kan dodon kunnen Sulaiman da ya nufo wajen, wanda kuma ya ƙara shiga kunnuwan Mummy da ta zo za ta sanar da Rahma cewa za ta fita, saboda ta kira wayar ta ta ji bata shiga ba, shi ne ta tasho don ta faɗa mata sai kuma kunnuwanta suka yi arba da wannan babbar maganar...
*INNA TASALLAH*
Zaune take a tsakar gida da yammacin ranar asabar, tana zaune hannunta riƙe da mangwaro irin mai ƙamshin gawasa, nunanne ne jawur da shi, tana sha tana lunshe ido har wani karkaɗa kai take saboda zaƙin da take ji har tsakar kanta.
Tana a wannan halin Lami ta shigo da sallama, idanu Inna ta buÉ—e ganin Lami afujajan ta dakata da shan mangwaron ta ce
"Lami lafiya kamar an hakaɗo ki?" Lami cike da jin haushin Inna tana wani ɓata rai ta ce
"Wato ke Inna har kin samu damar sha mangwaro har kina lumshe ido" Galala Inna take kallonta cike da takaici ta ce
"Haba Lami wai ni ku mutane mai ya sa bakwa son ku ga wasu sun ci gaba? Da raina da lafiyata ma ba zan sakata in wala na sai ana sanya min ido, yanzu kayan miyana sun ƙare duka don cikin ribar na ɗauki naira talatin na saya mangwaro in sha a ruwan raina shi ma sai ya zama ana mini baƙinciki, mutane bakwa so ku ga mutum duniya tana gara masa, wato kun fi so ake zaman kashe wando...
Wata harara Lami ta aikawa Inna ta ce
"Inna tsakani da Allah ko ana yi wa wani baƙinciki wa zai miki, ni wallahi a sana'ar kalwa da barkono da kuka ban ga abin baƙinciki ba" Kamar Lami ta yi saɓo haka Inna ta zaro ido ta ce
"Kina wasa da maƙiyi, maƙiyi ai shi ko alawa kake siyarwa sai ya maka baƙinciki, yanzu ni a wajena ai cigaba na samu tun da gashi a cikin ribar har ina shan mangwaro" Ta faɗa tana gutsuro fatar mangwaro,
Lami a zuciyarta ta ce
'Yanzu zan rikita miki lissafi, yanzu za ki kiÉ—ime don na tabbatar baki san da abin da nake tafe' A fili kuma sai ta ce
"Inna saƙon kira ne aka bani wajenki" Sai da ta suɗi mangwaron ta ce